Free chapter · Read without an account

THE SWEETEST DAYS

by Jiddaah Barkum · KADDARAR ZUCIYA

KADDARAR ZUCIYA

CHAPTER THIRTY-SIX: 36

THE SWEETEST DAYS

JIDDAAH BARKUM

——-

Wasu lokuta… Allah kan dawo wa zuciya da farin ciki ta hanyar da mutum bai taɓa tsammani ba, kuma wasu lokuta, mutum kan tsinci kansa yana murmushi saboda sunan wani kaɗai, tun bayan zuwan Aliyu gidan Alhaji Kabeeru da kuma amincewar Daddy, rayuwar Inteesar ta fara ɗaukar wani sabon salo, ba wai saboda ta manta da Ahmad ba, a’a, Ahmad ya kasance wani sashe na rayuwarta da ba za ta taɓa mantawa da shi ba, amma a hankali… Aliyu yana koya mata yadda ake sake rayuwa, yadda ake sake dariya, yadda ake sake jin daɗin farkawa da safe, da kuma yadda sunan mutum guda zai iya sa zuciya yin wani irin daɗaɗɗen bugawa.

Mommy Haleema ce ta fara lura da sauyin, tun da safe, Inteesar ce ta fara shiga kitchen, ba kamar kwanakin baya ba, lokacin da sai an yi ta lallashinta kafin ta fito, yau kuwa, da kanta ta shigo, sanye take da wata doguwar riga mai launin peach, fuskarta babu kwalliya mai yawa, amma annurin da ke fuskarta ya isa ya kawata ta, “Assalamu alaikum, Mommy,” Mommy Haleema ta juyo, “Wa alaikumus salam…” Sai ta tsaya tana kallonta, Inteesar na murmushi, murmushin da ya daɗe bai bayyana a fuskarta ba, Mommy Haleema ta kasa hana kanta murmushi, ta ƙaraso kusa da ita, “Alhamdulillah,” Inteesar ta yi dariya, “Mommy, me kuma?” “Babu komai,” ta shafa kuncinta a hankali, “Kawai ina godiya ga Allah,” Inteesar ta rungume ta ta baya tana dariya, “Mommy…” “Uhmm?” “Ina sonki,” Mommy Haleema ta yi dariya, “Ni ma ina sonki,” daga ƙofar kitchen, Daddy da ya fito a hankali yana dogaro da sandarsa ya tsaya, yana kallonsu, wani irin sanyi ya ziyarci zuciyarsa, ya daɗe rabon da ya ga yarinyarsa tana dariya haka, “Princess ɗina ta dawo,” ya faɗa a hankali, Inteesar ta juya da sauri, “Daddy!” Ta ƙarasa wajensa, “Daddy, me ya sa ka fito kai kaɗai? Ya kamata ka kira ni mana,” ta kama hannunsa cikin shagwaɓa, Alhaji Kabeeru ya yi murmushi, “Ni fa lafiya ta kalau,” Mommy Haleema ta yi dariya, “Dama yau tun safe akwai wani annuri a gidan nan,” Daddy ya ɗan lumshe ido, “Alhamdulillah,” domin shi kaɗai ya san yadda ya yi ta addu’ar Allah Ya dawo masa da murmushin Inteesar, ta kama shi a hankali, suka nufi falo.

Inteesar tana zaune a falo tare da Daddy da Khalil, wayarta da ke gefenta ta yi haske, Mi Amor ❤️ Wani irin murmushi ya bayyana a fuskarta ba tare da ta shirya ba, ta yi saurin ɗaukar wayar, saƙo ne daga Aliyu, my love, I just wanted to tell you something simple, but very true… you are my favorite part of every day, no matter how busy the world gets, you’re always in my thoughts like a soft song I can’t stop replaying, you make ordinary moments feel special just by being in them, I LOVE YOU ❤️ Inteesar ta yi wani sanyayyen murmushi, ta sake karanta saƙon, kamar tana son ta tabbatar cewa da gaske nata ne, sai ta ɗago, Daddy da Khalil duk suna kallonta, Khalil ya ɗaga gira, “Waye ne yake sa Princess ɗinmu murmushi haka?” Inteesar ta yi saurin ɗaukar pillow ta jefa masa, “Yaya!” Daddy ya yi dariya, “Ki amsa mana,” ta yi dariya, “Friend ne,” “Friend?” Khalil ya maimaita, “Eh mana,” “Friend mai saka mutum murmushi shi kaɗai?” Ta sake jefa masa pillow, “Daddy, ka yi masa magana mana!” Ta faɗa da muryar shagwaɓa, dariya ta cika falon, Khalil kuwa ya girgiza kansa yana kallonta, friend ɗin nan dai ya fi friend ɗin da na sani wani matsayi.

Da daddare… Inteesar tana kwance a kan gadonta tana duba wasu hotunan da Humaira ta turo mata lokacin da wayarta ta fara ƙara, da ganin sunan da ya bayyana a screen ɗin, sai wani murmushi ya bayyana a gefen laɓɓanta ba tare da ta shirya ba, Mi Amor ❤️ Ta ɗan gyara zamanta kafin ta ɗaga, “Assalamu alaikum,” “Wa alaikumus salam, Babygirl,” murmushinta ya ƙara faɗaɗa, “Mi Amor,” Aliyu ya lumshe idanunsa yana murmushi daga cikin motarsa, wallahi, babu abin da yake sa shi jin daɗi irin yadda take kiransa da sunan nan, “Ya kika yini?” “Alhamdulillah,” “Daddy fa?” “Yana nan lafiya kalau, yana falonsa tare da Mommy,” “Masha Allah,” ya sauke numfashi cikin farin ciki, “Allah Ya ƙara masa lafiya,” “Ameen,” “Mommy fa?” “Lafiya kalau,” “Yaya Abubakar fa?” “Shi ma lafiya,” Aliyu ya yi murmushi, kullum idan ya kira ta, dole sai ya tambayi iyalanta ɗaya bayan ɗaya, wani abu da ke ƙara sa Inteesar jin daɗi a ranta, yana nuna mata cewa ba ita kaɗai yake so ba, har da mutanen da take ƙauna, “Mi Amor…” “Uhmm?” “Ba ka gajiya ne?” “Da me?” “Da ni,” Aliyu ya yi murmushi, “Ban fara gajiya da ke ba ma,” ya yi dariya, “Wallahi, Babygirl, idan akwai abu guda da ba na gajiya da shi, to, ke ce,” wani irin shiru ya ratsa tsakaninsu, shiru mai ɗauke da wani daɗi na musamman, can Inteesar ta ce a hankali, “Ni ma…” “Uhmm?” Ta yi shiru, “Babygirl…” “Uhmm?” “Ina jinki,” “Babu komai,” Aliyu ya yi murmushi, “Babygirl…” “Na’am?” Sai ya rage muryarsa kamar yana rada mata a kunne, “I love you so much, ko wane bugun zuciyata, da soyayyarki yake bugawa,” Inteesar ta yi shiru, kamar ruwan da ya sauka a ƙasa ya shanye ta, ta kankame wayar a hannunta, kamar Aliyu zai fito daga cikinta, bayan ɗan lokaci, sai ya tambaya, “Kin ci abinci?” “Eh,” “Da gaske?” “Uhmm, na ci,” “Ban yarda ba,” Inteesar ta yi dariya, “Wallahi na ci!” “Toh, shikenan,” shiru ya ratsa tsakaninsu na wasu daƙiƙu, sai Aliyu ya sake cewa, “Yau na yi missing ɗinki sosai,” nan take kunya ta ƙara mamaye Inteesar, ta sunkuyar da kanta duk da cewa ba ya ganin ta, “Ki yi magana mana,” ya faɗa yana rage murya sosai, a hankali, cikin shagwaɓa, ta ce, “Mun yi waya da safe fa,” “Na sani,” “Mun yi da rana,” “Na sani,” ta ɗan yi shiru, sannan ta ƙara da cewa, “And you’re still missing me?” Aliyu ya yi murmushi, “Babygirl, ba na gajiya da ke, na matsu na ɗauke ki na dawo da ke gidana, kina kusa da ni,” ya ɗan dakata, sannan ya rage muryarsa, “I just wish I could spend tonight with you, my baby,” Inteesar ta ji tsikar jikinta ta tashi, ta runtse idanunta a hankali, sannan ta furta, “Hmm…” “Wannan hmm ɗin kuma?” “Babu komai,” “Babygirl…” “Na’am?” “Ki faɗa min gaskiya,” “Me?” “Ko da kaɗan ba ki yi missing dina ba?” Inteesar ta cije laɓɓanta, wani ɓangare na zuciyarta yana son ta faɗa masa gaskiya, amma kunya ta hana ta, sai kawai ta ce, “Na yi,” Aliyu ya saki dariya, dariyar da ta sa wani irin ɗumi ya bazu a zuciyarta, “Tun safe nake ta tunaninki,” nan take zuciyarta ta yi wani irin bugawa, da sauri ta canza maganar, “Ya aiki?” Ya fahimci abin da take yi, amma bai matsa mata ba, sai ya biye mata, suka shiga hira, suna magana, suna dariya, suna tsokanar juna, lokaci yana tafiya ba tare da sun lura ba, can Aliyu ya duba agogo, sai ya sauke numfashi a hankali, “Babygirl…” “Na’am?” “Zan shiga gida, tun daɗewa nake zaune a mota,” murmushin da ke fuskar Inteesar ya ɗan lafa, “Okay,” Aliyu ya lura da sauyin muryarta, amma sai ya yi murmushi shi kaɗai, “Me ya faru?” “Babu komai,” “Babygirl,” “Na’am?” “Ki kula da kanki,” “Okay,” “Ki gaishe min da Daddy da Mommy,” “In Sha Allah,” “Goodnight in advance,” “Goodnight,” “Sleep tight, I love youuu,” a hankali ta ce, “Sai da safe,” bayan sun yi sallama, Inteesar ta daɗe tana kallon screen ɗin wayarta, sai ta tura baki gaba kaɗan, ta ajiye wayar a gefenta, ba ta fahimci kanta ba, amma duk lokacin da Aliyu ya ce zai shiga gida, sai ta ji wani irin abu yana motsawa a zuciyarta, wani abu da ba ta son ta saka wa suna, a ɗayan ɓangaren kuma, Aliyu yana zaune cikin motarsa kafin ya fito, yana kallon wayarsa yana murmushi, ya riga ya fara gane Babygirl ɗinsa, ba ta faɗar abin da ke zuciyarta, amma canjin muryarta, yadda take yin shiru, da yadda take turo baki duk lokacin da zai yi mata sallama, duk sun isa su gaya masa abubuwa da yawa, a hankali ya furta, “My jealous Babygirl…” Sai ya yi murmushi, ya girgiza kansa, ba ki faɗa min komai ba, amma zuciyarki tana gaya min abubuwan da baki iya furtawa, kuma hakan ya isa ya sa ya kwanta da murmushi a wannan daren.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol