Free chapter · Read without an account
THE PROMISE BETWEEN US
KADDARAR ZUCIYA
CHAPTER THIRTY-SEVEN: 37
THE PROMISE BETWEEN US
JIDDAAH BARKUM
———
Kwana biyu kacal suka rage wa ranar komawar Inteesar Abuja domin kammala final year ɗinta, tun daga lokacin da aka fara shirye-shiryen tafiyar, wani irin yanayi na kewar juna ya fara mamaye zuciyarta, ba wai saboda makarantar ba, a’a, sai saboda wani mutum mai suna Aliyu, yamma ce mai sanyin iska lokacin da Aliyu ya iso gidan kamar yadda ya saba, ya kira ta a waya ya sanar da ita cewa ya ƙaraso, ta yi murmushi ta ce, “Toh, ka shigo mana, Daddy yana falo,” bayan sun gaisa da Daddy da Mommy Haleema, Inteesar ta sauko cikin nutsuwa, sanye take da wata atamfa mai launin ja da baƙin sirki, riga da skirt ɗin da suka yi mata matuƙar kyau, dinkin ya zauna a jikinta sosai, kamar an ɗinka rigar ne saboda ita kaɗai, ba ta ɗaura dankwali ba, sai dai madaidaicin mayafi da ta yafa a kanta, wanda ya sauko har kafaɗunta yana rufe kirjinta, fuskarta ta yi fes duk da babu kwalliya mai yawa, sheƙi take yi, tare da ɗauke da daɗaɗɗen ƙamshin turarenta, Aliyu ya kafeta da idanunsa yana yaba kyawunta a zuciyarsa, amma saboda Daddy yana wajen, dole ya sauke idanunsa ƙasa yana murmushi, da ta ƙaraso kusa da su, Daddy ya yi murmushi ya ce, “Princess, baƙonki yana ta kallon agogo tun ɗazu,” Inteesar ta ji kunya, Daddy ya ci gaba da cewa, “Ku je ku zauna a compound mana, ku sha iskar yammacin nan mai daɗi,” ya ƙarasa maganar yana kallon Aliyu, wanda ya sunkuyar da kansa ƙasa yana murmushi kamar ba shi ake magana a kansa ba, ita ma kunya ta mamaye Inteesar, a hankali suka fita zuwa garden, yayin da rana take shirin faɗuwa, iskar yamma mai laushi kuma take kaɗawa.
Wurin ya yi tsit tun bayan da suka zauna, babu wanda ya yi magana sai Aliyu, wanda ya kafeta da ido yana kallonta, duk lokacin da ya kalle ta, sai ya ji kamar zuciyarsa tana sake faɗawa cikin soyayyarta, wani lokacin har mamaki yake yi, ta yaya yarinyar nan ta zama wani sashe na rayuwarsa haka? Ya kira ta a hankali, “Babygirl…” Ta amsa cikin nutsuwa, tana ɗago kanta daga inda take kallon ƙasa, “Uhmm?” “Kinyi kyau sosai,” ta yi murmushi, “Ai ka fi ni kyau,” ya zaro ido yana dariya ƙasa-ƙasa, “Anya kuwa? Kin ga yadda kika yi kyau kuwa? Kamar na ɓoye ki ne na gudu da ke daga nan,” ta yi murmushi kawai ba ta ce komai ba, sai can ya sake kallonta, “Me yake damunki?” Ta yi shiru na ɗan lokaci, “Babu komai,” ya yi murmushi, “Wannan amsar ba za ta yi aiki a wurina ba,” ta yi murmushi kaɗan, sannan ta turo baki gaba, “Ba na son tafiyar nan,” Aliyu ya yi shiru kafin ya tambaya, “Saboda?” Ta sunkuyar da kanta, “Shikenan, na daina ganinka, ba na son tafiya,” ta faɗa ba tare da ta yi tunanin kalaman nata sosai ba, da alama ita ma ba ta san lokacin da suka fito daga bakinta ba, wani irin taushi da tsantsar farin ciki ya mamaye zuciyar Aliyu, “Kin fara jin kewata haka?” Ya faɗa a hankali yana kallonta da idanunsa da suka sauya saboda farin ciki, ta turo baki kaɗan, tana rufe fuskarta da hannunta, Aliyu ya yi murmushi, “Ina son shagwaɓar nan taki, but it has limits,” ta sake cusa fuskarta cikin tafin hannunta tana murmushi, wallahi, da ace son zuciyarsa ne zai bi, da bai bari ta tafi ba, da ya riƙe ta kusa da shi kullum, ya ji dariyarta, ya ji muryarta, ya kuma ga wannan shagwaɓar tata da take rikita masa tunani, tun lokacin da ta shigo rayuwarsa, bai taɓa sanin cewa mutum guda zai iya zama tushen nutsuwarsa haka ba, ya yi murmushi sannan ya ce, “Wallahi, Babygirl, da ace zan bi son zuciyata, da ba zan bari ki tafi ba,” ta ɗago da sauri, “Me ya sa?” Ya tsaya yana kallonta kawai, bai ce komai ba, ta sake sadda kanta ƙasa, sai a hankali ya ce, “Ko kuma na sace ki,” nan take ta yi dariya, “Mi Amor!” Shi ma ya yi dariya, amma daga baya murmushinsa ya ɗan lafa, “Karatu yana da muhimmanci, kina final year, kuma ba na son wani abu ya hana ki kammala abin da kika fara,” ta yi shiru, sannan ta ce a hankali, “Zan yi missing ɗinka,” kalmar ta fito kamar ba da niyya ba, amma ta isa ta sa wani irin sanyi ya ratsa zuciyar Aliyu, ya yi murmushi, “Babygirl, ni fa? Wai ni ba zan yi missing ɗinki ba ne?” Ta yi murmushi, “Mi Amor…” “Uhmm?” “Wallahi, ba na son tafiyar nan,” Aliyu ya matsa kaɗan kusa da ita ba tare da ya taɓa ta ba, “Distance ba ya canza soyayya, Babygirl, wani lokacin ma yana koya wa mutum haƙuri da darajar kasancewa tare da wanda yake so,” ya yi mata murmushi, “Duk lokacin da na samu dama, ko weekend ne, ko kwana ɗaya ne, wallahi zan zo Abuja,” idanunsa suka haskaka, “Da gaske, saboda ba zan iya ɗaukar lokaci mai tsawo ba tare da na ga Babygirl ɗina ba,” Inteesar ta yi murmushi tana kallon ƙasa, sai ya sake kallonta a hankali, “Thank you for loving me, Inteesar,” ta ɗago idanunta, ya yi murmushi mai cike da taushi, “Thank you for loving me duk da shekaruna, sannan duk da cewa ina da mata biyu, kika amince da ni,” ya sauke numfashi, “Wallahi, Babygirl, wani lokacin har mamaki nake yi, na san kina da samarin da suke sonki, waɗanda ba su taɓa aure ba, amma duk da haka, kika zaɓe ni,” Inteesar ta yi murmushi ta saka idanunta cikin nasa, “Mi Amor, kai nake so, da kai zan zauna, ba da matanka ba,” idanunsa suka ɗan faɗaɗa saboda mamaki, ta ci gaba cikin nutsuwa, “Wallahi, idan ina tare da kai, wani lokacin har mantawa nake yi cewa akwai wasu mata biyu a rayuwarka, ni ba na kallonsu a matsayin shamaki tsakanina da kai, kai nake gani, lokacin da nake tare da kai, ba na tunanin komai sai kai,” shiru ya ratsa tsakaninsu, Aliyu ya daɗe yana kallonta, wallahi, a wannan lokacin ji yake yi kamar ya rungume ta ya matse ta a ƙirjinsa, domin ta ji yadda zuciyarsa take bugawa saboda tsananin son da yake mata, sai ya ce a hankali, “Babygirl, kin san wani abu?” Ta girgiza kai, “Me?” “Wallahi, duk lokacin da kike kallona da idanun nan naki, sai na ji kamar ni kaɗai ne namijin da Allah Ya halitta a duniya,” ta yi murmushi tana wasa da yatsunta, shi ma ya yi dariya, sai can ya sake kallonta ya ce, “Thank you, thank you for loving me,” ta yi murmushi, “Ai ni fa ina kallonka kamar wani ɗan shekara ashirin ne, kwata-kwata ba na ganin shekarun da kake faɗa,” ta ƙarasa maganar tana lumshe idanunta cikin nasa, a lokacin nan, wallahi Aliyu ji yake kamar ya rungume ta, ko za ta ji yadda zuciyarsa take bugawa da ƙaunarta, domin a duk shekarun rayuwarsa, bai taɓa tsammanin wata mace za ta sa shi jin kamar saurayi ɗan shekara ashirin ba, kuma abin da ya fi ba shi mamaki shi ne, ba ta yin wani abu na musamman don ta burge shi, kasancewarta kawai ya isa.
A wannan daren, Inteesar ta daɗe tana murmushi ita kaɗai, tun bayan tafiyar Aliyu, har yanzu kalamansa suna yawo a cikin kanta, distance ba ya canza soyayya… Wallahi zan riƙa zuwa Abuja… Thank you for loving me… Sai ta rungume pillow ɗinta tana murmushi kamar yarinya, wani irin farin ciki mai cike da nutsuwa ya mamaye zuciyarta, karo na farko cikin shekaru, ba ta jin tsoron gobe, ba ta jin tsoron ƙaddara, kuma ba ta jin tsoron sake samun farin ciki, domin a hankali, Aliyu yana koya mata yadda ake sake yarda da rayuwa, aka ƙwanƙwasa ƙofa, ta ɗago kai, “Shigo,” ƙofar ta buɗe, sai ga Yaya Abubakar, nan take ta miƙe zaune, “Yaya,” ya yi murmushi kaɗan, “Princess,” ta lura da yadda fuskarsa take nuna seriousness, gabanta ya ɗan faɗi, ya zauna a kujerar da ke kusa da gadonta, “Zo ki zauna nan,” ta matsa kusa da shi, tun tana yarinya, idan Yaya Abubakar yana son yin magana mai muhimmanci da ita, haka yake kiranta, sai ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya sauke numfashi, “Princess… kin san cewa ina sonki, ko? Kuma kin san cewa babu abin da nake so fiye da farin cikinki?” Ta gyada kai, “Na sani,” ya dafa hannunta cikin taushi, “Shi ya sa zan gaya miki abu guda yau, ki tafi Abuja, ki gama karatunki, kada ki bari wani abu ya ɗauke miki hankali, kada ki bari soyayya ta sa ki manta da abin da ya kai ki can,” ta sunkuyar da kanta tana sauraro, “Daddy ya yi abubuwa da yawa saboda karatunki, Mommy ta yi addu’o’i da yawa, mu kuma, wallahi tun kina yarinya muke mafarkin ranar da za mu ga Princess ɗinmu ta gama jami’a,” hawaye suka taru a idanunta, ya ci gaba cikin nutsuwa, “Aliyu mutum ne mai hankali, kuma idan yana sonki da gaske, abin da zai fi so shi ne ya ga kin zama abin alfahari, ba wai ya ga kin lalace saboda shi ba,” ta yi saurin girgiza kai, “In Sha Allah, Yaya,” ya gyada kai, “Kar na ji cewa waya ko soyayya sun hana ki karatu,” “Toh, Yaya,” “Good,” ya yi shiru kaɗan, sannan muryarsa ta yi laushi, “Princess… kin girma, amma a wurina har yanzu ke ce yarinyar da take gudu tana ɓuya a bayana idan Khalil ya tsorata ta,” dariya ta kuɓuce mata tare da hawaye, “Yaya, zan yi missing ɗinku,” nan take ya amsa, “Mu ma, wallahi, gidan nan zai yi ba daɗi idan kika tafi, amma hakan ba zai hana ki tafiya ba, saboda tsuntsu ba ya koyon tashi idan kullum yana gida,” ta jingina kanta a kafaɗarsa, kamar yadda take yi tun tana yarinya, “Thank you, Yaya,” ya yi murmushi, “Ba ni za ki gode wa ba, ki gode wa Allah,” sai ya ɗan yi murmushi ya ƙara da cewa, “Kuma ki gode wa Alhajin naki,” nan take ta ɓoye fuskarta, “Yaya!” Ya yi dariya, “Eh mana! Wallahi, mutumin nan ya ba ni mamaki,” ta ɗago da sauri, “Me kuma?” Ya yi murmushi, “Yadda yake kallonki, yadda yake magana a kanki… wallahi yana sonki,” kunya ta mamaye Inteesar, “Yaya…” Ya miƙe tsaye, “Ki yi barci saboda gobe za a fara shirye-shiryen tafiya,” yana bakin ƙofa ya tsaya, ya sake kallonta, “Princess, ki yi farin ciki, Allah Ya tabbatar da alheri a tsakaninku,” sabbin hawaye suka cika idanunta, “Ameen,” bayan ya fita, Inteesar ta zauna ita kaɗai cikin ɗakin, ta ɗaga idanunta sama ta furta a hankali, “Alhamdulillah…” Zuciyarta cike da salama, domin idan har Yaya Abubakar ya yarda da son da Aliyu yake mata, to tabbas ta samu wani mutum da ya shirya tsayawa tare da ita, ta sake rungume pillow ɗinta tana murmushi.
Sai dai a can Abuja… A wani balcony mai duhu, Yaya Umar yana tsaye shi kaɗai, idanunsa na kallon sararin samaniya yayin da tunani masu nauyi suke yawo a zuciyarsa, a karon farko cikin kwanaki, wani abu a zuciyarsa yana gaya masa cewa lokaci yana ƙurewa, kamar dai akwai wani abu da yake gab da faruwa, wani abu da zai iya sauya komai, ya sauke numfashi a hankali, sannan ya lumshe idanunsa, wata rana, yana iya rasa Inteesar gaba ɗaya, ba wai saboda ta yi nisa da shi ba, amma saboda wataƙila zuciyarta ta riga ta zaɓi wani, sai ya jingina da dogon shingen balcony ɗin, yana ƙoƙarin danne tunanin da ya ƙi barin zuciyarsa ta huta, ba tare da sanin cewa wacce yake tunani a wannan daren tana kwance tana murmushi saboda wani mutum daban ba… Kuma a hankali, zuciyarta ta fara buɗe wa wani ƙofa da ya daɗe yana ƙoƙarin shiga.