Free chapter · Read without an account

003

by Aisha Muhammad Sanusi · BAUTAR ZUCI





"ba b'ata maka rai zan ba habiby kayi hakuri, na cika umarni ne kace nazo anjika shi ne nazo yanzu, kallonta yayi kallon rainin hankali sannan ya kwanta a saman bed dinsa yana kallon falmata wadda ita ma shi take kallo.

" idan kina buqatar wani abin ki dauka ga fridge nan bacci zanyi yanzu idan na tashi sai na rakaki gida ko, falmata har zatayi magana ta tina da maganar jamcy da farida hakan yasata jan baki ta tsuke tana kallon fridge din.

Ummi a ajin na islamiyya mamakin abinda ya hana falmata zuwa makaranta yau tayi, bayan ta hangeta ta fito da shirin tafiya makarantar,malamin su har tambayarta yayi dalilin da yasa falmata batazo ba amma bata da abin fada hakan yasa taja baki ta tsuke.

Yau dake antashi da wuri, ummi ce a ranta tace"yakamata naje wajen wancan tsinanne saurayin dan nasan falmata ba wanda zai hanata zuwa makaranta sai shi, dan haka maimakon tai hanyar gida sai tayi hanyar gidan su ibrahim.

Tinda ta shigo lungun gidan ba kowa a ciki hakan yasa ta k'ara sauki, karfe biyar da rabi a lokacin,ummi ce ta zauna a kan wani dakali tana kallon shagon domin ta gansa a rufe.

Ta d'auki tsawon minti sha biyar taga falmata da ibrahim sun fito suna dariya,falmata idanunta ne suka hade dana ummi, hakan yasaka ta lokaci guda hade rai kamar hadari.

Ummi bata damu ba sai ma tashi tayi tace"wallahi falmata kin bani mamaki ki rasa wanda zaki biyewa sai wannan sakaran mara sana'a, har a kansa kike kin zuwa makaranta, har kike zama a shagonsa bayan kinsa ba muharraminki bane, ke ko dan uwanki ne bai dace ba indai ba mijinki bane.

Sororo ibrahim yayi yana kallon ummi yayin da falmata ta karasa gaban ummi ta zabga mata mari sannan ta kalleta tace"wai ummi ina ruwanki da rayuwata, dan meyasa a gabana zaki na aibata abinda nakeso, ina ruwanki ko ma menene yaje ya dawo naga ba mutunci ki bane, ba kuma mutuncin uwarki bane balle na gidanku.

Ummi wadda ta dafe kuncinta ce ta dubi falmata tace"yanzu akan wannan shashashan kike zagin uwata, har kika d'aga hannu kika mareni falmata.

"karki kuskura ki kara zagin sa domin idan kin zageni nayi shiru bazan iya zuba ido naga kina zagin saurayi na a gabana ba kuma nayi shiru na kyaleki, bazaiyu ba wallahi.

Ummi ce tai wani murmushi wanda yafi dukanta da tayi mata ciwo tace"wallahi falmata indai har na haifu a cikin mahaifiya ta daga yau bani bake, bazan k'ara shiga cikin rayuwarki ba, nayi nayi dake akan ki gane gaskiya ki daina biyewa ibrahim amma kinki yadda,shikenan kije duniya ce.

Kallon ibrahim tayi tace"kai kuma kaje ai zaka haihu kaima, zaka haifa dik abinda kayiwa wani kaima za'ai maka, ka sani allah ba'a masa yawo, kuma allah bayasan zalunci.

Daga haka ta huce tana sharar kwallah.

Ibrahim ne ya dubi falmata yace"beb meye hakan dama har yanzu kina mu'amala da wannan shegiyar kawarta ki mai shiga abinda babu ruwanta.

Falmata murya na rawa tace"aa habibi ai gashi a gaban ka mun b'ata karka damu daga yanzu bazata k'ara shiga sabgata ba.

Ibrahim tab'e baki yayi ya juya yayi gaba ya barta a baya.

Da sauri ta biyo bayansa tana fad'in"beb muje ka rakani gida ko, juyowa yayi ya kalleta yace"ashe baki da hankali ko, ni zanje gidanlu, kin manta abinda mahaifinki yamini ko,shiru falmata tayi tana raba ido ya na munafuka.

Ni daga nan ma. Nasarawa zanje muna shirye shiryen birthday wani aboki na gobe.

Falmata da sauri tace"babe kaje dani mana please, wallahi ban taba zuwa irin wajen nan ba, kallonta yayi da kyau yaga dagaske take zataje din.

"shikenan gobe da karfe takwas na dare zamuje ki shirya kizo sai muje kawai ko babe, muje ayi chilling damu, murmushi gayi masa sanann tayi hanyar gida bayan ta gyara nikab nata.

Da sallama ta shiga gidan nasu, a harabar gidan taga mahaifinta tsaye da alama akwai wanda yake jira.

"sannu da gida baba, kallonta yayi ba tare daya amsa ba yace"daga ina kike, shiru tayi kasancewar ba gaskiya.

Cikin inda inda tace" daga makaranta nike,umma wadda ta fito daga d'akinta tace"karya kike munafukar allah wato yanzu falmata sakayyar da zaki mana kenan. 

"ke falmata yanzu tarbiyyar da muka baki kenan, kiji tsoran allah ki tuna zaki mutu falmata.


​

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol