Free chapter · Read without an account
12
by Asmy b Aliyu · OMRI HAYATII
OMRI HAYATII
by
Asmy b Aliyu
12.....
daga abba har mu'azzam basu bar cikin dinning area ba Sai da suka turawa kowane kudi a account dinsa masu nauyi. tun daga Fadeela,fareeda,da Ayusherh
ita Ayusherh lokacin da kudin suka shigo
tana dakinsu itada kaaka itada ya'yan Yaaya Fadeela,ajiyar zuciya Kawai ta sauke
tana Kara yiwa wannan family fatan Alkhairi da dukkan nasarar da xasu taka
a rayuwarsu .allah ya zama gatansu
ya cigaba da dafa masu acikin lamurransu,daga kaaka har ita sune gatansu dan baka taba cewa su din Yan aikine yadda suke sakewa a gidan
hatta makarantansu boko da islamiyya,
kallon da ake yimasu itada fareeda
ubansu daya asalinsu daya tunda ko a makarantar ma Ayusherh marafa take amfani dashi tun farkon kaita makaranta,
mu'azzam ne yayimata register da komai nata da sunan mahaifinsu batareda yaji komai ba,da Kuma sunan ta cigaba da amfani har inda yau ke motsi....
ASALINSU.......
Alh.ibrahim marafa haifaffen garin kaduna nane rayuwarsa da komai nasa a garin kaduna yayi ta ,tun a wancan lokacin
mahaifinsa mu'az marafa shaharren mai kudine Wanda suke cikin daula Suna juyata yadda sukaga dama shaharren dan kasuwane,har ya komawa mahalinccinsa tun a wancan lokacin mata biyu ya aura
hajiya rahamu,wacce itace ta farko
shekara goma basu taba haihuwa dashi ba
haka dangin suka sakata a gaba da tsangwama akan rashin haihuwa Sun zagaye asibitoci da dama,Sai dai abu daya Ake fadamasu lafiayansu kalau duk irin
yadda Alh.mu'az marafa ya toshe kunne akan ya Kara aure saboda tsananin kaunar dake tsakaninsa da rahamu,Sai da dangi
suka sakasa a gaba da masifa da balain,
da matarsa rahamu ta kamu da hawan jini mai tsanani. duk akan ta magance mu'az din ta hanasa kula ko wace macce
acikin dare ta daga masa hankali da wani irin kuka mai Sosa zuciya da ruhi
tayi masa rantsuwa akan muddin bai Karo
aure ba ta huta da tsangwamman Yan uwansa. to Xatabar aurensa ko ya bata takarda ko bai bata ba Zata tafiyarta
da wannan tashin hankalin mu'az din ya tashi
ya mata alkawarin xaiyi Aure idan hakan shine kwanciyyar hankalinta,bayan wani
lokaci Alh.mu'az tafiyar da yake yi
daga wannan kasa zuwa wannan kasa saboda kasuwancinsa,ya hadu da hafsat
wacce ta fito daga kasar marooco
itama ta fito daga gidan Yan boko
haka masu kasuwanci,Wanda kasuwancin
shine ya hada mu'az da iyayenta.nan take
yaji ajikinsa ya samu matar Aure
bayan wani lokaci ya samu kawunsa
da zancen nan ma cikin dangin aka kama karamar magana ga ya'mmata a gida
har Sai ya tsallake tun daga kasarsa
har zuwa wata kasar,abun yayi masu ciwo sosai .so sukayi ya auri cikin danginsu su cigaba da gallazawa matarsa.
haka ya toshe kunne bayan wani lokaci
ya tura kawunsa ta jirgi shida wasu makusanta nasa sukaje nemo masa Auren
hafsat wacce aka yanka masu sadaki da sisin gold mafi daraja nan take suka biya aka saka biki nan da wata daya,
suka koma Nigeria ya barwa uwargidansa
komai da komai na lefen da Zaa hada
kafin wata daya aka hada lefe nagani
na fada akayi tattaki aka Kai ,bayan wasu kwanakki aka daura Aure,satin amarya
biyu da daura aure danginta Suka biyo ta jirgi suka kawo hafsat cikin dangin
mu'az .danginsa Suka amsheta ganin kyakkyawar balarabar da ko Hausa bataji daga larabnci Sai turanci.hajiya rahamu hannu biyu ta karbi hafsat da tagama batada wasu shekaru,wani irin zaman lafia ke wanzuwa a gidan Alh.mu'az marafa
duk yadda dangin Alh.mu'az sukaso su kuntatawa hajia Rahamu su Jaye hafsat daga jikinta hakan bai faruba,dan farat daya hafsat taji tana kaunar hajia Rahamu
har aranta,haka dangin Alh.mu'az suka gaji suka xubawa sarautar Allah ido
shiru har hafsat tayi shekara biyu babu maganar ciki itama nan danginsa Suka fara sakota gaba,cikin ikon Allah acikin shekara ta biyar da aurensu allah ya bayyana ciki
ajikin hafsat zo kuga murna gun alh.mu'az da hajiya rahamu ,jin suke kamar su maida hafsat ciki dan tsananin so wani irin tattalin cikin da taka tsantsan aka riqayi daita.tuni hajia Rahamu tahana hafsat koda daukar tsintsiyane a gidan
duk da suna da Yan aiki kusan hidimar hafsat din ta dawo wurin hajia Rahamu,
duk kalar cimar da hafsat keso itake shiga kitchen ta tanadar mata haka ruwan wanka ita ke shiga toilet ta hadamata,
kusan dai tare akayi rainon cikin da hajia
rahamu,bayan watanni tara hafsat ta haifo santalelen jaririnta mai kama da uwarsa
tamkar tayi kaki fari tas dashi kyakkyawan balarabe,familyn marafa bakaramun murna sukayiba da samun wannan kyauta ta bayan shekarun da har Sun fitar da rai,
nan ma hajia Rahamu,ita ta rika kula da masu Jego,dan duk yadda dangin hafsat din suka so suzo su tafi da hafsat din
tayi wankan Jego a gida Sam Alh.mu'az ya hana yadai masu alkawarin bayan hafsat din tayi arbain zataje kasarsu ta Kai masu jariri .haka badan sunso ba suka hakura Sai mutum biyu cikin yayunta suka zo
har akayi Suna Wanda yaro yaci suna
Ibrahim.....wani irin so Ibrahim ke samu
tsakanin iyayen nasa guda 3 Alh.mu'az mafara da Kuma hajia Rahamu marafa,
iyakar hafsat a kawo matashi ta basa nono hajia Rahamu itace uwarsa,
tun daga Ibrahim Kuma hafsat bata taba ko bari ba daganan Kuma haihuwar ta tsaya Ibrahim Yana da shekara 7 a duniya
mahaifiyarsa hafsat ta rasu mutuwar data girgiza familyn marafa tabar masu wani tabo da har abada bazai cire daga zukatansu ba,hajia Rahamu ta cigaba da kula da Ibrahim Wanda a lokacin baima San menene mutuwa ba,haka Kuma
ya taso bbu wata shakuwa tsakaninsa da umminsa Sai dai hajia Rahamu wacce yake kira umma tun Yana yaro,
Ibrahim nada shekara 10 a duniya kwatsam
ciki ya bayyana ajikin umma,murna kamar me.yana cika wata 9 ta haifi kyakkyawar yarta macce wacce kamar an tsaga Kara itada mu'az marafa wani irin so
sukaji sunayiwa Yarinyyar da taci sunan hafsat,haka umma ta nemi alfarma akan acigaba da kiranta a hafsat dan Kar sunan hafsat ya bace a zukatansu,wani irin soyayya Ibrahim yake yiwa kanwarsa hafsat,ko kuda baya son ya tabata
bayan Kammala secondary school din Ibrahim mahaifinsa ya Shirya masa tafia zuwa US yin karatunsa na digree anan Ibrahim ya kafe akan Nigeria zaiyi karatu saboda hafsat,Sai da rarrashi da banbaki
aka lallabasa ya yadda zai tafi a bisa alkawarin idan su hafsat sun samu hutun makaranta Zata riqa zuwa itada umma
suna masa hutu.a haka aka kwantar da hankali Ibrahim ya tafi US.karatu da tsananin kewar little sister dinsa
hafsat marafa.........
haka Rayuwa ta cigaba da tafia
cikin kwanciyyar hankali da wani irin habakar arzikin mu'az marafa Wanda shi kansa baisan adadin kamfanonin da ya mallaka ba da nigeria da wajenta
Yana da hannun jarin da manyyan kamfanonin kasar waje,Alh.mu'az marafa Yana da shekaru 60 a duniya ya kwanta dama ,mutuwar da ta taba duk wani jinin mu'az marafa ta kwantar dashi
da taimakon allah da taimakon addu'a
daga umma har ya'yan nata suka fara tsayawa da kafafunsu,lokacin Ibrahim
ya mallaki hankalinsa Yana kokarin ma hada masters dinsa,har Kuma lokacin kusan shekara ishirin da biyar baiyi Aure ba,babu kalar ya'mmata da bai hadu dasu ba Amma har yanxu ya kasa samun
wacce tayi masa umma tayi fada tayi nasiha har ta gaji ta sakawa sarautar
Allah ido.
Rana tsaka ya hadu da maccen da ta canja rayuwarsa gabaki daya Aisha MAHMOUD MODIBBO cikakkiyyar ya'r barno maiduguri kallo daya yayi mata yaga matar aurensa,
itama hafsat tayi murnar da yayanta ya zabo Aisha MODIBBO a matsayin matar aurensa farat daya jinin hafsat da Aisha ya hadu,baa dauki lokaci ba aka je nemawa
ibrahim Auren Aisha har a maiduguri wacce itama marainiyya ce babu uwa babu uba,daga ita sai yayarta Asma'u
wacce tayi aure shekara biyu da suka wuce Sai ga Aisha itama lokacin yin nata Auren yayi anzo neman Aure aka saka
Rana aka biya sadaki aka tsayarda Rana
watanni shidda masu zuwa.daga hafsat har umma suka fara shirya lefe nagani
na fada lefen Yan gata a wancan lokaci
kudi suka saki tamkar basu San ciwon naira ba,itama lokacin Hafsat tana gafda Kammala karatunta...............
akayi auren Aisha MODIBBO da Ibrahim MARAFA daurin Auren da ya kafa tarihi
lokacin suka tattaro US suka dawo
kaduna dan Ibrahim yafi son zaman nigeria
Dan tun lokacin rasuwar mahaifinsu
Nigeria tayi masu wuyar zama Sai dai suzo suyi hutu.
watanni 9 da Auren Aisha da Ibrahim
ta haifo santalelen yaronta fari tas
Wanda duka ya dauko kyan uwa da uba.
ranar Suna yaro yaci sunan Ibrahim,
saboda Ibrahim yayiwa Aisha alkawarin indai ta haifi namiji Ibrahim takeso a saka masa wani irin so mai zafi Aisha keyiwa Ibrahim MARAFA tana haihuwa kuwa
Ibrahim ya cika mata burinta duk da ummah,taso a saka mu'az sunan nata mijin.haka ta hakura tace idan aka sake wata haihuwar Sai a saka tunda yanxu aka fara,cikin tsananin gata Ibrahim Ibrahim MARAFA ya taso Wanda Aisha ta mayar dashi mu'azzam,wata irin soyayya iyayensa ke nuna masa ga kakarsa a gefe da Kuma auntynsa hafsat,
daganan Ibrahim har ya fara girma Aisha bata Kara ko bari ba,duk da tsananin son ya'yan da familyn suke dashi haka
Ibrahim MARAFA yace dama babu family planning din da Aisha din zatayi tun a wancan lokacin,Sai gashi haihuwar shiru
har hafsat tayi aure ta auri wani
sojan ruwa Wanda ke zaune a malesia
Wanda yake abokin Ibrahim ne
Kuma dan jihar jegawa,kamar Kar hafsat tayi aure Sai aisha ta samu ciki
murna kamar me a hankali ta fara rainon cikinta har yakai lokacin haihuwa
ta samu kyakkyawar yarta macce
wacce ke tsananin kama da hajia Rahamu tamkar tayi kaki har dai duhu fatarta
cikin wata irin soyayya Ibrahim
ya rungumeta cikin jikinsa Yana yimata khuduba da sunan Rahamatullah marafa
kamar yadda cikakken sunan hajia Rahamu yake,Sai suka maidata Fadeela baayi wata da haihuwar ba itama hafsat ta haifi santaleliyar babynta ,wacce taci sunan maihaifiyar maigidanta Fatima Suna kiranta da ihsaan,ihsaan nada shekara daya hafsat ta Kara samu ciki
ta haifi hashim,Shima Yana shekara daya ta Kara samun wani cikin wannan lokacin tareda Aisha ,
Aisha ta haihu da kwana arbain hafsat
ta haihu Aisha ta samu macce
ta aka saka mata sunan mahaifiyarsa
zulaiha Suna kiranta da fareeda
itakuma hafsat namiji ta Kara samu
Sai aka saka masa sunan mu'az marafa
suna Kiransa Fahad.daga Aisha har hafsat daganan haihuwar ta tsaya ita hafsat
family planning tayi tana tsananin son ta huta itakuma Aisha Allah ne bai kawo ba.....
cigaban labari.....
#OMRI HAYATII
#LOVE/FATE
#BEST LOVE
# THE MARAFA'S
#ASMY B ALIYU
#***