Free chapter · Read without an account

Chapter 14

by Rukayya Ibrahim · Duhun da natashi ciki

Na gama share ɗakin Gwaggo, na ajiye tsintsiya a gefe, sannan na fito zuwa tsakar gida. Ina jin yunwa, ga gajiyar da ta riga ta mamaye jikina. Na yi tunanin ko zan samu damar zama na ɗan huta, amma da na fito sai na ji ƙamshin ƙosai yana tashi daga inda Mama take.

Tun da sassafe Mama ta fito tana dama kokon da za ta sayar tare da ƙosai. Tana zaune a gabanta, tana ta aiki ba kama hannun yaro, tana zuba garin dawa a cikin kwano tare da gauraya shi da ruwa.

Na ƙarasa kusa da ita. Na ga tana ta faman dama kokon, ga kuma kwandon garin ƙosai a gefe.

“Rammu, kin gama ayyukan can ne?” Mama ta tambaye ni ba tare da ta dakatar da aikin da take yi ba.

Na amsa mata, “Na gama, Mama.”

Ta ɗago kai ta kalle ni.

“To, zo ki taimaka min ki ɗan gyara nan. Ina so in gama damun kokon kafin in fara soyayyar ƙosai.”

Na zauna a gefenta, na fara taimaka mata wajen shirya kayan sana’arta. Na san sana’ar nan ce take taimaka mata wajen samun kuɗin biyan wasu buƙatun gida, don haka nakan yi ƙoƙarin taimaka mata gwargwadon ƙarfina.

Bayan ɗan lokaci, Mama ta kalle ni a hankali.

“Kin ci wani abu kuwa tun da safe?”

Na ɗago kai na kalleta. Ban san dalilin da ya sa tambayar ta ta taɓa zuciyata ba. Tun safe nake aikin gida, amma ba wanda ya tambaye ni ko na ci abinci.

Na girgiza kai.

“A’a, Mama. Ban ci komai ba.”

Mama ta kalle ni, sannan ta ce, “To, Rammu, je ki ɗauko kofi ki zuba kokon ki sha. Bayan kin gama, ki dawo ki taimaka min in gama soyayyar ƙosai kafin ku fita.”

Na ɗauki kofi, na zuba kokon, sannan na zauna a gefe ina sha a hankali. Bayan na gama, na wanke kofin na ajiye shi, sannan na koma wurin Mama domin in ci gaba da taimaka mata.

Ina cikin aikin ne sai ga Kuluwa ta fito daga ɗaki, riƙe da kofi a hannunta. Ta ƙaraso wurin Mama, ta zuba kunu a kofinta, sannan ta fara sha.

“Lafiya dai, Kuluwa?” Mama ta tambaye ta.

“Lafiya, Mama. Na ga kunun ne, shi ya sa na fito na ɗiba.”

Mama ta murmusa, ta koma ga aikinta. Ni kuma na ci gaba da tattara kwanukan da aka gama amfani da su.

A lokacin ne mutane suka fara shigowa suna sayen kunun Mama. Wasu suna zuwa da kofuna, wasu kuma da ƙananan mazubai. Mama tana zuba musu kunu tana karɓar kuɗi, yayin da ni da Kuluwa muke taimaka mata wajen kai-komo.

Gidanmu ya cika da hayaniya sakamakon yawan mutanen da suke shigowa sayen kunu. Mama tana yin sana’arta ne a cikin gida, don haka ba sai ta fita waje ba kafin ta samu kwastomomi.

Bayan ta ɗan gama kula da kwastomomin, Mama ta kalle mu.

“Rammu, Kuluwa, ku je ku wanke rogon nan, ku sa a tukunya ku ɗora a wuta ya dahu. Idan ya dahu, sai ku fita talla da shi.”

Na amsa mata, “To, Mama,” sannan na juya wurin Kuluwa.

Muka ɗauki rogon muka kai wurin wanki. Na fara wanke shi, Kuluwa kuma tana taimaka min, muna cire masa datti kafin mu zuba shi a tukunya.

Da muka gama wankewa, muka zuba shi a tukunya, muka ƙara ruwa, sannan muka ɗora a kan wuta.

“Yanzu dai sai mun jira ya dahu kafin mu fita,” Kuluwa ta faɗa tana kallon tukunyar.

Na gyada kai, na zauna kusa da murhun ina ƙoƙarin samun ɗan hutawa. Amma na san cewa hutun ba zai daɗe ba. Da zarar rogon ya dahu, sai mu shirya shi domin fita talla.

Na kalli Kuluwa, wadda ita ma ta zauna kusa da ni. Na yi shiru ina kallon wutar da ke ci a ƙarƙashin tukunyar, yayin da tunanina ya fara komawa kan rayuwarmu.

Wannan ita ce rayuwarmu. Babu karatun boko, babu makarantar allo. Tun da daɗewa muka daina zuwa makarantar allo saboda rashin kuɗin da ake kaiwa ranar Asabar.

A cikin gidanmu, ni ce na fi dagewa da zuwa makaranta. Ina da sha’awar karatu sosai. Duk lokacin da na ga yara suna ɗauke da allunansu ko littattafansu suna tafiya makaranta, sai na ji wani irin baƙin ciki a raina. Ni ma ina son in kasance cikinsu, in koyi karatu da rubutu kamar sauran yara.

Ko makarantar gwamnati da nake zuwa, ga shi ita ma na fara kasa zuwa yadda ya kamata saboda halin rayuwa…

Wani lokaci nakan tambayi kaina, me ya sa rayuwarmu ta kasance haka? Me ya sa wasu yara suke zuwa makaranta cikin farin ciki, yayin da mu kuma muke tashi da ayyukan gida da talla?

Amma ina za mu samu kuɗin makaranta, alhali kuwa abin da muke nema da safe shi ne yadda za mu samu abin da za mu saka a bakin salati?

Hakan ya sa burina na karatu ya fara tangal-tangal, ba don na daina son karatun ba, sai don halin rayuwa ya zama mana cikas.

Duk da haka, ban taɓa cire rai ba. Har yanzu ina riƙe da burin cewa wata rana zan koma makaranta, in ci gaba da karatuna kamar yadda nake fata. Ban san yadda hakan zai kasance ba, amma kullum ina roƙon Allah Ya buɗe mana ƙofar sauƙi.

Na sauke ajiyar zuciya, na sake kallon tukunyar rogo. A yanzu dai, ayyukan gida da talla su ne suka mamaye rayuwarmu. Ni da Kuluwa muna jiran rogon ya dahu domin mu fita sayarwa, kamar yadda muka saba.


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol