Free chapter · Read without an account

Chapter 38

by MARYAM STAR · ƊAURIN ZUCI

𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
Chapter 38

Duda caɓewar da hannayensa suka yi da ƙuna,  hakan bai hana shi saka hannun ba ya danne kan shi da ƙarfin, wan da yake jin tamkar zau tarwatse saboda tsananin ciwon da yake yi ma shi.
    Hannun shi na dama marar ciwon ya ɗaga tare da saka zaƙo-zaƙon faratansa a saitin ƙirjinsa ya soma kartawa da tsananin ƙarfi yana ihu haɗi da kururuwa wacce ta janyo hankullan matanen gidan suka rufu a bakin ƙofar ɗakin tare da ma'aikata suna dukan ƙofar.
    Bai daina ihu da kururuwar azaba ba kamar yanda bai daina karta naman ƙirjin shi ba yana jima kanshi mugayen raunuka.
     Wata razananniyar ƙara da saida gidan ya amsa da amon sautin ƙatuwar muryarsa ya saki, tare da saka faratan shi ya buɗe ƙirjin shi tare da janyo wani siririn abu dogo, ya jinga janyo shi yana ihu kamar zai suƙe.

   "Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un! na shiga uku ni Hafsatu mi zan gani haka?." Uwar gidan shi ta faɗa lokacin da jibga-jibgan securitys ɗin gidan suka yi nasarar malle ƙofar ta afka tana salati.

Jinin ne nauyi biyu baƙi ƙirin d  kuma ja ya soma malalowa daga du wata ƙofa ta jikin Makafa da kw shure-shuren azaba kamar ran shi zai fita. 
   Da gudu aka saɓe shi akai hospital da shi cikin mawuyacin hali.

In banda safa da marwa babu abin da Hajiya Hafsatu da gaba ɗaya ta tsure ta fice a hayyacinta saboda kaɗuwa da yanayin da Makafa mijinta yake ciki.
    Idanuwanta fal ruwan hawaye da ke shatata tamkar an buɗe fanfo, a lokacin da za'a nuna mata kalar fari ace mata wane kala ne wannan, kai tsaye zata ce kalar baƙi ne, domin kuwa duhuwa kawai idonta ke ganin saboda tsantsar razani da ɗumauta da ta yi....

****
MARYAM
A hankali wani irin sabo ya soma shiga tsakaninta da wannan matar, ga wata nutsuwa ta daban da take samu a ɗan zaman da suka yi da ita, matar bata da matsalar komi babu ruwanta, ga yawan fara'a da firar da suke yi jifa-jifa ita da matar, wacce sunanta ya zauna raɗau a bakinta a yanzu tun daga lokacin da magana me ɗan tsayi ta fara haɗa su.
   
"Sannu." Maryam ta ce tana jifanta da kallon tausayi.

Jinjina mata kai matar ta yi tare da yi mata ɗan guntun murmushi.
  Daga sannan du ɗan lokaci haka Maryam zata kalleta ta ce mata sannu, wani sa'in kuma ta ƙara da "Ko kina buƙatar wani abu?."
   Sai tace a taƙaice.
"A'a bani buƙatar komi amma da zan samu ruwa da zan so."
   Aikuwa Maryam bata gajiyawa wajen ziryar siyo mata ruwan, kafin daga bisani ta sayo leda ɗaya ta aje mata tare da faɗin.
    "Du sanda kike da buƙata ki ɗauka ki sha."
Murmushi ne nuni da jin daɗi matar ta yi mata, wasu fararen ruwa na taruwa a cikin idanuwanta ta ce da Maryam.
   "Nagode sosai Ubangiji ya biya ki da lada, miye sunan ɗiyar tawa?."

"Ameen." Maryam ta amsa sai kuma ta ɗora da faɗin.
   "Maryam Noor." 
Wannan karon sai da matar ta yi tari me hale da jini guda-guda sannan ta ce.
   "Ma sha Allahu Noor yake ya sunanki, ga ki da haske na zahiri dana baɗini Allah ya albarka ce ki."

Maryam ta amsa da "Ameen nagode Allah ya baki lafiya kema."

Murmushi ta kuma yi sannan ta amsa da "Ameen, Rimsha, sunana."

   "Rimsha?." ta maimaita sunan kamar me tambaya, tana jin yayi mata sauƙi da kuma daɗin faɗa a baki.

Daga lokacin fira jifa-jifa ta soma shiga tsakaninsu, har aka gangaro yau da suka sake matsawa daga inda suka yada zango suka kwana a jiya, suka shiga unguwar ƙofar sauri akan titi me tsawo wanda ya miƙe shantal.

    Kallon Maryam Rimsha ta yi tare da faɗin.
    "Harna soma kewarki Noor."
   Ta faɗa da iyakar gaskiyarta.
    Da sauri Maryam ta juyar da kallonta saitinta, tare da taƙune fuskarta kaɗan sannan ta ce.
   "Kewata kamar ya kenan, bayan gani tare da ke." 

"A yanzun muna a tare amma wataƙila anjima kaɗan, ko yanzu ƙaddara ta sake raba mu kamae yanda ta haɗa mu."

    Wani dummm kan Maryam ya yi nan take jikinta ya soma yin sanyi ƙalau, wani abu ya soma yawo a jinin jikinta, ba zata ce ga yanda aka yi ma, sai samun kanta ta yi da kama hannayen Rimsha duka biyu ta saka idanuwanta cikin kamar me karantar wani abu, lokaci ɗaya wani haske siriri ya fito daga idonta ya shiga cikin idon Rimsha.
   Da wata iriyar siririyar murya Maryam tace da ita.
    "Ƙaddarar data haɗani da ke ba zata taɓa bari muyi nesa da juna ba, ina iya hango duhu da hasken da ke baibaye da rayuwarki wanda hakan ke alamta min tabbas akwai wani lamari tare da ke, akwai ƙalubale tare da rayuwarki, ina son sanin miya assasa wannan duhuwar a tare da ke, wacce ta kusa gauraye sauran hasken da ke zagaye da ruhinki."
    Hawaye ne masu zafi suka soma silalowa daga idanuwanta, ta saka hannayenta duka biyun ta dafe na Maryam sannan tajata suka isa wajen wata kwana daba kasafai mutane ke giftawa ta wajen ba, a ƙasa suka zauna, Rimsha     ta nitsa idanuwanta a cikin na Maryam sannan  ta soma faɗin.
   "Rayuwata wata aba ce me kama da kaloli guda biyu, misalin Baƙi da fari.
    Ni kaina bana iya ƙayyade irin ƙalubale da ƙaddaririn dana rayu cikin su, bazance miki na kasance cikin farinciki ba na tsayin lokaci haka kuma bazance miki na kasance cikin baƙinciki, ababe biyu na tserayya tare da gugar juna a cikin rayuwata, wato farinciki da baƙinciki, ki nutsu ki kuma buɗe kunnuwanki da kuma zuciyar ki ki saurari tarihin rayuwata, wataƙila ke ki iya gano abin da ni na kasa ganowa tun usul, wataƙila ke ki iya banbance tare da fitar da baki a cikin farin da ke lulluɓe da rayuwata."
     Buɗe baki Maryam ta yi tare da shanye girman idonta kamar me jin barci ta sake matsar tattausar fatar tafin hannun Rimsha tare da bata  dukanin nutsuwarta sannan ta ce.
    "Ina tare da ke, ina saurarenki, kuma zan fahimce ki fiye da yanda kika kasa fahimtar kanki."
     Ɗauke ƙwallar idonta Rimsha ta yi tare da sakin murmushin da baida alaƙa da farinciki sannan ta fara da faɗin....✍🏻
Masu ƙaratu kuci gaba da kasnacewa tare da ni don jin yanda zata kaya cikin wannan zazzafan labari.

Nice taku har kullum.

M.STAR AMANAR BILYN ABDUL CE.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol