Free chapter · Read without an account

5:The Uncle she trusted

by Hauwa Jibrin Sulaiman · FADIANA

Da daddare gidansu Rahma ya cika da wani irin natsuwa mai daɗi. Hasken chandelier ɗin da ke saman dining area ya haskaka teburin da aka shirya abincin dare a kai, yayin da ƙamshin miyar kuka da aka haɗa da nama ya bazu ko’ina cikin parlon, kana gani kasan na masu kudi ne dai


Rahama ce zaune a gefen mahaifiyarta, sanye da wata riga mara nawi, gashinta a rufe cikin scarf mai laushi. Tun lokacin da ta fito daga sama ta canja kaya, take ta ba Mammy labarin abubuwan da suka faru da ita tun kafin ta gama exams, har zuwa tafiyar da ta yi


Baban kuwa, yana zaune a ɗaya gefen table, yana sauraron ’yarsa da murmushi a fuskarsa


“Baba, wallahi da ka ga yadda muka sha stress a lokacin exams, da ka tausaya mana. Sometimes, lecturers ɗin mu kamar suna ganin ba mu da wani abu da za mu yi a rayuwarmu sai karatunsu” Rahama ta faɗa, tana ajiye cokalin da ke hannunta dan ta iya bayyana abin da take nufi da kyau


Baba ya yi dariya a hankali “To ai karatu ba wasa ba ne Rahama balle ku yanzu ai naku da sauki, mu namu ai yafi naku”


“Baba your own stress is different! Wallahi namu wani level ne, wani lokaci sai ka ga lecturer ya ba mu assignment kamar zai biya mu kuɗin aikin da muka yi, the worst part is, idan ka gama ka kai masa, sai ya ce ba haka yake so ba”


Mammy ta girgiza kai, tana murmushi “Amma duk da haka kin gama Alhamdulillah, wannan shi ne abin da ya fi muhimmanci”


“Alhamdulillah Mammy wlh idan na tuna ranar da muka kammala komai, sai na ji kamar wani dutse ne aka sauke daga bayana. No more lectures, no more assignments, no more rushing to meet deadlines!”


Murmushi tayi “Finally, your daughter is free!”


Dariya duk suka yi


“Free from school, maybe” Baba ya faɗa yana murmushi “ba zaki wuni kina bacci kamar yadda kika saba ba, ga Mammynki nan zata baki aikin yi”


Rahama ta ɗan daure fuska “Baba please, haba mana at least na samu hutu amma sai kawai a bani wani sabon syllabus”


Mammy ta yi dariya sosai har sai da ta ajiye cokalin “Ka kyale ta tunda yau ne ta dawo gida, bari ta ɗan huta”


“Exactly Mammy!” Rahama ta faɗa, tana jingina da kujerarta “At least someone understands me in this house”


Baba ya girgiza kai yana murmushi, Rahama ta ce “By the way Mammy, abincin da kika yi yau ya fi wanda ake ba mu a makaranta sau dubu, wallahi da kin ga irin abincin da muke ci sometimes, da kina aika min da tuwo kullum”


“Ohh naga ta kaina da shirmenki wlh” Mammy ta faɗa “Duk abin da aka ba ki sai kin sami abin faɗa a kansa”


“Because food is important Mammy. Especially when you’re a student”


Suka sake dariya


Bayan sun gama cin abinci, ta taimaka wa Mammy wajen tattara wasu abubuwan da ke kan table duk da cewa mahaifiyarta ta ce ta bar su


“Ki je ki huta Rahama! Kin yi tafiya, kuma na san kina buƙatar bacci da wuri”


“Okay Mammy but tomorrow, I’m not doing anything. I want to sleep till whenever I want”


“Za mu gani” Baba ya faɗa yana murmushi


Rahama ta shagwabe fuska “Baba don’t start plssss!”


Ta yi musu sallama da fara’a, ta sumbaci forehead na Mammy, sannan ta nufi matakalar bene tana jin daɗin dawowarta gida


Bayan ta shiga ɗakinta, ta rufe ƙofar, sannan ta tsaya na ɗan lokaci tana kallon cikin ɗakin. Komai yana nan yadda ta bari


King size bed dinta, expensive curtains nata, littattafan da aka jera a shelf, har da ƙaramin teddy bear ɗin da Mammy ta saya mata tun tana ƙarama. Ta yi murmushi, sannan ta fara shirya kayanta na boxes da aka ajiye tun da rana


Bayan ta gama, ta ɗauki sleeping dress ɗinta ta shiga bathroom. Ta yi alwala, ta dawo ta yi sallah, sannan ta zauna a gefen gado tana karanta addu’o’in da ta saba yi kafin bacci


Da ta gama, ta gyara pillow ɗinta, ta kashe babban hasken ɗakin, ta bar ƙaramin bedside lamp yana haskakawa a hankali


Ta kwanta, ta jawo blanket ɗin ta rufe jikinta har zuwa kirjinta “Alhamdulillah” ta furta a hankali “Ya Allah, na gode da komai. Ka sa sauran rayuwata ta kasance mafi alheri fiye da abin da ya wuce” Ta juya gefe ɗaya, ta lumshe idanunta


Fuskan mutumin ne ya faɗo mata a rai


Gashi dogo, kyakkyawa, mai tsananin girman kai, sanye da farar shirt, yana kallonta da wani irin fushi kamar ta aikata laifin da ba za a taɓa gafarta mata ba


Rahama ta buɗe idanunta da sauri “Ugh!”

Ta juya ta kwanta da bayanta, tana kallon ceiling ɗin ɗakin “Why am I even thinking about that man?”


Ta daure fuska, ta jawo blanket ɗin ta rufe kanta gaba ɗaya


“Stupid man wlh ban taɓa ganin mutum mai masifar girman kai irin wannan ba. Kai fa ka tsaya a hanya, amma ka mayar da ni kamar ni ce na zo duniya domin in ɓata maka rai”


Ta ɗan yi shiru sai kuma ta tuna da yadda ya yi mata barazana a cikin jirgin


Ta buɗe idanuwanta daga ƙarƙashin blanket ɗin “Wai har ya ce zai tsole min ido fahh? Haba! Who does he think he is?” Ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta fitar da kanta daga cikin blanket ɗin


“Anyway, I don’t care ba zan sake ganinsa ba, kuma ko na sake ganinsa, zan yi kamar ban taɓa saninsa ba”


Ta jinjina kai kamar tana tabbatar wa kanta da wannan shawarar “Goodnight, Rahama” Ta juya gefe, ta rufe idanunta da ƙarfi, duk dan tayi baccin


Bayan wasu mintuna, numfashinta ya fara daidaituwa, jikinta ya yi laushi a kan gadon, bacci ya ɗauke ta


Washegari da sassafe alarm nata ne ya farkar da ita, agogon gefen gadonta ya nuna ƙarfe biyar da rabi lokacin da ta buɗe ido, ta lumshe su kuma, ta juya other side sai ta jawo blanket ɗin ta rufe kanta


“Five more minutes” ta rada muryarta cika da kasala


Ta tuna cewa ba’a makaranta take ba, babu lecture da za ta makara, babu assignment da za ta yi ta gaggauta gamawa, babu wanda zai yi mata waya yana tambayar inda ta tsaya


Murmushi tayi  “Alhamdulillah for this beautiful life!”


Ta zauna a kan gadon, ta miƙa hannayenta sama, ta yi gyaran murya, sannan ta sauko daga gadon tana jin daɗin sabon freedom ɗin da ta samu


Bayan ta gyara gadonta, ta shiga bathroom ta yi wanka, ta yi alwala, sannan ta yi sallah duk da yau ta makkara, ta dade tana karatu can ta sanya wata doguwar riga, ta ɗaure kanta da vintage, ta shafa lotion, sannan ta ɗauki wayarta tana duba mssgs da suka shigo mata


Wasu daga cikin ƙawayenta sun tura mata msgs na taya murna da dawowarta gida


Ta amsa musu, ta ajiye wayar, sannan ta fito daga ɗakinta


A ƙasa, ta samu already an fara ayyukan safe, an gyaran falon, ana tattara wasu abubuwa, ƙamshin Arabian tea da soyayyen ƙwai yana fitowa daga kitchen


Rahama ta sauko matakalar bene tana waƙa a hankali “Mammyyyy!”


“Na’am, my baby” mahaifiyarta ta amsa daga kitchen


Rahama ta shiga tana murmushi

“Good morning, my beautiful mother”


Mammy ta juyo, ta kalle ta daga sama har ƙasa “Good morning, pretty! Kin tashi lafiya?”


“Alhamdulillah! And I’m veryyy hungry”


Mammy ta girgiza kai “Ke da abinci dai bs ku rabuwa, zo ki zauna, na yi tea”


Rahama ta ja kujera ta zauna, ta ɗauki cup ɗin da aka ajiye mata


“Thank you Mammy, wlh if I had known that staying at home feels this good, da ban yi ta complain ɗin makaranta ba balle naje”


“Da kin zauna kina kallon bango kenan? Karatu yana da muhimmanci Rahama. Kuma yanzu da kin gama, ya kamata ki fara tunanin abin da za ki yi next”


Rahama ta ɗan ɗaga gira “Mammy har yanzu ban huta ba, akwai time”


“Ban hana ki hutawa ba, Ina so ne kawai ki kasance da shiri, rayuwa ba ta tsaya saboda kin gama karatu ba”


Rahama ta gyada kai “I know Mammy, In Sha Allah, zan yi amfani da abin da na koya wajen neman abin da zai amfani rayuwata”


Mahaifiyarta ta yi murmushi, ta shafa mata kai “Allah Ya sa albarka”


“Ameen”


Bayan ta gama breakfast, ta taimaka wa Mammy da wasu ƙananan ayyukan gida, sannan ta koma falon ta zauna tana duba wayarta


Da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe, suka ji ƙarar motar da ta shigo harabar gidan


Wani daga cikin ma’aikatan gidan ya fito domin buɗe ƙofa, motar ta shigo ta tsaya a gaban falon


Rahama tana zaune a kan sofa, tana duba wasu hotunan da ƙawayenta suka turo mata, lokacin da ta ji muryar mutumin daga waje


“Assalamu alaikum! Ina mutanen gidan nan?”


Aiko ta ɗago kanta da sauri, murmushi ne ya mamaye fuskanta “Uncle Fahad!”


Ta miƙe daga kan sofa, ta ajiye wayarta, ta nufi ƙofar falon tana murmushi


Uncle Fahad ya shigo cikin nutsuwa, sanye da wata babbar riga mai kyau, agogon hannunsa yana sheƙi, A fuskarsa akwai murmushi irin na mutumin da ya saba samun tarba mai kyau a duk sanda ya shigo gidan


“Ah-ah! Ga baby girl ɗinmu nan!”


Rahama ta ruga ta rungume shi

“Uncle! You didn’t even tell me you were coming!”


Uncle Fahad ya yi dariya, ya rungume ta da hannu ɗaya, ɗayan hannunsa yana shafa bayanta “Na ce bari in zo in ga ko kin dawo da gaske, ko dai Mammy ce ta ƙirƙiro labarin cewa ’yarta ta dawo”


Rahama ta fara dariya, ta janye jikinta tana kallonsa “Uncle wai har sannan kana min irin wannan wasan?”


“Ohh baby, har sannan baki gane wasa da kuma abun da ba wasa bane” 


Ta bugi hannunsa a hankali cike da shagwaba  “Stop teasing me!”


Uncle Fahad ya fara dariya, sannan ya kama kafadunta, yana kallon fuskarta da kulawa

“Amma kin yi kyau fah, kin ƙara girma, last time da na gan ki, kina ta complain ɗin exams, yanzu kin zama graduate no more complain”


Rahama ta ɗaga kanta cike da alfahari “Of course! Your niece is officially a graduate now”


“Alhamdulillah! Allah kawo miji Nagari”


“Ameen, Uncle”


Bayan sun zauna ta fara basa lbr sai dai da ta kusa ambaton abin da ya faru a jirgi, sai ta tsaya

Uncle Fahad ya lura da sauyin yanayin fuskarta

“What happened? Why did you stop?”


Rahama ta girgiza kai, tana ƙoƙarin danne murmushin da ya so bayyana a fuskarta


“Nothing Uncle, just something annoying that happened during the flight”


Fahad ya ɗan karkatar da kansa “Something annoying? Me ya faru?”


Rahama ta yi shiru na secs, sannan ta fara ba shi lbrin mutumin da suka yi karo a airport, yadda ya yi mata magana, da yadda ya ci gaba da yi mata barazana bayan ta zubar masa da abinci


Da take ba shi labarin, tana nuna masa yadda mutumin ya yi mata tsawa, tana kwaikwayon yanayin fuskarsa har ta sa Uncle Fahad ya yi murmushi


“Wai har ya ce zai tsole min ido, Uncle! Can you imagine? A cikin jirgi fa!”


Uncle Fahad ya girgiza kai, yana murmushi

“Some people have anger issues amma ke ma kin san halinki, kin san yadda kike zama idan kina cikin wani shauki, kina manta da duk abin da ke kusa da ke”


Rahama ta zaro ido “Uncle! So you’re blaming me?”


“A’a ban ce haka ba, Ina cewa dai ya kamata ki riƙa lura da abubuwan da ke kewaye da ke, amma shi ma bai kamata ya yi miki magana irin haka ba”


Rahama ta ɗan yi shiru “Exactly! That’s what I’m saying. I already apologized, but he behaved like I had committed a crime”


Uncle Fahad ya gyada kai, ya ɗauki cup ɗin tea da aka kawo masa, ya sha kaɗan

“Ki kyale shi, ba kowane mutum ne ya cancanci ki ɗauki maganarsa a zuciya ba, wasu mutane za su ɓata miki rai ne kawai idan kin ba su dama”


Rahama ta yi shiru na ɗan lokaci, tana tunanin maganarsa, daga ƙarshe ta yi murmushi “You’re right, Uncle I shouldn’t let him ruin my mood”


“That’s my girl”


Ya ɗan taɓa kumatunta cikin wasa, ta ture hannunsa tana dariya “Uncle, I’m not a baby anymore!”


“A idona kuwa, har yanzu ke ƙarama ce”


“That’s not fair!”


Uncle Fahad ya yi dariya, sannan ya fara tmbyrta ta game da shirinta na gaba. Ya tambaye ta ko tana da wani tunanin neman aiki, ko tana son ci gaba da karatu, ko tana son fara wani abu nata na kanta 


Rahama ta faɗa masa cewa har yanzu tana son ta ɗan huta kafin ta tsara abin da za ta yi


“That’s fine” ya amsa “Amma ki riƙa tunanin mai kyau, kin yi karatu, kuma ina son ki ga amfanin wannan karatun a rayuwarki, kada ki dogara da mutane su tsara miki rayuwa”


Rahama ta kalle shi da murmushi.

“Uncle, you always know what to say”


Fahad ya yi murmushi, ya jingina da kujerarsa “Domin ina son ki ga komaii perfect, kina cikin yaran da nake alfahari da su, kuma ina son ki kai inda kike burin kaiwa”


Ta ji daɗin kalamansa sosai. A gare ta Uncle Fahad ya kasance ɗaya daga cikin mutanen da za ta iya zuwa wurinsu idan tana da matsala, mutumin da ba ya gajiyawa wajen yi mata nasiha, ba ya raina burinta, kuma kullum yana nuna mata cewa yana son ta yi nasara


“Thank you Uncle” ta faɗa a hankali “wlh I really appreciate you”


Uncle Fahad ya kalle ta na ɗan lokaci, sannan murmushi ya bayyana a fuskarsa


“Ba sai kin gode ba Rahama! Ina son ki ne, that’s all”


A wannan lokacin ne Baba ya shigo falon daga ɗaya side na gidan

“Ah, Fahad! Dole naji muryanka tun daga waje tunda ga Rahama ta dawo”



Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol