Free chapter · Read without an account

Chapter 20

by Salis M Reza · MIJIN AMAL

MIJIN AMAL 

Chapter 20

Bayan sun zauna Likitan ya fara musu bayani "Anyi wa ƴarku aikin ƙoda gashi bata warkeba ta sake faɗuwa, wanda hakan ne ya haifar da samun matsalar ɗaya ƙodar da ta rage mata. Abun ya bani mamaki, ta yaya za'a yiwa mutum aiki bai warke ba a sallame shi har kuma ya sake faɗuwa? Kun san illar yin hakan kuwa. Babban haɗarin da mutum zai iya samu idan yana da ƙoda guda ɗaya kacal shine rashin samun madadin ƙoda (back-up) idan waccan ƙodar guda daya ta samu matsala. Ga wasu daga cikin manyan matsalolin da za su iya faruwa. Na ɗaya hawan Jini. Ƙoda tana taimakawa wajen daidaita jini, idan ƙoda daya ce, tana iya yin aiki fiye da ƙima, wanda hakan kan iya jawo hawan jini a tare da mutum. Na biyu. Ragewar aikin ƙoda. Saboda yawan aiki da ƙoda ɗaya ke yi na tace jinin jiki ɗan Adam gaba ɗaya, tana iya fara gajiya ko raguwa da aiki bayan dogon lokaci, musamman idan mutum yana da wasu matsalolin kamar ciwon suga ko ƙiba da kuma aikin da yafi ƙarfin na wannan ƙoda dayar, ko wani babban ciwon. Na uku. Fitar wani launi a Fitsari (Proteinuria) Wannan alama ce da ke nuna cewa ƙodar tana fuskantar matsin lamba wajen aiki. Na huɗu. Buguwa wato jin rauni. Idan mutum ya samu rauni alhalin yana da  koda guda daya (misali ta hanyar hatsari ko dambe), babu wata kodar da za ta taya ta aiki, wanda hakan zai zama babban haɗari ga rayuwarsa. To yanzu wannan matsalar ce ƴarku ke ciki. An mata aikin ƙoda wanda an cire mata ɗaya. Ko warkewa batayi ba gashi dayar ta samu matsala. Sannan abun tashin hankalin shine ƴarku tana ɗauke da cutar hiv wanda itace ta sake taimakawa wajen baiyanar wannan cuwokan na jikinta. Sannan kuma..." Ai kafin yaci gaba Mama ta kwaɗa wani uban ihu tana kirawa kanta shiga tara. Wanda shi kansa Yaya kallon likitan kawai yake ya kasa magana saboda tashin hankali. Likitan ya ce "Mai ya faru? Baku san tana da cutar bane? Ko kuma baku san an mata aikin bane?" Ya tambaya shima da mamakin. Mama ta ce "Likita cutar ƙanjamau fa? Likita kuma a jikin Amal? Innalillahi wa innalillahi raji'un, wallahi ƙarya ne, ba dai Amal ba, ta yaya a garin yaya, ko dai mijij nata ne ya saka mata". Likitan ya ce "Ina mijin nata yake?" Yaya ya ce "Ina zuwa bari na kira shi. Yaya ya nemo number Yasir jikinsa har rawa yake ya kira. Sai dai mata mai turancin MTN ta sanar da shi cewar an kashe wayar da yake kira. Ya sake kira matar dai ta sake tabbatar masa. Likitan ya ce "Ya kamata mijin nata yazo, domin dai shi ya dace yayi bayani, Kuma muddin haka ne sai dai ko a gurinsa ta samu. Likitan ya bawa Yaya takardar result ɗin domin ya karasa karantawa saboda akwai sauran ciwon dake damunta. Yaya ya riƙe yana kallon Mama da ta ke ta kuka. Ba tare da ya duba ba ya ce "Yanzu Dr meye abun yi?" Ya ce "Yanzu ƙoda za'a nemo a saka mata cikin gaggawa idan anyi sa'a tana da rayuwa a gaba zata tashi, amma dai zaiyi wahala gaskiya. Daga haka suka fito daga ofis ɗin.

Ai kuwa sauran na ganinsu suka yo kansu ganin Mama na kuka. Suna karasawa kuwa ta ce "Mun shiga uku mun lalace, Yasir ya cuce mu, ya sawa Amal cutar ƙanjamau sannan ya cire mata ƙoda ɗaya yaje yayi kuɗi da ita". Take kowa ya ɗauki salati suna direwa, suna Kuma kallon Yaya alamar tabbacin maganar daga bakin sa. Ɗaya daga ciki ta ce "Cutar ƙanjamau fa Mama? Hiv ba kenan?" Mama ta sake rushewa da kuka. Nana ma ta fashe da kuka tana faɗin shikenan muma duk sai an gwada mu, Allah ya tsinewa wannan Yasir ɗin. Anty Maryam dai gurin Yaya ta karaso ganin yadda ya kafe takardar da kallo ta ce "Wai da gaske ne?" Ya ce "Da gaske, amma ta yaya Yasir zai iya haka, duk yadda yake son yarinyar nana, duk yadda yake tsoron taɓa abun haram, gashi na kira shi bata shiga ya kashe waya. Abun da ya ƙara ɓata min rai ma ashe cikin da tayi ɓarin ma zubar wa aka yi, har ma mahaifarta ta samu matsala". Anty ta saki salati tana toshe baki cikin tashin hankali. Tace "bayan hiv da cire ƙodar ma. Yaya ya fita daga asibitin ya nufi gidan Yasir ɗin. Ransa a mugun ɓace. Tabbas yau zai tabbatar masa da cewar shi yayan sa. Sai dai koda yaje gidan nasa baya nan. Ya je shagonsa nan ma baya nan. Ya wuce shagon Ali, shima yace bai zo ba. Haka dole ya dawo asibitin ya samu ko numfashi mai kyau Amal bata yi, gata nan a kwance kamar gawa. Ya samu su Mama suna ta kuka, hankalin kowa a tashe. Nan aka fara neman wanda zai bada ƙoda. Itama Mama ta tsufa babu damar ta bada tata. Nana kuma tana ɗauke da juna biyu wanda hakan ba mai yiwuwa bane. Shi kuma yaya dama tun ba yanzu ba yana da matsalar ƙoda ɗaya, yanzu haka ma akan magani yake, shi yasa yake ƙara tausayawa Amal ita da yanzu ba ko ɗaya. Hakan yasa yace a samo masa na sayarwa zai saya. Sai dai likitan ya faɗa masa adadin kuɗin da zai iya biya masu yawa ne. Koda yaji kuɗin bashi da su. Amma zai kai kukansa gurin iyayen gidan sa, yasan za'ayi. Ai kuwa take ya ɗauki waya ya fara kira. Yace da likitan a bashi awa biyu. Ya shiga matarsa kenan saƙo ya faɗo masa. Hakan yasa ya tsaya yana karantawa. Bayan ya gama. Yasa wayar a aljihu yaja motar yayi gaba da gudu. Sai dai kafin Yaya ya tafi ya roƙi da su Mama da dan Allah kar su faɗawa kowa. Kuma su kwantar da hankali in sha Allah za'a mata komai. Cikin faɗa Mama ta fara zaginsa harda Yasir ɗin akan wallahi ba zasu haƙura ba, cutar hiv da aka ce ba'a warkewa, shine yake cewa suyi hakuri. Haka dai dole ya tafi. 

Yana fita kuwa Nana ta shiga gurin likitan akan suma duk a duba su da ita da Mama saboda hankalinta ya kasa kwanciya. Kana kallon Nana kasan a tsorace take. Likitan ya kwantar mata da hankali ganin harda kuka. Sai da ya tabbatar ta natsu kafin yasa aka gwada su ita da Mama. Yace "Idan result ɗin ya fito zai faɗa masu". Ƙasa da awa biyu kuwa Yaya ya dawo. Nan take aka shiga da ita gurin aikin ƙodar. Cikin ikon Allah kuwa aka mata aikin lafiya lau. Har washegari bata farka ba, kuma Yasir bai zoba, number sa bata shiga. Nana kuwa ta shiga ofis ɗin likita ya kai sau goma yana ce mata bai fito ba. Daga karshe dai yace mata sai gobe zai fito, wato yau. Misalin ƙarfe tara na safe Amal ta buɗe ido. Bakinta ya bushe sosai, ga shi ta kasa magana sai binsu da kallo. Tana ta raba ido a ɗakin ba'a san wa take nema ba. Nan likitan ya faɗa musu abun da zata iya ci, kuma kar wanda yayi mata magana koda kuwa sannu ne har sai idan itace ta fara magana. Koda result ɗin su ya fito ya tabbatar musu da cewa basu da ita daga ita har Maman. Hakan yasa suka sake ɗora faruwar hakan akan shi Yasir ɗin ne ya goga mata. Har kwana bakwai babu Yasir babu labrinsa. A kwana na goma ne Yaya yake faɗa musu cewar Yasir baya gari. An sauya masa gurin aiki izuwa Faransa tun washegarin ranar da aka kawo Amal asibiti. Kuma number sa bata shiga saboda ya sauya layi, shima abokinsa Ali ne yake faɗa masa. Gaba ɗaya suka kalli juna Amal da izuwa lokacin ta kan danyi magana gajere. Tun da ta farko taga bata ganshi ba, sai ta bari ko dai ya saketa ne. Kuma har lokacin bata san asalin abun da yake damunta ba, banta aikin da aka mata na ƙirji. Mama ta ce "Yana Faransa hankalinsa kwance bayan ya sawa ƴata cutar ƙanjamau, kuma ya cire mata ƙoda ɗaya, shine shi yake cen yana rayuwa abunsa". Ta faɗa cikin fitar haiyaci ta manta da shradin likitan, domin abun ya bata mamaki. Faransa fa. Amal ta kalli Mama. Sai ta kalli Yaya da shima ita yake kallo. Ta ce "Waye yake da ƙanjamau? Yasir ko dai ni?" Ta faɗa a hankali. Mama ta ce "Kece kike da ita, shine dalilin da yasa ya ɓoye ki a gidan sa yake ta cutar da ke, sannan ranar da kika kwana a asibiti ma ƙoda ɗaya suka cire miki, yaron nan ya cuce mu, Allah ya kwashe masa albarka". Nan Mama ta faiyace mata Komai. Amal ta rikice tana girgiza kai domin sam bata yarda ba. Ta ce "Mama ya ce min faɗuwa nayi jini ya taru a ƙirji na kuma aka min aiki. Sannan shi da wannan likitar sun ce min wai ɓarin da nayi ne ya haifar min da kamuwa da sabuwar cutar, kuma an bani magani ina sha, sannan..."  "To ɓarin ma da kike faɗa kinyi zubar miki da cikin yayi. Wallahi wannan yaron yaci amanar yarda, ya zalunce ki. Kuma abun da zai sake tabbatar miki da hakam shine tun da ya san an gano gaskiya bai zo ba, kuma bai kira kowa ba. Gashi yanzu ɗan uwansa na tabbatar da cewar yana kasar waje abunsa. Dan haka ki cire shi a ranki, idan aka sallame mu kawai zamu je kotu mu shigar da ƙara sai an bi mana kadin zaluncin nan wallahi". Amal tayi shiru wani irin zafi na ruruwa a zuciyarta. Take ta faɗa tunanin farkon faruwar abun. Idan bata manta ba. A ranar da suka je amsar result taga likitar a rikice, kuma ita kanta a lokacin bata gamsu da bayanan ba, amma ta yarda ne sabo da shi. Ta tuno yadda ya daina haɗa shinfida da ita, ya samo mata mai girki, baya cin abincin hannunta. Bata taɓa kawowa wannan ciwon bane. Sai ta tunano lokacin da tazo zata rungume shi ya kauce. Sai kawai ta saki wani ihu mai ƙarfin da yasa gaba ɗaya suka tsorota. Ta fara wani irin zabura tana ƙoƙarin jiwa kanta ciwo. Tana faɗin "Ina Yasir ɗin, a nemo mata shi yazo ya faɗa mata abun da tai masa. Shin soyayyar ce laifi ko kuma yardar da tayi da shi, ko bashi amanr rayuwata da tayi ce laifi. Shin tayi kuskure ne da ta mayar da shi komai nata, dan Allah a nemo mata shi tai masa wannan tambayr. Mai zai sa ya saka mata hivvvvv"? Ta karasa kalmar da wani irin tsayi sai ga jini na fitowa daga bakinta. Hatta ciwon da ke kirjin nata na ma ta fama shi jini ya keyi. Matan dake ɗakin ma duk da sun riƙe ta amma abubuwan da take faɗa ta basu tausayi. Haka suka dinga kiran likita. Gaba ɗaya ta fita a haiyacinta idan ta tuna da cewar wai Yasir ne yayi mata baka. Yasir dai wanda bayan shi bata taba kallon ko wanne namiji a matsayin Namiji ba. Mutumin da a kullum take ɗauka shine rayuwar ta, wanda ko mahaifiyarta bata jin ta kai shi sonta. Yasir dai mijin ta, Mijin Amal, abokin rayuwata. Gaba ɗaya zafin da take ji na wannan yaudarar da cin amanar ya kori zafin ciwon da take ciki. Har wani ƙaramin hauka ne ya hau kanta. Sai da Hafsah ma tazo asibitin abun ya sake tashi. Domin rungumeta tayi tana kuka tana tambayar ta mai tai wa Yasir a duniya, tana jinjiga hafsa akan ta faɗa mata. Soyayyar ce laifi ko kuma yardar, ko kuma zama da tayi da shi duk dad'i da wahala. Ita kanta Hafsa kuka take tana jinjina halin maza. Idan har Yasir zai iya yiwa Amal haka to tabbas auren ma abun tsoro ne. Kwana goma sha shida suka kwashe a asibitin nan suna jinya Kafin aka sallamo su. Izuwa lokacin ta warke sai ɗan kaɗan a gurin aikin. Duk Yaya ne ya dinga biyan komai. Hatta maganin hiv ɗin ma da ake bata shi yake biya. Sannan duk wata ance tazo ta dinga amsar magani. Da tace ba zata sha komai ba gara ta mutu. Amma Mama da sauran yan uwa harda Anty Maryam suke ta bata baki. Gaba ɗaya bata yiwa kowa magana. Kusan sati ɗaya kenana bata cewa komai sai bin kowa da ido da hawaye. Ta ɗaura aure da tunani, hakan ya ƙara taimakawa ramar jikinta, ta dawo kamar wata yar shekara sha huɗu. Sai ranar da aka sallame su da Yaya ya ce gidan ta zata je ko kuma gida zata koma. A lokacin kowa ya tsaya yana kallonta domin jin abun da zata ce. Ta ce "Gidan mu zanje". Ta faɗa a hankali kamar mai koyan magana. Ai kuwa ba wanda ya ce mata Komai, duk da yaya ya so ta tafi gidan ta, ko ba komai da aure a tsakaninsu har yanzu, haka suka wuce gida sai Nana ce da wasu suka je gidan ta suka kwaso mata kayan da zata saka.

 Tun daga ranar kuwa labari ya karaɗe unguwar da garin cewar Yasir ya shiga kungiyar asiri ne da matarsa. Yanzu ya sayar da ƙodarta daya da kuma wani abun nata. Labari dai ta ko ta ita harda gidan jaridu sun buga saboda yadda labarin ke ta trending a Social media. Babu ma wanda ya san a ina aka samu hotonsa da na Amal ɗin, lokaci tana gadon asibiti bakinta na jiki. Shi kuma aka ɗauko wani hotonsa a jikin motarsa. Sai aka haɗa hoton a haka, ake sanar da cewar yanzu ma haka baya ƙasar ya tafi Faransa, wasu ma na cewa yayi aure abunsa. Har tsawon sati ɗaya da daworsu labarin nan na yaɗuwa. Sai dai kuma Yaya da ya naimi alfarmar kar a kai maganar kotu. Mama ta ce to zai biya komai. yace ya yarda zai biya ko nawa ne. Shi zai biya, kuma idan ya dawo ya yarda shi da kansa zai kai shi. Amma Amal ta ce ita bata yarda a kai shi kara ba, kuma ko yaya ɗin ma karya ƙara kashe ko sisi akansu, kuma dan Allah idan yana son kansa da mutunci kar ya ƙara zuwa musu gida. Mama ta buɗe baki zatayi magana ta ce "Kema idan kin gaji dani zaki iya korata duniya da girma". Tana faɗa ta koma cikin dakin da ba Komai a cikin sa ko leda babu. Gadon ma bashi da maraba da tabarma. Tayi shiru tana kallon gefe ɗaya. Ta share hawaye. Tana jiyo Mama tana bashi hakuri. Hakan ya ƙara ɓata Mata rai ta fito a fusace ta ce "Hakurin me kika bashi? Na zage shi ne? Ko na ci amanar se? Ko na yaudare shi? To idan ya sake zuwa gidan nan wallahi sai na kashe shi". Ta faɗa da wani irin kuka na fita daga haiyaci. Tabbas soyayya bata mata adalci ba, soyayya ta kaita ta baro ta. Yanzu mai irin sunasa ma haushinsa take ji bare kuma wani ɗan uwansa. Ta kwanta a bakin ƙofa ta dinga kuka ta rasa ma kukn na menene. (Wannan shine dalilin da yasa Amal ta ce mijinta ɗan wuta ne.  wutar ma Hawiya. Saboda ko ganinsa ma bata sanyi, bata ma son tuna shi gaba ɗaya)

Hafiza ta sauke ajiyar zuciya ta na faɗin "Innalillahi wa innalillahi! Eh lallai dole Hadiza ki kasa ƙarasa wannan abun taikacin, wato shi yana ma Faransa abunsa. Kai Allah ya tsinewa wannan yaro, to shi ba ma iya Hawiya ba, in sha Allah a cikin wutar zai dauwama tsinanne shige. Ta fita daga littafin tana sake mamakin wannan abu. Sai lokacin ma ta kula da ruwan hawayen fuskarta. Ta share tana kokarin kiran Hadiza tana faɗin "Allah ya isar mana tsakninmu daku maza". Daidai lokacin Hadiza ta ɗaga. Ta ce "Hadiza Maza gaba ɗayansu ɗaya suke, ba na gari sai yan kaɗan. Na zo gurin da kika faɗa a littafin Mijin Amal, nima daga nan ba zan cigaba wallahi, dan ina ga zan iya haukacewa da tausayi domin ba zan iya jurar rayuwar Amal a gidan nan nasu ba. Sai ta tsinkayayo muryar Hadiza ɗin a sanyaye ta ce "Yanzu ni kuma na karasa karantawa gaba ɗaya". Ta ce gaba ɗaya har karshe?" "Eh har karshe na gama". " To ɗan iskan ya dawo yana sonta ko? Yana roƙonta ko? Ko kuma kuɗin ya ƙare ko? Da gaske yayi aure? Suna haɗuwa da Amal ɗin". Hadiza ta kwashe da dariya jin irin wannan tambayoyi. Ta ce "Ikon Allah, ga abu a wayar ki amma kina tambaya na". "Ni kawai ki faɗa mim, wallahi ina tausayin cigaba da karatun ne. Hadiza ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Hamm. Hafiza ba zan iya ce miki Komai ba sai kin karanta, amma dai akwai matsala da mamaki harda tashin hankali da rainin wayo. Ke dai kawai ki shiryawa ganin abun tausayi...📝

Shin wai da wani ido ma Yasir zai iya kallon Amal? Sannan da gaske yayi aure? Wai ma ya dace ace ya ɗauki har wannan lokacin bai ji lafiyar ta ba. Toma wai tun farko dama ba sonta yake bane?. Irin wannan yaudarar tsaf zai iya haukatar da mutum wallahi. Muje zuwa jin ya za'a kaya. Hiv

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol