Free chapter · Read without an account
Chapter 15
Na ɗan yi murmushi a hankali, ina ci gaba da aikin da ke gabana. Duk da gajiyar da nake ji, ban da zaɓin yin sakaci da aikin ba. Na san idan na yi sakaci, sai a mayar da maganar a kaina.
Kuluwa kuwa tana gefena, tana ta aikin nata cikin natsuwa. Mu kan yi wa juna magana lokaci-lokaci, amma ba mu cika surutu ba, musamman idan Gwaggo tana kusa.
Da muka kusa gamawa, na ɗauki kwandon rogon da muka gama shiryawa, na ajiye shi a gefe. A lokacin ne na hango Aisha da sauran ƙannenta. Su ma sun gama aikin abincinsu, suna zaune a gefe suna ta hira, babu alamar wata damuwa a fuskokinsu.
Na kalli Kuluwa, wadda take ƙoƙarin gyara wajen da muka yi aikinmu. Na matso kusa da ita, na ce, “Kuluwa, bari in je in ɗebo ruwa in yi wanka. Duk da dai na san ba ni da sabulun wanka, sai dai in watsa ruwa kawai.”
Kuluwa ta kalle ni, sannan ta ce, “Jira ni, bari in ɗauko hijjabina mu je tare.”
Tana gama faɗin haka, ta wuce ɗakinsu, ni kuma na nufi ɗakinmu domin ɗauko nawa hijjabin.
Da na shiga ɗakin, sai na nufi inda na ajiye jakar kayana. Na buɗe ta, na fara lalubo hijjabin da zan saka. Daga baya na zaro ɗaya daga cikin tsofaffin hijjabi nawa, wanda ya daɗe yana hannuna saboda yawan amfani da shi.
In ban manta ba, Zainab ƙawata ce ta ba ni hijjabin. Su Maman Zainab suna da ’yan uwa a cikin garin Kano. Wani lokaci ana kawo musu kayan da aka yi kwancen su, ko kuma waɗanda aka ba su kyauta. Idan kayan sun yi yawa, Zainab kan ba ni wasu daga ciki.
Duk da tsufansa, ina ƙoƙarin kula da hijjabin yadda zan iya. Haka ma sauran kayana. Wani lokaci idan na yi wanke-wanke, ko kuma su Mama suka ba ni Omo domin in wanke musu kaya, nakan yi amfani da damar wajen wanke nawa kayan ma.
Tun ina ƙaramar yarinya, Baba ya ɗora min aikin wanki, don haka na saba da kula da kayana. Ba na yawan barin su su yi dauda sosai, kuma duk lokacin da na samu sabulu, nakan yi amfani da shi wajen wanke su.
Wani abin da nake samu kuwa shi ne, idan na wanke wa mutane kaya, ba sa yawan tambayata ragowar Omon da aka ba ni. A haka nake samun abin da zan riƙa amfani da shi wajen wanke nawa kayan.
Shi ya sa, duk da ƙarancin abin da nake da shi, nake ƙoƙarin kula da kayana yadda zan iya. Idan mutum ya dube ni, ba lallai ne ya fahimci halin da nake ciki ba, domin na saba ɓoye damuwata a bayan murmushi.
Na ɗauko hijjabina, na fito daga ɗakinmu.
Da na fito, sai na tarar Kuluwa ta riga ta shirya, tana riƙe da bokiti a hannunta. Na ƙarasa wajenta, na gyara hijjabina, sannan muka nufi wajen ɗebo ruwa tare.
Muna cikin tafiya, kowacce riƙe da bokitinta, sai Kuluwa ta katse shirun.
“Rammu, kin ga yadda ranar nan ta yi zafi kuwa? Har jikina ya fara gajiya.”
Na kalle ta, na ɗan murmusa, amma ban ce mata komai ba.
Muna cikin tafiya ne muka hango Zainab, ƙawata, tana dawowa daga makarantar boko. Tana sanye da uniform ɗinta na makaranta, jakarta a kafaɗarta. Da ta hango ni, sai ta yi murmushi ta ƙara sauri domin ta ƙaraso gare mu.
“Rammu!” ta kira ni cikin murna.
Na ji daɗin ganinta, domin Zainab tana daga cikin mutanen da nake jin daɗin zama da su.
Zainab ’ya ɗaya tilo ce a wurin iyayenta, kuma Babanta mutum ne mai kula da iyalinsa. Yana sauke nauyin da ke kansa yadda ya kamata, don haka ba a hana ta zuwa makaranta ba.
A da, ni da Zainab tare muke zuwa makaranta. Muna tafiya tare, muna hira, muna kuma yin abubuwa da yawa tare. Amma tun daga lokacin da aka daina ba ni damar zuwa makaranta, rayuwarmu ta fara bambanta.
Zainab tana ci gaba da karatunta, ni kuma kullum ina cikin ayyukan gida. Da farko, tana yawan zuwa gidansu, amma daga baya ta rage zuwa, domin idan ta zo, sau da yawa sai ta same ni ina aiki. Ba na samun lokacin zama da ita ko yin hira kamar yadda muka saba a baya. A hankali, hakan ya sa ta daina zuwa gidanmu sosai, duk da cewa zumuncinmu bai yanke ba.
Zainab ta ƙaraso gare mu, tana murmushi. Ni ma na mayar mata da murmushin, domin na daɗe ban gan ta ba.
“Rammu, ina zuwa haka da bokiti?” ta tambaye ni, tana kallona.
Na kalli bokitin da ke hannuna, sannan na ce, “Mu je ɗebo ruwa ne ni da Kuluwa.”
“Au, to, shikenan. Amma dai idan kun dawo, ki shigo mu gaisa sosai. Na dawo daga makaranta ne yanzu, har yunwa nake ji.”
Na yi murmushi, na ce, “To, Zainab. Allah Ya taimaka.”
Ta juya za ta wuce, amma sai ta sake waiwayowa ta ce, “Rammu, kar ki manta fa!”
Na ɗaga mata hannu, ina murmushi.
“To, na ji.”
Zainab ta ci gaba da tafiyarta zuwa gida, ni kuma na bi ta da kallo na ɗan lokaci. A raina na yi tunanin yadda rayuwarmu ta bambanta. Ita tana zuwa makaranta, tana komawa gida ta samu abinci da hutawa, yayin da ni kuwa ko samun lokacin yin wanka sai na jira na gama ayyukan gidan.
Amma ba wai ina ƙin rayuwarta ba ne, a’a. Ina farin cikin ganin ƙawata tana samun damar karatu. Abin da nake ji a raina shi ne kewar zaman makaranta da kuma irin lokacin da muke kasancewa tare a da.
Ni ma burina shi ne wata rana in koma makaranta, in samu damar cimma abin da nake fata. Ina son in zauna a aji kamar sauran yara, in koyi abubuwan da ban samu damar koya ba, kuma in samu damar gina makoma mai kyau. Amma a halin da nake ciki, wannan buri ya kasance tamkar mafarki da nake riƙe da shi a zuciyata.
Kuluwa ce ta katse min tunanin.
“Rammu, ke kuma me kike kallo haka? Mu je mana, tun kafin rana ta ƙara zafi.”
Na juyo gare ta, na ce, “Ba komai, bari mu je.”
Muka ci gaba da tafiya, kowacce riƙe da bokitinta. A zuciyata kuwa, ina roƙon Allah Ya sa wata rana in samu damar yin karatun da nake mafarkin yi.