Free chapter · Read without an account
012
A haka rayuwa tayi ta tafiya yayin da nake fishi da iyayena saboda sun hanani zab'in raina, wai ai k'ara ma yanzu ina fitowa ina aikace aikace suma sai nayi niyya nakeyi, yayin da ba wanda yake ce mini ci kanki.
Baba ma yace na koma makaranta, nayi masa banza saboda nima a yanzu bana buqatar makarantar, yanzu kusan dik sati sai na had' u da khalil, indai mamanmu ta fita ni ma sai na fita, yanzu khalil ya canja mini waya na koma android inda ya siya mini har da power bank abuna, kuma a gidan mu ba wanda ya sani sai ni kad'ai.
Nidai naga umma tana ta siyan kayan kitchen ni dai ban tanka mata ba, ban tambayeta mai zatayi da su ba, ita kuwa dama ba magana take mini ba saboda ni nace nima ba zan manta ba.
Ban tab'a tunanin kuskure nake aikatawa ba hakan da nake, ummi tazo yafi sau nawa akan ta ganni amma ni yanzu na daina had'uwa da ita daga ni sai wayata sai khalil, sai numbern farida da jamcy wanda su suke d'orani a wannan turbar.
A wata ranar lahadi ummi ta had'u da su farida inda sukayi fad'a.
Farida ce ita da jamcy ke tafiya suna ta sauri ummi wadda ta shawo kwana ta kallesu ta hararesu.
"Ke dallah banza kina wani hararar mu wata uwar muka miki.
" Ban sani ba, banzaye kawai munafukai, ai nasan da hudubarku falmata take wannan abin, to wallahi ku sani dik wani zububi da ta d'auka har da ku za'a bawa shi.
Jamcy wadda ta k'araso ta d'auke ummi da mari, saurin dafe kuncinta ummi tayi yayin da ita ma ta d'aga hannu ta sauke mata mari, haka sukayi da fad'a, abinka da unguwar da suka taru aka rabasu.
"Aikin banza ita falmatar banza ce da idan munce tayi abu zatayi, ko kuwa 'yar mu da idan mun sakata zatayi farida ta fad' a tana hankoran dukan ummi.
" yo banza ce mana ummi tinda har zata iya bin shawarar da muke bata, saboda ita bata da kwakwalwa fad'in jamcy.
Haka dai da kyar aka rabasu kowa yayi hanyarsa.
Ummi direct gidan su falmata ta shiga, kofar d'akina ta tsaya tana dukan kofar iya k'arfinta.
Umma wadda ke tsaye ce take kallonta, k'arasowa tayi ta rik'eta tace"ummi lafiya kike dukan kofar nan.
"umma ki kyaleni, ban tab'a tunanin falmata bata da hankali ba sai yau, ashe dama kawaye take biyewa, su farida take biye wa ashe, yanzu mun taho hanya shi ne suke wani fad'ar maganganu.
" ya isa mana ummi, ki kyaleta dik abinda take jin daidai ne ki bar ta tayi, ke dai ina mai baki shawara kada ki d'auki irin halin falmata, ko da wasa kar na kuskura naga kin dauki wannan layin kinji ummi.
" D'aga mata kai ummi tayi alamun taji sai kuma ta juya ta bar gidan.
Haka dai rayuwar taci gaba da tafiya inda yau saura bikina sati biyu ciff ciff, dik wannan abu da akeyi ni bn tab'a sani ba sai wata ranar talata wadda a cikin watan july take, ranar da bazan manta da ita ba, rana ta farko da wanann lokacin na sake tabbatar da son da nakewa khalil.
Wanke wanke nake ummi ce ta shigo kasancewar ana hutun makaranta.
Tsugunnawa tayi da niyyar ta tayani, sai na kwace alamun banaso, murmushi ummi tayi ta mik'e ta bar wajen.
Sallamar da akayi dani je yasa ni jan mayafi na zan fita daidai lokacin da umma tace"gidan uwarwa zakije, ummi leka kiga wanene.
"to umma ta fad'a tana mik'ewa.
Ni kuwa a raina kira nake wai a hana mutum sukuni, kodan kawai nace ina son khalil, to son khalil ni yanzu ma na fara kuma bazan tab'a daina sonsa ba.
Sallamar aunty sanah ce kanwar mamanmu ta dawo dani duniyar da nake, mutanen lagos kenan, ita d'in ta kasance a lagos state take.
Tana gani na ta washe baki, nima fara'ar nakeyi na rungumeta.
D'agoni tayi tace"iyee ba shakka amarya har an fara gyare gyare kenan.
Shiru nayi ina tunanin maganar ta, amarya kuma na maimaita hakan a raina.
Umma ce ta k'araso taja hannunta ta barta anan tsaye tana tunanun maganar aunty sanah.
Ummi ce ta shigo da kaya bayan tafiyarta, akwatu ce babba.
Zata huce kenan ta finciko ta tace"ke ummi yaushe aka saka bikina, ba tare da an nemi izinina ba.
Ummi wadda tai mata kalloon sororo ta kyalkyale da dariya.
"Ko lallai sannu falmata ke yanzu dan iyayenki sun yanke miki hukunci shi ne kike fad'in ba'a nemi izininki ba,to ki

"Ko lallai sannu falmata ke yanzu dan iyayenki sun yanke miki hukunci shi ne kike fad'in ba'a nemi izininki ba,to ki sani idan baki sani ba bikin ki saura kwanaki goma sha hud'u ciff, ruwanki ne kiyi musu biyayya ruwanki ne kuma... Hucewarta tayi tana murmushi.
Inalillahi wa inna ilaihi rajiun ita ce kalmar da nake nanatawa saboda ni a tunani na an cuceni za'a rabani da masoyina.