Free chapter · Read without an account

014

by Aisha Muhammad Sanusi · BAUTAR ZUCI



Ina komawa d'akina sakon khalil na tarar inda yace muhad'u yau, jiki na b'ari na danna wayata nayi masa flashing, haka kuwa ya kirani, bayan ya gaya mini inda zamu had'u ya katse wayar.

"amir wai fa aure za'ayi mata ni narasa dalili da yasa mahaifinta baya k'aunata.

" kaine matsalar ai khalil abba ya fad'a yana zama, kai kace dole sai ka mallaki yarinyar nan, yarinyar nan bata san komai ba, ni da zaka bi ta tawa shawarar kawai ka kyaleta, idan har ka rabu d aita ita ma zata manta dakai.

Tsaki amir yaja yace" amma kai abba ciki ne wallahi, ana kokarin yadda khalil zai mallaketa kana fad'in a kyaleta.

"Kai ka kula sa ma, ai da kayi banza dashi, amir tasi muje ka bani shawarar daya kamata, jan amir yayi ya bar abba a zaune yana kallon hucewarsu.

Ummi gaba d'aya wunin ranar jin ta takeyi kawai dai gata nan ita, ta rasa taya ma take jin fad'uwar gaba har haka.

Ya kama gobe lahadi ranar d'aurin aurena ranar da bazan tab'a mantawa ba, ranar da na rusa kaina da kaina, ranar da na sakawa iyayena da abinda basuyi zato ba, ta dalikin abinda ya faru mahaifina ya kamu da cutar hawan jini.

Karfe 10 na dare na saci jiki na fit ba tare da kowa ya ganni ba, kasancewar kayan ummi dana gani a d'akina su na saka, dana fito dik sai suka d'auka ummi ce abinka da hijabin ta ne.

Ina fitowa nayi hanyar lungun su abba wanda khalil ya gaya mini anan zamu had'u da shi, sauri nake ta filfilawa kar wani ya ankare bana gidan a biyo sahuna.

A can cikin duhun bishiyar na hangesa, k'arasawa nayi daidai lokacin da ya bude hannunwansa ni kuwa kamar jira nake na fad'a ina kirjinsa ina sakin kuka.

Shi da kansa ya lallasheni ya goge mini hawaye na.

"Yanzu fa gobe ne aure na khalil, ya zanyi idan ban aureka ba.

" nima falmata ba zan iya rayuwa babu ke ba, shisa kawai na shirya mana wani abu.

Kallo na yayi yace"dama kince dik abinda nace kiyi shi zakiyi ko, saurin gyad'a masa kai nayi.

"yawwa babe so nake mu gudu mu bar garin nan, muje inda nake kasuwanci na indai har mukaje nan zamu samu wanda zai d'aura mana aure, kinga daga baya sai muzo mu gaya wa su baba munyi aure.

A wanannokcin da ya fad'i sai da naji fad'uwar gaba, domin ni ban tab'a kawo guduwa ba, sai da na nuna masa a'a sai dai me.

Hankadeni yayi gefe, ya ce"dama ashe dik soyayyar da kike mini ta karyace falmata, ashe bazance kiyi abu ba kuma kiyi, ashe akwai ranar da zan saka ki abu amma ki gagara yi.

A wannan lokaci da naga ransa yayi mugun b'aci a lokacin ne zuciya da kuma sharrin soyayyar da nakewa khalil suka rudeni suka tafka ni a wani kuskure na rayuwa wanda ban tab'a tunanin zan aikata sa ba, tabbas a wannan rana nyi dana sanin biyewa Ibrahim da nayi.

Haka inaji ina gani na biye masa muka huce tasha, ko sake tunanin gida banyi ba, muna zuwa mukaji ana Niger saura mutum biyu, haka muka shiga muna shiga motar ta tashi.

A wannan rana nayi nisa da iyayena, da mahaifata, k'annena, garin da na taso dik a wannan ranar nayi watsi da kowa da komai na kama Ibrahim.

A can kuwa gida kasancewar an riga an saki jiki da cewa ina d'aki ba wanda ya damu da ya duboni.

"Wai yanzu umma haka zaku saki baki kuyi shiru kuna kallon falmata tana wannan tijarar, aunty sanah take magana da umma.

" sanah ki kyaleta kawai, dika dika gobe ne ta tattara ta bar gidan ta tafi gidan mijinta, ita zataje taji idan har daidai takeyi ko kuwa ba daidai take aikatawa ba.

" Ai shikenan amma daiii, kiran da baba yayi mata yasa hirar tasu ta katse ta tashi ta tafi d'akin nasa.

Aunty sanah wadda ta fito daga d'aki ta kalli ummi wadda ke kwance a kan kujera ta takure tace" ummi lafiyar ki kuwa.

Ummi murmushi ta kak'alo tace"bakomai aunty, kawai ji nake banajin dad'i.

K'arasowa aunty sanah tayi tace"tohm allah ya baki lafiya, da ameen ta amsa ta mai da kanta ta kwanta yayin da kirjinta ke dukan uku uku, ta kuma rasa dalilin da yasa hakan ke faruwa da ita.

Mikewa aunty sanah tai tayi hanyar tsakar gida fik da a lokacin karfe 10 da arba'in dare ya ga ma yi. 

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol