Free chapter · Read without an account
WHEN LOVE MEETS REALITY
KADDARAR ZUCIYA
CHAPTER THIRTY-NINE: 39
WHEN LOVE MEETS REALITY
JIDDAAH BARKUM
———-
Daren farko na Inteesar a Abuja ya zo da wani irin sanyi da shiru mai cike da natsuwa, ta tura jikinta cikin bargo tana kallon silin ɗin ɗakinta, yayin da kewar gida da Daddy ke sake bijiro mata lokaci-lokaci, amma a gaskiya, akwai wani babban dalilin da ya sa zuciyarta ke bugawa tsakanin fargaba da farin ciki, tana jiran kiran masoyinta, idanunta suna kan wayarta da ke ajiye a gefen gado, tamkar tana magana da ita, kamar dai wayar ta san irin jiran da take yi, sai ga screen ɗin ya haska tare da kiɗan kira mai daɗi, ganin sunan wanda yake kiranta ya sa wani daddadan murmushi mai cike da shauƙi ya subuce mata, “Mi Amor…” Ta ɗaga wayar cikin muryar shagwaɓa mai taushi da sanyaya zuciya, daga ɗayan ɓangaren, Aliyu ya sauke nannauyan numfashi, muryarsa cike take da ƙauna da shauƙi, “Babygirl… Alhamdulillah da na ji muryarki, tun lokacin da jirginku ya tashi nake ƙirga daƙiƙai a agogona, na bar ki ne ki samu ki huta sosai, kin sauka lafiya? Fatan kowa yana nan lafiya?” Inteesar ta juya ta kwanta rigingine tana murmushi, yayin da take wasa da gashinta, “Lafiya lau, Mi Amor, Yaya Nana ce ta zo ɗaukana a airport, kuma komai ya tafi daidai,” ta ɗan yi shiru, sannan muryarta ta ƙara yin ƙasa, cike da kewarsa, “Amma wallahi tun yanzu na fara kewarka, gidan ya yi mini shiru da yawa,” Aliyu ya saki wata tattausar dariya, wadda ta nuna yadda kalamanta suka narke masa zuciya, “Haba, Babygirl ɗina, kin san cewa damuwarki kaɗai za ta iya sa na baro Katsina yanzu-yanzu in taho Abuja? Na yi miki alƙawari, duk lokacin da na samu sarari, zan zo in gan ki,” ya ɗan dakata kafin ya ƙara da cewa, “Don haka ki yi mini murmushi haka kawai, kin ji? Ki yi karatunki cikin kwanciyar hankali,” Inteesar ta cusa fuskarta cikin pillow tana dariya cikin farin ciki, “Zan yi ƙoƙarin jurewa, amma sai ka yi mini alƙawari cewa matsayina a zuciyarka ba zai taɓa raguwa saboda nisa ba,” Aliyu ya amsa cikin murya mai cike da gaskiya da ɗumi, “Na yi miki alƙawari, Babygirl, ke ɗin sashe ce ta musamman a rayuwata, wadda take ba ni cikakkiyar natsuwa,” ya ɗan yi shiru, sannan muryarsa ta ƙara yin ƙasa cikin yanayin nuna kulawa, “Babygirl… umm, zan…” Kafin ya ƙarasa maganarsa, Inteesar ta katse shi da sauri, tana turo baki gaba tamkar yana gabanta yana kallonta, “Za ka shiga gida, ko? Yanzu haka kana mota, ko?” Aliyu ya saki wani daddadan murmushi, ya ji tsantsar kishinta da damuwarta a muryarta, abin da ya daɗe yana faranta masa rai, “Ki yi haƙuri, kin ji, Babygirl?” Inteesar ta yi shiru, ba ta ce uffan ba, bayan wasu daƙiƙu, Aliyu ya sake gyara murya, sannan ya ce cikin wani yanayi mai cike da shauƙi, “Ki yi haƙuri, Babygirl, wata rana irin haka muna tare da ke, kin yi pillow da ƙirjina kina barci cikin kwanciyar hankali, na rufe ki da bargo gaba ɗaya… babu maganar late-night calls kuma,” wata irin kunya ce ta lulluɓe Inteesar lokaci guda, ta kasa cewa uffan, nan take ta yi saurin kashe wayar saboda yadda zuciyarta ke bugawa da ƙarfi, Aliyu ya kalli screen ɗin wayarsa yana murmushi mai cike da ƙauna, bai ɓata lokaci ba, ya shiga rubuta mata saƙo, “I LOVE YOU, Babygirl, sleep tight,” Inteesar tana kwance sai ta ji sautin shigowar saƙon, ta ɗauki wayar da sauri ta karanta, wani sabon murmushi mai daɗi ya bayyana a fuskarta, ta matse wayar a ƙirjinta, tana jin ɗumin ƙaunar Aliyu yana ƙara ratsa zuciyarta, ta lumshe idanunta a hankali, tana murmushi ita kaɗai, duk da nisan da ke tsakaninsu, a wannan daren ta ji kamar Aliyu yana kusa da ita.
Safiya ta waye cikin farin ciki da annuri, bayan Inteesar ta idar da sallar Asuba, ta shirya tsaf cikin shigar da ta dace da ɗalibar jami’a, ta sanya doguwar riga mai launin ruwan toka (grey), wadda ta zauna mata daidai, sannan ta yafa madaidaicin mayafi a kanta, ta sauko ƙasa domin yin karin kumallo, tana sauri saboda lokaci yana tafiya, bayan ta gama cin abinci, ta shiga ta yi wa Nana sallama kafin ta fito zuwa harabar gidan, inda direba yake jiranta a cikin mota, ta shiga, aka ɗauki hanyar zuwa jami’a, sai dai wannan tafiyar ta bambanta da yadda ta saba, maimakon hankalinta ya kasance kan abin da zai faru a makaranta, zuciyarta gaba ɗaya tana can Katsina, tare da Aliyu, tana tunanin muryarsa, murmushinsa da kuma alkawarin da ya yi mata na zuwa Abuja a ƙarshen mako, ta yi murmushi ita kaɗai, amma a ƙasan wannan farin cikin, akwai tambayoyin da har yanzu ba ta samu amsoshinsu ba.
Da motar ta tsaya a babban filin ajiye motoci na jami’a, Inteesar ta fito riƙe da jakar makarantarta, ba wai sabon semester aka dawo ba; laccoci sun riga sun yi nisa, ita ce kawai ta tafi gida Katsina, ta ɗan katse karatunta saboda rashin lafiyar Daddy da ya kwanta, yanzu da jikin Daddy ya samu sauƙi, ta dawo domin ta ci gaba da karatunta har ta kammala, tana takawa zuwa farfajiyar sashensu, ta hango kawarta kuma aminiyarta, Amira, tana tsaye riƙe da wasu littattafai, da Amira ta hango Inteesar, fuskarta ta faɗaɗa da wani daddadan murmushi na murna, ta taho da sauri ta tarye ta, sannan ta rungume ta sosai, “Intee! Mutanen Katsina, kun ɗauke mana kai kamar ba ku son dawowa makaranta!” Amira ta faɗa cikin zolaya da farin ciki, “Wallahi makarantar nan ta yi shiru ba kya nan, barka da dawowa!” Inteesar ta yi murmushi, “Barka dai, Amira, wallahi ni ma na yi kewarki,” Amira ta ɗan ja da baya tana duban fuskarta cikin kulawa, “Ya jikin Daddy? Da fatan an baro shi ya samu sauƙi sosai?” Inteesar ta gyaɗa kai cikin sanyin rai da godiya, “Alhamdulillah, Daddy ya samu sauƙi sosai yanzu, shi ya sa ma kika gan ni na dawo, don mu fuskanci karatun nan mu gama,” Amira ta sauke ajiyar zuciya, “Alhamdulillah! To, madalla, tunda jiki ya yi kyau, yanzu haka ma muna da lecture nan da minti kaɗan, mu shiga ciki kafin malami ya tsare mu,” suka juya zuwa cikin babban ɗakin karatu, wato lecture theater, suna ci gaba da tattaunawa cikin farin ciki.
Bayan sun fito daga lecture theater, Inteesar da Amira suka nufi babban wajen cin abinci na jami’a domin su ɗan huta kuma su tattauna, suna zaune a kan wata kujera mai daɗi, Inteesar tana juya straw a cikin kofin lemun da ke gabanta, yayin da hankalinta yake wani waje daban, wayarta da ke kan tebur ta fara ringing, da ta ga sunan Aliyu a screen, nan take annuri da daddadan murmushi suka gauraye a fuskarta, ta ɗaga wayar cikin muryar shagwaɓa, “Mi Amor…” Amira, wadda ke zaune a gabanta, ta gyara zamanta, ta haɗe hannayenta a ƙirji tana kallon Inteesar da wani murmushi mai cike da fahimta, ta lura da yadda muryar kawarta ta sauya a take, Inteesar tana wasa da gefen mayafinta yayin da take amsa kalaman Aliyu cikin wani salo na musamman, Aliyu yana can ɓangaren yana tambayarta yadda laccocin safiya suka kasance da kuma ko ta ci abinci, ita kuma tana ba shi amsa cikin natsuwa, “Eh, na ci abinci, Mi Amor, kada ka damu,” Amira ta kasa ɓoye murmushinta yayin da take kallon kawarta, bayan sun gama wayar cikin tattausan sallama, Inteesar ta ajiye wayar tana sauke ajiyar zuciya cike da annuri, Amira ta ɗan matso kusa da ita, ta harare ta cikin wasa, “Gaskiya, Inteesar, kallon yadda kike murmushi kawai ya isa ya bayyana mini komai, ashe kin faɗa cikin son gayen nan da gaske?” Inteesar ta yi dariya ƙasa-ƙasa, sannan ta ɗago ta kalli aminiyarta da idanun da ke cike da ƙauna, “Wallahi, Amira, son da nake wa Aliyu ba zai gushe haka kawai ba, shi ne mutumin da ya koya mini yadda ake sake yarda da rayuwa, da kuma yadda ake samun farin ciki bayan duk abubuwan da suka faru a baya,” ta ɗan yi shiru, murmushin da ke fuskarta ya ragu kaɗan, muryarta ta sauya zuwa mai cike da damuwa yayin da ta sunkuyar da kanta, “Amma, Amira… akwai abu guda ɗaya da yake firgita ni, kuma yake damuna a zuciya kullum,” Amira ta daina murmushi, ta kalle ta cikin kulawa, “Mene ne shi?” Inteesar ta haɗiye yawu, sannan ta yi magana cikin sanyin murya, “Tsorona ɗaya ne… Aliyu yana da mata har biyu a gida, duk da cewa ina son shi, wani lokacin idan na tuna cewa akwai mata biyu a tsakanina da shi, sai na ji gabana ya faɗi, ina tsoron yadda zamanmu zai kasance a nan gaba,” Amira ta saurari duk bayanan Inteesar cikin natsuwa, tana kallon yadda damuwa ta bayyana a fuskarta, ta miƙa hannu ta dafa kafaɗar aminiyarta domin ta kwantar mata da hankali, “Maganar gaskiya, Inteesar, batun kishiyoyi yana iya zama abin tsoro, amma idan mace tana da hankali da haƙuri, kuma mijinta yana adalci, abubuwa za su iya tafiya cikin kwanciyar hankali, idan har Aliyu yana sonki da gaske, zai kula da ke kuma ya kiyaye mutuncinki a gidansa,” Inteesar ta ɗan gyaɗa kai, amma damuwar da ke zuciyarta ba ta gushe ba, sai dai ba zato ba tsammani, murmushin fuskar Amira ya ɓace, ya maye gurbinsa da wani tunani mai zurfi, ta gyara zamanta, ta dubi ƙwayar idon Inteesar sosai, “Amma ban da maganar matansa biyu da kika faɗa… akwai wani abu guda ɗaya da nake so ki duba da kyau, kuma nake tsoron kada ya zama miki matsala a nan gaba, kin taɓa yin tunani a kai kuwa?” Inteesar ta gyara zamanta, fargaba ta bayyana a fuskarta, “Mene ne shi, Amira?” Amira ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta yi magana a hankali, “Inteesar, yanzu shekarunki ashirin da biyu kacal a duniya, yayin da Aliyu kuma yake cikin shekaru hamsin da wani abu, idan kika yi lissafi, nan da shekaru goma kacal, ke za ki shiga shekarunki na talatin, amma shi zai ƙara kusantar shekarun tsufa,” ta ɗan dakata, tana ba Inteesar damar fahimtar abin da take nufi, “A lokacin ne mace take iya kasancewa cikin ƙoshin ƙuruciyarta, tana da buƙatar mijinta ya kasance kusa da ita, ya ba ta kulawa, lokacin ne jikinki ke buqatar mijinki da kyau,” muryar Amira ta ƙara yin ƙasa, tana bayyana abin da take ganin ya kamata kawarta ta yi tunani a kai, “Amma a daidai wannan lokacin da kike buƙatar waɗannan abubuwan, Aliyu zai kasance ya ƙara tsufa, ƙarfinsa da yanayin rayuwarsa za su iya sauyawa, ta yaya kika tsara rayuwarki a lokacin? Yaya kika hango wannan yanayin a zuciyarki, Inteesar?” Wani irin sanyi ya ziyarci zuciyar Inteesar, kalaman Amira sun sanya ta cikin wani sabon nazari da ba ta taɓa yin zurfinsa ba, ta sunkuyar da kanta tana kallon kofin lemun da ke gabanta, amma a wannan karon, ba ta sake juya straw ɗin ba, a karon farko tun bayan da ta amince da soyayyar Aliyu, ta fara tambayar kanta wata tambaya mai nauyi, shin soyayya kaɗai za ta isa ta shirya ta fuskanci duk abin da makomarsu ta tanadar musu?