Free chapter · Read without an account
14
by Asmy b Aliyu · OMRI HAYATII
OMRI HAYATII
by
Asmy b Aliyu
14....
nan take taji kwakwalwarta na juyewa
haka taji falon na juya mata. baya ta tafi xata Fadi da sauri ta dafe kujera
tana kafe kofar da mu'azzam ya fice acikinta ido. wanda babu shi babu alamarsa
Sai kamshin turarensa da duk duniya shi kadai ya mallaki kamshi yake tashi acikin falon kamar Yana a gurin.Runtse idonta
tayi zuciyarta na wani irin tafasa
girgiza Kai tayi da gaske batason ta tsani Mami haka bata son ta fara kishi da Mami
akan mu'azzam Sai dai da alamar
Mamin na kokarin shiga rayuwarta ta karfi
da yaji .a yau mu'azzam din da baya boye mata komai shine xai kasa daga wayar Mami a gabanta me haka ke nufi?.
tambayar da ta rika jerawa kanta kenan
Kuma ta kasa samun amsa.
bayan ta koma cikin gida har bedroom ta samu mum na waya tsaye tayi dan ta kagu mum din ta gama wayar ta raba wannan bakin cikin da mu'azzam ya saukar mata tareda mum din ko Zata samu abun da ya danne zuciyarta ya sauka.itama mum ganin yanayinta tayi sallama da Wanda take wayar dashi
a natse take karewa malaak din kallo
wacce nan take yanayinta ya nuna tana cikin tsananin damuwa.
nan ta fadawa mum yadda mu'azzam
yayi da maminsa ta kira a gabanta,
wani murmushi mum din ta saki irin nasu na cikakkun Yan duniya.kafin mum
ta bude baki a natse ta fara magana.
"ke me kika fahimta a yanayinsa
bakya tunanin akwai wata a kasa?"
mum nima shine abun ya bani mamaki
akwai daure Kai a wannan lamarin
bai taba yimun haka ba Sai yau....
"ki yadda akwai dalili da gaske
mahaifiyarsa batayi na'am dake a matsayin suruka ba.!!!"wani irin bugawa kirjin malaak din yayi ,wata daria ta fashewa mum din daita wacce babu alamar wani farin ciki acikin daria.mum ki daina wannan
maganar dan Allah ,idan bata aminta dani a matsayin suruka ba wacece Zata kawo
cikin rayuwar mu'azzam din cikin sauki Ina a raye??"mum kallon malaak din kawai take,tau zamu dorasa akan layi
ga shawara me zai hana ki tuntubesa da zancen aurenki?"meyasa iyaye bazasu shiga maganar kuba lokaci yaja dayawa
Kara ayi aurenku haka??"
shiru malaak din tayi tamkar ruwa ya canyeta tana juya maganganun mum din tata aranta.
zan gwada mum zanyi masa magana.
wani murmushi mum din tayi
Amman mum idan har da gaske ne
maminsa bata so na a matsayin surukarta
ta kunnawa kanta wutar da bazata
iya kasheta ba babu maccen da ta Isa
ta auri mu'azzam marafa bayanni.
babu wata maccen da ya isa ya aura
Ina numfashi a duniya koda masifa koda balai mu'azzam marafa nawa ne ni kadai
ko uwarsa bata isa ta hanani aurensa ba.
Dan wallahi tallahi idan haka ta faru
zan iya Kai karshen numfashinta,
yadda malaak take fadar maganganun
mum ta san da gaske malaak din xata
aikata girgiza legs mum ta shigayi
tana sakin wani shu'umin murmushin da ita kadai ta San ma'anarsa cike da alfaharin malaak din haka ta nuna mata ta haihu dan halinta sak na mum din
babu abunda ta rage tamkar ma zatafi
mum zama masifa da balai anan gaba kadan.lokaci yayi kenan lokaci
yayi da Zata Kai Ayshaa marafa a kasa
tana son taga karshen ikonta da izzarta,
tun ba yau din ba mum ke mugun hassadar Mami taren kawai ake ta ciki
na ciki ,kasancewar sanadin mazajensu
dake kasuwanci suka fara zumunci
duk da Alh.ibrahim marafa yafi Farook
Rano kudi yayi masa fintinkau nesa ba kusaba.,mum ta fara hassadar mamin
yadda taga Kuma Alh.ibrahim marafa
naji da mamin dan wasu kamfanoni
na marafa'$ mamin ke juyasu
a hannunta ,duk wani cigaba a Rayuwa
Mami tayiwa mum fintinkau
duk wani kalar sitira designer kafin
ta gansa ajikin kowa ajikin Mamin take
ganinsa,lokaci yayi da Zata tabbatarwa
da miss Ayshaa marafa ita ba kowan kowa
bace ta dai samu malaak ta auri mu'azzam
Sai ta saka rabin dukiyar marafa ta dawo
hannunsu.....
#####
Sai da ya tabbatar yabar gidansu
malaak yayi nesa da gidan sa'annan
ya kira wayar mami.har yagama ring bata dauka ba Kara Kira yayi Yana addu'ar
Mamin ta dauka dan har yanzu zuciyarsa
bugawa take.sai yayi sa'a Mamin ta dauka
da sallama,ya amsa Yana gaisheta da respect,bayan ta amsa gaisuwarsa
Sai shiru ya biyo baya.a natse ya fadawa
Mami ta kira baya kusa ga Wayan,
Yana hanyar zuwa gida yanxu haka.
Yana jin yadda Mami ta sauke ajiyar zuciya tana fadamasa Sai ya iso kawai,
kafin ta katse Kiran.
koda yaje gida Sai da ya shiga bangaren Mami,kafin ya fito ya nufi bangarensa.wanka yayi Yana fitowa da alwalar la'asar ajikinsa.sai da ya dawo massalaci ya nufi bangaren Mamin.
abinci ya xauna Yana ci akan table
suna chart da malaak a natse,
koda wasa bata nuna masa ranta ya baci ba ,dan tabi shawarar mum dinta
ta dai fadamasa taso suyi wata magana Mai muhimmanci Sai gashi ya tafi.
yanzu Sai yaushe??"
ya fadamata akwai ayyukan da xaiyi clearance cikin wannan sati,idan yagama Sai suyi maganar,Suna cikin chart din ne
mami ta fito ta zauna a falon
tana amsa Kiran waya.
bayan ya Kammala cin abincin
ya dawo cikin falon Yana sauraren mami din tana masa bayanin dole ya aje komai
yaje Lagos na sati biyu ya xauna acan
akwai wasu Estates dinsu da suke kokarin an Kammala acikin sati biyu duk da babu kama hannun yaro ake aikin ginasu manyyan kudi ake saki Sai dai Mamin ganin take komai bayamata sauri Kara
ya shirya ya tafi daga baya Zata bisa.
bayan yagama da Mami ya fice daga gidan kafin ya fita Sai da ya biya ya gaisheda kaaka dan duk ranar basu hadu ba.
da dare da ya dawo Sun Kara tattaunawa da Abba akan maganar estate din,
kafin yayiwa iyayensa sallama
Yana yimasu Sai da safe.ranar ma sunyi waya da malaak lafia lau anan yake fadamata zaije Lagos na sati biyu.duk tabi
ta damu akan tafiyar da zaiyi shiyasa ma
ta matsa masa lamba gobe kawai su
hadu suyi maganar da zasuyi.yaso ta fadamasa a waya ko a chart ta fadamasa maganar mai muhimmanci ce bazai yuyu a Wayan ba. su dai hadu a gobe.
babu yadda ya iya akan goben xasu hadu,
acan Kuma kasan ransa damuwar yadda Mami ta hanasa mu'amala da malaak din ne yake damunsa da daga masa hankali.
duk lokacin da yake kokarin bude baki
ya fadawa malaak din gaskiyyar su hakura da juna tunda Mamin bata so Sai
ya kasa wani irin tausayin malaak din
ya dannesa ya kasa fadamata ,bai San wane irin yanayi Zata shiga ba musamman da yasan irin tsananin kaunar da takeyi masa.
washegari wuraren 11 ya nufi clinic
Yana gama parking Sai ga motar malaak
ya fito tasa motar ya nufi motar tata dake da dan tazara a tsakaninsu.tana gama parking yasa hannu ya bude Mata kofar
wani irin kallo take masa tana jin zuciyarta na narkewa da soyayyarsa.fararen kayane
a jikinsa na kaftan da sukayi matuqar yimasa kyau,a natse ta fito daga motar
cikin shigar doguwar rigar atamfa dinkin
fitted da ya kama jikinta sosai
sai dan yololon mayafin da ta axa akan kafadarta mai shige da kayan jikinta
tayi kyau sosai.
good morning my babe."
ta fada tana dan juya masa ido
good morning to my princess,
ta matsa gabansa suka jera a natse suka fara tafia duk inda suka wuce Sai
an kallesu an gaishesa,wani irin girma
ake basa cikin clinic din,koda suka karasa office Yana da tarin petient da xai duba,
Dan haka malaak ta wuce can cikin
makeken bedroom dinsa dake cikin office
din ta haye kan kyakkyawan italyn bed
dinsa ta jawo waya ta kunna data
ta fara chart.....
sosai lokaci yaja har wurin qarfe 1 na rana
ya shigo office din Yana kallonta
tana vidcall da sassarfa ya nufi bathroom
Yana nade hannayen rigarsa,
baijima ba ya fito da alwallah da alamar massalaci zai tafi.
Sai kusan 1:30 ya dawo daga massalacin dake cikin clinic din Kai tsaye cikin bedroom din ya nufa,koda ya shiga babu waya a hannun malaak din kwance take rufda ciki
ta dora kanta akan pillow idonta a rufe
dan buga filon yayi ta bude idonta a hankali da har Sun fara canja Kala saboda bacci.sallah fa?"
ya fada Yana kallonta ,da sauri ta fadamasa tana period dan tsaf xai sakata a gaba Sai tayi sallah.tunda acikin wardrobe dinsa dake cikin bedroom din
akwai hijabs na sallah sunfi Kala goma
saboda ita da kannensa idan Sun zo clinic din ,Wanda duk bayan wata 3 Sai an kwashe an zuba wasu sabbi.
ta mike tsaye ta nufi bathroom bata jimaba ta fito.ta samesa a tsaye Yana danna waya.ya daga Kai ya kalleta,
"beb muje eatry muyi lunch kaga ma
idan munje Sai muyi maganarmu a natse.
Yana da meeting da staff din clinic zuwa
4 ya kalleta Yana fadin"ita ta shiga motarta ta tafi Shima xai shiga tasa
yabi bayanta dan dole Sai ya dawo clinic,
da wannan shawarar kowane yaja motarsa
suka fice daga clinic din...
#OMRI HAYATII
#LOVE /FATE
#BEST LOVE
#MU'AZZAM MARAFA
#MALAAK FAROOK RANO
#ASMY B ALIYU
#***