Free chapter · Read without an account
EP_________ 5️⃣
🕊️ DESTINED MARRIAGE 🕊️
*HAUSA EDITION*
🕊️ QADDARARREN AURE🕊️
SWRITES
A-K-A
YOUNG WRITER✍🏻
Ina son sake jaddada cewa wannan labari ƙagagge ne, kuma ban rubuta shi da nufin cin zarafin wani ko wata ba. Idan kuma ya yi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata, to a sani arashi ne.
EP_________ 5️⃣
"Hmm, ba za ki fahimci yadda abin yake ba ne. Aiki ne mai kyau a idanun masu kallonsa daga nesa, dan wasu mutane kayan kawai suke gani, musamman ku mata. Amma mu lauyoyin mu kaɗai muka san yadda aikin yake caza mana kai da tunani. Tunda aiki ne da muke tsakanin wuta da aljanna, dan sai wanda Allah ya kiyaye ne kawai zai iya ɗorewa akan wannan gskyr, tunda mutane da yawa ma kallon maƙaryata suke mana".
Faryal ta ɗan yi dariya kafin ta ce, "Haba Barr, ai ba duka aka taru aka zama ɗaya ba".
"Haka ne Faryal, na san ba duka aka taru aka zama ɗaya ba. Amma kusan kaso casa'in cikin ɗari, we are liars and corruptible saboda wani lokaci za'a ɗauke mu aiki, ga gsky dai mun sani, amma a haka zamu take ta sannan mu kare ƙarya, har ma mu ɗaukaka ta. Money quickly changes our thoughts. Wani lokaci sai a samu attajiri ko ɗan sa da laifi, kuma mun sani, amma haka zamu juya al'amarin ta yadda za a wanke shi a matsayin marar laifi. Ko da kuwa laifin ya kai laifin girman kisan kai ne. Imagine the final destination of those who do this?".
Faryal ta dan furzar da numfashi a hankali kafin ta ce, "Haka ne Barr. Amma idan ka kawar da hankalinka daga son abin duniya, ka yi amfani da aikinka ta hanyar da ta dace, za ka kasance cikin masu nasara. Saboda a duk inda aka riqe gsky to babu faɗuwa a ciki. Allah dai ya taimaka".
"Amin ya Allah! Wannan shi ne abin da muke ƙoƙarin kwatantawa. A cigaba da yi mana addu'a dai".
Haka suka cigaba da tattaunawa har na tsawon mintuna biyar kafin su yi sallama. Faryal ta tashi ta adana wallet ɗin Aryan tana tunanin yadda Barr Hashim ya sake da ita da wuri haka kamar wanda suka dade tare har yana buɗe mata sirrin aikinsa, ta tuna yadda yake jero mata addu'o'i samun nasara tare da kalaman ƙarfafa gwiwa akan al'amuran rayuwa. Murmushi tayi tana kallon Hadiyyah da ta shigo ɗakin. Ta ce, "Ke ban ba ki labarin yadda muka ƙare da Barr Hashim jiya ba".
"Barr Hashim dai? Wannan mutumin da yake crushing akan ki?".
"Shi dai. Baki manta ba ashe?".
"Ehen! Bani in sha ya kuka ƙare?".
Dawowa Faryal tayi ta haye kan gadon ta zauna a gefen Hadiyyah, sannan ta fara ba ta labarin yadda suka yi dashi a waya jiya da hirar su ta yanzu, sannan ta ƙara da labarin Fayyad, wanda ya sa Hadiyyah dariya sosai.
Ɗan kallon ta Hadiyyah tayi bayan ta gama bata labaran, kamar zata ce wani abu sai kuma ta fasa, Saboda ta san halin yayarta ta, ta san ba lalle ta fahimci abin da take son faɗa mata ba, dan haka ta bar abin ta a cikinta. A haka Beta ta shigo ta same su, nan kuma suka shiga wata hirar daban, kafin daga bisani su tashi su koma falon su cigaba da kallo suna hira da Daadee har wurin 12am dan Maama tun 11pm ta shige ciki ta kwanta.
Washegari ta kama Saturday ne. So bayan sun kammala ayyukan da suka saba yi, suka yi breakfast sai suka koma bacci ita da Hadiyyah da Faryal, basu suka tashi ba sai wurin Azahar.
Faryal ce ta fara farkawa, miqa tayi, kafin ta tashi ta shiga bathroom ta wanko fuskarta da bakinta ta fito. A bakin gado ta zauna ta ɗauki wayarta ta fara kiran mahaifinta. Sai da ta kusan katsewa kafin ya ɗaga.
Sallama Faryal tayi masa, ya amsa cikin kulawa yana ƙarawa da faɗin, "Faryal ya kike da sauran yan uwan naki?".
"Dukkanmu muna lafiya Appa. Kai fa? Yaya aikin?".
"Alhamdulillah Faryal. Akwai wani abu ne da ya shafi Company?".
"A'a, Appa. Everything's fine here".
"To Masha Allah Faryal, haka ake so ai. Ina da baƙi da zan gana da su yanzu. Ki gaishe min da Daadee".
Tunda taji haka ta fahimci kashewa yake shirin yi dan haka ta amsa da, "To Appa In sha Allah". Daga haka sukayi sallama ya kashe. Wayar ta zubawa ido bayan ya katse kiran, tana sake mamakin wannan busy schedule ɗin na mahaifinsu. A matsayinsu na ya'yansa, ace sam bashi da lokacin su. Idan dai har ba batun aiki za su tattauna ba, ba zata taɓa yin doguwar hira da shi ba, ballantana sauran yan uwanta, da ko yana gari ma watarana sau ɗaya kawai suke ganinsa a rana. Duk da cewa babu wani abu da ya gagare shi yi musu, musamman ta fuskar kuɗi, ba su taɓa neman wani abu sun rasa ba. Amma sun rasa lokacin mahaifinsu, sun rasa kulawarsa.
Ta sauke ajiyar zuciyar kafin ta kalli Hadiyyah, wadda ta farka. "Lafiyar ki kuwa?". Hadiyyah ta tambaya tana kallon fuskar Faryal ɗin.
"Babu komai". Faryal ta amsa a sanyaye, tana ƙoƙarin kawar da tunanin mahaifin nasu, tunda hakan ba wani sabon abu ba ne a gare su, sun riga da sun saba ma tun suna ƙanana.
Tashi tayi ta nufi ƙofa tana faɗin, "Bari in ga Maama. Idan babu wani abun da zan yi, ina ganin zan je gidan su Walida". Ta faɗa tana ƙarasa ficewa ta rufowa Hadiyyah ƙofar.
Bayan kusan mintuna arba'in ta dawo ɗakin, in da ta tarar da Hadiyyah har lokacin tana kwance tana dannar waya kawai.
Bata ce mata komai ba ta wuce bathroom, ta ɗauro alwala ta fito. Hijab ta ɗauka ta sanya sannan ta shimfiɗa prayer mat kafin ta kalli Hadiyyah ta ce. "Ke ba za ki yi sallah ba ne?".
Hadiyyah wadda hankalinta yake kan wayarta ta amsa da, "An yafe min".
"Okay". Faryal ta faɗa tana gyara tsayuwarta ta tada sallar azahar dan ta gane dalilin Hadiyyah.
Bayan ta idar da sallar, ta tashi ta sauya zuwa kaya zuwa simple boubou gown. Tana cikin neman colour mayafin da zai dace da rigar ne, ta ɗan juyo ga Hadiyyah tare da faɗin, "Hadiyyah, kina buƙatar cash ne?".
Hadiyyah ta ɗan ɗago ta kalleta kafin ta ce, "Not really, dan ko shekaran jiya ma Abubakar ya ba ni wasu". Ta ƙarashe tana buɗe bedside drawer ɗin dake side ɗin ta, ta fito da bundle ɗin 1k, tana ƙara faɗin, "Kin gansu ko taɓa su ma banyi ba".
Faryal ta ɗan yi ƙasake tana kallonta cike da mamaki ta ce, "Hadiyyah, ɗawainiyar baza ta yiwa Abubakar yawa ba kuwa? Yana miki hidima da yawa fa. Duk lokacin da zai zo fa haka zai kawo miki tulin gifts, ga shopping kamar wadda take boarding school sannan ya ƙara da kuɗi? Ko ba komai ai zakiji nauyin karɓar kuɗin".
"Ni ina ganin hakan ai ba wata matsala ba ce, tun da aure zamu yi da zarar na kammala karatu na, to kuma dan ya hidimta min ai ba wani abu bane. Gifts da shopping kuma ai abu ne dake nuna kulawa da kyautatawa, ko bakiji ana cewa zuciya na son me kyautata mata ba. And moreover hakan na nuna ba budurwar zuciya bace dashi kuma yana da ƙarfin yin fiye da hakan ne shiyasa yake yi". Hadiyyah ta bata amsa tana ɗan jujjuya idanunta.
Faryal ta ɗan yi murmushin gefen baki me sauti, dan da ta fahimci shaguɓe Hadiyyah tayi mata akan Hamdan, wanda a cikin shekaru biyar ɗin da suka shafe tare bai taɓa yi mata wata kyautar azo a gani ba, sai ma ita da duk shekara in birthday ɗin sa yazo sai ta haɗa masa something special. Amma kuma ta kan ɗaukan hakan a matsayin rashin aikin yin da bashi dashi, duk da kuwa ta san mahaifin Hamdan ɗin marigayi me kuɗi ne sosai, kuma ya bar musu gado mai tarin yawa duk da ma ba'a raba ba. Amma ita ai ba ta damu da wannan ba. Hamdan take ƙauna, ba abinda yake dashi ba, ko abinda zai iya bata ba. Soyayyar gaskiya take masa, shiyasa in dai har zaizo ya ganta duk abinda zai kawo mata ganinsa take da girma bata kuma taba rainawa ba. Katse tunanin nata tayi da faɗin, "Amma dai kin san ke ma your father is capable of all this, kuma kin san da cewa bamu rasa komai ba. So focus on that and be contented. Kada ki dogara da kuɗin saurayin ko abinda yake baki. Idan da za ki karɓi shawarata ma, da na ce ki dakatar da shi daga wannan shopping ɗin yan makarantar da yake miki ki kuma rage nuna kwadayin abin hannunsa. Tunda ba Auren kuka yi ba tukuna, kuma mahaifinki bai gaza ɗaukar nauyin ki ba". Tana gama faɗin haka ta jawo mayafin da take nema, ta warci jakarta da makullin mota tayi waje. Ta bar Hadiyyah zaune ta rasa ta cewa ma, sai bin ta da harara da tayi har ta rufo ƙofar kafin ta ce, "Wahallur my foot". Ta gyara kwanciyar ta ba alamun maganganun Faryal ɗin sun shiga kanta.
Ko da Faryal ta fita, ɗakin Maama ta shiga ta shaida mata zata wuce gidansu Walida. Maama ta yi mata addu'ar dawowa lafiya, kafin ta bata sautun siyo mata wasu spices idan zata dawo.
Sai da ta hau hanya sannan ta kira Walida ta tabbatar da tana gida. Ta ɗauke ta kusan mintuna ashirin kafin ta isa gidan nasu.
Tana zuwa tayi horn, mai gadin ya buɗe mata ta shige. Tana sako kan motarta ciki ta hango Walidan tsaye da wani mutum tana magana, amma yanayin yadda take maganar seemed rude.
Sai da ta daidaita parking ɗin ta kafin ta fito daga motarta ta nufi inda suke, tana sake kare musu kallo. A dai dai lokacin ne ta ji Walida na faɗin, "Kada ka sake zuwa gidan nan. Na gaya maka ka fita a rayuwata. Kana tunanin saboda Maganar auren dake shirin shiga tsakanin mu ne zai baka damar controlling ɗi na yadda kake so? Ka ga kai ne damu na da kira safe, rana, yamma har dare. Kuma duk da haka bai maka ba, duk ƙarshen sati kana gidan nan. Haba jalo, baka da aikin yi ne? Nace baka da aikin yi ne? To in ma kai baka dashi, ni ina dashi, dan haka karka ƙara kirana ballantana ka tako kafarka cikin gidan nan, kaji na sake maimaita ma".
Tana gama faɗin haka, ta kama hannun Faryal suka nufi cikin gida, suka bar Jalo tsaye sake da baki ya ma kasa Magana sai bin su da yayi da ido kawai har suka shige. Wani Murmushi me kama da na mugunta ya yi kafin ya ce, "Wallahi, ba ki isa ba Walida. Ba zan taɓa barinki ki auri wani na ba. An halicce ki ne dan ki zama matata, ni kaɗai. Kuma muddin ba ki aure ni ba, to ba za ki taɓa auran wani ba a rayuwarki". Yana gama faɗin hakan ya koma motarsa ya shiga aka buɗe masa gate ya fice.
Ita kuwa Walida ba ta saki hannun Faryal ba sai da suka shiga ɗakinta. Ta zaunar da ita a bakin gado kafin ta ce, "Yi haƙuri fa Faryal. Kin zo kin tarar da ni wancan banzan ya bata min rai".
Da mamaki Faryal ta ce, "Wai Walee, ba Jalo ba ne? Saurayinki?".
"He's fucking witch!".
"Me ya faru ne haka? A iya sanina, you two love each other".
"Point of correction. Ex ɗi na dai, Yanzu ai Matsayina ya fi nasa, dan haka na gama da babinsa".
Faryal ta waro idanu kafin ta ce, "Kina nufin kin rabu da Jalo?".
"Eh, bazan iya da halin sa ba". Ta amsa tana zama haɗi da yiwa chewgum ɗin bakinta taunar wulakanci.
"Amma Walida, Jalo fa yana masifar son ki, he cares for you. Shi ya sa ba ya iya ɓoye yadda yake ji game dake. Ni a ganina, wannan duk a cikin ƙauna ce da kulawa".
"Kinga dan Allah, mu bar maganarsa. Kada ki ƙara ɓata min rai ma. Bari in kawo miki abin sha".
"A'a, kar ki damu. I'm Okay ". Buɗe baki Walida tayi da niyyar yin Magana sai wayarta tayi vibrating alamar shigowar saqo. Ɗaukan sabuwar iPhone 16 ɗin ta ta tayi ta buɗe saƙon. Wani kayataccen Murmushi ta saki, kafin ta furta, "Shege Alhaji Barau Idon Naira!". Ta ƙarashe tana danna masa kira.
Ringing ɗin farko ya ɗaga. Ta sassauta murya kafin ta ce, "Alhaji na, na ga alert yanzu. Ina godiya kwarai da gaske".
Daga ɗaya ɓangaren, Alhaji Barau Idon Naira ya amsa, "Ah, kada ki damu big girl. Kin cancanta ne ai. Ni a wuri na kin fi ƙarfin wannan ma. So kar ki damu, wannan ƙaramar kyauta ce kawai".
"Thank you once again. Allah ya ƙara arziki".
"Amin ya Allah! Big girl. To ya labari? Me zan samu?".
Walida ta ɗan saci kallon Faryal, wadda take kallonta take kuma jin hirar da suke yi. "Ina tare da baƙuwa yanzu. Friend ɗi na ce ta kawo min ziyara. I will call you back".
"To, babu matsala. Sai munyi Magana".
"Alryt, bye". Daga haka suka yi sallama ta katse kiran.
"Shi kuma wannan ɗin yaushe kika haɗu dashi?". Faryal ta tambaya.
Yar dariya tayi kafin ta ce, "Wani tsoho ne da yake neman wadda za ta taimaka masa wajen cin kuɗinsa, duk da kuwa iyalinsa na can cikin qangin rashi. Wallahi Faryal baki san kuɗin Alhaji Barau ba, amma kin san abin takaicin?".
"A'a, sai kin faɗa?". Ta faɗa tana gyara zama.
"Ya'yansa a Federal University suke karatu. Daga waje haka, za ki yi tunanin familynsa is well off, amma a cikin gidan su kaɗai suka san halin da suke ciki".
"So shi yake gaya miki duk wannan?". Taɓe baki Walida tayi cikin nuna halin ko in kula kafin ta ce, "Ya gaya min wasu dai, sauran kuma na bincika da kaina. Ai har gidan nasa naje ba tare da ya sani ba, su ma matan nasa basu san ko ni wacece ba. I just manipulate them to get information kamar yadda ya faɗa min dama sun aure shi ne saboda kuɗinsa, and they are seeking to harm him because of his wealth".
"Ikon Allah, to hakan punishing ɗin su yake ko me?".
"Oho! Ni dai abin da na sani shi ne not all the wealthy are givers. Wasu yan mata kawai suna ganin idan mutum yana da kuɗi kuma he's famous, to wannan kaɗai ya isa suji zasu iya auransa. Ba ruwansu da binciken halayensa ko ɗabi'unsa, saboda a ganinsu, kuɗi da matsayi su ne komai. Basu san wani zai iya kashe Miki ko nawa bane a waje, amma da zarar kin shiga gidan sa to fa kin shiga tsilla tsilla kenan duk irin tarin dukiyarsa kuwa".
"Yanzu knowing all this, Me zai sa ki saka kanki a cikin irin wannan mummunan yanayin ta hanyar aurensa?".
"Waye ya gaya miki cewa aurensa zanyi? Haba Faryal, ai ni cin kuɗinsa kawai nake, tunda raba arne da makami ai ibada ne. Amma ya min tsufa da yawa. Mutumin da ko ƙaramin ɗansa ya girme ni".
Faryal ta jinjina kai, tana sauke numfashi tace, "To ya Abuja? Yaushe kika yi sabuwar waya kuma?".
Walida ta ɗan jujjuya idanunta kafin ta ce, "Eh thou Abuja dai nasan zaki iya fahimtar yadda take daga kallo na? Ko ba ki ga yadda na yi fresh dani ba. Waya kuwa kyautar ta aka bani. Dama ina taso in zo in muku tsiya ke da Jamjam, this time dai na riga ku riqe latest iPhone, ni ma na wuce gori". Ta ƙarashe tana dariya haɗi da kaɗa kai.
"Iyye? Kai yarinyar nan kin faso gari fa. Kar ki ce min itama Alhaji Barau ɗin ne ya saya miki?".
"A'aaa". Ta faɗa tana yin kwai da chewgum ɗin bakinta. Kafin ta cigaba da faɗin, "Ba Alhaji Barau ba ne. Wani mutumin ne daban. Ai bari kiji Faryal, na zaune bai ga gari ba. Ni na san abin da na gani. Ai cibiyar arziki tana Abuja. Ke kinga attajirai kuwa, yadda suke wasa da kuɗi kamar basu san zafin nema ba? Habaa, rayuwa me daɗi tana Abuja yarinya".
"Ummm, Walidaaa! A cikin waɗannan yan kwanaki biyun da kika yi a can ɗin duk kika karance su haka? Wai tsaya, wurin wa ma kikaje to?".
"Kishiyar kakata". ta amsa ba tare da ta kalli Faryal ɗin ba.
Faryal ta fashe da dariya, kafin ta ce, "Kishiyar kakarki? Walida Allah ƙarya kike yi. Faɗa min gaskiya dai".
"Wallahi, haka na faɗawa Umma ".
"And then?".
"Na je wurin saurayina".
"Saurayinki? Yaushe kika yi saurayi a Abuja kuma?".
"Mtsew! Ke fa kina da matsala, sai ki dinga abu kamar wata bagidajiya. Ɗaya daga cikin ƙawayena ce ta haɗa ni da shi mana. Ai tare ma mukaje ta gabatar dani tunda bamu taɓa haduwa ba".
"Walida, do you really mean what you are saying?". Faryal ta tambaya unbelievably.
Walida ta gyara zama dan taga alama duk abinda take faɗa baya shiga kunnen Faryal ɗin, ta kalle ta kafin ta ce, "Wai kina tunanin duk abinda nake faɗa miki wasa ne kawai just for fun?".
"Eh mana! Saboda na san ki Walida. Na san ki da tsalle tsallen samari, yau wannan gobe wancan. I know you are a real player amma ban taɓa tunanin cewa abin ya kai wannan matakin ba, har za ki iya tafiya wani gari dan kawai ki haɗu da wani. Sannan kuma Umma ta yarda da karyar da kikayi har ta bar ki kika tafi?".
Walida ta yi kamar ba ta ji maganar da Faryal ɗin tayi a farko ba, kafin ta ce, "Umma fa ba ta nan. She went on a business trip. Daga ni sai brothers ɗi na biyu. Shiyasa ma da nace zanje wurin Kishiyar mamansu kafin ta dawo bata hana ni ba".
Faryal data fahimci ƙawarta fa ta fara ɗaukan gurbatacciyar hanya ta ce, "Amma kin san abin da kika yi ko kuma wanda kikeyi ba daidai ba ne ko? So kike ki lalata Rayuwar ki ne?".
"Dan Allah, ki bar batun nan Malama. Ni fa ba ƙaramar yarinya ba ce. We just have to flow with the era, and embrace it as it comes".
"Saboda abun duniya Walida?". Faryal ta tambaya cikin tsananin takaici. Sannan ta ƙara da faɗin, "Allah Ya faɗa mana a cikin Alƙur'ani me girma.
وَلَا تَقْرَبُوا۟ ٱلزِّنَىٰٓ ۖ إِنَّهُۥ كَانَ فَـٰحِشَةًۭ وَسَآءَ سَبِيلًۭا
(Kada ku kusanci zina. Lallai ita ta kasance alfasha ce, kuma mummunar hanya ce). Walida ki ji tsoron Allah. Kin san yadda zina take ɓata sunan mutum da martabar ahalinsa kuwa? Kinsan yadda take bin zuri'a kuwa? Idan da zaki tambayi wanda suka kasance suna aikata ta kuma zasu faɗa miki gsky, to hakika zasu ce miki ne suna yi ne kawai, amma ba su samun wani farin cikin ko jin daɗi a cikinta. Sannan abu ce da idan tabi jininka sai ka yi da gaske kafin idan Allah yasa in kana da rabo ka tuba. Me ya sa zaki bar gurbatattun ƙawaye su rinjayi tunaninki haka? Kina tunanin da Baba yana raye zaiyi farin ciki da wannan hanyar da kika ɗauka?".
Ta ɗan yi shuru kamar maganganun sun shige ta kafin ta ce, " Faryal kenan, na dai san kinsan ba'a shiga tsakanin bawa da Ubangijinsa, saboda Allah gafurur rahim ne. Yanzu dai, ya ya Hamdan ɗinki?".
Faryal ta ɗan girgiza kai, har yanzu ta kasa yarda da abinda ke faruwa da ƙawarta ta. Amma kamar yadda take hangowa Walida ta riga da tayi nisa a ciki, baza ta fahimci komai ba. Addu'a kawai take da buqata.
Murmushi ta ɗan yi kafin ta ce, "Yana lafiya. Bari ma in kira shi". Ta faɗa tana ɗauko wayarta, ta shiga contact, ta lalubo numbersa ta danna masa kira.
Ɗan lumshe ido tayi a yayin da muryarsa ta ratsa kunnuwanta. Amsa masa sallamar da yayi ta yi kafin ta ce, "Barka da rana, yallabai".
"Afternoon Love. Yaya kike?".
"I'm good as long as my Man is Okay".
"Umm, same Alhamdulillah. Yaya komai?".
"Komai yana tafiya daidai. Kana gida ne ko kuwa ka fita?".
"Na je yi wa Umma shopping ne. Kin ganni a hanyar komawa gida".
"Amma ka san dai na faɗa maka ka daina amfani da waya yayin da kake tuƙi ko?"
"Sorryyy, baza a ƙara ba. Yanzun ma dan kiran ki ne shiyasa na ɗaga". Ya faɗa yana yar dariya.
"To naji. Za ka zo ɗin ne kamar yadda kace?".
"Eh, in sha Allah".
"To me kake so in girka ma?".
"Funnel cake".
"Kana son funnel cake ɗin nan da yawa Habiby".
"Yana da daɗi ne sosai. Wai yaya ake yin sa ne?".
"Kar dai ka ce min zuwa zaka yi ka girka?". Ta tambaya tana dariya dan ta san ƙaramin aikin sa ne.
"A'a, Amna zan koya wa, ta dinga yi mana".
"Umm to, it's our traditional snacks, flour ne kawai sai sugar, eggs, milk, baking powder, vanilla extract and oil. Da farko, za a haɗa dry ingredients din ne a cikin kwanu ɗaya a juya su har sai sun hade sosai. Sai kuma a samu wani kwanon daban, a haɗa wet ingredients din, sannan a riƙa zuba dry ingredients ɗin a hankali ana mixing har sai sun haɗe jikinsu sosai. Sai a zuba mai a fry pan in a medium low heat, then slowly drizzle a thin stream of batter in a zig zag pattern in to the hot oil. A bar shi har sai ya soyu ya dan yi golden brown haka, sannan a tsame shi a ɗora a kan paper towel lined plate, and dust it with powdered sugar, Shikenan fa".
"Ai kuwa zan gaya wa Amna. Barin in shiga gida ko?".
"Har ka isa ne?".
"Eh mana".
"Alryt to sai mun haɗu".
"Bye bye, take care". Daga haka sukayi sallama ya kashe.