Free chapter · Read without an account
BOOK ONE CHAPTER 22
*ZAINAB*
Tayi duk tinanin da zatayi na soma sabon sana'a.
Har zama tayi itada Ramlat suka tattauna, daga ƙarke suka tsayar da sana'a guda na snacks.
Hausawa suka ce da zafi zafi ake dukan ƙarfe. Taje kasuwa itada Ramlat suka siyo duk wani abu da tasan zata buƙata wurin sana'arta. Amma bata siyo da yawa ba, gudun asara. Idan sana'ar ta karɓu sai ta rinƙa yinsa da yawa.
Aiki tuƙuru suka sha itada Ramlat da Anis harda ma Khalid dake aikin yana lumshe ido saboda baccin dabe wadace shiba. Ita Zainab tasha normal baccine na ƙiyasin hankali da baya samu sakamakon rashin Khadija.
Milky doughnut sukayi, sai cake, buns and chin-chin.
Suna gamawa sukai packing dinsu. Khalid ya ɗau wayarta yai video mai kyau na advertising ya ɗora a TikTok, status ɗinta na WhatsApp harda face book da I.G
Ramlat na ta mai dariya ganin yanda ya zage ye voice over mai jan hankali yana koɗa products din nasu.
Tun bai kalleta ba daga ƙarke seda ya tanka mata"ke banza ce wallahi. Watching movies and videos kawai ki keyi basa miki amfani."
Ramlat ta ƙara tuntsirewa da dariya"to ai kaine Yaya ka zage kanata exaggerating snacks dinnan over and over."
"Kema ba haka ki keyi idan kinaso Mami ta siya miki kayan kwalliya ba."
Anis ya bata amsa.
Ita dai Zainab tai shiru tana kallon su. Gardaman da suke yi akan sana'ar da walwalansu ya sanya tinaninta ɗibanta ya kaita wani lokaci can baya daya wuce.
*
Zaune take itada Ahmed suna hira yana gaya mata irin riban daya samu a business ɗinsa.
Cikin farin ciki take ta yasa murna itama tace"honey inaso ka ɗan tai maka idan Allah ya ƙara maka ƙarfi ka bani jari na soma saida abaya na mata ina....."
"No Baby ba zai yiwu ba."
Ahmed ya katse mata maganarta da nasa cikin rashin jin daɗin abinda take fadi.
Tun farkon aurensu ya gaya mata ba zatai aikin gwamnati ko na wani wuri ba saboda cuɗayyan maza da mata, kuma ta amince masa duk da gwagwarmayar karatun da tayi itada mahaifinta da family dinta gabadaya.
Akan business ne batai tinanin za sui haka dashi ba. Shima kasancewar sana'ace da zatayi acikin gidanta.
Amma sai ta ƙara cewa"meyasa bazanyi kasuwanci ba?"
"Saboda bana so."
Kallonsa tayi. alokaci guda fuskarsa ta sauya. dagaske bayaso, sai kawai tai murmushi tunda bayaso itama bataso. bama zata ƙara maganarba har abada.
Hucin zafin da zuciyarta keyi ya sanya numfashinta sarƙewa. Ta shiga tari mai ƙarfi tana ambaton Allah.
Hankali atashe yaran sukayo kanta suna mata sannu.
Seda tarin yafaɗa mata sannan ta iya kallonsu da jajayen idanunta tana amsawa ahankali.
Hankalin Khalid na kan wayan. Ya ɗauka yayi connecting v.p green data, kamar ana jira sai ga messages suna shigowa.
TikTok ya soma shiga. Haba aise jinsa sukai ya silale ƙasa da wayar a hannunsa yai sujjada yana furta"Alhamdulillah!."
"Yaya mai ya faru?..videon ya tafi viral ne?!!"
Ramlat ta fada tana dariyar tsokana.
Be amsa ba seda ya ɗago. 250 views daga ɗorawa. 20 messages masu tambayar location.
Abin nima ya samu. Suka rungume juna suna murna. Ita kam Zainab tayi zaune tana godiya ga Ubangijinta tare da tasbihi agaresa.
Seda suka gama farin cikin. Khalid ya zauna yana musu reply. Akai sa'a 15 daga cikinsu duk ƴan zaria ne anan kusa dasu.
Adaren Zainab ta soma karɓan kuɗin snacks. Shi kenan kuma sai yazama kamar an buɗe ƙofa. Sana'a ta tashi ranga ranga. Customers kamar ana watso mata su.
Itada yaran gabadaya imbanda godiya ba abinda suke ma Ubangiji. Sanin kansu ne ba wayonsu ko da baransu bane, kawai taimakon Ubangiji ne.
BaAYAN WATA DAYA
*JAMILA*
Yau zaria tayi kira. Ɗaya daga cikin manyan aminanta za tai aure. Gashi bayan amintakar dake tsakanin ta da Nady harda zumunci.
Tun sati guda daya wuce ta turama Samir message na tafiyarta baiyi reply ba.
Shi yasa ta haɗa kayanta ta fito, driver ya ɗauketa acikin tsadaddiyar motar da kallonta kaɗai na sanya wani alfaharin kasancewar ta amatsayin mai iko dashi ya cika zuciyar ta.
Tafiya sukayi mai dogon zango. Kasancewar motar su mai kyauce kuma drivern yasan hannun shi yasa suka iso acikin awanni hudu.
Yana packing a ƙofar gidansu, ta fito tana kallon ƙofar gidan da jan siririn tsaki.
Allah ya gani wannan takurarren ƙofar gidan takaici yake bata. A lokuta da dama yana bata kunya tare da zubar matada mutunci.
Duk wanda ya ganta yaga rainon carpet, tashin a-c, wangalan gate yayin fita. sedai me ana zuwa wannan gidan akaga ƙofar gidannan mutuncinta ke zubewa.
Ciki ta shige tana takunta ɗaya bayan ɗaya. Lokaci zuwa lokaci takan yamutse fuskanta. Yanda ta tafi tabar gidan hakanan yake babu gyara babu komai. Yanzu ace za'ai ma Baba wani abin arziki sai yace bai san zancen ba.
Tana sallama Mommy ta fito daga ɗakinta itada Nady da su Yaya Yasir dake tsumayin zuwanta.
Cikin ɗoki suka rungume juna. Mommy nata kallonta tana murmushi. Baicin ita waya isa yace Jamila tanada wani matsala a gidan mijinta? Ta ƙara haske, tayi fess da ita, har wata ƴar ƙiba tayi na musamman irin na masu kuɗi.
Ummi ta fito da fara'arta tana mata sanda zuwa, Zahra na saɓe akan kafaɗarta tana shafa bayanta kasancewar madara tagama bata.
Fuska Jamila ta ɗaure tana kallon ta. Itapha matannan ɗun gun haushi take bata. Yanda bata ƙaunarta, itama bata ƙaunarta samm.
Imbanda munafurci da kinibibi babu abinda yake ɗawainiya da ita. Allah ma yaga abinda yaganine shiyasa bai bata ƴaƴan dayawa ba. Tunda ta haifi Aliya ƙwallin ƙwall kamar rai shikenan.
Ciki-ciki ta amsa sanda zuwan suka shige cikin ɗakin suna kashewa da dariya.
Ummi ta girgiza kai kurum tace"Allah shi kyauta." Ta koma ɗakinta.
Dama tasan mai hali ai bazai sauya halin saba. In zaka shekara dubu bakaga mutum ba ka tambaye shi komai amma banda halinsa.
Tarba mai kyau ta samu daga Mommy. Ba abinda yai mata daɗi irin yanda su Yaya Yasir sukai zaune sunata hira. Nishadi sosai takeyi tana farin ciki har ƙasan ranta.
*
Da yamma itada su Yaya Naim suna hira sukaji sallamar Baba ya dawo.
Suka amsa suduka suna mai sanda zuwa. Jamila ta sunkuyar da kanta tana aro natsuwarta ta gaidasa.
"Ina yini Baba..."
"Lafiya."
Ya amsa yana wucewa. Jamila tai tsam!kalmar yawwa daya fadi na mata yawo. Duk da tayi tsammanin faruwan haka idan tazo ba tai tinanin jin wannan zafin ba.
Tun tana yarinya taima kanta alƙawarin bazata ƙara zubarma da Baba hawaye don yaƙi bata kulawa kamar sauran ƴaƴansa ba.
Ayanzu sai taji hawaye sun ciko kwarmin idanunta.
"Wai kuka zakiyi saboda Baba. Tab ga yaya umar nanan kin san da yanzu ba wannan maganar akeyi agidannan ba."
Yasir yafaɗi. Nabil yace "ai tafiyarsa N.Y.S.C dinnan ke aka taimaka wallahi."
"Harda ku fitinar Yaya waya bari."
Cewar Jamila tana share hawayenta. Naim yace"Bom!" Duk se suka kwashe da dariya.
Ummi tazo ta wuce ta gabansu goyeda Zahra ta shiga ɗakin Baba.
Jamila ta kyaɓe fuska tana hararanta ƙasa-ƙasa.
Su Nabil sun ganta sarai amma sukai mata shiru basu tsawatar mataba.
*ALIYA*
Socket ya kashe yana jin gine ion din agefe. Aliya ta ɗauki kayansa tana mai sannu. Dama nata kayan ya soma gogewa harseda ya kammala. Tina draman ma da akasha wurin wanke wannan kayan nasu ɗazu da safe kaɗai na sanya dariya kamata. Shi alalen dole waishi sai ta bashi brezian ta ya wanke ta...."
"Idan kin shiga ki bude side drawer ɗina can ƙasa zakiga wani littafi an rubuta riyadus salihin ki ɗauko min shi na kwana biyu banyi nazarin sa ba."
Maganarsa agareta ya katse zancen zucin da take yi. Amsa mai tayi tana shiga dakin. Seda ta fara ajiye kayan a muhallinsu sannan taje ta ɗauko mai littafin.
Seda ta ɗaga wasu manyan litattafai taga littafin. Aƙasan shi taga wani farin envelope an rubuta Qurratul Aini da yaren larabci cikin rubutu mai tsari daya kasance mallakin Ustaz.
Batasan me yaja hankalinta kan envelope din ba, duk da tasan ko mai zata gani zai danganci Jamila ne saboda sunane daya bata kuma kuwwa ya shaida saboda baya alkunyan kiranta da sunan agaban kowanene.
Kyawawan hotunan Jamila tai katari dasu masu jan hankali. Zuciyarta ta buga da ƙarfi. Me Ustaz yake yi da hotunan Jamila awannan lokacin? Shin kenan har yanzu yana sonta? ta tsinci kanta da jefa ma kanta tambayoyin da bata da amsoshin su.
Wannan wa..... "Habibty....Habibty..." Ustaz ke kiran sunanta jinta shiru. dasauri tasa hannu ta goge hawayen da suka ciko idanunta. Ta maida hotunan dasauri ta fita da littafin a hannunta.
Ahanyar ɗakin sukai kaciɓiss dashi zai biyo ta. Ganinta yasan yashi riƙota yana fadin
"lafiya na jiki shiru?"
"Ba komai."
Ta amsa da disashshiyar muryanta tana miƙa mai littafin. Yana yinta ya kalla duk da taso danne abinda ta keji seda hawaye suka sauko mata. Ya kai hannunsa da tambayar ta cikin kulawa.
"Meya faru?...wani abu akai miki.?"
Shiru bata amsa shiba. Sai ambaliyar hawaye da take mai.
"Meya sameki acikin ɗakin?."
"Ba komai pha."
Tafaɗi cikin kukan da take yi.
"Wannan ba gaskiya bane."
Yafaɗi yana kamo fuskarta cikin tafukan hannayen sa tare da ƙoƙarin saka idanunsa acikin nata.