Free chapter · Read without an account
PAGE 27
SAWU BIYU
Khadijah Sulaiman
YOTA
Book 1
Page 27
Gidan yayi tsit bayan an kai ko wacce amarya gidanta,Zarah ta karasa part ɗin Hajja riƙe da handbag ɗinta.
Har cikin bedroom ɗin ta shiga,tana zaune kan gado Abdallah zaune kusa da ita yana danna waya.
Ta wani taɓe baki,shi bai da aiki sai zama a ɗaki kamar mace.
Hajja na ganinta ta ce"gara da Allah ya kawo ki,miƙo min jakata in fara duba abinda ke ciki kar in ga ba dai dai ba".
Ta miƙa mata jakar ta tsaya tana kallonta,sai da ta caje jakar tsaf sannan ta ajiye a gefe ta ce"to ai kun ga haka ya fi, ɓarawo bai da kunya sam".
Zarah ta juya za ta fita don a mugun gajiye take,gashi dai ba wani aiki tayi ba amma bacci kawai ta ke son yi.
"Dawo nan ban gama da ke ba".
Ta juya ta zuba mata ido kamar ta fashe da kuka.
"Akwai sauran frad rice ɗin nan a wurin ku?"
"Babu ya ƙare,sai dai ko wurin Mama".
Ta watsa mata harara ta ce"wacece kuma Mama,ai tun kafin a haife ki na san da ita a gidan nan,shegen iyayi da feleqe,kin zata ban san abinda ke tsakanin ki da ɗanta ba kenan,to bari ki ji,ko za ki mutu babu mai aura miki shi,idan za ki gwale ido ki hango masu son ki gara ki gwale,babu ruwana da shirme,nansense".
Zarah ta harare ta ƙasa ƙasa ta juya ta fita Abdallah ya bita da kallo.
Jin sai mita take ya sa ya juyo ya ce"gaskiya kin dame ni".
"Dallah rufe min baki nansense,kana kallo wani zai aure ta ka tsaya shashancin banza,ka kasa buɗe baki ka nuna mata kana sonta,sai kwana kwana ka ke kamar ba namiji ba".
Ya ajiye wayar ya fuskance ta da kyau ya ce"idan nace ina so za ku bani?"
"Ji wani zancen banza,idan kana so mai zai hana a ɗaura muku aure,ai sai gida ya ƙoshi ake kaiwa waje".
Ya jinjina kai ya ce"to ina so".
Ta washe baki da sauri ta ce"kai Masha Allah na ji daɗi sosai,da ka yi magana da wuri babu abinda zai hana a haɗa auren da na ƴan uwanta,ubanta ya ce sai ta fara karatu,Allah na tuba menene boko,mu da ko aji ba mu taɓa shiga ba ai mun zauna gidan miji lafiya lau babu abinda ya cinye mu".
"Kuma haka ne Hajja,ki san yadda za ki yi convincing ɗinsu su yarda da hakan especially Oum,sai ayi kawai da wuri".
Hajja ta ce"sai ma ka faɗa?"
Washegari da sassafe ta dannawa Daddy kira,Oum na bacci ta taso ta.
Bayan ya iso ya ce"Allah ya sa lafiya Hajiya".
"Lafiya ƙalau sai alheri,kira matar ka Hafsah ta zo yanzu".
Bai ce komai ba yayi daliling number ta,bayan ta ɗauka ya ce"ki same ni a parlourn Hajja".
Sanye da hijabinta dogo har ƙasa ta shigo,ta gaida Hajja a ladabce ta zauna kusa da Oum.
Oum ta juyo ta ce"Ina kwana Aunty?"
"Mun tashi lafiya Oum?"
"Alhamdulilah Aunty".
Hajja tayi gyaran murya ta ce"ba komai ya sa na tara ku anan ba face alheri, Abdullahi ya sanar da ni ya ga yarinya kuma yana so,shi yasa na ga ya dace kuma ku sani".
Daddy ya ce"Masha Allah, wannan abin farin ciki ne sosai,tunda har an gama karatu kuma an sami aiki,babu abinda ya dace da shi sai auren".
Oum dai jira take ta ji wacece don bata san yaushe yayi budurwa ba.
Hajja ta ce"to cikin ikon Allah dai yarinyar ba bakuwar kowa ba ce anan,ƴar gidan Hafsah ce Zarah".
Mami ta zuba mata ido,Daddy ya ce"toh,Masha Allah,ai wannan ba abin damuwa bane,ya yiwa ita yarinyar magana ne?"
Hajja ta ce"a'a bai sanar da ita ba kam,tun zuwan su na fahimci hakan amma bai fito ya sanar min ba sai jiya."
Daddy ya ce"to babu laifi,amma Zarah bata fara karatu ba for now, za'a ajiye magana,idan tayi nisa da karatun sai a sa lokacin auren ina ga hakan zai fi ko?"
Yayi maganar yana kallon Hajja.
"Wani irin karatu kuma,Allah na tuba da an san da hakan da tare za'a aurar dasu jiya kowa ya huta,itama Hafsah hankalinta ya kwanta tayi bacci har da minshari,mutum nada ƴaƴa mata a gaba ina ya ga bacci,sai dai ta ji da mutum ɗaya kawai,amma tunda hakan ya riga ya faru kawai ayi magana da mahaifin yaron a sa auren kawai".
Oum ta gyara zama ta ce"shi ya shirya miki hakan ko Hajja,to kamar yadda ya gama karatu ya fara aiki haka ƴata dole tayi karatu,kuma dole sai da amincewarta za'a yi wannan auren".
Mami ta sauke wani ajiyar zuciya jin abinda Oum ta ce.
Abdallah da ke laɓe ya rintse ido da sauri ya ce"Oum".
**********
Bayan sati ɗaya
Doctor ya dube shi ya ce"poison was behind the death,sai dai bayan duba sauran abincin dake cikin su babu wani abu mai kama da hakan Sir,nayi magana da Brigadier General,mun je har gidan mun ɗauko sauran abincin dake tukunya kuma tabbas an sami traces na poison ɗin a ciki".
Ya miƙa masa hannu ya ce"thank you so much doctor".
Headquarter ya nufa daga can,ya isa inda aka ba da ajiyar key ɗin gidan ya nemi Idayat suka fita.
Babu komai a parlourn sai pillown kujerun dake barbaje a ƙasa,ya wuce kitchen ta bishi a baya.
A nutse ya dinga examining komai,ya fita ya koma wurin makociyarta ya ƙwanƙwasa ƙofar.
Nan da nan ta gane shi,ta gaishe shi da fara'a,Sadauki ya sake mata fuska ya ce"ki yi haƙuri kin ga na dawo ko?"
Tayi dariya ta ce"babu damuwa".
"Na gode,ranar da abin ya faru,ko kinga maman Bisola a waje?"
Da alamar tunani ta ce"eh,na ganta,kamar cefane ta yo don riƙe da baƙin leda na ganta tana dawowa".
"Kamar ƙarfe nawa?"
Ta ce"ƙarfe shida ya wuce Sir".
Ya ce"kasuwa ta tafi kenan?"
Ta girgiza kai ta ce"a'a,akwai wata mata a bakin hanya dake zama under umbrella,a nan muke cefane".
Ya gyaɗa kai ya ce"Nagode sosai".
Bai tsaya kiran Idayat ba ya kunna mota ya tafi bakin hanya, matar na zaune ta kasa kayan abincinta,ya sauko ya gaishe ta,ta amsa da kulawa.
Ya ce "Mama dan Allah wasu tambayoyi zan miki?"
Ta waro ido a tsorace ta ce"toh,Allah ya sa na sani?"
"Kin san wata mata maman Bisola da Tobi?"
"Na santa sosai,tana siyan kayan abinci a wuri na".
"Yaushe rabon ki da ita?"
"Ya kai kwana biyu cikin satin da ya wuce".
Ya ce"za ki iya tuna abinda ta siya a wurin ki?"
"Shinkafa ta siya mudu ɗaya,da kaina na auna mata".
Ya gyaɗa kai ya ce"Nagode sosai".
Daga nan ya shiga mota ya koma gidan, Idayat na zaune a parlour tana danna waya,ya wuce ta ya shiga kitchen ya hau bincike.
A cikin wani roba ya ga sauran shinkafar ɗaure a leda,ya miƙawa Idayat dake tsaye a bakin ƙofa ya ce"za mu tafi da wannan".
Wurin Doctor ya koma ya bashi shinkafar akan ayi bincike a kai.
Washegari Doctor ya kira ya sanar dashi babu komai a cikin shinkafar.
Yayi shiru riƙe da wayar,babu poison a cikin shinkafar,hakan na nufin lokacin da mutumin ya isa gidan misalin ƙarfe goma na dare a wannan lokacin ya basu poison ɗin,sai ya zuba cikin sauran abincin data dafa saboda badda sawu.
Ya hargitsa suman kanshi ya ce"lahaula walaquwwata illabillah".
Bilal ya shigo da sallama,da mamaki ganin shi ko shiryawa bai yi ba ya ce"wai ba ka shirya ba?"
Ya ɗago ya kalle shi da rinannun idanuwan shi ya ɗauke kai.
Bayan ya isa Headquarter office ɗin Brigadier ya tafi,a can ya haɗu da Colonel Barau,kallon kallo su kayi a tsakanin su sannan ya sara mishi.
Ya maida hankalin shi kan Brigadier ya ce"Sir,permission to speak".
Brigadier ya ce "Granted".
Ya ce"Sir, I have completed my investigation into Olatunji family's deaths. I have gathered enough information to present my findings."
Ya jinjina kai ya ce"Go ahead Captain".
"Sir, I don't believe this was an ordinary poisoning. Someone wanted us to believe the food was the cause of everything. But the uncooked rice was clean. Someone had access to the house later that night, and I believe that person is directly connected to what happened."
Brigadier ya jinjina kai ya ce"Do you have evidence identifying this person?"
Ya ce"Not yet, Sir".
Brigadier ya ce"so you believe the case isn't over?"
Ya juya ya kalli inda Colonel Barau ke zaune ya ce"Not yet Sir,saboda akwai wasu abubuwa da ban gama fahimta ba".
Ya kalle shi da kyau suka haɗa ido ya ce"kuma nake son sanin amsar su".
Brigadier ya ce"very good,a tsayar da case ɗin iya haka,kayi submitting complete report ɗinka sai ka bar sauran aikin a hannun mu".
Ya sara mishi ya ce"Yes,Sir".
**********
The Dark Network
Chief yayi jifa da kwalbar giyar dake gaban shi tare da glass cups kusan biyar.
Rai ɓace ya ce"kun yi sakaci da yawa,how on earth za ku bar ƙaramin yaro kamar wannan ya yi wannan binciken?"
Tun farko sai da na sanar da ku leave no traces,gashi cikin sauƙi ya kamo bakin zaren".
Panther ya yi ƙarfin halin cewa"Sir,babu abinda ya gane,duk buga buga ce kawai,i assure you bai fahimci komai ba".
Bracket ya ce"idan bai fahimci komai ba,ya akayi ya san guban ba cikin abinci yake ba,duk iya ƙoƙarin mu sai da ya gano hakan".
Wolf yayi wani shegen murmushi ya ce"wannan yaron da kuke gani ya wuce duk tunanin ku,he is so determined,wanda hakan cikas ne a gare mu,dole ne mu yi maganin shi kafin nan gaba ya fi haka".
Panther ya ce"faɗa ɓata baki Wolf,dole ne mu biyo mishi ta bayan gida,dole mu canza taku".
Chief ya gyara zama ya ce"ina ga it's high time da ya kamata mu canza Broker a wurin nan,bai da wani amfani".
Bracket ya gyaɗa kai ya ce"nima na fahimci hakan gaskiya".
"A samo wani da zai iya mana aikin babu wani gardama".
"An gama Chief".
**********
Bayan kwana biyu baƙi suka fara tafiya,Aunty Maryam har ɗaki ta sami Mami ta sallame ta,Mami ta haɗa ƙaton jaka cike da kaya ta ba da a kai mata.
A ranar Umma ta tashi da shirin komawa gida.
Ƙarfe takwas na safe ya iso gidan,bacci ne a idon shi sosai saboda gajiya da zirga zirga.
A parlour ya tarar da Umman har ta shirya,ya gaida su gabaɗaya sannan ya zauna.
Mami ta ce"na yiwa driver magana,shi zai kaita".
Ya kalleta da sauri,bai kawo hakan a ranshi ba,yayi tunanin motar haya za ta shiga,duk da ya so kaita da kanshi amma motar ba ta da cikakkiyar lafiya.
Sai da suka bar gidan sannan ya koma gida.
Sai da Oum ta ƙara sati biyu sannan suka koma gabaɗaya,sosai Abdallah ya so a tsayar da magana kafin su tafi amma Oum ko nuna ta fahimci abinda yake nufi ba tayi ba.
Bayan sati ɗaya admission ɗin Zarah ya fito a BUK,aka fara neman driver da zai dinga kaita school ya koma ya dauko ta.
Mai wankin gidan yace akwai wani ɗan uwan shi yayi aikin driver a da amma yanzu yana zaune babu wani aiki.
Mami ta ce babu damuwa ya zo ta ganshi.
Bayan kwana biyu sai gashi,ya ce sunan shi Sammani,Mami ta ce ya fara aiki kawai.
Sai bayan kusan kwana uku da fara aikin shi Sadauki ya zo gidan,yana wanke mota yana ƴan waƙoƙin shi ya shigo da mota.
Suna haɗa ido ya sunkuyar da kai da sauri, Sadauki ya dinga bin shi da kallo har ya isa part ɗin Mami.
Mami na zaune tana magana a waya ya shigo,sai da ta gama wayar da take ta ce"Faruq,sannu da zuwa".
"Ina wuni Mami".
"Lafiya ƙalau Faruq,ya aiki?"
"Aiki Alhamdulilah Mami".
Ta shiga ƙare mishi kallo ta ce"wai me ke damun ka ne Faruq,ko dai abinci ne ba ka ci?"
Ya shafa kai ya ce "babu komai Mami,gajiya ce kawai".
"Idan anyi magana ka ce gajiya,ka dinga komai a hankali Please,komai sai da lafiya,gashi tuwo mu kayi a gidan yau".
"Mami kun yi sabon driver ne?"
"Eh,ka san Zarah zata fara zuwa makaranta,shine aka samo mata personal driver".
Kamar zai yi magana sai kuma ya fasa.
Ta miƙe ta shiga kitchen tunda babu kowa a gidan.
Yayi shiru yana sake tuno fuskar mutumin,haka kawai ya ji hankalin sa bai kwanta da shi ba.
Yana nan zaune Mami ta iso parlourn riƙe da plate ɗin indomie,ya tashi da sauri ya ce"Mami !da kin barshi,na ci abinci kafin in fito".
"Ba zai yiwu ka zo gida ka koma haka ba,ba don kayi insisting ba babu abinda zai sa ka bar gidan nan".
Yayi shiru don bai da abinda zai ce.
Ta koma ta kawo mishi ruwa,bayan ta zauna ya ce"Mami anyi bincike a kan mutumin?"
Cike da rashin fahimta ta ce"wani mutum kenan?"
Ya sauke kai ya ce"drivern Mimie".
Ta ce"Oh ! Wai driver ?ai ɗan uwan jamilu ne,Jamilu mai wanki".
Bai sake cewa komai ba yayi bismillah ya fara cin abinci.
A waje ya tarar dashi lokacin da ya fito,da sauri ya ɗauke kai ya durƙusa har ƙasa ya ce"ina wuni".
Ƙasa bashi amsa yayi,ya cigaba da ƙare mishi kallo har sai da Iliya mai gadi ya ce"mazan fama ana gaisuwa".
Sannan ya dawo hayyacinsa ya amsa masa.
Book 1 ya kusa ƙarewa,Book 2 na kuɗi ne.
Pay 1k into *** Khadijah Sulaiman Opay,evidence of Payment Via ***.
Thank you.