Free chapter · Read without an account
MATAR GIDA PAGE 87
by Maimuna Bala · MATAR GIDA
*MATAR GIDA BOOK* 2
*SHUUKRAN*/022
P87
Compound ɗin gidan Hajiya Biklisu ya cika da matan gida zaune saman kujeru,daga can gefe guda kuma an ware wasu kujeru huɗu wa Alhaji Babah da Hajiya daga gefen su kuma Hajiya Bilkisu ce tare da Hajiya Zulfa'u dukkaninsu zaune saman kujeru da aka tanadar domin su yayin da kujerun nasu ke fuskantar inda matan gidan ke zaune,kusan gaba ki ɗaya matan kungiyar hankali ya koma kan Alhaji Babah,ganin kamilin dattijo mai cikar kamalah da dattakun yasa duk hankali ya yi kansa, kallo ɗaya zaka yiwa Alhaji Babah ka fahimci lallai atajirin dattijo ne,sanye yake cikin wata farar shaddah da aka yiwa ɗinkin babbar riga da zahariya idanunsa sanye da farin glass,hannusa riƙe da manyan wayoyi smart phone irin na zamani,babu laifi ita ma Hajiya ta yi fita ta kamalah,sanye take cikin wata atamfa super exculsive kalar purple wanda aka yiwa ado da fararen flower inda ta yafa farin mayafi,ta fito ras da ita kyakkyawar bahausiyar mace,kwanciyar hankali da hutu haɗi da tarin dukiyar Alhaji Babah su suka ɓoye tsofar Hajiya,wanda in ba faɗa aka yi ba ba lallai a yarda ita ta haifi su Hajiya Bilƙisu ba,Hajiya Zulfa'u ce ta buɗe taro da addu'a yayin da Hajiya Biklisu ya fara bayani kamar haka ''da fari ina mai baku hakuri kan kiran gaggawa da na yi maku ba tare da sanar da ku dalilin kiran ba,sannan ina godiya da amsa gayyata ta da ku ka yi''..wajen ya yi shiru baka jin motsin komai sai muryar Hajiya Bilƙisu gaba ɗaya matan kungiya sun mayar da hankalin su kan Hajiya Biklisu suna sauraron ta yayinda zuciyoyin su ke cike da tambayoyi kowace burinta bai wuce son sanin dalilin kirar gaggawa da Hajiya Biklisu ta yi masu ba,abu na biyu kuma shine baƙin fuskoki da suka gani,wanda wasu daga cikinsu suna da tabbacin iyayen Hajiya Zulfa'u ne da Hajiya Biklisu duba da yadda Hajiya Biklisu ta yi mutukar kama da Alhaji Babah yayinda ita kuma Hajiya Zulfa'u ta biyo Hajiya gyara tsayuwa Hajiya Biklisu ta yi daga haka ta daura da ''kamar yadda ku ke gani a yau na zo maku da manyan baƙi'' daga haka ta juya ta kalle inda Alhaji Babah da Hajiya ke zaune ta ce ''su ɗin iyayena ne Alhaji Babah kenan wato mahaifinmu sai kuma Hajiya wacce ita ce mahaifiyar mu'' daga haka ta mayar da dubanta ga matan kungiya da suka tashi tsaye dan nuna girmama ga Alhaji Babah da kuma Hajiya,Alhaji Babah ya yi masu alama da su zauna,bayan sun zauna ne Hajiya Biklisu ta cigaba da magana inda ta ce ''kamar yadda na kafa wannan kungiya a shekarar 2019 wanda hakan ya kama shekaru bakwai daga ranar da na kafa wannan kungiyar zuwa yau''..shiru Hajiya Biklisu ta kuma yi na wasu ƴan mintina kafin ta daura da ''Jiya ina tare da Alhaji Babah mahaifina,ya yi mun nasiha kan kungiya yadda ya fahimtar dani kuskure da barna da nake aikatawa,ban taɓa sanin cewar ina kuskure ba,dalilina na buɗe wannan kungiyar ita ce kwatarwa mata ƴanci amma duba da yadda auren ƴan kungiyar ke mutuwa a kullum mahaifina ya bani shawara na rufe kungiyar wanda tun dah can ba shi da masaniya kan kungiyar matan gida daga baya ya samu labarin kungiyar wanda hakan yasa ya kira ni jiya,ya kuma fahimtar da ni kungiyar bata da amfani,ya kuma nuna min barna da illoli da kungiyar nan ke yi cikin al'umma wanda hakan yasa na zauna na yi tunani mai zurfi na kuma fahimci gaskiya mahaifina ya faɗa'' shiru ta yi na wasu ƴan sakanni tana ƙara saita nitsuwarta,yayin da matan kungiya sun yi cirko cirko zaune sun kafe Hajiya Bilƙisu da ido kamar yau suka fara ganinta,gajerar ajiyar zuciya ta sauke daga haka ta daura da ''na kasance ƴa mai biyayya ga mahaifina bai taɓa bani umurni na saɓa ba saboda haka zan bi umurnin mahaifina,ina mai baku hakuri daga yanzu babu kungiya an kuma rufe kungiya har abada''shiru ta kuma yi a karo na babu adadi can ta buɗe baki a hankali ta ce ''ku cire son zuciya ku zauna ku yi tunani kan abubuwan da na faɗa maku tabbas wannan kungiyar bata da amfani'' daga haka ta zauna tana murmushin yaƙi,kusan gaba ɗaya matan kungiya kansu ya kulle tambayoyi cike a zuciyoyinsu kowacce ta yi shiru tana tunani, suna cikin wannan yanayi Hajiya Zulfa'u ta tashi daga kujerar da take zaune ta yi sallama,ga dukkan alamu da akwai abinda take son faɗi lokaci guda matan kungiya suka mayar da hankulansu kan Hajiya Zulfa'u
Jiki a sanyaye suka amsa sallamar Hajiya Zulfa'u bayan sun amsa mata sallama ne Hajiya Zulfa'u ta fara magana kamar haka''bisa wasu dalilai da wasu abubuwa da suka faru masu kyau da akasin haka,kamar dai yadda ku ka sani ɗaya daga cikin mu Allah ya yi mata rasuwa yau kawanaki tara da rasuwarta,wanda kafin rasuwarta ta samu saɓani da mijinta wanda hakan ya kai ga rabuwar su,ina da tabbacin dukkanin mu mun san dalilin rabuwar Unaisa da mijinta wanda rabuwa ce ta dalilin kungiya,ba iya Unaisa ba mata da yawa sun rasa aurensu sannan sun shiga matsaltsalun rayuwa duk dalilin wannan kungiya,duba da waɗannan abubuwa yasa ni da ƴar uwata muka yanke hukunci rufe kungiyar gaba ɗaya bisa umurnin mahaifin mu,saboda haka ina son yin amfani da wannan dama na roƙe ku gafara dan girman ku yafe mana ni da ƴar uwata duk wacce ta samu matsalah da mijinta ko iyayenta dalilin wannan kungiya ina mai bata hakuri ta yi hakuri ta yafe mana,sa'anan ina baku shawara da ku bi mazajen ku sau da kafa ku kasance masu yi masu biyayya a ko da yaushe hakan zai sa ko haɗu da Allah lafiya kamar yadda kuka sani aure ibadah ce sannan duk matar aure abu ɗaya zai sa ta shiga aljannah shine biyayya ga mijinta bisa shara'a,sannan abu na gaba kamar dai yadda kuka sani ranar da muka tafi taro gidan Unaisa mun haɗa mata kuɗin taro,toh yanzu kuma bata nan bisa tsari duk wacce ta bawa Unaisa kuɗin taro Unaisa zata yi mata zubi sanda nata taron ya zagayu,amma yanzu da bata nan kunga babu wannan zancen,kamata ya yi mu sanar da iyayenta tun kafin a yi jana'iza,tabbas na yi wannan tunanin san da aka sanar da ni haɗarin amma na yi shiru ban faɗawa iyayenta maganar kuɗin ba saboda na kudira zan biya mata,wanna dalilin yasa ban sanar da su ba,a takaice dai duk wacce ta san baza ta iya yafewa ba ta tura min account number insha Allahu yau zan sa mata kuɗinta,sannan dan Allah mu yafewa juna saboda yau ita ce rana ta karshe da zamu sake haduwa irin haka,da yardar Ubangiji daga rana irin ta yau babu kungiyar matan gida insha Allah,wassalamu alaikum''...daga haka Hajiya Zulfa'u ta zauna a kujerarta fuskarta sake,wajen ya dauki shiru,sosai matan kungiya sun yi mamaki zantuka Hajiya Biklisu da Hajiya Zulfa'u ko kaɗan basu taɓa kawo kungiya zata mutu cikin ƙananun shekaru haka ba,duba da yadda kullum Hajiya Bilƙisu cikin kawo sabbin tsare tsare take cikin kungiya,kusan duka matan kungiya basu ji dadin rufe kungiya ba,zuciyoyin su cike da tambayoyi amma sun ƙasa furta komai,kenan shikenan babu kungiya duk yadda ake ji da kungiyar a garin Kaduna,kusan duka matan kungiya kullum cikin alfahari suke kasancewan su ƴan kungiya saboda duk inda suka shiga hankalin jama'a na dawowa garesu,bikin dangi ko makwabta in suka shiga za a yi ta nuna su wanda hakan na masu dadi kaman wasu celebrities haka suka zama,amma gashi dare ɗaya za su rasa wannan matsayin fuskokin su cike da damuwa suka fara yiwa juna raɗa a kunne,Alhaji Babah yana lura da yanayin da matan kungiya suka shiga wannan dalilin yasa yaƙi tashi daga wajen yana jiran su tafi,suna zaune sai ƙananun maganganu suke,ƴar aikin Hajiya Biklisu ta fito hannunta riƙe da katan ɗin guda lemo ɗaya,ɗaya hannu kuma riƙe da katan ɗin ruwa,haka tayi ta kaiwa da komuwa har ya gama fitar da ruwa da lemo babu wacce ta taimaka mata,ko kallo bata ishe su hasalima hankalinsu baya kanta,duk wasu bayanai da Hajiya Biklisu tare da Hajiya Zulfa'u suka yi masu basu gamsu da bayanan su ba suna bukatar ƙarin bayani,haka dai suka yi ta ƙananun maganganun da junansu,tare da yiwa juna raɗa a kunne,shi dai Alhaji Babah na nan zaune,daga karshe dai suka dauki ruwa da lemo sun yi tafiyarsu bayan sun yiwa Alhaji Babah da Hajiya sallama,washe gari kamar yadda Alhaji Babba ya faɗa Hajiya Zulfa'u tare da Hajiya Biklisu za je neman gafara gidan iyayen matan da aka saka dalilin kungiya hakan ne kuwa ya faru,ranar da Hajiya Zulfa'u ta sanar da Alhaji Babah labarin kungiyar matan gida a ranar ya tambayeta sunaye da kuma adireshin gidajen matan da mazajen su suka saka dalilin kungiya,ɗaya bayan ɗaya Hajiya Zulfa'u ta lissafowa Alhaji Babah sunayen su,daga karshe ya ce ta rubuta sunayen su da adireshun su cikin takarda ta basa,misalin ƙarfe goma da wasu mintina Alhaji Babah da iyalan sa suka fita yau ma kamar jiya driver Alhaji Babah shi ya yi driving ɗinsu ɗaya bayan ɗaya suka bi gidajen iyayen matan da aka saka,da gidajen tsuffen mazajensu kamar yadda Alhaji Babah ya faɗa,duk wani tsoro da firgice da ya cika zuciyar Hajiya Biklisu da Hajiya Zulfa'u wanna tsoron ya kaura dalilin gidaje biyar cikin jerin gidajen iyayen mata da aka saka dalilin kungiya iyayen mata sun yafewa su Hajiya Biklisu sun kuma yi masu nasiha da addu'ar shiriya ɗaya daga cikin iyayen matan mai suna Mallam saminu ya kalle Hajiya Bilkisu ya sake murmushi cikin kwantar da murya babu hayaniya ba tare da hayaniya ba ya ce ''ita aure wata aba ce mai rai ko Hajara ta shiga kungiyar matan gida ko bata shiga ba Allah ya rubuta cikin kaddararta akwai mutuwar aure saboda haka ni ban ga laifin ki ba kaddararta ce hakan,kuma na yi farin ciki da zuwan ku na kuma yi murna da ku ka ce kun rufe kungiya Allah ya tsare ƴan baya Allah kuma ya yafe mana baki ɗaya'' sosai Hajiya Biklisu da iyayenta suka ji dadin addu'ar da mahaifin Hajara Mallam saminu ya yi hakan yasa Alhaji Babah daukan kudaɗe masu yawa ya basa,da kyar Alhaji Babah ya shawo kan Mallam saminu ya karɓi kudin,bayan fitowarsu daga gidan Mallam saminu basu tsaya ko ina ba sai gidan Mallam Murtalah mahaifin khadijah,tun bayan isowarsu gidan suka fahimci za a samu matsalah,tun sanda Hajiya Zulfa'u ta gabatar da kanta da kuma ƴar uwarta Hajiya Biklisu da kuma iyayensu suka ga canji fuskar Mallam Murtalah da fari gida ya shiga ya barsu zaune soro tsawun mintina ashirin kafin daga bisani ya fito,bayan fitowarsa ne Hajiya Biklisu ta shiga jero bayanai yadda Hajiya Zulfa'u na bin bakinta suna magana tare,wajen ya yi shiru baka jin motsin komai sai muryuyin Hajiya Biklisu da Hajiya Zulfa'u,har suka idah zancen su Mallam Murtalah bai tanka su ba,bayan wasu ƴan sakanni ya ɗago ya kalle su shiru tsawon mintina can ya buɗe baki ya ce ''allah ya isa ban yafe maku ba ina roƙun Allah ya yi maku abinda ku ka yiwa ƴata'' ya yi magana cikin tsananin zafin zuciya,da wani irin sauri Hajiya Bilƙisu ta sunkuyar da kanta ƙanta ƙasa haka zalika Hajiya Zulfa'u kamar hadi baki lokaci guda hawaye ya fara bin fuskokin su,abinda suke gudu kenan shi yasa dukkaninsu basu so zuwa neman gafara ba sai dai baza su iya yin musu da mahaifinsu ba,ba iya su Hajiya Biklisu ba har Alhaji Babah da Hajiya sai da suka yi mamakin furucin Mallam Murtalah,fuskokinsu dauke da tsantsar mamaki suke kallon Mallam Murtalah dukansu sun ƙasa cewa komai gyara zama Mallam Murtalah ya yi kafin ya ce ''ina da ƴaƴa uku duka mata dukaninsu na aurar da su,cikin ƴaƴana Khadijah ce kadai ta yi dacen miji na gari yaron kirki da sanin ya kamata sosai wannan yaron ya taimaki rayuwarmu ya bani jali masu yawa ni da ƴan uwan khadija da suke aure cikin wahalah,Allah ya daurawa matata mahaifiyar su Khadijah cutar ciwon ƙoda duk wata ake tafiya da ita Abuja ana kwashi ruwa daga cikinta wanda tsohon mijin Khadijah ya dauki nauyin komai,bayan rabuwar Khadijah da tsohon mijinta,ya cigaba da biyan kuɗin asibitin mahaifiyarta amma a kwana a tashi aikin da ake mata duk bayan wata guda ya dawo bayan watanni biyu daga karshe ma ya daina bada kudin aikin na sani mutuwa da rayuwa ta Allah ce amma wannan tsinanniyar kungiyar taku ita ce sanadiyar mutuwar matata'' yana kaiwa nan ya kai hannu ya goge hawaye tare da sauke ajiyar zuciyar zuciya, kallo daya zaka yi masa ka fahimci yana cikin kunci da bakin ciki,duk suka yi shiru babu wanda ya iya cewa komai can Mallam Murtalah ya yunƙura tare da miƙewa tsaye yana shirin shiga cikin gida Hajiya ta ce ''bawan Allah,muna yiwa mahaliccin mu laifi mu nemi gafara sa ya yafe mana,tabbas Biklisu da Zulfa'u basu kyauta ba wanda sun gane kuskuren da suka yi suna neman yafiyarka ka yi hakuri ka yafe masu ba dan halin su ka dubi girman Allah ka yafe masu'' wata iriyar murmushi mai sauti Mallam murtalah ya yi kafin ya ce ''dalilin wannan kungiya yanzu haka khadija na can ƙyauye ta yi aure ta na rayuwa irin na ƴan uwanta,tabbas haka Allah ya tsara masu bana da wata dabara ko hikimar canza kaddarar su amma Hajiya ki sani ƴaƴanki sune silah'' a hankali Alhaji Babah ya mike ya fita daga soron,driver na ganinsa ya buɗe masa mota ya shiga ya zauna,har cikin zuciyarsa bai ji daɗin kalaman Mallam Murtalah ba amma da ya yi duba da irin barnar da kungiyar ta yi masa sai ya masa uzuri,ya riga da ya yi tunanin hakan zai iya faruwa shi yasa tun kafin su taho Kaduna ya ce ba zai bada hakuri ba duk wanda ya ga zai iya yafe masu daidai wanda kuma ya ce ba zai yafe ba shima ya yi daidai saboda haka ba zai taɓa bawa Alhaji Murtalah hakuri ba,a can soro kuwa duk yadda Hajiya ta yi dan ganin ta shawo kan Mallam Murtalah ya yafewa su Hajiya Biklisu abin ya ce tura,sosai hankalinta ya tashi ganin zallar ɓacin rai kwance ƙarara fuskar Mallam Murtalah yasa hankalin Hajiya ya kasa kwanciya in har Mallam Murtalah bai yafe masu ba tabbas za su rayu ne da hakkinsa kansu,gaba ki ɗaya Hajiya ta ji baza ta iya dauka ba a kan idonta rayuwar ƴaƴanta ya tagayyara, bata san sanda ta fara kuka ba tana rokon Mallam Murtalah,ganin Hajiya na hawaye na rokon Mallam Murtalah ya yafe masu ya sa Hajiya Biklisu nadamar duk wani abinda ta aikata,tare da Hajiya Zulfa'u suka shiga bawa Mallam Murtalah hakuri suna kuka tare da Hajiya,ganin yadda Hajiya ke kuka yasa Mallam Murtalah kallon Hajiya na wasu ƴan sakanni tabbas shi kadai yasan irin halin kunci da ya tsinci kansa ciki bayan mutuwar auren Khadijah amma ganin yadda Hajiya ke kuka sosai ya sa ya bawa zuciyarsa hakuri muryarsa a dakeli ya kalle Hajiya ya ce ''shikenan Hajiya Allah ya yafe mana baki daya'' Hajiya ta sauki wata iriyar ajiyar zuciya daga haka ta shiga jero masa godiya,tabbas babu uwa ta gari da zata yi sake rayuwar ƴaƴanta ya shiga haɗari kan idanunta,tabbas Hajiya ta kasance ko yaushe tana goyon bayan Alhaji Babah amma a wannan baza ta biye masa ƴaƴanta su rayu da hakkin wani kansu ba sam baza ta lamunta ba
*SHUUKRAN*