Free chapter · Read without an account
Chapter 40
by MARYAM STAR · ƊAURIN ZUCI
Channel link
***
Whatsapp group link.
***
𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
Chapter 40
Cikin abin da bai rufe watanni uku ba aurena da Abubakar Saminaka ya tabbata da izinin Ubangiji, daga lokacin na tattare komi daya danganci kasuwancina na jingenar a gefe, kasancewar nima babu laifi na tara abin duniya sai kawai na nemi share a companyn da nayi aiki da su, ɗaya na kayan yara ɗayan kuma na kayan kwalliyar mata da gold, sai da komi ya kammalu sannan muka tattaro ni da mijina muka dawo ƙasar shi ta haihuwa.
Babban ƙalubalen dana soma cin karo da shi tun farkon isowata ƙasar ita ce matar shi Hajiya Hafsa, da fara'ata na nufe ta zan rungumeta ganin ta rungumi mijina, amma sai mi zai faru, wani baƙin kallo me cike da gargaɗi da tsana ta watsa min, nan take jikina ya yi sanyi ƙalau, kasancewar ita ce ta zo ɗaukar mu a airport dole haka na bi bayansu na shiga motar ƙirar golf.
A hanya in banda kalle-kalle babu abin da nike yi, ƙasar Nigeria nada abubuwa masu ɗaukar hankali sosai, tun daga mutanen cikinta zuwa abubuwa da hidindumun da suke yi na yau da kullum, komi abin sha'awa.
A bakin wani wawakeken gida wanda a zamanin ya kasance me tsananin kyau kuma gini me inganci ta faka motar, dakanta ta buɗe get ɗin sannan ta dawo ta shiga da mu ciki.
Sosai na buɗe idona ina ƙarewa dukiyar da Abubakar ya narka wajen ƙera gidan shi kallo, har bansan lokacin da ya zagayo kusa da ni ba ya rungume ni kaɗan tare da yi min raɗa a kunne.
"Waya faɗa miki amarya na kalle-kalle irin haka a ƙasarmu, so kike ace baki da kunya?."
Ya raɗa min fuskar shi ƙayace da murmushi.
Bandamu da inda muke ba na saka hannayena na rungume shi ina dariya tare da faɗa ma shi gidan ne ya burge ni.
Ba tare da nasani ba ashe na buɗe wata ƙofa ta ɓaraka tsakanina da matar Abubakar Saminaka.
Ina jingine a jikin shi yaja hannuwana muka shige ciki ba tare da ya ko kalli sashen da take a tsaye ba, da shigar mu kuma yayi sashen sama da ni yana ɗauke hankalina da tattausar firar ƙauna.
A wannan ranar kuma soma gudanar da rayuwar auren mu ni da Saminaka, bai ɓoye min komi ba nadaga maraicin shi da kuma jinkirin haihuwa da matar shi ta samu domin kuwa cikin shekara ta huɗu suke da yin aure amma Allah bai basu haihuwa ba, kuma a washe garin ranar ne na soma gane wasu daga cikin ɗabi'un Hafsa, domin kuwa ƙiri-ƙiri ta ke nuna tsanata akan fuskarta, lokacin dana fito daga ɗaki ni da Saminaka na same ta tana shirya kayan kari sai na nufi wajenta da fara'a da zummar in rungume ta mu gaisa, da wani irin sauri taja da baya tana ɓallamin harara, nikuma sam bana jin daɗin yanayin yanda bata sake min, na yi zaton yanda nike son mijinta da zuciya ɗaya haka itama zata soni ta ƙaunace ni mu haɗu mu bashi farinciki.
Soyayya da kulawa sai abin da yayi gaba tsakanina da Saminaka, banajin kunyar yarairayar shi ako ina kuma gaban kowa, kamar yanda shima baya iya ɓoye tawar soyayya da ta yi ma shi mugun kamu.
Bamu jima sosai ba da yin aure ya amshi riƙon ɗan uwansa Muhammad daga hannun wata ƙawar mahaifiyarsa, kasancewar a wajen haihuwar Muhammad ɗin ta rasu kuma batada dangin na kusa da zasu riƙe ɗan shine ƙawar ta amsa, ashe kafin ya aure ni ya nuna zai bawa matar Hafsa riƙon yaron amma fir taƙi amincewa, nikuma a kallon farko yaron ya shiga raina har nace a barmin shi ɗan Allah, kamar da wasa Saminaka ya ce min yabar min yaron.
Cike da tsantsar soyayya naci gaba da rainon Muhammad dan kuwa sosai ya shiga raina.
Wata rana ina zaune a ɗakina ina shirya Muhammad sai Saminaka ya shigo, dama daga inda nike ina jiyo hayaniyar muryar matar shi da bata gajiya da kai ma shi ƙorafi a kaina, ni kuma bana damuwa idanma a gabana ta yi maganar don a zauna lafiya cike da girmamawa nike bata haƙuri duda bansan abin da nayi mata ba.
"Yanda kike kulawa da yaron nan ba ƙaramin ƙara ƙaunar ki nike ba, naso ace Inna na raye taga yanda addu'arta ta yi tasiri akaina Allah ya haɗa ni da irin macen da take roƙa min." Bai bani damar yin magana ba yaci gaba da faɗin.
"Rimsha nasan ko wacece ke, kuma nasan abin da za ki iya da wanda ba zaki yi ba, ina so ki fahimce ni dan Allah bawai na zartar da hukunci bane don na tauye ki kawai ina buƙatar nutsuwa a cikin gidana ne."
Sai da ya lumfasa sannan yaci gaba da faɗin.
"Ina roƙon ki alfarma du ranar da Hafsa ke da girki ki ɗauki Muhammad da abin buƙatar shi ki kaiwa Hafsa shi, bayan kwana biyu sai ki dawo da shi ɗakin ki, dan Allah kiyi biyayya kamar yanda kika soma yi adukanin abin da na zartar."
Ya ƙare da roƙona fuskar shi da ƴar damuwa.
A lokacin naji babu daɗi sam saboda na soma sabawa da rainon Muhammad ɗin, amma sai na shanye hakan na ƙawata fuskata da murmushi, cike da nuna ma shi na fahimce shi na ce.
"Habiby hukuncin daka zartar ya yi, Allah ya raya mana Muhammad akan sunna, da wajena da wajen Anty Hafsa du ɗaya ne tunda dai a gida ɗaya zamu rayu ba rabamu ka yi ba zan iya ganin shi du sanda na buƙata.
Yanzu zuwa yaushe zan kai mata shi?."
Na tambaya ina danne kewar yarona data fara taso min.
Jana ya yi a jikin shi ya manna min sumba sannan ya ce.
"Ko yanzuma tunda a shirye ya ke za ki iya kaishi sai ki dawo nima kiji da ni."
Aiko ban musa ma shi ba na soma tattaro kayan Muhammad na haɗa tsaf na saɓe shi ina aika ma shi sumbata na fice da shi.
Kamar zan yi kuka haka na miƙawa Hafsa shi wacce ke zagina gami da jefamin mugayen maganganu da yaren hausa ni kuma ba sosai nike fahimtarta ba shiyasa bana damuwa idan tana surutanta.
A ranar sosai na zage wajen kulawa da Saminaka har yake tsokanata dama saboda Muhammad na rage ba shi kulawa aikuwa da wuri zai kai shi kamaranta.
Ashe dama du dan Hafsa na ƙuntata min ta saka ake kai mata Muhammad wajenta, sam bata wani kulawa da shi, haka nan zata barshi wasarairai idan na je da niyyar ɗaukar shi kuma ta balbale ni da zafaffan maganganu marasa daɗi, ta kuma hana ni ɗaukar shi, daga ƙarshe ta sanarwa Saminaka kar ya sake barina naje sashenta da niyyar kawo Muhammad ko ɗaukar shi, yanda bata zuwa ɓangarena nima kar in kuma zuwa mata ɓangaren.
A lokacin ina mamakin yanda babuja Saminaka ke biyewa maganganunta, sai de bantaɓa ƙullatar hakan ba, sai in share in nuna babu komi inci gaba da sabgogin gabana.
Rayuwa ta miƙa mana, zamana da mijina lafiya babu wani damuwa saima daɗa shaƙuwa da fahimtar juna haɗi da kusanci da muke samu ni da shi, yanzu Muhammad ya soma yin wayo yana banbance ni sosai ya daina yarda da Hafsa, kuma sam baya fahimtar yaren Hausa shima da larabci nike yi ma shi magana.
Ɓangaren Saminaka kuwa sai de ace alhamdulillah domin kuwa sosai ya miƙa a sabgar kasuwancin shi ƙofofin arziƙi sai daɗe buɗewa suke yi.
A lokacin da aurena da shi ya cika shekara ɗaya da watanni a lokacinne na samu juna biyu, lokacin kuma Muhamamd nada shekara ɗaya shima da watanni, laulayi nayi ɗan gaske domin kuwa bana iya yiwa kaina komi kamar yanda bana iya cin komi, sosai muke ziryar yawon asibiti kusan kullum ni da Saminaka, yanzu Muhammad baya wani samun kula ganin haka sai kawai aka ɗauko min ƴar aiki.
Sunanta Ma'u ita ke yi min aikin komi saboda bana iyawa kuma ita ke kula min da Muhammad, ana biyanta albashinta yanda ya dace shiyasa take jin daɗin aiki a gidan.
A mafi yawanci lokuta ina ganin Hafsa tsaye a kaina tana ƙaremin kallo, sannu ko ya jiki bai taɓa haɗani da ita ba, haka zata gama ƙare min kallo ta juya ta tafi abinta.
Bayan kwana biyu na soma samub sauƙi jikina ya fara kyau, kwatsam a wata rana da baƙar ƙaddara ta soma wanzuwa tsakanina da Hafsa, ƙaddarar data zama sanadiyar ƙula ƙullaliyar gaba tsakanina da ita, gabar data kusa zama sanadin watsar da zaman lafiya a gidan Abubakar saminaka.
Da safe ne ranar Saminaka yana da meeting a company, ya fita ya barni daga ni sai ƴar aikina, bayan tafiyar shi da kamar awa ɗaya Hafsa ta shigo sashe na ita da Ma'u, tana jifana da wulaƙantacen kallo ta ɗora ƙafarta ɗaya akan gadona ta kalleni a lalace sannan ta ce.
"Ba ke me mahaifar ɗaukar ciki ba, naga ta yanda za'ayi kizo bayana sannan ki rigani ajewa Abubakar ɗa, muddin ba haihuwa babu macen da zata taɓa haihuwa a gidan nan, zan lalata mahaifarki inga abin da zai faru, shi kanshi wanda kike taƙama da shi ɗin a tafin hannuna yake, sai abin da nace zai yi bar ganin yana yana rawar ƙafa akan ki na kusa saka wuƙa na yanke zaren daya haɗa alaƙar ki da shi."
Tana gama faɗin hakan ya turani da ƙarfi na faɗi akan bed, ta danne ni da duka ƙarfinta ta miƙawa Ma'u hannu ta bata wani kofi, ta matse bakina da ƙarfi ta soma ɗura min ruwan maganin.....
Kuyi haƙuri da wannan pls
MARYAM STAR AMANAR BILYN-ABDUL.