Free chapter · Read without an account

Chapter 21

by Narrnarhh Bukar · BA NI DA MADOGARA

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*












*Ba ni da Madogara*
  (Sai Allah...)




 

021
    

A daidai lokacin Arqam ya ƙaraso wurin a fusace kuma ya ji mai Akmal ya ce. Sake tamke fuska ya yi sannan ya dubi Akmal ido cikin ido ya ce

"She will never be yours Akmal Saboda wannan da kake ganinta a gabanka she is mineee!!! Sannan akwai aure a... " 

"Arqamm!!!" cewar Mas'ud yana ƙarasowa wurin da sauri don yasan Arqam kaɗan daga cikin aikinsa ya ce Hujayrah matar Uncle Ayyub ne, shi ke nan ya rusa musu plans ɗinsu. Yasan waye Akmal akan bin diddigin abu, zai iya cewa sai ya yi bincike a kai wanda a ƙarshe a samu matsala. Arqam da ya ji Mas'ud ya kira sunansa sai kawai ya fasa ƙarasa abin da ya yi niyyar faɗa ya jira ya ƙaraso wurin shi da Mahmoud. Suna ƙarasowa wurin Mas'ud ya ce

"Arqam let's go in kasan Hajiya momma na jiranmu ko, Ke Hujayrah ku zo ku wuce ciki sarakan wasa" ya yi maganar ne don ya kawar da hankalin Khalil da Akmal don tun lokacin da Arqam ya fara magana Akmal da Khalil suka tsura masa ido suna so su ji last statement ɗinsa. 

Tafiya Hujayrah da Razina suka fara yi wanda lokaci guda Akmal ya tsura wa bayan Hujayrah ido, saboda yadda take tafiya a hankali ƙugunta na juyi kamar da gangan take yinsa. Inda Akmal ya tsura wa ido a nan Arqam ya kai dubansa, lokaci guda ya tamke fuska tare da furta "Casanova wannan tafi ƙarfinka wallahi " 

Wani munafikin murmushi Akmal ya saki yana shafa ƙasumbarsa ya dubi Arqam ya ce

"Arqam da alamu ka manta halina, ka manta idan na ƙwalla rai akan abu saina sameshi koda kuwa ran kowa zai ɓaci, Hmmmm saina mallaketa ko ka ƙi ko kaso, she will definitely be mine, and me alone! " 

"Never!" cewar Arqam yana niyyar kai wa Akmal naushi. Da sauri Mas'ud ya riƙe hannunsa tare da jansa shi da Mahmoud zuwa ciki sai, tirjewa yake amma sun ƙi sakinsa don idan basu ja Arqam cikin gida ba, faɗa zai kaure a tsakaninsa da Akmal daman sun saba, a duk lokacin da za su haɗu sai sun sai da hali ko a ina ne, kamar yadda mahaifansu basa ga maciji haka suma suke. 

"Akmal kwantar da hankalinka cikin ruwan sanyi za mu yi maganinsa, nima na yi maka sha'awar yarinyar don tanada komai na hutawa wanda ɗa namiji yake buƙata,yanzu mu shiga ciki don a gajiye nake wallahi" cewar Khalil yana miƙa tare da hamma. Murmushi kawai Akmal ya saki yana sake tuno da surar Hujayrah yadda ƙugunta ke juyi, bai taɓa arba ta macen da faradɗaya ta shiga ransa sai akan wannan ɓakar yarinyar mai Koren idanu, sosai yake jin ƙaunarta a ransa. Gyara parking ya yi sannan ya fito suka ƙarasa sashen Hajiyan Sama. 

Bayan Mas'ud da Mahmoud sun ja Arqam ciki, kai tsaye suka wuce part ɗinsa. Suna shiga ya fizge hannunsa daga riƙon da suka yi masa yana cije lips. Kai kawo yana fara yi a ɗakin ya kasa zama sai can ya furta

"Dammn It! Ƙarya kake Akmal! Never wallahi! " 

Murmushi mai sauti Mas'ud ya yi don ya daɗe da harbo jirgin Arqam, kishin Hujayrah yake yi tun a ranar da ya dawo Nijeriya ya fahimci Arqam na son Hujayrah sai dai shegen miskilancinsa ya hana ya bayyana hakan sai dai kishin da yake nunawa a kanta. Basu bi takansa ba sai ma fita suka yi daga ɗakin zuwa part ɗin Hajiya momma wanda daga can wucewarsu  suka yi. Sun san halinsa tunda ya yi fishi babu mai iya bashi haƙuri ko yi masa magana shi da kansa zai sauka, Suna fita ya wuce bedroom ɗinsa, a nan ma bai tsaya ko'ina ba sai a toilet, sakar wa kansa ruwa ya yi daga bisani ya fito ya sauya kaya zuwa farar jallabiya mai taushi yabi lafiyar gado... ✍️?

           🌎🌎🌎🌎🌎🌎 

*ƙarfe 10:12pm na dare*

A daidai wannan lokacin Hajiyan sama da Alhaji suna kwance da bedroom ɗin Alhaji kasancewar ita ce da kwana. Tashi daga kwance Hajiyan Sama ta yi tana duban Alhaji ta ce

"Alhaji akwai maganar da nake so mu tattauna a yau don Allah" 

Alhaji da ke latsa wayarsa ya ɗago yana dubanta ya ce

"OK ina sauraronki Izzatu" ya yi maganar  yana tashi daga kwancen sai ya zuba mata idanu.

Gyara zama ta yi sannan ta fara magana cike da barikanci. 

"Alhaji daman akan su Arqam ne da Khalil har dasu Nazima da Fauziyya, ganin su Arqam da Khalil sun kammala karatunsu sannan Alhamdulillah kowannansu yanada aikin yi, sannan su Nazima da Fauziyya kowacce a cikinsu Allah ya bata nasarar kammala karatunta har da bautar ƙasa kowannansu ya yi. Mai zai hana ya yi ƴar cikin gida, ayi tuwona mai na" ɗan numfasawa ta yi tana sauraron abin da zai ce. Murmushi kawai ya yi tare da cewa

"Ina jinki Izzatu" 

Murmushin nasara ta yi sannan ta ci gaba da cewa

"Ganin haka yasa wani tunani ya zo min a rai, mai zai hana a haɗa Arqam da Fauziyya sai Khalil da Nazima kaga shi ke nan mun yi dakan ɗaka shiƙan ɗaka, wani zumunci mai ƙarfi zai saƙe kulluwa a tsakaninmu, nasan Mubina ma za ta yi farin ciki da hakan" ta karashe maganar tana sakar masa sanyayyan murmushi. 

Ɗan shiru Alhaji ya yi yana tunani, sun daɗe  a haka har gaban Hajiyan Sama ya fara bugu, tsoro take kar ya ƙi amincewa, ta tsura masa idanu tana jiran ta ji amsarsa, sun kai kusan minti biyu a haka daga bisani Alhaji ya sauke ajiyar zuciya. Cike da damuwa ya fara magana

"Izzatu ba naƙi taki shawarar ba ne sai dai wani hanzari ba gudu ba, wannan haɗin da kike so ki yi ba zai taɓa yiwu ba" 

Rassss! Ƙirjinta ya bada, lokaci guda ta waro idanunta  waje tana kallonsa, cike da fargaba da tashin hankali ta ce

"Alhaji! Ke nan baka son auran?" 

Girgiza mata kai ya yi sannan ya ce

"Ko ɗaya Izzatu sai dai abin da baki sani ba shi ne,ita Nazima tun tana yarinya na bada auranta ga Mas'ud ɗan Nafisa, kasancewar bai ƙarasa ginin da yake yi ba yasa na jinkirta auran nasu. Shi kuma Arqam yanzu haka an saka ranar auransa da Tahseen ɗiyar ƙanwata Ramla daman zuwa gobe da safe na yi niyyar faɗa miki auran Arqam, da yake ba a saka ranar mai tsayi ba, in two weeks coming in Shaa Allah za a yi bikin"

Hajiyan sama ta kai maƙula a ɓacin rai ke nan plans ɗinta ya rushe wanda ta yi shekara da shekaru tana shiryawa. Ashe kuwa kowa zai rasa don babu wanda ya isa ya hanata cika burinta akan dukiyar Hajiya Mubina. Wani munafikin murmushi Hajiyan Sama ta saki sannan ta ce

"Ai duk ɗaya ne Allah ya kaimu lokacin"  Bata jira amsarsa ba kwanta abinta. Daren ranar bata rintsa ba, Allah-Allah take gari ya waye ta kira Hajiya Zinatu su fara shiri don gobe take so ta fara cika aikinta akan Hajiya Mubina da Arqam , don shi yafi tsole mata idanu ba Nazima ba. 

Washe gari da wuri misalin ƙarfe 9:30am na safe Hajiyan sama tabar gidan ita da amintaccan dribanta . A daidai wani junction ta haɗu da Hajiya Zinatu da yake Nadiya ta yi driving ɗinta. Motar Hajiya sama Hajiya Zinatu ta koma sai Nadiya ta wuce gida, su kuma suka nausa hanya zuwa Rigar Alhaji Baushe wanda take a cikin ƙurmin daji a cikin garin Bauchi, duk da ba cikin rigar bokan yake ba sai sun sake nausawa cikin dajin kafin su kai daidai inda dutsen da boka Turnuss yake da zama.

Sun daɗe suna tafiya kafin su isa kasancewa akwai nisa sosai daga inda suke zuwa rigar Alhaji Baushe. Bayan sun isa rigar Alhaji Baushe sun ɗan huta daga bisani suka sake nausawa cikin dajin wanda sai da suka yi tafiyar mintuna ashirin kafin amintaccan dribansu ya yi parking a wani wuri, sai suka ƙarasa cikin dajin inda dutsen da boka Turnuss yake ciki. Suna isa kowaccansu ta zube ƙasa lokaci guda suka fara yin wasu surkulle da cewa 

"Turnuss tusun-tusun tunsaaaa!!! Turnuss tuwat tuwiii tuntar tutun!" 

Lokaci guda babban dutsen ya fara girgiza yana fidda baƙin hayaƙi daga bisani dutsen ya rabe biyu, wata ƙofa ta bayyana mai girman gaske, a saman ƙofar kungi ne mai suffar zaki yana fidda siririn hayaƙi fari. Buɗewa ƙofar ta yi sai su Hajiyan Sama suka shiga ciki ba tare da tsoro ko firgici a tattare dasu. Suna saka ƙarfarsu ciki haske ya karaɗe ko'ina a cikin wurin,lokaci guda ƙofar ta rufe ruf! Dutsen ya koma yadda yake kamar bai taɓa tsagewa ba. 

Ɗakin babba ne sannan a kowani ɓarayi akwai kungin zaki yana fidda siririn hayaƙi kamar na waje, bakin zakin a buɗe yake sai ya kasance akwai candle a ciki an kunna, a daidai tsakiyar ɗakin rami ne mai zurfi wuta na ci a ciki. Wata halitta ce a gaban wutar amma ta juya  baya, sosai na razana da ganin bayan mummunar halittar, akwai ƙusumbi a bayansa, sannan duk ilahirin baya nasa akwai huji-huji kamar rani ƙananu babu kyawun gani. Ƙeyarsa a suɗe take kamar ba a yi wani abu wai shi gashi ba, don kana iya ganin ƙallin wutar a ƙeyarsa. Kusa da wutar suka samu wuri suka rakuɓe kamar marasa gaskiya. Sun Kai tsawan mintuna uku bai juyo ya kallesu ba. Daga bisani kamar walƙiya ya juyo tare da tsura musu manya-mayan idanunsa masu kama da na mujiya. Boka Turnuss bai da kyawun gani, domin yanada ƙaramar fuska kamar ta yaro ɗan shekara biyar da manyan idanu sun kusan cike fuskar, sai hancinsa wanda ya wuce bakinsa. Ba ma ka iya ganin bakinsa saboda ƙanƙantarsa. 

Da sauri suka sauke idanunsu ƙasa, bushewa da dariya ya yi wanda hakan ya haifar da ɗaukewan hasken wurin, sai da ya yi dariya sosai daga bisani ya tamke fuska kamar ɗaukewar ruwan sama. Lokaci guda candles ɗin ɗakin suka kawo haske. Cikin muryarsa mai amo haɗin da ƙaraji ya fara magana

"Meke tafe dakuuuu!!!" 

Kasancewar tun a hanya Hajiyan sama ta sanar wa Hajiya Zinatu amsar da Alhaji ya bata akan auransu Arqam da Fauziyya, nan ta kai a hanyar suka ƙulla abin da kowannansu ya dace ya faɗa da kuma abin da suke so boka Turnuss ya yi musu. Gyara zama Hajiyan Sama ta yi sannan ta fara magana da cewa

"Ya kai sheɗanin boka mai zaki! Na zo gareka akan wata matsala tawa wanda nasan ka kaɗai ne mai iya maganinta,ina so ka saka wa kishiyata cutar da bata da magani, wanda za a kashe kuɗi ba tare da biyan buƙata ba, Ina so dukiyarta ta ƙare akan nema mata magani"

Jinjina mata kai ya yi sannan ya ce

"Mun ji kuma za mu yi!!! Aikinki an gama! " 

Yana ƙarashe zance ya miƙa hannunsa na hagu  sama, surkulle ya shiga yi daga bisani wata tukunyar ƙasa mai murfi ƴar ƙarama baƙa ta bayyana a hannunsa, kamar walƙiya  tukunyar ta koma gaban Hajiyan Sama. 

"A ciki tukunyar akwai kwalba da laya, za a yi amfani da ruwan kwalbar a girka mata abinci ta ci, sai layar a birneta a cikin gidan ko a ina ne, da zarar kin yi haka to shi ke nan za mu tura mata ciwo" 

Jinjina masa kai ta yi cike da farin ciki. Daga bisani idanunsa suka koma kan Hajiya Zinatu, ko ba a faɗa mata ba tasan mai kallonsa yake nufi. Gyara zama ta yi sannan tafara magana da cewa

"Ya kai shaiɗanin boka mai Zaki! Na zo gareka akan wata matsala tawa wanda nasan ka kaɗai ne mai iya maganinta, Ina so a zubar da cikin da ke jikin kishiyata sannan a hanata haihuwa har abada,bayan haka ina so nasan wane ne ya cire asirin da na birne?" 

"Mun ji kuma za mu yi, wacce ta cire aikin sheɗaniyar kanta ce, don jinsin masu taimakonta shuwagabanin mu ne, mu bayi ne  a ƙarƙashinsu"

Yana gama maganar ya miƙa hannunsa na hagu tare da yin wasu surkulle wanda ba iri ɗaya da wanda ya yi a lokacin da Hajiyan sama ta faɗa masa nata buƙata ba . Wani kwalba ne baƙi ya bayyana a hannunsa, sai kuma ɓata! Ya ɓace wanda bai bayyana a ko'ina ba sai a gaban Hajiya Zinatu. 

"Za ki zuba ruwan da ke cikin kwalbar a cikin abin shanta sannan ki tabbata ta ci daga baya za ta fara ciwo a tsai-tsaye har na tsawan sati uku daga ƙarshe cikin zai ɓare sannan ba za ta sake haihuwa ba har abada. Idan aiki ya yi za ku yanka mana baƙaƙyen karnuna goma-goma, baƙaƙyen bunsura biyar-biyar, sai manya-mayan al'adun guda 85 kowannanku." 

Jinjina masa kai suka yi daga bisani suka bar ɗakin zuwa ƙofa, haɗa baƙi suka yi da cewa

"Turnuss tusun-tusun wutartarrr!! Turnuss sutun sutun suntaaaa!" 

Ƙofar ce ta buɗe suka fito sai dutsen ya haɗe, sai suka fara tafiya cikin dajin zuwa inda motarsu take wanda lokacin yamma har ta yi. Suna isa wurin motar babu ɓata lokaci suka shiga ciki driver ya tada suka bar wurin. Basu suka iso gidansu ba sai wurin 9:34pm na dare, sai da suka ajiye Hajiya Zinatu a ƙofar gidanta daga baya suka ƙarasa estate ɗinsu. Sai kusan 10:11pm na Hajiyan sama ta dawo gida,tana isa part ɗinta kai tsaye ta wuce toilet ta yi wanka, sannan ta sauko cin abinci daga nan ta haura bedroom ɗinta taɓi lafiyar gado. Ta daɗe tana tunanin yadda za ta aiwatar da aikin, daga ƙarshe ta sakar wa kanta wani munafikin murmushi ganin da samu maslaha sai kawai ta jawo ɗayan filonta ta rungume daga haka bacci ya sureta... ✍️

          🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Legacy Housing Estate, Bulunkutu, Maiduguri, Borno State. Nijeriya* 

A ranar da Abdul da mahaifiyarsa suka zo maganar auran Halima a ranar Sheikh Munnir ya saka ranar Halima nan da kwana biyar kamar yadda ya faɗa.Washe gari ya sanar wa Halima, sosai ta ci kuka iya kuka don ranar ko abinci ta kasa ci, yinin ranar tana ɗaki kwance sallah ce ke tasar da ita. Cikin dare ta sanar wa Abdul abin da ke faruwa, shi kuma ya sanar wa mahaifinsa ta waya wanda a ƙarshe suka umurci Halima idan ta samu damar fita daga gidan, to ta kirasa zai san yadda zai yasa a ɗaukota daga Maiduguri ta dawo Kaduna. 

Cikin hukuncin Allah washe gari da safe mom ta shigo ɗakinta ta sanar mata ta shirya za a gaita gidan Ya kura wacca take wa yaran gidan gyaran jiki idan za su yi aure. Da murnarta ta shirya bayan ta kira Abdul da sanar masa yau kaɗai take da damar fita. Bayan driver ya kaita gidan Ya Kura kasancewar kwana za ta yi sai washe gari za ta dawo gidansu da yamma, har an fara mata gyaran jiki sai kwatsam! Aka yi wa Ya Kura rasuwa a maƙotansu, hakan yasa ta tashi daga gyaran jikin da take yi wa Halima ta tafi gidan maƙotansu. Haba jiki na rawa Halima ta kira Abdul ta sanar masa mai yi mata gyaran jiki ta fita, sai ya ce at any moment za a zo a ɗauketa, sannan ta yi ɓadda kama kar kowa  ya fahimci bata nan,suna kammala wayar ta miƙe ta fita zuwa sashe Ya kura, yarinyarta ta samu ta faɗa mata za ta amshi saƙo yanzu ta dawo, wanda za ta aura ne ya zo, yarinyar bata kawo komai a ranta ta ce shi ke nan har tana ce mata ta kawo mata tsaraba. Cikin raha ta yi sallama da yarinyar ta bar gidan. Tana fita wanda Abdul ya aiko ya ɗauketa ya iso, daman ta saka nosemask sai kawai ta faɗa motar suka bar Layin. 

Bayan sun sha tafiya sosai sai suka tsaya a daidai wani junction, nan motar Abdul ya iso Halima ta koma ciki. Kan motar ya juya suka nufi hanyar Bauchi kasancewa bayan Abdul ya sanar wa mahaifinsa abin da ke faruwa, sai mahaifin nasa ya sanar wa ɗan uwansa Prof akan hukuncin da mijin ƴar uwarsu ya yankewa Halima na aura mata wanda bata so. Prof ne ya ce idan har sun samu dama kawai a ɗaukota ta dawo wurinsa, shi kuma Sheikh za su san yadda za su yi da shi tunda haka ya zaɓa. Sai wurin 11:00pm na dare suka isa gidan Prof da ke cikin Bauchi, kai tsaye Prof ya miƙa wa Hajiya Nafisa riƙon Halima kafin komai ya daidaita ta koma gidansu. Bayan ta ci abinci ita da Abdul sai ta nufi ɗakin Nazima ta kwanta shi kuma Abdul ya wuce ɗakin Mas'ud ya kwana. Washe gari da safe Abdul ya bar gidan kasancewar yana da aiki a Office. Wannan ke nan... ✍️

           🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Kwanar Faru ƙwai, Kaduna state. Nijeriya*

A can gidan makokin washe gari Alhaji Zakari ya tafi Giwa bikon Hannatu. Duk yadda ya so Hannatu ta dawo gidanta ta ƙi, ce masa ta yi ta haƙura da shi ya zauna da amaryarsa ita ta yafe auran, ko mahaifiyarta da ƙaninta sun yi ta bata haƙuri ta koma ɗakinta amma ta ƙi. Abin da basu sani ba shi ne, uwar gidan mai unguwa ta kirata tare da sanar mata abin da ke faruwa na rasuwan yaron Zaliha da ɗan kishiyarta wanda ƴan shan jini ne ku sa yi aikin. Da yake kowacce a cikinsu tasan sirrin abin da yake yi a waje sai kawai suka yi shawara akan kar ta dawo garin, ita ma uwar gidan mai unguwa tafiya za ta yi kuma za ta daɗe kafin ta dawo. Don da alama abin da suka yi wa ƴaƴan wasu haka ake shirin yi wa yaransu. Gwara su kama kansu in ya so daga baya komai ya lafa sai su dawo. Da wannan shawarar suka yanke kira. Rai bai so ba haka Alhaji Zakari ya dawo kwanar faru ƙwai gwiwa a saɓule. 

A can gidansu Alhaji Zakari Zaliha da Murja suna zaune a tsakar gidan suka ji sallamar wata mata ta riƙon yaro ƙarami wanda bai wuce shekara 4 a duniya, da fara'a a fuskarta ta ƙaraso tsakar gidan inda Zaliha da Murja suke zaune. Kafin matar ta zauna a saman tabarma Fatsima da Mammin Hujayrah suka shigo gidan bakinsu ɗauke da sallama. Sun je barka a maƙotansu waɗanda suke shiri dasu, suma ƙarasowa inda su Murja suke sai suka  zauna Bayan sun zauna sai Murja ta dubi matar ta ce

"Baƙuwa muka yi ne, don ban ganeki ba" 

murmushi matar ta yi sannan ta ce

"Eh Baƙuwa ce ba a garin nan nake ba" 

"Allah sarki sannu da zuwa ya hanya, ya mutanan gida, hala kin zo gaisuwan Ɗahiru ne"  cewar Murja 

"A'a ba gaisuwa na zo ba, hasalima ban san da rasuwa ba, wurin Alhaji Zakari na zo" 

Banbaraƙwai kowanne a cikinsu ya ji maganar, har da Zaliha wacce sai yanzu ta ɗago tana kallonta. Murmushi Murja ta sake saki a tunaninta ko ƴar uwarsu Alhaji Zakari ne ta zo. Miƙewa ta yi zuwa ɗakin Kakulle tare da sanar mata sunyi baƙuwa,Kakulle barin abin da take yi ta yi jin ta yi baƙuwa, ƙarasowa tsakar gidan ta yi ita da Murja, a daidai lokacin Alhaji Zakari ya shigo da mashin ɗinsa,dawowarsa ke nan daga Giwa. 

Yana ƙarasowa cikin gidan kamar ance ya kalli inda su Zaliha suke, karaf! Idanunsa ya sarƙafe da na matar, lokaci guda hantar cikinsa ta kaɗai, cak! Ya tsaya yana kallonta wanda ita ma shi ɗin take kallo. Miƙewa ta yi fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙaraso inda Alhaji Zakari yake rike da hannun yaron. 

"Murja ina baƙuwar da kike ce na yi" cewar Kakulle tana baza idanu taga ƴar uwarta. 

"Inna ai ga matar can ta nufi wurin Zakari" cewar Murja ta saki baki tana kallon Ikon Allah meke shirin faruwa. 

Matar na isa wurin ta miƙa wa Alhaji Zakari hannun yaro Still bata bar murmushi ba ta ce

"Ga ɗanka wanda ka ce ba zubar da cikinsa,kai yaranka sun isheka, Ni kuma a gaskiya ban zan iya laifi har biyu ba, ga laifin zina ga kuma laifin kashe rai, shiyasa kawai na haƙura da zubar da cikin.Yanzu haka na yi aure Allah ya shiryar dani, mijina ya ce na kawo yaron gidan ubansa shi yasa na kawosa Wurinka saboda Kai ne ubansa, Ni kaga tafiyata " tana gama maganar ta juya  za ta tafi sai kuma ta dawo tana murmushi ta ce

"Au! Na manta Sunanka na saka mishi, takwaranka ne Zakari, nasan kana da kuɗi shi yasa ban ɗauko masa kayansa ba". 

Daga haka ta juya ta wuce abinta. Tashin hankali wanda ba a saka masa rana. Kallon-kallo matan gida suka shiga yi da Alhaji Zakari, musamman Zaliha da Kakulle sun kafesa da ido kamar suna son gano wani sirri da yake ɓoyewa. Kakulle ta katse shirun da cewa

"Ɗan inna ban gane abin da matar can take faɗa ba, fahimtar Dani mai take shirin cewa"

Shiru babu amsa sai ma ƙara sunkuyar da kansa ya yi zufa na kwaranyo masa a duk ilahirin jikinsa still hannunsa riƙe da hannun yaron. (Ni kuma na ce little Zakari, su Zaliha sai a shirya riƙon shege🤭🤭🤭) 

"Na rantse Allah bazan riƙe shege ba, haka nan ni ban yi ba sai wani zai yi ya kawo na riƙe, Tab Allah sittiri buƙwi! " cewar Zaliha tana Miƙewa daga zaman da ta yi ta wuce sashenta. Fatsima da Mammin Hujayrah miƙewa suka yi tare da yin Allah shi kyauta suka wuce sashensu. Murja ma sashenta ta koma tana taɓe baki. Kakulle da Alhaji Zakari kawai aka bari a tsakar gidan. Shi dai ya kasa ɗago idanunsa ya kalli Kakulle ita kuma taƙi daina kallonsa. Sun daɗe a haka daga bisani ta zo har inda yake ta riƙon hannun yaron ta wuce dashi ɗakin ta, saiaka bar Alhaji Zakari riƙe da mashin yana karanta wasiƙar jaki... ✍️

          🌎🌎🌎🌎🌎🌎

Kwance take a gadon  asibiti an saka mata na'urar da ke taimaka wa wurin fitar numfashi, a hankali numfashinta ke fita da taimakon na'urar, kowa ka gani a ɗakin ya yi tagumi yana kallonta, wasu a cikinsu har da zubda hawaye saboda tausayi, sosai ta rame daman ba ƙiba ta cika ba gashi yanzu farardɗaya ciwo ya kwantar da ita. Alhaji Sambo dala ne a gefen mta yana zaune a wata kujera ya zuba mata ido, abin duniya duk ya gama jagule masa, ya rasa ina zai saka rayuwarsa ya ji daɗi. Hajiya Mariya da Haj Ramla suna zaune a cushion wacce ke fuskantar gado, Akmal, Sakhiyya da Tahseen suna ɗayan kujerar zaman mutum uku hankalin kowannansu tashe. Senata kuma yana kusa da Alhaji Sambo Dala a wata kujera irin tasa. Kowa da abin da yake saƙawa a ransa musamman Alhaji Sambo Dala wanda ke saƙa da warwarar yadda zai ɓullowa wannan tashin hankalin da ke shirin tunhkarosa. Gashi tun kan kwana biyu su cika kamar yadda demon king ya ce har Sabrin ta fara fita daga cikin hayyacinta. Kusan sumanta biyar ke nan tana farfaɗowa, bayan haka tasha ledar jini kusan huɗu na biyar ɗin ne yanzu. Sauke nauyayyan ajiyar zuciya ya yi sannan ya miƙe ya fita, Senata ma ya biyosa a baya. Wajan asibitin suka fito, sai suka samu wuri a inda aka tanadar na shan iska suka zauna. Cike da damuwa Senata ya dubi amininsa ya ce

"Linkaku har yanzu basu ga yarinyar ba?" 

Sai da ya sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya sannan ya dubi Senata da jajayan idanunsa ya ce

"Har yanzu Senata, I don't want to lose Sabrin, ita ce raunina, a duk yarana babu wanda nafi so kamarta, ban san ya zan yi ba Senata just one day  left demon king ya yi hukuncin akanta, just one day, one da..." 

Kuka ne ya ci ƙarfinsa har ya kasa magana, rabon da ya zubda hawaye tun rasuwar mahaifiyarsa, ko lokacin da mahaifinsa ya rasu bai yi kuka ba. Sosai Alhaji Sambo dala yaba Senata tausayi don yasan yadda yake ƙaunar ƴarsa. Lallashi ya fara bashi tare da ban baki akan komai zai daidai kawai su tsananta bincike ne. Shi ne kawai abin da ya dace su yi, shi ma zai saka yaransa su taya shi binciken. Sun daɗe suna tattaunawa daga bisani suka miƙe zuwa cikin asibitin. A hanyarsu ta komawa Senata yake ce wa Alhaji Sambo dala an saka ranar auran Tahseen da Arqam. Fatan alkhairi ya yi masa duk da ba shiri yake da ɗan uwansa Alhaji Imran ba amma ya yi murna sosai. 

Cikin asibiti hira ce ta ɓarke tsakanin Hajiya Mariya da Hajiya Ramla, duk akan shirye-shiryan bikin Tahseen ne da Arqam. Domin tun a ranar da aka saka lokacin auran Hajiya Ramla ta yi ordering furnitures da kayan kitchen. Hajiya Mariya ta yi farin ciki sosai,daman ƙiyayyar daga Alhaji Sambo dala ne, sai Akmal wanda ke taya shi, ko Sakhiyya babu ruwanta da wannan tana zama cikin ƴan uwanta sannan tana zuwa gidan kowannansu idan ta kama.Sai wajen yamma su Hajiya Ramla ta Tahseen suka bar asibitin da yake Senata da Alhaji Sambo dala a tare suka bar asibitin. Akmal ma ya koma gida shi da Sakhiyya ɗauko abinci da wasu kayan da ake buƙata. Da daddare da suka dawo suka tarar da Khalil ya zo buda jikin Sabrin sai kusan 10:12pm Khalil da su Akmal suka bar asibitin... ✍️

        🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*Gida dubu, Gubi Housing Estate, Bauchi state, Nijeriya*

A ɓangaren Hajiya momma tun lokacin da aka saka lokacin auran Arqam ta fara shiri don har ƴan uwanta na Nijar da sanar musu. Kasancewar lokaci kaɗan aka saka sai kawai ta fara shirinta. Ƙawarta Hajiya Radiya wacce take haɗa kayan lefen  ta kira, bayan ta zo suna zaune a falo ta ce

"Hajiya ina so ki haɗa akwati na gani na faɗa" 

Murmushi Hajiya Radiya ta yi tana kai apple bakinta, bayan ta ci sai ta ce

"Haba Hajiya ai bikinki na daban ne, dole a haɗa miki kayan lefe na gani na faɗa ko ɗan shugaban ƙasa sai hada" 

Gyara zama Hajiya momma ta yi sannan ta ce

"Yanzu nawa ne kike buƙata na haɗa kayansa akwatin, bana son old design if possible  akwatin ya kasance ba a taɓa irinsa ba" 

"Miliyan ashirin sun iya komai da komai, Ni kuma zan fidda ke kunya da yardar Allah " cewar Hajiya Radiya tana cire ƙwallon apple. 

"Zan baki miliyan talatin, Ina so komai ya zama classy and expensive, Ina son Dubai gold banda Saudiyya gold, sannan if possible a saka diamond necklace a ciki.kin dai gane everything should look  Maa shaa Allah Tabarakallah yadda ko'ina za a dinga maganar kayan" cewar Hajiya momma. 

"In shaa Allah, nan da kwana bakwai zan haɗa komai" 

"Turomin da account number na tura miki kuɗin" 

Babu ɓata lokaci Hajiya Radiya ta faɗa mata account details ɗinta wanda within some minutes ta tura mata kuɗin. Sun ɗan yi hira kaɗan daga bisani suka yi sallama tabar gidan cike da farin ciki. 

Bayan fitar Hajiya Radiya ba a daɗe ba, Hajiyan Sama da aiko Zahriyya da Basket ɗin abinci ta kawo wa Hajiya momma, buɗe kula ta yi cike da farin ciki ganin masoyinta Hajiyan sama ta kawo mata wato burabusko da miyar taushe taji gyaɗa da busasshen kifi da ƙashi sai kunun gyaɗa mai kauri sai ƙamshi yake yaji citta da kamunfari. Bayan fitar Zahriyya Hajiya moma ta zauna ta ci abincin sosai sannan tasha kunun, ɗaukar sauran kayan abincin ta yi zuwa kitchen bayan ta ƙoshi. Tana dawowa falo Hajiya Nafisa ta shigo da ita da iyalanta, Nazima da Halima wacce jiya ta iso garin, Mas'ud ya wuce ɗakin amininsa Arqam. Ko awa ɗaya basu yi ba Hajiya Ramla ta iso falo kasance tana so su tattauna yadda bikin zai kasance. Suna cikin hira sai Hajiya momma ta ce bara ta yi fitsari ta dawo. Shigarta bayi keda wuya ta tsandar ihu daidai lokacin da Arqam da Mas'ud suka shigo falon. Da gudu suka isa bedroom ɗinta, cikin sauri Arqam ya buɗe bayin, lokaci guda ya waro idanun yana faɗin

"Ammie me ya samu jikinki, Innalillahi wa'inna Ilaihi Raji'un" tsigar jikinsa na tashi. 

Hajiya momma susar jikinta take tana ihu sannan duk inda da sosa sai ƙurji ɓaƙi ya fito da kuma zarar ta sake susa wurin sai ya fashe wani ɓaƙi ruwa mai ƙarni da wari ya fito. Cike da tashin hankali ya cicciɓo Ammie ya fito da ita zuwa saman gadonta, Alhaji ma ya shigo bedroom ɗin shi da Hajiyan Sama kasancewar suna tare. Sosai hankalin kowa ya tashi ganin Hajiya momma lokaci guda Allah ya sauya mata halitta. Duka ilahirin jikinta baƙaƙyen ƙuraje ne sai fidda ɓaƙin ruwa suke mai warin gaske.har ta da cikin bakinta ƙurajen ne gashi bata fasa susar jikinta ba, ihu take tana kuka. Babu wanda a cikin ɗakin bai zubda hawaye ba, Nazima da Hajiya Nafisa ba a maganarsu daman tun jiya Hajiya Nafisa ta ji yanayin jikinta ta sauya. To yanzu ga wani tashin hankali mai zaman kansa. Hajiyan sama kuka take yi sosai don har ta so fin su Nazima kukan, sai fama cewa take

"Don Allah a kaita asibiti, Arqam ka yi wani abu,Alhaji! wayyo Mubina" 

Hajiya Ramla ma hankalinta a matuƙar tashe yake. Kiran waya Alhaji ya yi akan Family doctor ɗinsa ya zo. Babu jimawa sai gashi,bayan ya yi wasu gwaje-gwaje ya ce

"Alhaji a gaskiya sai kun kai Hajiya India asibitin fata a dubata " 

Caraf! Hajiyan sama ta ce

"Gaskiya kuwa kar ciwon ya ci ta sosai" 

Zai yi magana ke nan sai ga Razina a gaba Hujayrah na biye da ita cikin bedroom ɗin, ƙwalla ƙara Razina ta yi wanda nan take ta sume. Da taimakon likita Razina ta farfaɗo, da kuka da farfaɗo tana taɓa Ammienta. Hujayrah dai bata ce komai ba tana  kallon mutanan ɗakin ɗaya bayan ɗaya tana nazarin kowanne. Tana haɗa ido da Hajiyan sama gabanta ya bada sautin Dummmmmmm! Da sauri ta dafe saitin zuciyarta. Juyawa kan Hajiya momma ta yi, ta daɗe tana kallonta daga bisani ta ƙaraso cikin ɗakin da kyau. 

"Hello Doctor Ina da patient a gidana, so Family doctor na ya ce Sai an kai patient ɗin India asibiti fata saboda ciwon ya yi chronic sosai" cewar Alhaji yana waya. A can aka yi magana sai ya ce

"A yau za mu yi mata visa zuwa India, Sai mun haɗu" yana katse kiran Hujayrah ta dube Alhaji ta ce

"Abbu ka bani dama na yi magana? " 

Wata uwar harara Hajiyan sama ta aika wa Hujayrah tana faɗin

"To uwar iyayi uban me ya kawoki cikin dangi, Kin wani shigo cikin mutane za ki soma zuba zance kamar an saka ki, maza ki bar mana ɗaki don bama gayyar soɗi" 

Taɓe baki Hujayrah ta yi sannan ta juyo gun Alhaji ta ce

"Abbu ka bani dama na ce wani abu? " 

Jinjina mata ya yi ba tare da ya ce komai ba. Arqam da Mas'ud kallonta kawai suke suna nazari musamman Mas'ud tun lokacin da yaga ta dafe ƙirjinta yasan akwai matsala. A hankali ta ƙaraso inda cikin ɗakin sosai tana kallon Hajiya momma ta ce

"Abbu ba komai ke ɗawainiya da Mammin ba sai asiri guda biyu masu mugun ƙarfin sannan Hajiya Nafisa ma akwai asiri a jikinta wanda bai daɗe da shiganta ba" 

Daram! Dam! Daram! Babu wanda a cikin ɗakin gabansa bai buga ba musamman mutane biyu, Hajiyan sama da Hajiya Ramla don kowanne yasan abin da ya yi. Wata uwar tsawa Hajiyan Sama da daka wa Hujayrah tana cewa

"Ke dan kutumar ubanki a gidan uban wa aka ce miki akwai asiri a jikin Hajiya momma da Nafisa" 

Madadin Hujayrah ta ji tsoro ko fargaba, sai ita ma ta daka wa Hajiyan sama wata uwar tsawar da ta gigita kowa a cikin ɗakin tare da mamaki. Muryarta a kausashe ta fara magana tana waro wa Hajiyan sama manya-mayan idanunta masu tsoratar da mara gaskiya da cewa

"Dallah ki rufe mana ruɓabɓan bakinki a nan wurin kafin yanzu na kwance miki zani a tsakiyar kasuwa! Ke har kina da bakin magana! To na ce akwai asiri guda biyu a jikin Hajiya momma sannan mutane biyu suka yi asirin, bayan haka akwai mugun asiri a jikin Hajiya Nafisa wanda zai saka cikin jikinta ya ɓare idan ba a saurin karya shi ba, Ni nan da kike ganina bana ƙarya bana zalunci kuma sannan ba a yi a gabana. Mammi kamar uwa take a wurina bazan iya bari wani abin cutarwa ya shafe ina gani, ba tare da na kawai dashi in har ina da ikon haka ba, Ina gargaɗinki karki sake shiga gonata idan ba haka ba wallahi wallahi wallahi saina kwance miki zani a gaban kowa, da ita ɗayar wacce tasan ta yi mugu abu to a hirɗinta. koma wace ce tasan da ita nake"

Tsuru-tsuru Hajiya Ramla ta yi tana raba ido don tasan Hujayrah ta ita take, duk ilahirin jikinta ya jiƙe da gumi. Hajiyan sama kuwa ganin mutanan ɗakin sun kusa harbo jirgin sai kawai ta fashe da kuka tana cewa

"Shikenan don anga ban haihu ba shi ne a gaban kowa ɗiyar cikina take gasa min magana son ranta, babu wanda ya ce komai yeeee! Yeee!" 

Babu wanda ya bi takan kukanta sai Alhaji da ya dubi Hujayrah cike da farin ciki ya ce

"To yanzu Hujayrah mene ne mafita" 

Zuwa inda Hajiya momma take Hujayrah ta yi tana dubanta ta ce... ✍️






*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
 ***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol