Free chapter · Read without an account
A NEW BEGINNING
CHAPTER 40: JUSTICE AND A NEW BEGINNING
Maryam riƙe take da Aisha sosai kamar wadda take tsoron idan ta sake ta, za ta sake ɓacewa daga rayuwarta.
“Yaya… Yaya Aisha…” Maryam ta faɗa cikin kuka, muryarta na rawa. “Da gaske ke ce? Ashe kina raye? Ashe duk waɗannan shekarun kina raye yaya?”
Aisha ma ta fashe da kuka, tana shafa bayan Maryam a hankali.
“Maryama ta… I’m sorry. I’m so sorry, little sister.”
Maryam ta girgiza kai, ta ƙara rungume Aisha.
“Mun yi tunanin mun rasa ki har abada. Na yi ta addu’a, Yaya. Na yi ta tunanin ko ina kika shiga, ko me ya same ki. Allah na gode maka!”
Aisha ta riƙe fuskar Maryam da hannayenta biyu, tana kallonta da idanunta da suka cika da hawaye.
“Ki dube ni, Maryam. Ina nan. I’m here. Na dawo gare ki.”
Maryam ta sake rungumarta, tana kuka kamar ƙaramin yaro da ya daɗe yana neman mahaifiyarsa.
A gefe guda, Mammi ta kasa riƙe nata hawayen, saboda tausayin Maryam da kuma baƙin cikin abin da Fahad ya yi mata.
“Alhamdulillah… Alhamdulillah, Allah ya dawo mana da ke” ta faɗa cikin rawar murya.
Maryam ta kalleta, “Mun yi kewarki sosai, yaya Aisha. Kin bar mana babban gibi a rayuwarmu.”
Hajiya Raliya ma ta goge hawayenta, tana kallonsu cikin farin ciki da tausayi. Zaid kuwa sai kallonsu yake da tausayawa.
Bayan wasu mintuna, Maryam ta ɗan ja baya daga jikin Aisha, amma har yanzu ta riƙe hannunta ba ta son ko da na daƙiƙa ɗaya su rabu.
“Yaya, I need answers,” ta faɗa, muryarta cike da raɗaɗi. “Ina kika kasance duk waɗannan shekarun?”
Aisha ta kalli Mammi, sannan Zaid da Hajiya Raliya, kafin ta mayar da idanunta kan Maryam.
“Zan gaya miki komai, Maryam. Babu abin da zan sake ɓoyewa daga gare ki. Amma abin da zan faɗa miki ba abu ne mai daɗin ji ba.”
Ta ɗan yi shiru, tana jan numfashi.
Hajiya Raliya ta katse su.
“Maryam, ki bar yayarki ta shigo daga ciki ta zauna mana. Jin daɗin ganinta ya sa kin bar ta a tsaye.”
Maryam ta yi murmushi tana jawo hannun Aisha, suka nufi parlor ɗin Mammi.
Suna zaunawa, Aisha ta gaida Mammi da Hajiya Raliya cikin girmamawa. Ta kalli Zaid, sai ya yi mata murmushi, wanda daka kalla kasan na yaqe ne yakeyi, a qasan zuciyar shi akwai wani irin baƙin ciki a cikin idanunsa.
Kafin ta yi magana, ya rigata.
“Antynmu, sannu da dawowa. Mun gode wa Allah da ya dawo mana da ke lafiya.”
Aisha ta yi murmushi.
“Alhamdulillah. Sannu da ƙoƙarin kula da ƙanwata.”
Maryam ta katse su.
“Yaya, gaya mana.”
Aisha ta ɗan sunkuyar da kai, tana jin nauyin kallon Mammi da Zaid.
“Abin da ya raba ni da ku… da abin da ya faru da Baba… duk suna da alaƙa da mutum ɗaya.”
Maryam ta matse hannunta.
“Fahad?”
Aisha ta runtse idanunta na ɗan lokaci, sannan ta buɗe su a hankali.
“Eh,” ta samu ta furta da ƙyar saboda jin nauyin Mammi.
Daga nan ta yi shiru, ba ta ci gaba da magana ba. Maryam ta lura tana jin nauyin Mammi, shi ya sa ba ta son ta ci gaba da magana a gabansu. Ita ma sai ta daina tambayarta game da wannan maganar.
Daga nan suka shiga hira, Maryam tana ba Aisha labarin gida da su Mama. Ta gaya mata cewa Hauwa Kulu da Maryam ƙarama suna can tare da Mama.
Aisha ta yi murmushi, hawaye na sake taruwa a idanunta.
“Har yanzu ina tunanin su kullum,” ta faɗa a hankali.
Maryam ta matse hannunta.
“Ai ynzu zaki sake ganinsu, Yaya”
Aisha ta gyada kai, ta kasa magana saboda cikar zuciyarta da motsin rai.
Haka suka ci gaba da hira, suna dariya, suna kuma nuna tsananin murnar ganin juna
Zaune yake a kan kujerar office dinshi yayi zurfi sosai a cikin tunani se qarar da wayar shi tayi yasa ya dawo daga duniyar da ya tafi, dauka yayi ya kara a kunne ba tareda yache komai ba
“Sir inaga kamar sun bude akwatin nan”
Yayi shiru yana jin kamar kanshi ze rabe biyu, zaune ya kwana a office yana tunani ya rasa inda zesa kan shi
“Ali, ya akayi suka bude shi?”
“Naga wani mutumi yazo gidan dazu, da aka tare shi a gate yache ma securities shi locksmith ne zayd ya kira shi, ya dauki lokaci a ciki kafin ya fito”
Yana kaiwa nan kawai ya zare wayar daga kunnen shi yayi chilli da ita ta fadi qasa
Dare ya riga ya mamaye Balarabe Mansion, komai ya yi tsit, amma zuciyar Maryam ta ƙi samun natsuwa.
Maryam ta kalli Zaid, wanda yake zaune shiru, shi ma yana nazari.
“Rouhi, yanzu da muka san cewa Fahad shike da hannu a cikin duk abin da ya faru, me za mu yi?”
Zaid ya ɗaga kansa a hankali. Idanunsa sun yi tsananin ja
Zuciyar Maryam ta karye. Ya ba ta tausayi sosai.
“Haya, ni kaina ban sani ba. Fahad ɗan uwana ne. Ban san abin da zan yi ba.”
Maryam ta yi shiru na ɗan lokaci, tana nazarin maganarsa.
“Rouhi, ina ganin kawai ai tunda Allah ya riga ya nuna mana gaskiya, shikenan. A bar shi ya je da halinsa. Abin da kawai zai ci gaba da tsaya min a rai shi ne zargin da mahaifina ya rasu ana yi masa”
Muryarta ta fara rawa, hawaye suka cika idanunta.
Zaid ya matsa kusa da ita, ya riƙe hannunta.
“Na san abin da kike ji, Haya. Ni ma hakan yana damuna, tunanin cewa an ɓata sunansa, kuma wanda ya yi hakan ɗan uwana ne, yana karya min zuciya.”
Maryam ta share hawayenta.
“Kayi hakuri rouhi, haka Allah yaso, kuma ina tsoron abin da zai faru idan Fahad ya gano cewa Aisha tana raye.”
Zaid ya yi shiru na ɗan lokaci.
“Ko ya sani ynzu ai, ba abin da zai iya yi mata saboda yanzu ba ita kaɗai ta san abin da ya yi ba. Kowa ya san gaskiya. Kuma muna da shaidar da za ta hana shi sake ɓoye abin da ya faru.”
Maryam ta jingina kanta a kafaɗarsa.
“Allah Ya ba mu ƙarfin zuciya, Rouhi.”
“Ameen, Haya. Allah ya ba mu ƙarfin zuciya.”
Bayan duk ta qare abnda zatayi wurin Aisha taje ta kwana, yau kam zayd se hakuri yayi ya batta taje wurin yar uwar ta
Da safe, gidan ya tashi cikin sabon yanayi. Aisha tana tare da su Maryam, Mammi da Hajiya Raliya, kuma duk da farin cikin da suke ciki, akwai wani abu da ya rage a zuciyarsu, dole ne a fuskanci Fahad, zayd ya riga yayi magana da Ali ya gaya mishi abnda zeche idan Fahd ya kira shi, don haka koda ya kira se Ali yache mishi ai yana tunanin gidan Lfya qalau saboda bega alamar wani tashin hnkali ba, qila basu samu komai a akwatin ba, da haka Fahd ya samu qwarin gwiwar shigowa gidan
Suna zaune a parlorn mammi ya shigo parlor ɗin cikin yanayin da ya saba, se murmushi yake,
“Wow! Reunion ake? Me ya sa kowa ya taru haka? Akwai wani family meeting ne ban sani ba?” Ya fadi yana murmushi
Babu wanda ya amsa masa sukayi shuru kowa yana nazartar shi
Yabi kowa da ido yana kallon yadda suka qura mishi ido, se a lokacin ya lura da Aisha zaune kusa da Maryam, ta dan chnja kadan akan yadda ya santa a baya, amma haka be hana shi ganeta ba
Murmushin da ke fuskarsa ya gushe a hankali.
Ya tsaya cak, yana kallonta kamar wanda ya ga fatalwa.
“A..A..Aisha?”
Aisha ba ta ce komai ba. Ta kalle shi kawai, idanunta cike da hawaye da wani irin raɗaɗin da ya daɗe yana chin ran ta
Fahad ya juya ya kalli Maryam, sannan Mammi da Zaid.
“Wannan… ta yaya? Ta yaya Aisha ta dawo?”
Zaid ya tashi tsaye.
“Ka san abin da ya fi ban mamaki, Fahad? Ba wai Aisha ta dawo ba ne. Abin da ya fi ban mamaki shi ne yadda ka yi tunanin za ka iya ɓoye gaskiya har abada, Fahad meyasa? Wannan ba halinka bane Fahd, ya akayi ka bari shaidan yayi galaba akan ka?”
Fahad ya yi ƙoƙarin yin murmushi.
“Ban..Bann..umm..ban fahimci abin da kake nufi ba, Zaid.”
Zaid ya ɗauko takardun FILE 17 ya ajiye su duka a kan table gaban Fahd
“Wannan shi ne abin da kake nema tsawon shekaru, yarjejeniyar asali tsakanin Baba da Baba Bashir. Takardun da ke nuna cewa sun mallaki Northern Crest Holdings daidai-wa-daida. Kuma ga bayanan kuɗaɗen da aka karkatar, takardun da aka canza, da shaidun da ke nuna yadda aka yi ƙoƙarin ɗora wa Baba Bashir laifin da bai aikata ba”
Ya dan yi shuru sannan yachi gaba, “gasunan ka dauka kaje kayi abnda zakayi dasu”
Fahad ya kalli takardun, amma ya yi ƙoƙarin ɓoye tashin hankalinsa.
“Zaid, ku saurare ni. Kuna kallon wannan al’amari ne ta hanya ɗaya kawai, tsaya ka saurari bayani na”
Maryam ta kasa jurewa.
“Ta wace hanya kuma ya kamata mu kalle shi, Fahad? Ka ɓata sunan mahaifina! Ka sa mun rayu da tambayoyi da ba su da amsa! Ka sa mun yi tunanin cewa mun rasa Aisha har abada!”
“Maryam, ki saurare ni….”
“A’a! Kai zaka saurareni” Maryam ta katse shi, hawaye na zubo mata. “A wannan karon, kai ne za ka saurare mu!”
Fahad ya yi shiru.
Mammi ta sauke kanta qasa hawaye nata zarya a Idonta
“Fahad, ni ce na riƙe ka a matsayin ɗana. Na ba ka soyayya kamar yadda na ba Zaid. Ban taɓa bambanta tsakaninku ba. Me ya sa ka zaɓi ka yi mana haka?”
Fahad ya juya ya kalleta, a karon farko fuskarsa ta nuna damuwa.
“Mammi, na yi duk abin da na yi ne domin ku! Domin kare dukiyar iyali! Na ga yadda abubuwa suke tafiya, na san idan ban ɗauki mataki ba, za mu rasa abin da muka tara tsawon shekaru. I was trying to protect this family and its wealth!”
Zaid ya girgiza kai a hankali, yana kallon ɗan uwansa cikin takaici.
“Kare iyali? Ko kare abnda zuciyar ka take muradi?”
Fahad ya buɗe baki zeyi magana, amma Zaid ya ci gaba.
“Idan da gaske kana son kare iyali ne, da ka bi hanyar gaskiya. Da ka bayyana abin da ke faruwa, ka nemi mafita tare da mu. Amma ka karkatar da kuɗaɗe, ka canza bayanai, ka ƙirƙiri hujjojin ƙarya, sannan ka ɗora wa bawan Allah laifin da bai aikata ba, wannan duk be isheka ba, ka qirqiri hatsarin da yayi sanadiyyar rayuwar shi, wannan be girgiza ka ba, har ka biyo diyar shi kana neman ka halaka ta, Wannan ba kare iyali ba ne, Fahad. Wannan son kai ne.”
Hajiya Raliya ta girgiza kai cikin baƙin ciki, mammi kuma se qoqarin addua takeyi cikin ranta gudun kar kukan da taketa dannewa ya fito da qarfi
“Ka sa mutane marasa laifi suka sha wahala saboda kwaɗayinka. Ka sa Maryam ta rasa mahaifinta, ka sa Aisha ta ɓace daga rayuwar iyalinta, kuma ka sa wannan gida ya rayu cikin rashin yarda da juna, daddy da ya riqeka da amana ya rasu amma baa sauke hakkin da ke kanshi ba, dukiyar marayu, dukiyar marayu Fahd! Wace irin kariya ce wannan?”
Fahad ya yi shiru, yana kallon fuskokin waɗanda ya quntata ma
Mammi ta share hawayenta.
“Duk abin da muka mallaka ba shi da darajar da za ta kai darajar rayuwar ɗan Adam, Fahad. Ba mu taɓa buƙatar ka lalata rayuwar wasu domin mu ba”
Fahad ya sunkuyar da kansa.
“Na yi kuskure,” ya faɗa a karye, kan shi a ƙasa. “Amma abubuwan ne suka wuce yadda na tsara su.”
Maryam ta kalle shi cikin zafi
“Ba kuskure kaɗai ka yi ba, Fahad, ganin dama ne, A duk lokacin da ka samu damar faɗin gaskiya, ka zaɓi ka sake ɓoye ta. A duk lokacin da za ka iya dakatar da cutarwar, ka zaɓi ka ci gaba.”
Fahad ya ɗago kansa, idanunsa suka haɗu da na Zaid.
Zaid ya yi shiru na ɗan lokaci. Wannan shi ne mutumin da ya girma tare da shi, wanda ya kira ɗan uwansa tsawon rayuwarsa. Duk da irin laifukan da ya aikata, ba abu ne mai sauƙi ga Zaid ya yanke alaƙar da ke tsakaninsu a zuciyarsa ba.
“Ka san abin da ya fi min ciwo, Fahad?” ya tambaya cikin sanyin murya. “Ba wai ka yi laifi ba ne kawai. Amma ka yi laifin ne kana kallonmu a matsayin iyalinka, kana cin abinci tare da mu, kana murmushi tare da mu, kana kuma ɓoye mana gaskiya, Fahd miye ainahin fuskar ka? Na rasa ganewa, kalli mammi, kalli yanayin da kasa ta a ciki, shin idan an ba margayi bashir kason dukiyar shi zamu samu karayar arziki ne? Ko zamu walakanta ne? Kadarorin da baba ya mallaka maka kai kadai zasu ishemu muyi rayuwa dukan mu cikin wadata”
Ya dafe kanshi kafin ya chi gaba da magana
“Fahd, idan gabadaya company din northern Crest mallakin alh Bashir ne Idan ya karbi abun shi kasan dai inada rufin asirin da zan kula daku duka”
Fahad ya sunkuyar da kansa, bai ce komai ba.
Zaid ya numfasa.
“Ba zan iya share abin da ka yi ba. Kuma ba zan kare ka daga gaskiyar abin da ka aikata ba. Dole ne ka fuskanci sakamakon zaɓin zuciyar ka, Fahad, kayi sanadiyyar rayuwar mutum, mutum dan Adam”
Babu wanda ya sake magana na ɗan lokaci. A ƙarshe, Fahad ya tashi a hankali, fuskarsa cike da nadama da rashin abin cewa.
Ya kalli Mammi, yaje gabanta ya duqa
“Na san na ɓata miki rai. Ban san ko za ki taɓa iya yafe min ba mammi”
Mammi ta share hawayenta.
“Fahd, Yafiya ba abu ne da ake tilasta wa zuciya ba, Idan da gaske ka yi nadama, ka fara da amincewa da abin da ka yi, sannan ka daina neman uzuri, wa’inda ka zalunta su zaka nemi yafiyar su, sauran kuma tsakanin ka da ubangiji ne kayita istigfari”
Fahad ya gyada kai a hankali. Ya kalli Zaid, sannan Maryam da Aisha, yana qoqarin yayi magana ya kasa, ya juya da sauri ya bar parlor ɗin.
Babu wanda ya bi shi, zaune sukayi shuru se sheshekar kuka da ke tashi a hnkali a parlor din
Bayan kwana biyu
An shirya tafiyar Aisha zuwa Sokoto, baa gayama mama komai ba harynzu, Mammi da Hajiya Raliya sun yanke shawarar raka ta, saboda ba sa son ta yi wannan tafiyar ita kaɗai bayan duk abin da ta fuskanta, kuma suna son suje suba mama hakurin duk abnda ya faru kuma suyi mata bayanin komai
Maryam kuwa zata zauna a Abuja tare da Zaid saboda cikin da take ɗauke da shi, tayi kuka tayi roqo amma zayd yaqi yadda, se lallashinta yakeyi yana lallabata
Yau ne tafiyar, Maryam ta rungume Aisha, hawaye na taruwa a idanunta.
“Yaya, zan yi kewarki.”
Aisha ta yi murmushi, tana share hawayen Maryam.
“Ni ma zan yi kewarki, Maryama ta. Amma wannan karon, ba zan ɓace miki ba. We’ll talk every day, and I’ll come back to see you.”
Maryam ta gyada kai, tana ƙoƙarin murmushi.
“Ki gaida Mama sosai. Ki gaya mata ina sonta, kuma ina kewarta.”
“Zan gaya mata. Kuma ke ma ki kula da kanki da..” ta kalli cikinta da ya dan fara fitowa
Zaid ya matso kusa da su.
“Yayar mu, ki kwantar da hankalinki. Zan kula da Maryam sosai, kuma Duk lokacin da kuke buƙatar wani abu, don Allah ki sanar da ni.”
Aisha ta yi masa murmushi.
“Na san za ka kula da ita. Thank you for being there for my sister.”
Mammi ta rungume Maryam Tana lallashinta kafin suka shiga mota.
“Ki kula da kanki, maryam, kada ki wahalar da kanki. Ki huta, ki ci abinci sosai, kuma ki bi duk shawarar dr dinki.
Maryam ta yi murmushi.
“In shaa Allah Mammi.”
Hajiya Raliya ma ta rungume ta.
“Allah Ya qara mi ki lafiya, Maryam”
Maryam ta yi murmushi cikin kunya.
Dukansu suka yi dariya, kuma wannan dariyar ta kawo ɗan haske bayan dogon lokacin baƙin ciki.
Motar ta tashi, ta bar Maryam da Zaid a Abuja, yayin da Mammi, Hajiya Raliya da Aisha suka nufi Sokoto domin sake haɗa iyalin da suka daɗe suna kewar juna.
A Sokoto
Lokacin da Mama ta ga Aisha ta shigo gidan, sai ta tsaya cak, kamar ba ta yarda da abin da idanunta suke gani ba.
“Aish..aishh..” ta kasa qarasawa
Aisha ta kasa magana se hawaye daketa zubo mata.
“Mama…”
Mama ta rungume ta, tana kuka mai tsanani.
“’Yata! Aisha ta! Ashe kina raye? Ashe Allah Ya bar min ke a raye haryanzu? Ina kika tafi?”
Aisha ta rungume mahaifiyarta sosai, tana kuka kamar ba za ta sake ta ba.
Mama ta riƙe fuskarta, tana ta shafa kumatunta, kamar tana tabbatar da cewa ’yarta ce a gabanta da gaske.
“Me ya faru da ke, Aisha? Ina kika kasance duk waɗannan shekarun? Na yi kewarki har na rasa yadda zanyi da rayuwata, na fawwalawa Allah komai saboda in ba qaunar ki qwarin gwiwar chigaba da rayuwarta”
Aisha ta kasa ba ta amsa se qara rungume ta da tayi kawai, tana kuka, yayin da Mammi, da hajiya Ruqaiya, da Hajiya Raliya suka tsaya kusa da su, suma idanunsu cike da hawaye.
Se Bayan ɗan lokaci, Mama ta dago kai ta kalle su
“Subhanallah, Hajiya don Allah kuyi hakuri wallahi bn lura daku ba, wannan yayar maryam che wadda ta bache tun shekaru fiye da uku da suka wuche shine ynzu nike ganinta, kuyi hakuri mu shiga daga ciki”
Hajiya Ruqaiya da haryanzu mamakin abnda Fahd yayi da su mammi suka bata labari a mota be saketa ba, tayi murmushi
“Ai hajiya mune mukazo da ita”
Mama ta kallesu da mamaki amma dai batache komai ba se murmushi tayi tana musu iso zuwa parlour, seda ta kawo musu abubuwan motsa baki sannan ta zauna suka qara gaggaisawa
A natse Hajiya raliya tayi mata bayanin komai tun daga farko har qarshe, koda ta qare bayanin shuru ne ya biyo baya se kukan da sukeyi a hnkali dukansu
Se bayan dan lokaci sannan mama ta bude baki ta fara magana cikin muryar kuka sosai
“Alhamdulillah ya Allah, hajiya Na gode muku. Na gode da kuka dawo min da ’yata, na gode da duk halaccin da kuka yimin, Allah ya saka muku da alheri, Allah ubangiji ya jiqan Alh Rahman da Alh Bashir, Allah ya gafarta musu yasa sun huta, shi kuma Allah ya shirya shi yasa ya gane gaskiya”
Mammi ta riƙe hannunta.
“Hajiya kiyi hakuri don Allah, kukan ya isa haka, sannan kuma duk hukuncin da zaku yanke akan Fahd muna jira, kada ku ji shakkun daukar duk matakinda kukaga ze dache in dai be kauche wa shari’a ba”
Aisha ta kalli mahaifiyarta, sannan ta rungume ta
A ƙarshe, gidan da ya daɗe yana ɗauke da kewar ’yar da ta ɓace yanzu kuma ya cika da muryarta da motsin ta, Duk da tambayoyin da har yanzu suke akwai, kasancewarta a gida ya isa ya ba su sabon fata.
Kwana biyu su mammi sukayi gidan hajiya Ruqaiya sannan suka koma abj
Fahd kam tun da wannan abun ya faru be sake fitowa daga part dinshi ba, ko abnci baya fitowa ya chi, seda ya kwana ya yini sannan cooks suka gayama zayd chewa Fahd be fito daga part dinshi ba, yaje ya dubashi ya ganshi beda lfya, ya kira dr ya dubashi sannan yache ma cooks idan suka dafa abnci su rinqa kaima Fahd part dinshi,
Har bayan mammi ta dawo Fahd be iya fitowa daga part dinshi ba, se ynzu yake tunanin duk abubuwan da ya aikata, me ya kaishi? In dai ta kanshi ne ai ga dukiyar da Alh Rahman ya mallaka mishi, tsantsan dana sani da nadama da kunya duk sun mishi rubdugu, ynzu hakkin rasuwar alh Bashir ta sanadiyyar abnda sukayi ya hanashi sukuni gabadaya, shi ya ya zeyi da wannan hakkin?
A haka dai yake rayuwa a kulle a part dinshi, mammi takan shigo lokaci zuwa lokaci tayi mishi nasiha cikin hikima, haka ma tasa shi ya shirya ya tafi sokoto ya roqi yafiyar maryam da mama, suka che sun yafe mishi kuma dama ba wani mataki da zasu dauka akan shi
Shi da kanshi ya ajiye aiki a northern crest, sannan ya nemo qwararrin lawyers da zasu raba komai aba su maryam hakkin su, mammi chewa tayi ta yafe nata kason, zayd ma haka yache, don haka gabadaya company din northern crest ya dawo mallakin family din Alh Bashir maisalati, a qarqashin kulawar Aisha
Bayan watanni
Rayuwa ta fara komawa yadda ya kamata a hankali. Maryam da Zaid suna jin daɗin zaman aurensu, zayd yayi niyyar komawa Amsterdam amma mammi tache sedai ya bar maryam don babu inda zataje se bayan ta haihu, ai ko haka shima ya zauna don yache baze iya nisa da ita ba, duk abnda ze iya yi online shi yakeyi, se Nadia da ke kula da ayyuka a chan, yayin da Maryam ke ci gaba da kula da cikinta. Zaid kuwa ya ƙara zama mai kulawa gareta, yana kuma tabbatar da cewa ba ta wahalar da kanta da aikin gida, saboda ynzu ta nache ita ke yimusu abnci, hadda na part din mammi
A wani yammaci, Maryam tana zaune a kan kujera, tana kallon Zaid da murmushi yayin da yake yanka mata apple yana bata tana chi
“Rouhi, sometimes I still can’t believe how much has happened in our lives.”
Zaid ya juya ya kalle ta.
“Me ya sa, Haya?”
“Mun sha wahala, mun yi kuka, mun rasa mutane, mun gano gaskiya masu zafi. Amma duk da haka, muna nan tare, da farko da kake recieving messages dinnan bakayi zargina ba?”
Ya dan kalleta
“Banyi zargin ki ba, Kin san abin da na koya daga duk wannan?”
Maryam ta girgiza kai.
“Me?”
“dukiya ba ita ce mafi muhimmanci ba a rayuwa, Mutanen da suke tare da kai, gaskiya, soyayya, da zaman lafiya, su ne ainihin arziki.”
Maryam ta yi murmushi, idanunta suka cika da hawaye na farin ciki.
“I love you, Rouhi.”
“I love you more, Haya.”
Yayi kissing goshinta a hankali, sannan ya ɗora hannunsa a kan cikinta, ai ko kamar yasan an taba shi ya fara motsawa
Zayd yayi murmushi, yana jin daadin yadda yake ganin cikin yana motsawa
“Hey baby girl, Daddy is waiting for you.”
Maryam ta yi dariya.
“Ka riga ka yanke shawarar cewa yarinya ce?”
Zaid ya yi murmushi.
“Ko namiji ne ko yarinya, zan so shi. Amma idan yarinya ce, I’m definitely going to spoil her.”
Maryam ta yi dariya sosai.
“Allah Ya taimake ni akan kula da ku biyu”
ya rungume ta, suna dariya tare.
A waɗannan watannin, labarin Imran da Hauwa Kulu ma ya samu chigaba sosai. Bayan duk lokacin da suka dauka suna fahimtar juna, soyayyarsu ta ƙara ƙarfi, har anyi magana an tsayar da loakcin aure. Imran ya ci gaba da tallafa wa Hauwa a karatunta da burinta, ita kuma zata kasance abokiyar rayuwarsa mai ƙarfafa masa gwiwa. A ƙarshe, sun kusa su fara gina nasu gida cikin soyayya da fahimtar juna.
A yau Maryam ta fara nakuda, tun tana jin ciwo kadan har abun yafi qarfinta, dama kayan da suka saye daga Amsterdam sun iso tun tuni har maryam da zayd sun shirya akwatin zuwa asibiti, kuma zayd ya zabi daki daya da ke tsakanin na maryam da nashi sukayi transforming dinshi zuwa nursery, nan aka jera kayan baby da gado da komai, idan ka shiga zaka dauka ko wani shagon kayan yara ne
Zaid ya shiga damuwa fiye da yadda ya taɓa shiga a rayuwarsa, koda ya wuche da maryam asibiti be ma samu natsuwar gayama su mammi ba se daga baya ya kirasu a waya bayan sun isa asibiti
Private labour room ne suke ciki a Dedah hospital da ke nan cikin unguwar su Katampe, shi da ita da midwives ne ke cikin dakin
“Haya, are you okay? Should I call the doctor again? Do you need anything?”
Maryam ta kalle shi, duk da zafin da take ji sai ta yi mishi murmushi.
“Rouhi, please calm down. You’re making me more nervous than I already am!”
Zaid ya dafe kansa, yanajin kanshi na barazanar watsewa saboda yana ganin yadda take mishi mgana cikin qarfin hali
“Sannu haya, Allah ya sauke ki lfya”
Maryam ta qara damqe hannunsa
“Just pray with me. That’s all I need.”
Zaid ya matse hannunta yane jero addu’o’i
“I’m not going anywhere, Haya. I’m right here.”
Bayan dogon lokacin tsananin wahala da suke ganin kamar lokaci baya wucewa, maryam ta sha wahala, zayd kanshi ya jigata, yayi addu’o’i sosai kuma yana nan tare da ita har loakcin da akache ta fara pushing, ta dauki dan lokaci tanayi yana share mata zufa yana tofa mata addua har daga daga ƙarshe suka ji kukan jaririya.
Zaid ya tsaya cak.
“Is that…?”
Dr din ta dago musu baby da murmushi ta dora ta akan qirjin maryam
“Congratulations! You have a beautiful baby girl.”
Zaid ya rufe fuskarsa da hannayen maryam da ke cikin nashi na ɗan lokaci, hawaye suka gangaro masa, yasa hannu yana shafa goshin maryam da ke jiqe da zufa, sannan yayi kissing din goshin, yanata jero mata addu’o’i
“Alhamdulillah… Alhamdulillah!”
Daga nan sukache ya dan tsaya daga waje zasu kimtsa maryam da baby, seda suka kimtsa su sannan aka basu damar shiga, tare ya shiga da mammi da hajiya raliya
Zaune sukaga maryam akan gado tana riqe da babyn a hannu tanata tofa mata addu’o’i, idanunta cike da gajiya ta dago ta kalli zaid, ya karbi yarinyar daga hannunta, yayi mata addu’o’i da aqeeqah da sunan mama sannan ya miqa ta hannun mammi dukda be gaji da ganinta ba, ya zauna kusa da maryam yana shafa bayanta, se sannu yake mata yana samata albarka, kukan yarinyar sukaji a hannun hajiya raliya, zaid ya miqe ya karbeta ya qura mata ido, dariya ta kucce mishi ganin yadda taketa yamutsa dan qaramin bakinta da fuskar ta, ya shigar da ita cikin jikinshi se tayi shuru ta lafe a jikin shi, wani irin feeling yaji yana ratsa shi da ya kasa gane kowane iri ne, sake kallon yarinyar yayi, duk da anche baa gane kamar jarirai amma yasan dashi take kama, dan qaramin bakinta ne kawai irin na Maryam, ya kalli gashin kanta yaga yadda yake cike sosai har ya kwanto ya rufe eyebrow dinta yana qoqarin rufe mata idanu, daga baya kuma ya kwanta sosai har a wuyan ta, murmushi yayi a ranshi yana chewa ai dole kiyi gashi yarinya kinyi gado
Zaid ya sauna kusa da maryam yanata murmushi
“Thank you, Haya. Thank you for giving me this beautiful gift.”
Maryam ta yi murmushi.
Hajiya Raliya tayi dariya
“Mammi inaga yau zayd baze bari mu dauki jikanyar mu ba”
Maryam ta sunkuyar da kai tana dariya cikin kunya
Suma duka sukayi murmushi
Ya kalli jaririyar, yana shafa ƙaramin hannunta da yatsansa.
“Hello, my princess. I’m your Daddy.”
Jaririyar ta motsa hannunta kaɗan ta matse yatsan kamar tana amsa masa.
Zaid ya yi murmushi sannan ya kalli Maryam.
“Allah Ya raya mana ita cikin imani, lafiya, da farin ciki.”
“Ameen,” Maryam ta amsa cikin yanayin gajiya sosai
Daga baya, labarin haihuwar ya isa ga mama da Aisha, wadda dama Aisha ta riga tayima mama bayanin dalilin da yasa maryam ta kasa gaya mata, murna a wurinsu baa magana, amma da akache za’aje Abuja mama tache ita bazata ba, akayi akayi amma taqi, se innar su imran da mamar su maryama qarama da Aisha da hauwa koulou ne sukaje, imran yaji daadi sosai kuma har number din zayd ya karba ya kirashi ya tayashi murna
Yau ne daren suna, kai da ganin shirye shiryen da akeyi a Balarabe mansion kasan wanna taron sunan ba na wasa bane, kuma a yau ne Fahd ya daure ya fito daga part dinshi yazo har part din mammi yaga jaririya kuma yayi mata addua sosai, Abun da yaba kowa mamaki shine yadda yazo da duk takardun kadarorin da maryayi alh rahman ya bashi, gabadaya haka ya mallaka ma jaririya yache nashi gift kenan zuwa ga baby, kowa yaji daadin wannan sauyin da aka samu kuma mammi a ranta tayi alqawarin zataba Fahd jari me kaurin gaske da zeje qasar waje shima ya kafa nashi business kamar dan uwan shi
Zayd ya shigo dakin mammi da su maryam suke saboda yayi musu seda safe, ya gansu kwanche a kan gado
Maryam ta kalli jaririyarta tana murmushi, sannan ta kalli Zaid, wanda tunda ya shigo ya kasa daina kallon ’yarsa.
A wannan lokacin, duk wahalar da ta sha, duk tambayoyin da suka dame ta, da duk hawayen da ta zubar sun zama wani ɓangare na labarin da ya kai ta ga wannan rana.
Ba wai komai ya zama cikakke ba ne, amma ta fahimci cewa wani lokaci, bayan duhun da ya daɗe, Allah kan buɗe ƙofa zuwa sabon haske.
Ta samu mijin da yake sonta, ta sake haɗuwa da yayarta, iyalinta sun fara warkewa, kuma yanzu tana riƙe da kyautar da Allah ya bata
Zaid ya rungume Maryam a hankali, suna kallon jaririyarsu tare.
“Rouhi,” Maryam ta kira shi cikin murmushi.
“Na’am, Haya”
“Baby lalla fah dakai take kama”
Yayi wani irin murmushin jin daadi yana rungumesu a jikinshi su duka biyu
Kuma a wannan lokaci, labarin Maryam ya kai ga bude sabon shafi, shafin da ba ya cike da tambayoyi da tsoro, se bege, soyayya, da sabuwar tafiya
Wani lokaci… Kiran Ƙaddara ba ya zuwa ne domin ya gaya maka abin da zai faru. Yana zuwa ne domin ya kai ka inda ƙaddararka take jiran ka.
Kuma wannan… ita ce ƙaddarar Maryam da zaid❤️
But remember, in KIRAN ƘADDARA, every blessing comes with a story… and destiny is never done writing.
Alhamdulillahilladhi Bi Ni’matihi Tatimussalihaat❤️
Ya Allah, muna gode Maka da Ka ba mu ikon kammala wannan littafi mai suna KIRAN ƘADDARA. Ya Allah, Ka sanya duk abin da muka rubuta ya zama alheri a gare mu da duk wanda ya karanta shi.
Ya Allah, Ka saka wa duk masu karanta wannan littafi da alheri. Ka biya musu buƙatunsu na alheri, Ka sauƙaƙa musu duk wata damuwa da suke ciki, Ka maye musu gurbin duk abin da suka rasa da mafi alheri. Wanda yake neman aure, Ka ba shi abokin rayuwa nagari. Wanda yake neman haihuwa, Ka azurta shi da zuri’a ta gari. Wanda yake fama da damuwa, Ka saukar masa da nutsuwa da farin ciki. Wanda yake neman arziki, Ka buɗe masa ƙofofin halal.
Ya Allah, Ka kare mu daga hassada, zalunci, cin amana da duk wani sharri na bayyane da na ɓoye. Ka sa mu zama masu gaskiya, haƙuri, tausayi da yafiya. Allah kasa mu gane cewa dukiya ba ta fi mutunci ba, kuma duk wani zalunci yana da ranar da gaskiya za ta bayyana.
Ya Allah, Ka gafarta wa iyayenmu da waɗanda suka riga mu gidan gaskiya. Ka jiƙan su, Ka haskaka kaburburansu, Ka sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsu.
Ya Allah, Ka albarkaci rayuwarmu, iyalanmu da duk waɗanda suke tare da mu cikin alheri. Ka ba mu ƙarfin zuciya a lokacin jarabawa, Ka sa mu gode Maka a lokacin ni’ima, kuma Ka sa ƙarshen lamuranmu ya zama alheri.
Ya Allah, kamar yadda Ka kai mu ƙarshen wannan labari, Ka kai mu ƙarshen rayuwarmu cikin imani, rahama da yardarka. Ka sa mu kasance cikin waɗanda Ka yafe wa zunubansu, Ka karɓi ayyukansu, kuma Ka shigar da su Aljannatul Firdausi ba tare da hisabi mai tsanani ba.
Ameen Ya Rabbal Alameen. 🤲❤️
Ga ku masu karatu, Allah Ya saka muku da alheri bisa kasancewa tare da mu tun daga farkon wannan tafiya har zuwa ƙarshenta. Muna ƙaunarku, muna godiya da goyon bayanku, kuma muna roƙon Allah Ya sa ku sake kasancewa damu a wasu labarai masu cike da darasi da alheri masu zuwa nan gaba in shaa Allah
Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh. ❤️🔥
— The Unnamed Writer
Join our WhatsApp group