Free chapter · Read without an account

42. ...At night...🖊️

by Noor · RU'UYAA (The dreams we never lived)




Ya yi shiru yana kallona cikin ido, don bai da kunya.

Ina jin kamar zan yi fitsari, ga ƙafafuna da suke rawa har na manta da yadda ake numfashi.

“Breathe! Babu abin da zan miki!” ya furta tare da ja da baya, kamar ba shi ne ya gama maganganun rashin ɗa'a ba.

Samun kaina na yi da kaiwa zaune a ƙasa, ina jan numfashi sosai, har da yi wa kaina fifita da hijabi.

What a pervert! na ayyana a raina.

“I'm not a pervert...” ya amsa kamar ya san abin da nake tunani.

“But yeah, don't provoke me... unless you wanna scream my name. You seem to be a good girl! Idan kuma kina so ki zama bad girl, I can give you lessons from every angle!”

Ya yi maganar yana kashe min ido, sannan ya juya min baya yana kwashe gashin kansa da ya walwale.

Na bi bayansa da kallo, baki a buɗe, ba tare da na san na yi hakan ba. Hannuna da nake fifitawa ya tsaya.

Wannan Roman ɗin ya gama goge min hadda tas!Na ɗauka bai san irin waɗannan abubuwan ba. I thought he was innocent. Ashe, ashe...

“I'm just an innocent man with an innocent heart!” ya furta a ƙarshe kafin ya shige elevator.

Wai innocent? Tab ɗi jam!

Da daddare...

Dukkan ahalin gidan suka tattaro suka zo dining, har da Alhaji da suka dawo jiya da daddare. Roman da Khalil ma duk suna nan.

Farzan ke bina da wani irin kallo da ban fahimta ba. Idonsa ciki-ciki, kamar yana ƙoƙarin calculating wani abu. Sai ya kalli sashen Roman, sannan ya sake kallona.

Na haɗe fuska. Shi kuwa ya saki murmushi da shi kaɗai ya san abin da hakan ke nufi, sannan ya ci gaba da cin abincinsa.

Daga lokaci zuwa lokaci, Alhaji Hussein kan kalli sashen Roman, wanda bai kalli kowa ba tun lokacin da ya zauna a wurin.

Khalil ma kamar hankalinsa ba ya kan abincin. Turawa kawai yake yi.

Takaici ɓaro-ɓaro a fuskar Alhaji Hussein, amma bai ce komai ba. Hajiya Momma kamar an biya mata kujerar Makka! Hajiyoyin da ke ɗayan gefen babu fara'a tattare da su.

Samari da 'yan matan gidan ba su san abin da ke faruwa ba. Ni ina tsaye a bayan Khalil, Diyaam a bayan Roman, sauran ma'aikatan kuma a gefe.

A karo na farko, ake cin abinci ba tare da faɗa ko hantara ba. Su Alhazawan suna hira a kan business, yanayin wurin cike yake da nishaɗi.

Sai dai fuskar Roman kamar zai yi aman wuta.

Can sai ya zaro wayarsa da ta yi ding daga cikin aljihunsa.

Cokalin da ke hannunsa ya faɗi bayan ya karanta saƙon. Ya miƙe da sauri, har ya kusan jefar da kujerar da yake zaune a kai.

Kowa ya dawo da idonsa kansa.

Ya ja wani dogon numfashi tare da runtse idanunsa, yana tauna leɓɓansa kafin ya fara barin dining ɗin da manyan takunsa.

Mutanen wurin suka fara kallon-kallo kafin su bishi da ido.

“Romano, ina za ka kuma?” Alhaji Mansir ya tambaya.

Ya ɗan tsaya na 'yan seconds kafin ya amsa da wata irin murya:

“I have an important issue to take care of!”

“Wato za ka je ka yi abin da ka saba, ko?” Hajiya Momma ce ta faɗi hakan, tana hura ƙaton hancinta.

Seraphina ta ɗaure fuska.

Sauran matasan gidan suka shiga ƙus-ƙus a tsakaninsu.

Ba tare da ya juyo ba, Roman ya ce, “What's a man without a little violence!”

Ya yi maganar yana cracking ɗin hannayensa kamar wanda zai je faɗa, fuskarsa cike da wani irin mugun murmushi.

Bai sake cewa komai ba, ya fita daga gidan gaba ɗaya.

Na ji ƙafafuna suna ƙaiƙayin son bin bayansa, sai da na mintsini kaina a cinya sannan na iya hana kaina.

“Allah ya wadaran naka ya lalace!” in ji Hajiya Ruƙayyah.

Wasu suka amsa da, “Ameen.”

“Rashin uwa ba ƙaramin abu ba ne. Ku daina ganin laifinsa, don Allah!” Hajiya Hafsah ta faɗa cikin tausayawa.

Farzan ya ɗaure fuska yana caccakar abincinsa.

“Shi Ibrahim da uwarsa ta yi nesa da shi bai lalace ba, sai shi Roman ɗin ko? Wai idan ba shi da uwa, ba shi da uba ne?”

Hajiya Wareesha ta faɗa tana juya ido.

Khalil ya ajiye cokalin nasa ya bar wurin. Yanayin tafiyarsa kamar wanda ya sha wani abu.

Ban tsaya na gama jin abin da suke faɗa ba. Na sulale na bi bayansa.

A maimakon ya shiga elevator, sai na ga yana bin stairs. Yana ɗaukar lokaci kafin ya taka kowane mataki, kamar ƙafafunsa sun yi masa nauyi.

“Khalil!” na kira daga ƙasan stairs ɗin.

A hankali ya juyo yana kallon ƙasa.

“Yeah... is everything fine?” ya amsa.

Na ƙarasa inda yake.

“Ni ya kamata in tambaye ka. Kana lafiya?”

Ya tsare ni da ido na ɗan lokaci, sai kuma ya yi min murmushin yaƙe.

“Eh, lafiya ta ƙalau. Na gaji ne, shi ya sa...” ya ƙarasa maganar tare da yin gaba da sauri, kamar yana tsoron kada in sake tambayarsa.

Rufe ƙofar ɗakinsa ya yi, ya jingina bayansa da ita yana mayar da numfashi.

Jiki a sanyaye ya isa bakin gado ya zauna, tare da tallafo haɓarsa.

Ya gaji da pretending kamar a duk lokacin da ya ga kowa a zaune da iyayensa a dining, ba ya jin wani irin ciwo a zuciyarsa.

Ya gaji da pretending kamar zama shi kaɗai a gida, nesa da uwarsa, ba ya ƙuntata masa zuciya.

A da can, ba ya complaining saboda ya san yadda Ma ke tsananin son mahaifinsa. Shi kuma ya yi kama da mahaifinsa sosai, har a duk lokacin da ta kalle shi, sai ya ga ta fashe da kuka.

Da gangan yake nisanta kansa da ita saboda ba ya son ta ji baƙin ciki.

But at the cost of what? His own happiness?

Shi ma yana son ƙaunarta, kulawarta da duk wani abu da uwa za ta iya ba ɗanta.

Daga ƙarshe, ta sallame shi zuwa wata ƙasa, ita kuma ta ci gaba da business ɗinta saboda kawai ba ta son ta ci gaba da jin raɗaɗin rashin mahaifinsa.

Ta shagaltar da kanta da harkokin kasuwanci domin ta manta da zafin da take ji. Amma a ƙarshe, sai ta manta da kanta, ta kuma manta da ɗanta.

A duk lokacin da ya nemi ya gan ta, sai ta ce masa tana zuwa. Idan ya dage, sai ta zo, watakila na minti talatin ko ma ƙasa da haka, kafin ta tafi.

Ya kasance yana gamsuwa da hakan, tunda tana zuwa aƙalla.

But as time went on, sai ta daina zuwa gaba ɗaya. Idan ya kira ta, sai dai ta turo masa da kyaututtuka.

Ba ta san cewa ba kyauta ko wani abu yake nema ba.

He only wanted his mother. Nothing more.

Da ace tana kusa da shi, watakila da bai tsinci kansa a rayuwar da ya faɗa ba.

Ko wane second na rayuwarsa, yana nadamar ranar da ya bar Najeriya zuwa Berlin.

Yana nadamar ranar da ya fara zuwa Marple Woods Academy.

He regrets every second of it.

Ya sulale ya kwanta a kan gadon, tare da zaro wani hoto da yake ajiyewa a ƙarƙashin pillow ɗinsa.

Ya ɗaga hoton ya daidaita shi da fuskarsa.

A cikin hoton, shi da mahaifinsa ne, sanye da kayan pirates, tsaye a kan deck na jirgin ruwa, suna yi wa juna murmushi.

Khalil ya lumshe idanunsa.

'Idan ban nan, Ma tana nan, za ta kula da kai!'

Ya tuna kalaman mahaifinsa.

Wani ɗan ƙaramin murmushin baƙin ciki ya bayyana a fuskarsa. Ba tare da ya buɗe idanunsa ba, ya furta:

“Zafin mutuwarka has numbed her emotions, Pah... I'm insignificant!”

Ya yi maganar cikin raɗaɗi.

Ya ji ƙasan idanunsa ya fara zafi, alamun hawaye na shirin fitowa. Da sauri ya buɗe idanunsa, ya sauka daga kan gadon, sannan ya fara safa da marwa yana yi wa kansa magana kamar wanda ya rasa nutsuwarsa.

“You're not going to cry, Ibrahim... real men don't cry. Yeah... you're not hurt... you're not sad... Ma tana sonka... she's doing everything for you... yeah... suck it up...”

Yayin da yake ƙoƙarin shawo kan kansa cewa komai yana lafiya, sai ya ƙara jin baƙin cikin yana maƙure masa numfashi.

Ya faɗi a kan guiwowinsa, ya rufe fuskarsa da hannayensa biyu, yana jan numfashi da ƙarfi, kamar wanda ya rasa nutsuwarsa gaba ɗaya.

“It hurts!” ya furta daga ƙarshe cikin raunin murya.

Ya ja jikinsa ya koma kan gadon, amma ya kasa yin barci.

Ya fara juyi-juyi kafin ya juya yana kallon ceiling, yana sauraron bugun agogo da kuma bugun zuciyarsa.

Daga baya ya sauka daga kan gadon, zuciyarsa tana ingiza shi da ya je ya yi abin da ya saba yi.

This way, the pain will go away before I even realize it. Daga baya kuma sai in yi istighfar.

Ya tsaya a tsakiyar ɗakin, yana ta saɓani da kansa tsakanin bin son ransa da kuma cika alƙawarinsa na ba zai sake komawa waccan rayuwar ba.

Tunaninsa bai kai shi ko'ina ba, sai ma ya ji kansa yana ƙara ƙullewa.

Zafin da ke zuciyarsa yana ƙara ƙaruwa, kuma a wannan lokacin, yana jin zai iya yin komai don kawai ya dakatar da shi.

Ya figi mukullin motarsa, ya ɗaura farar jacket a saman kayan da yake sanye da su, sannan ya fita.

Bai ma damu da kunna fitilar parlour ɗin ba. Kai tsaye ya nufi ƙofar fita.

Cikin duhun, sai ya ji ya ci karo da mutum.

Su biyun suka faɗi a kan kujera.

Fuskarsa ta faɗa a ƙirjin yarinyar.

“Ahhh!” Diyaam ta saki ƙara, idonta a waje.

Da sauri Khalil ya rufe bakinta da tattausan hannunsa, jikinsa yana rawa.

Diyaam ta ci gaba da zaro ido cikin duhu, tana jin nauyin Khalil a jikinta.

Tun daga lokacin da ta ga ya bar dining ɗin, ta lura da yanayinsa. Ko da ta koma ɗaki, ta kasa barci, tana ta juyi-juyi daga wannan gefe zuwa wancan.

Bayan ta yi fama da kanta na tsawon lokaci, ta sauka daga kan gadon, ta yafa farin mayafi a saman jajayen PJs ɗin da take sanye da su.

Ta fito daga ɗakinsu tana tafiya a hankali, har ta iso gaban ƙofar ɗakinsa. Nan ma sai da ta ɗan tsaya kafin ta tura ƙofar parlour ɗin ta shiga.

Sai dai babu abin da take iya gani saboda duhun.

Ta fara lalube har ta kai tsakiyar parlour ɗin, a daidai lokacin da suka ci karo.

“Who is it?” ya tambaya cikin ƙaramar murya, tare da cire hannunsa daga fuskarta.

“Ni ce, Diyaam,” ta amsa cikin rawar murya, har tana jin zafafan numfashinsa a ƙirjinta.

KHALIL ya ɗan zaro ido kafin ya fara ƙoƙarin sauka daga jikinta. Tun kafin ya gama tashi, ita ma ta yi ƙoƙarin tashi.

Aikuwa, ta sarƙafe ƙafarsa, hakan ya sa ya yi tuntube.

Ya sake faɗowa kanta ba da gangan ba, hannunsa ya bugi ƙirjinta.

Diyaam ta fasa ƙara.

“Wayyo Allah, ƙirjinaaaa!”

Khalil ya sake rufe bakinta, yana shafa ƙirjinta a ruɗe, domin ihunta ya gama hargitsa masa lissafi.

“I'm so... sorry... does it hurt? Akwai zafi?”

Diyaam ta ji numfashinta ya ɗauke. Da sauri ta buge hannunsa daga wurin, ta ture shi daga jikinta.

Da mugun gudu ta fita daga ɗakin.

Khalil ya biyo bayanta, hankalinsa a tashe.

A hallway ya yi saurin riƙota. Da zarar idonsu suka haɗu, Diyaam ta fashe da kuka.

Khalil ya dinga kallon ko'ina a hallway ɗin, gumi yana tsatstsafo masa.

Cikin kwantar da murya ya ce, “I'm sorry, Sophia... kin ji? Ki daina kuka, don Allah. It wasn't intentional.”

Diyaam ta gama ruɗewa. Ita fa tsoronsa ya gama cika ta.

Who does that? ita namiji ne da zai shafa ƙirjin ta a haka?

Ganin yadda ya gama fita hayyacinsa ya sa ta sassauta kukan. Sai ta sunkuyar da kanta tana share hawaye.

Khalil ya sauke ajiyar zuciya, yana share gumin da ke goshinsa.

“Me kike yi a nan?” ya tambaya bayan ɗan lokaci.

Nan ta shiga rarrabar ido, alamun rashin gaskiya.

“Ni... n... nazo... in duba ka ne!” ta faɗa da sauri, tana kau da idonta daga nasa.

“Thanks,” ya faɗa a ƙarshe.

Idonta ya sauka a kan mukullin da ke hannunsa.

“Fita za ka yi?”

Ya gyaɗa kansa, yana tunawa da inda ya yi niyyar zuwa.

Once more, ya sake shiga yanayin saɓani da kansa. Ko ya koma ya kwanta, tunda ya ɗan rage jin zafin da ke zuciyarsa, ko kuma ya je ya yi abin da ya yi niyya?

Sai da ya ja dogon numfashi kafin ya ce, “I'm going to the beach. Wanna come along?”

Diyaam ta ɗago idanunta cikin mamaki ta kalle shi.

Murmushi ya fara bayyana a fuskarta.

“Yes!!!” ta amsa da sauri, muryarta a sama, har ta yi tsalle.

Khalil ya karkatar da kansa gefe yana dariya.

Da sauri ta juya masa baya, kunya ta kamata sosai.

Ya ajiye mukullin a corridor ɗin saman wani flower vase.

“Mu tafi!”

Ya yi gaba, ita kuma ta bi bayansa, tana jin kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha.

Suna tafiya cikin shiru mai natsuwa a ƙasa.

Diyaam ta rungume jikinta saboda sanyin da ake zubawa.

Lura da hakan ya sa Khalil cire jacket ɗinsa. Ya zagayo gabanta yana saka mata shi.

Diyaam ta ɗago idanunta, suka shiga cikin nasa.

Da sauri ta sunkuyar da nata, zuciyarta na harbawa da sauri.

“Do you want me to carry you?” ya tambaya cikin zolaya, yana gyara mata gashinta.

Diyaam ta buɗe baki, amma ta kasa cewa komai. Sai blushing kawai take.

“Ahah! Abin da nake son gani kenan!” ya faɗa yana kallon yadda kumatunta suka yi ja.

Diyaam ta rufe fuskarta.

“Hammaaa!” ta kira a shagwaɓe, tana juya masa baya.

Khalil ya yi dariya, yana ci gaba da zolayarta har suka iso bakin teku.

Wurin ya yi kama da lokacin rana ta fito.

Saboda hasken da ke wurin, da kuma tarin mutanen da suka zo beach party, komai ya yi kyau. Samari da 'yan mata sun cika wurin. Akwai firecrackers, confetti da sauran abubuwan nishaɗi.

Ga kuma masu sayar da abubuwan ciye-ciye.

Diyaam tana bin wurin da kallo cike da burgewa, duk da cewa ba ta son ƙarar loud music ɗin da ake kunnawa.

A hankali Khalil ya fara jagorantar ta zuwa wani wuri da ba mutane sosai, yana kare ta da jikinsa har suka isa.

Ya zaunar da ita a wurin cikin kulawa irin ta gentleman.

Diyaam kuwa tana satar kallonsa, zuciyarta na bugawa a wani irin yanayi mai daɗi da raɗaɗi a lokaci guda.

Tambayoyi da yawa ne ke yawo a zuciyarta.

So many wishes, hopes and dreams, all with him.

“Ya dai, da kallo?” ya tambaya.

Da sauri ta sunkuyar da kanta, tana wasa da jacket ɗinsa, feeling embarrassed.

Ya zauna yana fuskantarta, da ɗan murmushi a fuskarsa. Kunyarta na burge shi sosai.

Waiter ne ya kawo musu menu.

Diyaam ba ta san abin da za ta ci ba.

“Okay, drink fa?” ya tambaye ta.

“Ban san wane ba...”

Khalil ya gyaɗa kansa.

“Okay... ki ɗago ki kalle ni mana.”

Ya tauna gefen bakinsa, yana ƙoƙarin hana kansa murmushi.

“Nidai a'a!” ta faɗa tana rufe fuskarta da tafin hannunta.

Ya yi wata ƙaramar dariya kafin ya faɗa wa waiter ɗin a hankali abin da zai kawo musu.

After a while, waiter ya dawo da kofuna biyu. Ɗaya bitter gourd smoothie ne, ɗayan kuma milkshake.

Ya miƙa wa Diyaam bitter gourd ɗin, sannan ya ajiye milkshake ɗin a gaban Khalil.

“Here's your drink, Sophie.”

Ba tare da ta ɗago ba, ta karɓa.

“Na gode.”

“My pleasure, Sophie!” ya amsa, yana danne dariyarsa.

Diyaam ta kai straw ɗin bakinta ta fara sha.

r

smoothie ɗin na shiga bakinta, ta waro manyan idonta

Fuskarta ta yamutse, ta gunɗe baki, sannan ta ɗago idonta waje tana kallon Khalil kamar za ta yi kuka.

Ta karkatar da fuskarta gefe ta tofar da abin.

Khalil ya tuntsire da dariya har sai da ya faɗi daga kan kujerarsa.

Numfashin Diyaam ya tsaya.

Ganin irin kyawun da ya yi yayin dariyar ya sa ta kasa kawar da idonta daga gare shi. Sautin dariyarsa ya ratsa kunnenta like a melody.

Har ta manta da masifar da ta so zazzaga masa.

Her heart drummed painfully sweet in her ears.

Ganin ta daina motsi ya sa ya miƙe yana kakkaɓe hannunsa. Ya matso kusa da ita.

“Hey, sorry... I only wanted you to look at me.”

Sai a lokacin ta dawo hayyacinta.

Ta juya masa baya tana turo baki.

Khalil ya ɗauko strawberry smoothie, yana ci gaba da danne dariyarsa, sannan ya miƙa mata.

“Ga wannan, ki wanke baki da shi...”

Diyaam ta ƙi sauraron sa sai da ya yi da ƙyar sannan ta karɓa.

Daga baya suka bar wurin. Ta cire takalmanta, shi ma ya cire nasa, suka fara tafiya a bakin teku, suna barin sawun ƙafafunsu a baya.

Diyaam ta ji daɗi sosai. Da sauri ta shanye smoothie ɗinta, ta ajiye kofin, sannan ta fara gudu a bakin teku.

Khalil yana tafiya a hankali daga bayanta.

He felt grateful to her.

Da ba don Allah ya kawo ta ba, da ya karya wa kansa alƙawari a karo na ba adadi.

Ya hangi Diyaam tana gudu, mayafinta ya faɗi, gashinta yana bin iska yayin da take wasa kamar ƙaramar yarinya.

“She's just a kid!” ya amsawa kansa yana murmushi.

Wani gaye mai sayar da kayan kwalliyar gashi ya sha gabansa.

“Yallaɓai, ga hair clips masu kyau. Ka sayawa budurwarka.”

Khalil ya kalli hair clips ɗin masu matuƙar kyau, sannan ya kalli Diyaam.

Sai ya ɗauki wani hair clip mai red rose a jikinsa, ya biya kuɗin, sannan ya ci gaba da tafiya zuwa inda Diyaam take.

Sai da Diyaam ta ga ta kusa kaiwa inda daji yake kafin ta juyo ta sake dawowa, tana tsalle-tsalle.

Ta tsaya a gaban Khalil tana haki, sannan ta sakar masa murmushi.

Shi ma ya mayar mata da murmushin kafin ya matso kusa da ita.

“I got this for you.”

Ya nuna mata hair clip ɗin, sannan ya kama gashinta daga gefen kunnenta ya saka mata shi.

Diyaam ta riƙe numfashinta, idanunta a rufe saboda kusancinsu.

Sai ta saki numfashin a hankali, tana shaƙar ƙamshinsa mai daɗi, tana jin kamar tana son su ci gaba da kasancewa a nan har abada.

She wasn't wrong to have fallen for him.

A da ta ɗauka crush kawai take yi masa, amma yanzu ta tabbatar cewa abin ya fi haka zurfi.

“You look beautiful...” ya furta yana ja da baya.

“Na gode,” ta amsa cikin murna, kanta a ƙasa.

Can kuma ta ja hannunsa suka isa bakin teku.

Sanyin ruwan ya fara shafar ƙafafunsu tun kafin ta tsoma nata ciki.

Khalil ya tsaya yana kallonta.

Diyaam ta ƙara matsawa kusa da ruwan, ta tsoma ƙafarta ciki tana dariya kafin ta sa ɗayar ƙafar ma, bayan ta tattare wandon da ke jikinta.

“Kai, ruwan nan yana da sanyi sosai!”

Ta sunkuya ta kwaso ruwa, ta juyo ta watsa wa Khalil, wanda ya yi nisa cikin tunani.

He was startled.

Hakan ya sa ta sheƙe da dariya, saura kaɗan ta faɗi.

Da sauri Khalil ya riƙota, ta faɗo a jikinsa.

“You're blushing again...” ya furta cikin ƙaramar murya.

Da sauri ta miƙe da kyau, tana kallon ko'ina ban da fuskarsa.

Ta ba shi dariya.

“Hey, thanks...” ya furta.

“Da me?” ta tambaya tana ɗan juyowa.

“You saved me!” ya amsa yana shiga cikin ruwan shi ma.

Ganin haka ya sa ta sake juyawa. Nan ma ta kusa faɗuwa, ya sake taro ta, bayanta ya jingina da ƙirjinsa.

Numfashin Diyaam ya fara fita da sauri, jikinta duk ya yi zafi.

Sai da ya tabbatar ta tsaya daidai kafin ya duƙa ya kwaso ruwa mai yawa ya watsa mata a fuska.

“Ahhh!” ta saki ƙara haɗe da dariya, kafin ita ma ta fara watsa masa ruwa.

Su biyun suka koma kamar wasu ƙananan yara.

Eventually, Khalil ya fita daga ruwan da gudu, ita kuma ta biyo bayansa.

Sun ɗauki lokaci suna gudu kafin ya cim ma ta.

Khalil yana dariya ya juyo.

“Wait... excuse... I'm... HHH... I'm no—”

Ya kasa ƙarasa maganar saboda yadda ta yi karo da shi, ga dariyar da ta ƙi tsayawa.

A daidai lokacin da ta ɗaga ƙafa don ƙara taku, ƙafarta ta sauka a kan banana peel da ba su gani ba.

Ta zame, ta faɗa kai tsaye a kansa.

Su biyun suka faɗi a ƙasa, ita a samansa.

Gashinta ya zubo gefe da gefen fuskarta har ya zama kamar rumfa a saman fuskarsa.

Her doe eyes met his hazel ones.

Kamar lokaci ya tsaya musu.

Numfashinsu yana fita a tare, yayin da hasken wata ya sauka a fuskar Khalil, yana haskaka kyawawan siffofin fuskarsa, musamman... leɓɓansa.

Diyaam ta ƙifta idanunta a hankali kafin ta sauka daga jikinsa, feeling so embarrassed.

Ganin bai tashi ba ya sa ta ɗan matsa, ta kwanta a gefensa.

Su biyun suka yi shiru, suna kallon sararin samaniya da ke cike da taurari da kuma ƙaton wata.

Ƙarar kiɗan beach party ta yi nisa da su.

Kowa da abin da yake tunani a zuciyarsa.

Diyaam ta buɗe bakinta sau da dama, tana son tambayarsa abin da ya daɗe yana maƙale mata a zuciya, amma a ƙarshe babu abin da ke fitowa sai iska.

Finally, ta tattaro duk wani ƙarfin gwiwa da take da shi.

“So... kai da Abeedah... are you guys in love?”

Ta yi maganar cikin rawar murya, ƙirjinta na lugude, musamman da ya yi shiru bai amsa ba.

Sai ta juya fuskarta zuwa gare shi, ta ga shi ma yana kallonta.

Ta kawar da kanta da sauri, tana jin haushin kanta saboda tambayar da ta kira wauta.

“Nope! We're only friends!”

“Woah! Da yawa mun ɗauka sonta kake... ni da masu aikin!” ta furta, tana jin wani irin sanyi a ranta saboda amsar da ya ba ta.

“Why would you think so?”

“Saboda yadda kake ɗaukarta... fiye da kowa,” ta amsa cikin ƙaramar murya.

“Hmmm... just like Rome is nice to you without attaching feelings to it, I'm also nice to her in the same way. Babu wani abu tsakaninmu!”

Ya amsa yana kallon wani tauraro da ya fi sauran ƙyalli.

“Na gane,” ta ce tana gyaɗa kanta.

Suka sake yin shiru.

Khalil ya lumshe idanunsa, yayin da Diyaam ta ji wani irin daɗi ya mamaye zuciyarta.

Of course! Ya kamata ta yi tunanin hakan tun da farko.

Ita ma Roman yana yi mata irin wannan kulawar duk da cewa Roman da Khalil suna da bambanci sosai.

While Khalil is outgoing, Roman isn't receptive 

A haka suka ci gaba da kasancewa, har bacci ya fara figar Diyaam.

Da ƙarfe sha biyu da rabi na dare, Khalil ya miƙe. Da ya juyo, sai ya ga ta naɗe wuri guda, tana barci cikin kwanciyar hankali.

Ya yi wani ɗan ƙaramin murmushi, sannan ya sunkuya ya ɗauke ta.

Ya ɗauke ta a hankali, domin a ganinsa kamar ƙaramar yarinya ce.

Yadda ba ta da nauyi ya sa murmushinsa ya faɗaɗa.

Ya nufi hanyar fita daga bakin teku, ransa cikin walwala, har wani irin nishaɗi yake ji.

For once, his heart felt a little lighter.


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol