Free chapter · Read without an account
Chapter 19
Da muka shiga zauren gidan, sai muka ji hayaniya tana tashi daga tsakar gida. Muryar Gwaggo ce ta fi tashi, tana ta masifa, har muka tsaya muna kallon juna.
“Anas! Ka saki ɗana! Kai, me ya sa ba ka da hankali ne? Ka fasa masa baki!”
Na kalli Kuluwa, ita ma ta kalle ni.
“Me ya faru ne haka?” na tambaye ta a hankali.
“Mu je mu gani,” ta amsa.
Da muka isa tsakar gidan, sai muka tarar da Anas da Ayuba suna ta faɗa. Ayuba, ɗan Gwaggo Tapito, ya ɗauki takalmin Anas ya saka a ƙafarsa, amma takalmin ya tsinke. Hakan ne ya sa Anas ya fusata har ya kai masa naushi a baki.
Amma Gwaggo Tapito, maimakon ta fara tambayar abin da ɗanta ya yi, sai ta damƙi Anas tana ƙoƙarin janye shi daga kan Ayuba.
“Ka sake ɗana! Ka ji ni ko? Ka sake shi!” ta yi ihu, tana jan Anas da ƙarfi.
Anas ya fizge jikinsa, ya sake kai wa Ayuba naushi, har Ayuba ya riƙe bakinsa yana kuka.
“Wayyo, Mama! Ya fasa mini baki!”
Gwaggo ta zabura, ta juya ga Anas cikin tsananin fushi.
“Wallahi, sai ka gane kuskuranka! Kai ba ka da kunya ne? Saboda takalmi kawai za ka fasa wa ɗana baki?”
Anas ya kalle ta cikin fushi.
“Saboda takalmi? Ai shi ne ya ɗauke min takalmina ya tsinka min shi! Amma saboda ɗanki ne, ba za ki ga laifinsa ba!”
“Rufe bakinka! Ba zan tsaya ina sauraron rashin kunyarka ba!”
Gwaggo ta ci gaba da masifa, tana kare Ayuba, yayin da Anas yake ta ƙoƙarin komawa kansa. Daga ƙarshe aka samu nasarar raba su, amma har lokacin Gwaggo ba ta daina yi wa Anas faɗa ba.
Na tsaya ina kallonsu, ina mamakin yadda Gwaggo ta mayar da dukkan laifin a kan Anas, alhali Ayuba ne ya fara ɗaukar takalminsa.
Kuluwa ta ja hannuna a hankali, muka matsa gefe, muna kallon yadda rikicin ya ci gaba.
Ana cikin wannan hayaniyar ne, sai ga Baba ya fito daga ɗakinsa. Da alama yana cikin jin daɗin zamansa, domin da ya fito sai ya tsaya yana kallonmu, yana jin yadda muryoyinmu suka cika tsakar gida.
“Lafiya kuwa? Me ke faruwa ne a gidan nan? Tun daga ɗakina nake jin hayaniyarku!” Baba ya faɗa cikin kakkausar murya.
Nan take kowa ya yi shiru na ɗan lokaci. Anas yana tsaye yana huci, Ayuba kuma yana riƙe da bakinsa, yayin da Gwaggo Tapito take tsaye kusa da shi, har yanzu fuskarta a murtuke.
Baba ya sake kallonmu, sannan ya tambaya, “Na tambaye ku, me ya faru ne?”
Gwaggo Tapito ta yi saurin magana.
“Ka ga abin da Anas ya yi wa ɗanka, Malam? Ya fasa masa baki! Wallahi, da ka ga yadda ya yi masa, da kai ma za ka fusata!”
Anas ya juya gare ta cikin fushi.
“Gwaggo, ki faɗi gaskiya mana! Ayuba ne ya ɗauke min takalmi ya tsinka min shi, sannan yana yi min rashin kunya. Shi ya sa na kai masa naushi!”
Baba ya ɗaga hannu yana nuna su duka.
“Ku yi shiru! Zan saurari kowa, amma ba zan yarda da wannan hayaniyar ba!”
Na tsaya a gefe tare da Kuluwa, ina jiran jin abin da Baba zai ce. Na san idan Baba ya fara tambayar abin da ya faru, kowa zai yi ƙoƙarin kare kansa.
Gwaggoo ta kalli Baba, ta ce cikin fushi:
“Malam, ya kamata ka shiga tsakanin Ayuba da Anas. Ai shi Anas tantirin yaro kawai
Baba ya kalli Gwaggo da idanunsa, yana girgiza kai cikin fushi, sannan ya ce:
“Shin, shine za ku mayar da gidana gidan ’yan dambe? Kullum sai hayaniya da rigima! Ba ku da abin yi ne sai faɗa?”
Baba bai tsaya dogon tunani ba, sai ya kalli kowa cikin fushi ya ce, “Na kashe maganar nan! Kowa ya watse ya ba ni wuri! Ba na son sake jin wata hayaniya a tsakar gidan nan!”
Ya ci gaba da masifa yana faɗin albarkacin bakinsa, har sai da kowa ya fara watsewa. Daga ƙarshe, ya juya ya nufi ɗakinsa, yana ta mita a ƙasan ransa.
Anas kuwa yana gefe, fuskarsa a murtuke, bai ce komai ba. Na ƙarasa inda yake tsaye, na tsaya kusa da shi.
“Anas, ka yi haƙuri. Ka bar maganar nan ta wuce, don Allah. Kada ka sake shiga wata rigima da Ayuba.”
Ya kalli inda nake, amma bai amsa mini ba. Duk da haka, na san yana jin maganata. Anas ba ya cika sauraron maganar kowa, amma idan ni ce nake yi masa magana, yana saurarona. Wani lokaci ma, idan ya samu kuɗi, yakan ba ni in ajiye masa.
Na sake kallonsa, na ce, “Ka dai yi haƙuri, Anas. Ka san Baba ba ya son irin wannan hayaniyar.”
Ya ɗan yi shiru, sannan ya kawar da kansa, amma ban damu da rashin amsarsa ba. Na san halinsa, kuma na saba da shi.
A gefe guda kuma, Mama Hauwa tana cikin ɗakinta. Ba ta fito ba, duk da cewa ta ji hayaniyar da aka yi. Wataƙila ba ta ga dalilin fitowa ba, domin ba ɗanta ne aka yi wa ba. Haka kuma, ba ta son shiga maganar da za ta iya jawo mata saɓani da Gwaggo Tapito.
Na kalli Anas a hankali, ina tunanin irin rayuwar da ya taso a cikinta. Duk da halinsa na taurin kai da saurin fushi, na san akwai wasu abubuwa da yake ɓoyewa a zuciyarsa, waɗanda ba kowa ne yake iya ganewa ba.
Anas ɗan matar Baba ne, wadda ta rabu da Baba tun yana ƙarami. Tun bayan barin mahaifiyarsa, bai samu kulawar da yaro yake buƙata yadda ya kamata ba. Duk da cewa gidanmu cike yake da mutane, kowa yana harkokinsa, shi kuma yana ta girma ba tare da wanda zai zauna ya fahimci halinsa ko ya yi ƙoƙarin gyara masa tarbiyya ba.
Tun yana ƙarami ya saba bin yaran unguwa, har daga baya ya fara shiga cikin halaye marasa kyau. Daga nan ne ya fara shaye-shaye, kuma wasu daga cikin mutanen gidan sun daina ƙoƙarin yi masa nasiha saboda tsoron halinsa. Anas ba ya tsoron kowa, kuma idan ya fusata, ba ya la’akari da wanda yake gabansa.
Amma duk da haka, yana girmama ni sosai. Ya ɗauke ni a matsayin yayarsa, kuma ko da yake ba ya cika sauraron maganar kowa, idan na yi masa magana, yana sauraro. Wani lokaci ma, idan ya samu kuɗi, yakan ba ni in ajiye masa. Wannan ya sa na fahimci cewa duk da halinsa, akwai wani ɓangare na Anas da yake nuna min yarda da girmamawa.****