Free chapter · Read without an account

PAGE 28

by Khadijah Sulaiman · SAWU BIYU

SAWU BIYU
Khadijah Sulaiman 
Young Talented Writers Association (YOTA)

Book 1
Page 28

Tana fitowa daga lectures ta ciro wayarta a jaka,ganin mai kiran yasa tayi guntun murmushi.
"Love kin gama?"
Ta ce"yanzu na fito".
Ya ce"alright,Ina parking space".
Ta kashe wayar ta nufi inda yake,tun daga nesa yake ƙare mata kallo,Allah kaɗai ya san irin son da yake yiwa wannan baiwar tasa.
"Kar a cinye ni da ido".
Tayi maganar tana aika masa wani kallo da ya kusan narkar da shi.
"Idan na cinye ki kinga dai dai kenan,babu wani namiji da zai sake kallon wannan kyakkyawar fuskar".
Ta ƙarasa ta buɗe kofa ta shiga,yayi murmushi ya buɗe driver seat ya zauna.
A hankali ya ce "Zarah".
Ta ɗan juyo ta kalle shi ta ce"Ya Sudais".
Fuskar shi ɗauke da damuwa ya ce"wannan ɓoye ɓoyen na damuna,ina sonki,amma iyayenmu sun ƙi bamu haɗin kai musamman Mama,ba zan iya rabuwa dake ba Zarah".
Ta gyara zama da kyau tana fuskantar shi ta ce"nima haka Ya Sudais,ni kai kawai nake so,idan an rabamu mutuwa zanyi".
Yayi murmushi ya ce"ba za ki mutu ba my love,har sai mun haifi yara kyawawa kamar ki".
Ta sunkuyar da kai ta ce"Allah yasa".
Ya amsa da Amin yana kallon fuskarta,ya kai hannun shi back seat ya ɗauko wani farin leda.
Ya ciro abincin dake ciki ya ce"i know you're hungry my love,ga abinci na kawo miki".
Ta ɗanyi murmushi ta ce"tea kawai na sha da safe".
Ya ce"na sani ai,shi yasa kullum gaki nan babu wani jikin kirki,amma nafi son ganinki a haka,in ɗauke ki in yi juyi dake".
Ya kai ƙarshen maganar tare da kashe mata ido.
Ta ɗauke kai da sauri tana turo baki.
Da kanshi ya dinga bata abincin har ta cinye,ya buɗe nashi abincin ya ce"oya,ita your turn".
Babu musu ta karɓa ta fara bashi a mutane,bin ta kawai yake da kallo,a zuciyarsa addu'a kawai yake Allah ya nuna mishi ranar da za ta zama matar shi.
Ta turo baki ta ce"Wannan kallon fa?"
"I love you Zarah".
Ta ɗauke kai da sauri,yayi dariya ya ce"wai kunyata ki ke ji? Lallai zan kama ki ne,kin gama lectures ne?"
"Na gama,yanzu zan kira driver".
Ya girgiza kai ya ce"mu tafi gidan gabaɗaya".
Da sauri ta ce"a'a babu ruwana dan Allah,ka bari in kira driver".
"Don't say so please Zarah,idan mun saka tsoro a ranmu yaushe za mu sami abinda muke so?ni da ke muna son junanmu,bai kamata mu dinga ɓoye hakan ba".
Bai bata damar cewa komai ba ya tada motar,driving kawai yake amma babu mai cewa komai a tsakaninsu.
Har yayi horn mai gadi ya buɗe mishi gate hankalinta bai kwanta ba,ta ɗago da niyyar buɗe ƙofa ta hango Mama saman corridor ɗinta tare da ƙawarta.
Ta sake ƙofar da sauri gabanta na faɗuwa ta ce"na shiga uku".
Da sauri ya kalleta ya ce"lafiya?"
Da yatsa ta nuna mishi Hajiya Mama,ya koma ya kwantar da kanshi ya lumshe ido.
A hankali ya ce"i assure you komai zai wuce Zarah,watarana za ta so ki,ko ba yanzu ba,i know idan munyi aure ki ka haifa mata beautiful grandchildren dole she'll love you".
Ta ɗan kalle shi don maganganun shi sun ɗan kwantar mata da hankali.
A ɓangaren Mama tunda motar Sudais ta shigo suka dakata da hirar da suke, ƙawarta Zainab ta ce"kamar motar Sudais?"
Mama ta ce"shi ne".
Hajiya Zainab"amma ya batun zancensa da waccan ƴar farar?"
Mama ta taɓe baki ta ce"wa ya san masa?anya haka aka bar min yaron nan kuwa?ban cika ganinsu tare ba amma na san ba zai rabu da yarinyar cikin sauƙi ba wallahi....."
Ta waro ido da sauri ganin sun haɗa ido da Zarah dake ƙoƙarin shiga part ɗinsu.
Ta miƙe da sauri ta ce"kai ! Me na ke gani haka?"
Hajiya Zainab ta miƙe ta riƙe ta da sauri ta ce"ina kuma za ki je haka Hajiya Ramla,koma ki zauna dan Allah".
"Zainab ƙyale ni in ci uban yarinyar can,shegiya mara kunya,uban me take a motar ɗana?"
Ta sake waro ido ganin Sudais yayi reverse ya bar gidan.
Jiki na rawa ta ce"kin gani ko Zainab,wallahi sun asirce min ɗa, Sudais ne zai hango ne ya fita da mota da gudu?"
"Dan Allah ki zauna Ramlah, matsalata dake kenan,ki nutsu a samo mafita kin tsaya shirme".
Ta koma ta zauna sai huci take kamar kumurci.
Hajiya Zainab ta gyara zama ta ce"yanzu ke so kike ya aure ta?"
A firgice ta ce"wani irin zancen banza ne haka Zainab,wallahi da Sudais ya auri yarinyar can gara na bar gidan nan".
Hajiya Zainab ta riƙe baki ta ce"ki bar gidan nan a wani dalili,saboda kishiya,kishiyar ma wacce ta aure miki miji?
Ina,ai yanzu an daina wannan shirmen,ki fita ki bar wa kishiya gida ai ita ke da riba".
"So nake ki saurare ni da kyau Ramlah,idan kin tsaya shirme sai dai ki ga an kawo miki ita a matsayin sirika".
Mama ta ce"ki ma daina wannan zancen Zainab".
Hajiya Zainab ta ce"abin nan dai da baki so shine mafita,don wallahi idan ba hakan aka yi ba babu abinda zai sa Sudais ya rabu da yarinyar nan".
Mama ta girgiza kai ta ce"a'a Zainab,kin san bana son wannan zancen ko?ki daina kawo wani amma banda wan can".
"Hmm,Ramlah kenan, wannan fa da nake magana a kai Malami ne wallahi,a zaure yake,zaki ganshi da carbin shi harda Qur'anai".
Tayi shiru alamar tunani,can ta sauke numfashi ta ce"to shikenan,sai dai babu inda zan tafi gaskiya, tunda kin san komai ki tafi kawai,duk yadda ku kayi sai ki sanar dani".
"Ko ke fa,amma kin zauna tunani da damuwa su kashe ki a banza,zuwa gobe zan shirya in tafi in sha Allah,shi da ita sai dai kallo daga nesa".

**********

Yana zaune cikin office aka yi knocking,sai da ya ɗan ɗago sannan ya ce"Yes,come in".
Lieutenant Idris ya shigo ya sara mishi ya ce "Good morning Sir".
Tulin files dake hannun shi ya ce"Sir,the General sent me to bring this file to you. He wants you to review it and report your findings to him.”
Ya ajiye pen ɗin hannun shi ya bi files ɗin da kallo ya ce“What is it about?”
“It's a personnel and operational records file, Sir.”
Sadauki ya ce“Did the General give you any specific instructions?”
“No, Sir,he only said you should go through it carefully.”
“Alright. You may go.”
Ya sake Sara mishi ya ce“Yes, Sir.”
Bai sake bi ta kan files ɗin ba har ya fita sallar azahar,bayan ya dawo idon shi ya sauka a kansu,ya ja guntun tsaki ya koma ya zauna,yunwa ya ke ji sosai don rabon shi da abinci tun jiya da yamma,da daddare coffee kawai ya sha ya kwanta.
Ya miƙe ya ƙarasa gaban coffee maker ya ɗauki cup ya ɗauraye ya haɗa coffeen ya koma ya zauna.
A nutse ya buɗe files ɗin ya fara bi ɗaya bayan ɗaya,ya kai kusan na biyar ya ga an rubuta "Colonel Yaqub Tafida".
A ƙasa kuma an rubuta "DECEASED".
Ya buɗe file ɗin ya ga shekaru goma kenan da rasuwar shi.
Ya mishi addu'a ya cigaba da buɗe sauran files ɗin a nutse,har zai ajiye ya ga a ƙasa an rubuta
"Authorized by :Colonel Yaqub Tafida".
Ya duba date ya ga tuwo years back,da mamaki ya maimaita sunan,ya buɗe file ɗin daga farko ya fara karanta bayanan dake ciki.
Lokaci ɗaya ya fahimci komai,anyi signing file ɗin ne wajen shigo da makamai,amma akwai wani mai irin sunan ne ko shine bai karanta dai dai ba.
Ya ajiye file ɗin a gefe ya cigaba da duba sauran,can tsakiya ya sake cin karo da wani,still sunan Colonel Yaqub Tafida tare da signature ɗin shi, ya sake duba date ya ga shekaru uku da suka wuce,da mamaki ya buɗe file ɗin.
Shi kuma anyi signing ne wurin shigo da kaya,babu wani ƙwaƙƙwaran bayani akan kayan,sai sa hannun shi kawai akan shi ya ba da izini.
Zuwa sannan kan Sadauki ya fara caji,bai sake rikicewa ba sai da ya sake cin karo da wani still da sunan shi,wannan ma bai wani daɗe ba watanni shida ne da suka wuce.
Shi kuma anyi amfani dashi ne wurin shiga wani wuri mai hatsari,ba zai yiwu ordinary civilian ya shiga ba tare da authority ɗin military ba,ga dai sa hannun Colonel Yaqub Tafida a kan shi ya bada izinin shiga wurin.
Ya miƙe ya tattara files ɗin guda uku ya fita, Colonel Barau na tsaye kusa da office ɗin shi yana magana da wani Lieutenant,ganin yadda Sadauki ya fito a rikice ya sa ya zuba mishi ido.
Ya juya ya kalli Lieutenant ɗin ya ce"Gideon !"
"Yes,Sir".
"keep an eye on Captain Sadauki. Find out what he's after".
"Yes, Sir".
Personnel Records Office ya shiga,bayan sun gaisa da officers dake wurin ya ƙarasa shiga ciki ya kalli wanda ke zaune alamar shi ke duty ya ce“Good morning. I'm Captain Umar Sadauki. I need to verify the service record of Colonel Yaqub Tafida.”
Mutumin ya ce "Okay Sir".
Ya kunna system ɗinshi ya hau danne danne,Sadauki ya harɗe hannu ya zubawa system ɗin ido ko motsi ba ya yi.
Bayan kusan minti shida ya ɗago ya ce"Sir,Colonel Yaqub Tafida is dead".
Sadauki ya gyaɗa kai ya ce"when?"
Ya sake duba system ɗin ya ce"about ten years ago".
"Ka tabbata babu wani officer mai wannan sunan?"
Ya girgiza kai ya ce"no Sir, mutum ɗaya ne mai wannan sunan kuma ya daɗe da rasuwa".
Sadauki ya ce"What about the entire military records?"
Ya sake girgiza kai ya ce"babu sir, gabaɗaya military records ɗin mu shi kaɗai ne da wannan sunan da service number".
Sadauki ya gyara tsayuwa ya ce"then ya akayi sunan shi yayi appearing a recent document?"
"I don't know Sir".
Sadauki ya ce"akwai Jami'in dake da damar accessing records ɗin?"
"Yes Sir, Jami'an da aka ba izini ne kawai ke da damar shiga".
Ya gyaɗa kai ya ce"ina son ganin bayanan duk wanda suka duba records ɗin kwanan nan".
Ya maida hankalin shi kan computern ya ce"Yes,Sir".
Can ya juyo ya ce"Sir,an shiga record ɗin watanni shida da suka wuce".
"Wanene?"
Officern ya ce"Lieutenant Gideon Sir".
Sadauki ya waro ido ya ce"Gideon na da damar accessing records ɗin ne?"
Idon shi a kan system ɗin ya ce"Yes,Sir,an bashi izini na wucin gadi".
Kanshi a matuƙar ɗaure ya koma office,ya jawo telephone dake saman table ɗin ya aika a kira mishi Gideon.
Bayan wani ɗan lokaci aka yi knocking ya bada izinin shiga.
Sir,You asked to see me".
Ya ce "Yes".
Ya tura mishi file ɗin gabansa ya ce"do you know this officer?"
Gideon ya ce"no,Sir, I don't".
Sadauki ya gyara zama da kyau ya ce"kuma na ga ka duba records ɗin few months ago".
Gideon yayi shiru na ɗan lokaci sannan ya ce"umurni aka bani sir".
Da mamaki Sadauki ya ce"Umurni,by whom?"
"An bani izini ne daga sashen kula da bayani Sir".
Sadauki ya ce"ba wannan na tambaye ka ba,waye ya baka wannan umurnin?"
Gideon ya ce "ba zan iya tunawa ba Sir".
Sadauki ya ɗage gira ya ce"ba za ka iya tunawa ba?"
Ya sunkuyar da kai ya ce"Yes, Sir".
Kasa bacci yayi a wannan daren,sosai file ɗin ya tsaya masa a wuya,ya kasa gane dalilin da zai sa ayi amfani da sunan mutumin da bai raye.
Washegari yana isa office ya koma personnel Record Officer,mutumin jiya ya samu,ya ja kujera ya zauna ya ce"Colonel Yaqub Tafida,ko zan iya sanin dalilin rasuwarsa?"
"Ya rasu a operation ne Sir".
Ya ce"wani irin Operation?"
"Field Operation Sir,anyi attacking unit ɗin su during the operation,and he was among the officers who lost their lives".
Sadauki ya ce"Zan iya ganin cases da yayi handling kafin ya rasu?"
Ya girgiza kai ya ce"Sir,files ne keɓantattu,only authorized personnel can access them".
Sadauki ya gyara zama ya ce"ka ɗauka wannan ɗin ma hakan ne".
Babu yadda ya iya ya shiga ya hau binciko files ɗin,duk sunyi ƙura tsabar ajiya.
Sai da ya kakkaɓe kuran sannan ya miƙa masa.
Ya sa hannu ya ƙarba ya ce"thank you".
Tunda ya ajiye file ɗin a office bai sake bi ta kansu ba har ya koma gida.
Ya fito daga toilet ya ga Bilal tsaye kusa da file ɗin,Bilal ya kalle shi ya ce"me ka ke yi da wannan tsohon takardar,da gani sun kwana biyu?"
Ya ɗan kalle shi ya ɗauke kai, ganin ba zai ba shi amsa ba ya ce"nayi ordern abinci, yana parlour".
"Alright Ina zuwa".
Ƙarfe uku na dare ya farka,bayan ya idar da sallollin shi kamar yadda ya saba ya koma bakin gado ya zauna ya buɗe file ɗin farko.
Yaqub Tafida yayi bincike a kan ɓatan wani babban ɗan kasuwa,amma bai sami damar kai ƙarshen case ɗinba aka rufe saboda rashin isasshen evidence.
A ƙasa yayi rubutu kamar haka
"Bayanin da aka bayar bai yi daidai da hujjojin da aka samu ba".
Yayi shiru yana sake nanata abinda ke rubuce.
Ya ajiye wannan a gefe ya buɗe na biyun.
Yaqub Tafida yayi bincike akan wasu kaya da suka ɓace kafin su isa inda ya dace,takardun hukuma sun nuna cewa komai ya tafi yadda ya kamata,amma sai ya rubuta alamar question mark a ƙasa.
Na ƙarshen yana bincike ne akan wasu shaidu da ake yiwa barazana daga unknown numbers,daga ƙarshe dai duk shaidun sun mutu,wanda har yau babu wanda ya san sanadin mutuwar su.
Daga ƙasa ya rubuta saƙonnin 
“Forget what you saw.”
“Some things are better left alone.”
Daga ƙarshe ya rubuta“I pray that one day, someone will uncover what has been hidden and bring the truth to light.”
Ya rubuta sunanshi,signature da kwanan wata.
Ya sake duba file ɗin mutuwarsa ya ga yayi rubutun ne sati ɗaya kafin rasuwarsa.


Book 1 ya kusa ƙarewa, Book 2 na kuɗi ne.
Pay 1k into ***, Khadijah Sulaiman Opay.
Evidence of Payment Via ***.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol