Free chapter · Read without an account

Chapter 20

by Rukayya Ibrahim · Duhun da natashi ciki

Da muka shiga ɗaki, muka ba Mama kuɗin tallar da muka yi. Ta karɓa, sannan ta ce mana:

“Ku je can, ga dambun hatsi, ku ci.”

Na ji daɗi sosai da jin haka, domin ba kasafai ake samun irin wannan abincin a gidanmu ba. Na ɗauki nawa, na wuce ɗakinmu.

Da na shiga, sai na ajiye dambun a gefe, na ɗauki ruwan alwala na yi alwala, sannan na shimfiɗa sallaya na yi sallah. Bayan na idar, na zauna na ɗauki dambuna, ina ci a hankali. Gaskiya na ji daɗin abincin, domin yunwar da nake ji tun da muka dawo daga talla ta fara raguwa.

Ina nan zaune ina cin dambuna, sai na ji muryar su Aisha. Sun dawo daga talla, suka shiga ɗakinsu. Na kalli lokaci, na ga har ƙarfe shida na yamma ta yi.

A da, tare muke fita talla da su Aisha. Mukan je tare, mu dawo tare, amma yanzu komai ya canza. Sun kawo kuɗin tallarsu ne suka miƙa wa uwarsu.

Na tuna da maganar da aka yi cewa wai ina ɓoye kuɗi. Saboda haka, aka yanke shawarar cewa daga wannan lokacin, ba za a ƙara fita da ni talla ba, domin ita ma tana da ’ya’yan da za su riƙa yi mata talla. Wai idan aka fita da ni, sai a yi asara, domin ina da bakin jini.

Na yi murmushi mai ɗaci a raina, ina kallon dambun da ke gabana. Ashe ba su san irin sauƙin da aka samu mini ba. Yanzu ba zan ƙara fita talla tare da su ba, sai dai in yi aikin gida da na abinci.

Duk da haka, ban tsira daga wahala ba, domin duk lokacin da suka dawo daga talla, ni ce zan wanke kayan tallarsu. Idan an gama cin abinci, ni ce zan yi wanke-wanke. Ko da yake ba zan ƙara fita talla tare da su ba, amma aikin gidan bai ragu mini ba.

Na ci gaba da cin dambuna a hankali, ina tunanin yadda rayuwata take tafiya. Wani lokaci nakan ji kamar duk abin da zan yi, sai an sami dalilin ɗora mini wani laifi. Amma duk da haka, na saba da jurewa, domin na san ba ni da wanda zan kai wa ƙara.

Aisha ta yi haka ne domin kada in ci gaba da ganin abin da take yi a wajen talla. Tana tunanin cewa idan aka daina fita da ni, to ba zan ƙara sanin abin da take yi ba. Amma abin da ba ta sani ba shi ne, ina da labarin komai.

Ta ɗauka cewa ta rufe mini idanu, alhali kuwa na san abubuwan da take yi. Na dai yi shiru ne, ban taɓa nuna mata cewa na san komai ba. Na bar ta da tunaninta, domin ba kowane abu ne ya dace mutum ya fito ya bayyana abin da ya sani ba.

Na gama cin dambuna, na ajiye kwanon a gefe, sannan na zauna ina tunani.

Ina nan zaune aka kira sallar Magariba. Na ji lokacin da Baba ya fito ya fita, ni ma sai na tashi na yi sallata.

Ina gama sallah, sai na fita na haɗa duk wanke-wanken da na san zan yi, domin ina son gobe aikin ya yi mini sauƙi. Daga nan sai na je wajen Gwaggo na karɓo ƙullin.

Ina nan ina wanke-wanke, har aka kira sallar Isha’i, amma ban gama ba. Ina cikin aikin ne sai ga Anas ya zo. Ya zo kai tsaye wajena, ya tsaya kusa da ni, sannan ya ce:

“Anty, kina da naira ɗari biyu? Ki ba ni ko aro ne. Ina so in sayi ko biredi ne.”

Na ɗago kai na kalle shi, sannan na tambaye shi:

“Ba ka ci abinci ba ne?”

Ya girgiza kai ya ce:

“Kin san ba za su ba ni ba sai sun ga dama. Anty, ki ba ni ko aro ne, in sayi ko biredi ne in ci.”

Na kalle shi, sannan na ce:

“Bari zuwa anjima kaɗan, idan Kuluwa ta fito. Zan ba ka, domin na san idan na kira ta yanzu, za a zarge mu da wani abu.”

Anas ya gyada kai, ya tsaya yana kallona, kamar yana jiran in faɗi wani abu. Na ci gaba da wanke-wankena, ina tunanin yadda zan taimaka masa ba tare da na jawo wa kaina wata matsala ba.

Da na gama komai, na shiga ɗaki, na zauna tare da Kuluwa. Sai na juya gare ta na ce:

“Ki ba ni naira ɗari biyu cikin kuɗin da muka samu ɗazu, ko?”

Kuluwa ta dube ni, sannan ta ba ni kuɗin ba tare da ta yi tambaya ba.

Ina tunanin yadda zan ba Anas kuɗin, sai ga shi ya shigo. Na miƙa masa naira ɗari biyu ɗin, na ce:

“Ga kuɗin, Anas.”

Ya karɓa yana kallona, sannan ya ce:

“Na gode, Anty.”

Gaskiya, duk da halin Anas, ina iya taimaka masa da abin da nake da shi. Yaron ba ya jin magana, amma duk lokacin da ya samu wani abu, yakan kawo mini. Wani lokaci har kuɗi yake ba ni in riƙe masa.

Na san Anas ba ya tafiya a hanya mai kyau, domin yana yawan zuwa wajen masu shaye-shaye. Amma duk da haka, ina tausaya masa saboda irin rayuwar da ya taso a cikinta. Mahaifiyarsa ta rabu da Baba tun yana ƙarami, kuma tun daga lokacin bai samu kulawar da ya kamata ba. Wannan ne ya sa nake ƙoƙarin taimaka masa gwargwadon ikona.

Bayan ya karɓi kuɗin, sai ya juya ya fita. Ni kuma na ci gaba da zama tare da Kuluwa.


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol