Free chapter · Read without an account
Chapter 22
Tun daga lokacin da na fara sabawa da Farouk, na fara lura da irin kulawar da yake nuna mini. Duk lokacin da muka haɗu a wajen talla, yakan tambaye ni yadda aikina yake, ko na samu ciniki mai kyau, da kuma ko ina lafiya. Wani lokaci ma, idan bai gan ni ba, yakan tambayi Kuluwa game da ni.
A hankali, na fara sabawa da kasancewarsa. Idan na gan shi daga nesa, nakan ji wani irin yanayi a zuciyata, musamman idan na tuna yadda yake magana da ni cikin natsuwa. Duk da haka, ina ƙoƙarin kada in bari hakan ya rinjayi tunanina, domin har yanzu ban san komai game da shi sosai ba.
Wata rana muna tsaye tare da Kuluwa a wajen talla, sai ta kalle ni tana murmushi.
“Rammu, yanzu dai kin fara sabawa da Farouk ko?”
Na juya na kalle ta.
“Kuluwa, me ya sa kike yawan tambayata wannan tambayar ne?”
Ta yi dariya a hankali.
“Saboda na lura da ke. Da can, idan kika gan shi, sai ki sunkuyar da kanki, amma yanzu har kina iya amsa masa cikin nutsuwa.”
Na yi shiru na ɗan lokaci, sannan na ce, “Ai ba komai ba ne. Mun dai fara sanin juna ne kawai.”
Kuluwa ta gyada kai, amma murmushin da ke fuskarta ya nuna cewa ba ta gama yarda da maganata ba.
Ban san cewa ba da daɗewa ba, Farouk zai ɗauki matakin da zai sa sunansa ya shiga cikin gidanmu ba.
A ranar da Farouk ya fara zuwa gidanmu, Baba yana zaune a tsakar gida tare da sauran iyalinsa. Lokacin ya kusan ƙarfe takwas na dare, ana ta hira, sai ga wani yaro ya shigo yana sallama.
“Assalamu alaikum! Ana sallama da Rammu.”
Da jin haka, sai kowa ya ɗago kai ya kalli yaron. Wasu suka kalli juna cikin mamaki, wasu kuma suka mayar da kallonsu gare ni.
Ni kuwa ina zaune ne a gefe. Da na ji an ambaci sunana, sai gabana ya faɗi. Na ji kamar an tsayar da numfashina na ɗan lokaci. Na ɗago kai a hankali, na kalli yaron, sannan na mayar da kallona ga Baba. Ban san wanda yake neman ganina ba, kuma ban san abin da ya kawo shi a wannan lokaci na dare ba.
Gwaggo ta juya ta kalle ni, sannan ta ce cikin mamaki:
“Rammu ko Aisha?”
Maganarta ta ƙara ruɗa ni. Na sunkuyar da kaina, ina jin kamar duk mutanen da ke tsakar gidan sun zuba mini ido. Na so in yi magana, amma bakina ya kasa furta komai.
Baba ya gyara zamansa, ya kalli yaron ya ce:
“Je ka tambaye shi waye.”
Yaron ya amsa, “To, Baba,” sannan ya fita.
Ina zaune a wurina, amma hankalina ya bi bayan yaron. Na kasa samun nutsuwa, domin tambayoyi ne kawai suke ta yawo a raina. Na fara tunanin ko akwai wani abu da na yi ne ban sani ba, ko kuwa wani abu ne ya faru a wajen talla.
Bayan ɗan lokaci, sai yaron ya dawo ya tsaya a gaban Baba.
“Baba, an ce in gaya maka cewa Farouk ne yake neman Rammu.”
Da jin sunan Farouk, sai na ji zuciyata ta buga da ƙarfi. Na kasa ɗago kai na kalli kowa.
Farouk ne? Me ya kawo shi gidanmu? Me ya sa bai gaya mini cewa zai zo ba?
Tambayoyi suka fara yawo a raina ba tare da na samu amsarsu ba. Na ji kunya sosai, musamman ganin yadda kowa ya mayar da hankalinsa gare ni. Na so ƙasa ta tsage in ɓuya, domin ban san yadda zan fuskanci tambayoyin da za su iya biyo baya ba.
Gwaggo ta sake kallona, fuskarta cike da mamaki da shakku.
“Farouk kuma? Rammu, wane ne wannan Farouk ɗin?”
Na buɗe baki zan amsa, amma kalmomin suka ƙi fitowa. Na ji kamar an kama ni da wani abu da ban san laifinsa ba. Ban san abin da zan ce mata ba, domin ni da kaina ban san dalilin zuwansa ba.
A wannan lokacin, Baba ya kalle ni, sannan ya ce:
“Rammu, tashi ki je ki ga wanda yake neman ki.”
Na miƙe a hankali, amma na ji ƙafafuna sun yi mini nauyi. Na nufi ɗakinmu domin ɗauko hijjab, ina jin kamar duk motsina yana jan hankalin mutanen da ke tsakar gidan.
Da na shiga ɗakin, sai na tsaya na ɗan lokaci ina ƙoƙarin kwantar da hankalina. Amma ina jin bugun zuciyata, sai tashin hankalina ya ƙara tsananta.
Ya Allah, me ya kawo Farouk gidanmu da wannan dare? Me zai ce mini? Kuma yaya zan fuskance shi bayan duk waɗannan idanun da suke kallona?
Na ɗauki hijjabina na sanya, amma hannuwana suna rawa kaɗan saboda tashin hankalin da nake ciki. Na gyara hijjab ɗin a jikina, sannan na yi numfashi a hankali, ina ƙoƙarin samun ƙarfin hali.
Bayan na gama sanya hijjab ɗin, na fito daga ɗakinmu, na nufi ƙofar gida domin ganin Farouk. Duk da ƙoƙarin da nake yi na nuna nutsuwa, zuciyata cike take da tsoro, kunya da tambayoyi marasa amsa.
A tsakar gida kuwa, Gwaggo ta juya ga Baba , ta ce:
“Malam, ka ga abin da yarinyar nan ta fara yi? Har maza suna zuwa. neman ta a gidanka hmmm
Mama Hauwa ta shigar da baki, tana cewa:
“Ni dai abin nan ya ishe ni. Malam, idan ka ci gaba da kare ta, wata rana za ka gane cewa mu muka faɗa maka tun farko.”
Gwaggo. ta sake cewa:
“Yanzu fa har ta kai ga kawo mana maza gida. To, idan ba iskanci ba, mene ne wannan?
Baba dai yana zaune yana sauraron maganganunsu. Shi mutum ne mai saurin fushi da faɗa, amma idan ba ya cikin yanayin fushinsa, kowa yana iya yin abin da yake so a gabansa. Ko ana ta sa-in-sa a tsakar gida, ba lallai ya sa baki ba; zai iya ci gaba da sauraron rediyonsa kamar bai san abin da ke faruwa ba.
Haka suka ci gaba da maganganunsu har suka gaji, amma Baba bai ce musu komai ba. Ya ci gaba da sauraron rediyonsa kamar bai ji abin da suke faɗa ba.
Hakan kuwa sai ya ƙara rura wutar rikicin, domin ganin Baba bai ce musu komai ba, ya sa suka ƙara zage-zage da maganganu marasa daɗi a kan Rammu, suna ganin kamar bai damu da abin da suke faɗa ba.