Free chapter · Read without an account

17

by Asmy b Aliyu · OMRI HAYATII

OMRI HAYATII 
by
Asmy b Aliyu 

17......

da gudu mum ta Karasa wurinta tana fisgota gefe daya.ganin ta saka kafafuntaa
cikin fasasshen glass na turarrukan da ta tarwatsa nan take kafarta ta dama ta fara fitar da jini.mum ta zaunar daita gefe
bed jikinta na rawa ganin yadda fuskar malaak din ta canja.masu aiki ta fara kwalawa kira nan take mutum biyu suka karaso dakin ,ganin yadda dakin malaak din ya xama lokaci daya.dayan maiaikin ta fita dan dauko abun kwasa.dayan kuwa
mum ta dubeta tace ta kama mata ita zuwa dakin mum din.

mum ta mikar da malaak din,da sauri maiaiakin ta matso jikin malaak din tasa hannu da nufi ta taimaka mata mum ta rikata ta dayan gefe.hannu malaak din ta saka da dukkan karfinta ta ture maiaikin
da ta tafi ta bugi mirror ta fasa wata irin kara.agigice mum ta kalli malaak din,
ganin haka malaak ta fisge hannunta ta nufi kofa jini na fita a Kafanta da sauri mum ta kalli maiaikin da har lokacin bata dawo daidai ba tace taji da kanta
Kuma su tabbatar Sun fitar da duk abunda 
ta fashe.da haka mum ta nufi bayan malaak hankali a tashe.

da sauri ta nufi saratun da har lokacin
bata dawo daidai ba ,saratu mai ya sameki?"nan saratun ta fadamata
hajia karamace ta turara a jikin mirror 
girgiza Kai zaliha tayi tana mata sannu.
a hankali take fadin"Allah ya isar maki
malaak din nan muguwace ta karshe
har tafi uwarta mugunta.ni bana jin tanada cikakkiyyar lafiyar kwakwalwa.
mum agigice ta kira family doctor dinsu
kafin ya iso ta samu ta cirewa malaak din
kwalbar data shige cikin jikinta,
malaak na azaune gefe daya ta kurawa wuri daya da ido duk Mum tsorace take da yanayinta gashi maleeka tun Ranar da suka samu matsala ta tattara kayanta ta koma gidan Mijinta .daga mum din sai malaak a gida Sai Kuma masu aiki.da security ,dad dinsu ba zama yake ba.
da doctor ya karaso tun a falo mum
ta taresa tana fadin harda allurar bacci 
ya hadawa malaak din da ba wani isasshen bacci take samu ba.haka ko akayi bayan doctor ya gama yimata dressing kafar ya bata magani mum ta bata tasha 
yayi mata allura ,a haka ta samu bacci.

a daren mum Sai da ta kira maleeka Cike da damuwa tana fadamata halin da malaak din take ciki.tana fadin"har yanxu bata dawo walwalarta ba,nidai maleeka
ko wurin Boka kawai zan Kai mu'azzam din can ya haukacewa uwar idan taga ya haukace dole ta yadda ayi auren nan........da sauri maleeka tace kedai mum
karkiyi haka kibarta ta samesa Yana cikin hayacinsa. ke bakiji me tace tun ranar ba.
a fusace Cike da jin zafin maganar maleeka mum ke fadin"to Sai a zuba mata ido har ta samesa ke kinga alamar Ayshaa
Xata yadda da auren nan cikin sauki ne.
Dan tabe baki maleeka din tayi tamkar mum din na gabanta take fadin."ke dai ki bata lokaci mum Kar Kuma taji kinje wurin boka harka ta Kara lalacewa kin San halinta batada saiti."dan shiru mum din tayi  cike da damuwa tana sauraren maleeka.babu yadda ta iya haka ta yadda da shawarar maleeka,sukayi sallama.
a daren mum ta tsinewa Mami babu adadi
musamman idan ta juya taga halin da malaak din ta shiga....

#######
wuraren qarfe goma mum ce a gaba
taci ado Sai zuba kamshi take Sai taku take da daya daya ,tamkar mai Shirin zuwa wani gagarumin baki.itace a gaba
zaliha na a bayanta dauke da katon tray
har kan table ta karasa ta dora tray din.
ta juya ta fice daga dakin..Malaak na zaune akan bed ta jingina bayanta 
ta dauki filo ta rungume cikin jikinta,
kallo daya tayiwa mum ta dauke Kai
cike da kulawa mum ke kallonta,
ta karasa gaban table tana nuna mata kayan breakfast din da ta saka akayi mata.....bude baki tayi xatayiwa mum magana mum ta dakatar daita,
ki fara yin breakfast tukuna.bari na hadamaki tea.da haka mum ta dauki 
cup ta soma hadamata tea,Cike da rarrashi mum din ke bata a baki tamkar Yarinyyar ya'r shekara biyu.babu laifi
ta dan ci abinci sosai ,Sai dai ko kadan
babu wata walwala a tare daita 
Banda kallo daya xakayiwa fuskarta kasan tana cikin kunci.

mum ta dubeta Cike da kulawa ta bude baki zatayi magana akayi knocking kofar bedroom din mum.mum ta bada umurnin shigowa,kanta a kasa ta sanar da mum din 
malaak nada baki.da sauri malaak din ta kalli mum,ita ba wasu friends gareta ba acikin garin kaduna 
bayan Fadeela marafa.a natse mum din 
tace kice tana zuwa,da haka maiaikin ta juya tabar kofar dakin.........mum koma wacece kije kice bana nan banda lokacin koma wacece malaak ta fada da rigima sosai a muryarta tana kokarin gyara kwanciyyarta.bazaayi haka ba zanje naga wacece tukuna,da haka mum din ta mike ta nufi kofa.kifa kanta kawai tayi akan filo
tayi nisa da tunanin da take.banda suya babu abunda zuciyarta keyi a wannan lokacin.........

Malaak!!!!
murya da taji yasa ta daga Kai da mamaki da wani irin yanayin a fuskanta ta xubawa kofar ido ko kiftawa batayi.a hankali taji
Rabin damuwarta na tafiya.tamkar a mafarki take kallon best friend din tata.
da wani irin sauri noor tazo ta shige jikin malaak din da ta saki baki da ido tana kallonta saboda shiga shock din ganinta
adaidai wannan lokacin da take tsananin bukatar wani kusa daita.
"I miss you so much my best friend."
noor din ta dago cikin jikin malaak
ta fada sounding so very happy, murmushi malaak din ta kirkira tana fadin."I miss you to noryyna.yaushe kika shigo Nigeria
babu waya babu text, langabe Kai noor
din tayi ban samu Kaina ba Sai yanxu
kusan sati daya kenan,munyi bikin Kanwar maama ne na zama busy.amman ya akayi kika zama wani iri malaak komai naki ya canja ,yanayinki muryarki komai da komai
kamar ba kawata ya'r gayu ba."murmushi malaak din ta saki tana jin wani sanyin zuwa noor din har aranta.

noorulhooda tare sukayi makaranta a US
a university suka hadu taren da ta zama a tsakaninsu tamkar Yan uwansu ,a school din da sukayi babu Wanda baisan noorulhooda ba da malaak itama 
noorulhooda babanta minister kudine 
a abuja.bayan minister kudi yayi senator ,yayi deputy governor na gombe state.kasancewar Yan asalin jihar gombe ne,Sai dai Suma rabin rayuwarsu a kusan turai sukayita tamkar su malaak din.noor ta Kara kallonta a Karo na babu adadi kodai bakida lafia ne malaak??"da sauri malaak din ta girgiza Kai
kafin tace babu komai fa lafiyana kalau
so yasu maama da yaa JB?"kowa Yana lafia 
yaaa JB Yana Poland kin San bai fiye son Nigeria ba."Yaa marafan ki?"noor 
ta fada tana kallon Malaak din jin sunan 
da aka ambata yasa zuciyarta ta Karayin wani nauyi.shiru malaak din tayi 
Sai noor din tayi murmushi,kina nan da halinki malaak na mugun son marafan nan
Yana ta wahalar dake malaak kinki ki gane
ki rage wannan soyayyar da kike yimasa 
yayi yawa.kibar zuciyarki ta huta haka malaak."noor din ta fada duka cikin harshen turanci.....Yanzu dai ki tashi ki shirya mu fita yawo saboda ke kawai na shigo kd.dan murmushi malaak din
tayi tana Kara jin noor din aranta 
bedroom dinta suka koma lokacin an gyara komai tamkar babu abunda ya faru a jiya.ta kalli gaban mirror dressing dinta
tana jin mugun daci aranta yadda tayiwa
kanta hasarar tsadaddun turarruka
yanxu dole Sai ta Kara yin order wasu
da baxaa ma samesu a Nigeria ba....
anan malaak din tabar noor ta shige bathroom.duk da tayi wanka da safe
Kara wani wanka ta sakeyi saboda 
taji kwarin gwiwar fita da noor,
bayan ta fito daga wanka ta shirya kanta 
cikin wani saukakkan material dinkin boubou Wanda yayi mata kyau,
"noor ta kalleta sama da kasa kafin tace 
kinyi kyau."Amman ki saki wannan fuskar 
taki.dan dole malaak din ta saki fuska
wuraren 12 sukayiwa mum sallama,
a motarta suka fita saboda noor
a hotel ta sauko koda ta shigo kaduna
da Zaa kawota gidansu malaak din
abokin yaayanta ta kira a waya
ya aiko driver ya kawota.
Ina muka nufa my girlfriend?"
malaak ta fada tana Kara danna sitiyarin mota,
duk inda yayi maki muje kawai.
kin San me zai faru mu koma hotel din da na sauka naji daga bakinki meya hadaki da marafanki ,zuwa yamma idan rana 
yayi sanyi Sai mu fita yawo.da wannan shawarar malaak ta dauki hanyar zuwa hotel din da noor din ta sauka.
"wai Ina wayanki??
kin San ko yau da safe nata kira a Kashe.
Sai lokacin malaak din ta tuna
yadda ta buga wayar a kasa.wani tsanar Mami taji ya rufe mata zuciya.
a motar ma duk yawan hirar da sukeyi a tsakaninsu noor ce karfin hirar,
bayan Sun isa hotel din data sauka
ta saka aka kawo masu lafiyayyen lunch anan cikin hotel din,

malaak na zaune akan doguwar soofa 
ta jingina bayanta jikin soofa tana kallon 
noor,kafin tace noor da alamar mahaifiyar mu'azzam banyi mata ba."da wani irin mamaki noor ta aje glass cup din hannunta mai dauke da orange juice acikinsa.da mamaki take fadin."kamar ya??"dama har yanxu akwai irin waya'nnan iyayen aduniya.wani murmushin takaici
malaak din ta saki kafin ta fara bata labarin yadda mu'azzam din ya rika Jaye 
mata har tafiyan da yayi a Lagos 
batareda ta sani ba.......


meyasa Sai shi malaak??"
ki hakura dashi dan Allah ba mijin aurenki bane,mama boyyy fa."wani murmushin takaici malaak din ta saki tana fadin"akan me zan hakura."ai ban fara dan in daina ba,idan nabarsa burinta ya cika kenan."
meyasa zan barsa malaak bancin shi kadaine zuciyata keyiwa soyayyar aure.
Shima Yana sona nooor.mu'azzam Yana sona nooryy kawai uwarsa ce ke shiga tsakaninmu wallahi baxan iya barinsa ba
baxan iya barwa ko wace macce shi ba
noory na shirya na shirya karbar duk wani balai da masifar da uwarsa zatayi.
yadda jikin malaak din ya fara rawa 
idanunta suka ciko da kwallar bakin ciki
yasa noor din ta dawo gurinta ta jata ajikinta ta fara shafa sumar kanta,
yi hakuri xaki samesa babu mai shiga tsakaninku.da gaske kike noory ,zan samu mu'azzam zai zama nawa ni kadai"magana take a birkice noor ta shiga daga Kai tana bata tabbacin samun mu'azzam din
acan Kuma kasan ran noor din
wani irin tausayin kawarta ta ya lullubeta.
tana ganin yadda kawartata take yiwa 
mu'azzam din wani irin son da har ya fara taba hankalinta.dakyar ta samu malaak din ta dan dawo daidai........

#OMRI HAYATII 
#ASMY B ALIYU 
#LOVE/FATE
#HOT LOVE
#MALAAK 
#NOOR
#***

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol