Free chapter · Read without an account

23

by Rukayya Ibrahim · Duhun da natashi ciki

A cikin zuciyar Baba kuwa, yana jin duk abin da suke faɗa, amma ya zaɓi yin shiru. Ya san halinsu, domin idan samarin ’ya’yansu suka kira su, ba sa cewa komai; sai dai su jira har sai an dawo da leda. Amma idan maganar Rammu ce, sai su fara zagi da maganganu marasa daɗi.



Na isa ƙofar gidan, inda Farouk yake tsaye yana jirana. Da na ƙaraso, na ɗan tsaya a gabansa, ina kallonsa cikin mamaki.

“Assalamu alaikum,” na gaishe shi cikin sanyin murya.

“Wa alaikumus salam, Rammu,” ya amsa, yana kallona.

Na tsaya a gabansa cikin kunya. Ya kalle ni na ɗan lokaci, sannan ya ce:

“Rammu, ina fatan ban yi laifi ba da na zo gidan nan?”

Na girgiza kai a hankali, na ce, “A’a, ba ka yi laifi ba.”

Ya yi murmushi kaɗan, sannan ya ce, “To, na ji daɗi. Na dai zo ne in ga ko kina lafiya.”



Ya yi murmushi kaɗan, sannan ya ce, “Na kasa jira har gobe, shi ya sa na zo in yi tozali da kyakkyawar fuskarki.”

Na ji kunya matuƙa da jin waɗannan kalaman nasa. Na sunkuyar da kaina, ina ƙoƙarin ɓoye yadda maganarsa ta sa zuciyata ta buga.

“Ka dai zo lafiya,” na faɗa a hankali.

Ya gyada kai, sannan ya ce, “Lafiya lau. Amma Rammu, ina fatan zuwana ba zai jawo miki wata matsala a cikin gida ba?”

Na ɗan yi shiru kafin na amsa, “Ban sani ba. Amma ka dai san yadda gidanmu yake.”

Ya kalle ni cikin nutsuwa, kamar yana son ya fahimci abin da nake nufi.

“Na fahimta. Ba zan daɗe ba, na dai so in gan ki kafin in koma.”

Na gyada kai kawai, domin ban san abin da zan ƙara cewa ba. A gefe guda kuma, ina tunanin yadda waɗanda ke tsakar gida za su ɗauki zuwansa.



Ya kalle ni na ɗan lokaci, sannan ya ce cikin sanyin murya, “Rammu, ina sonki. Ina fatan ba za ki rabu da ni ba.”

Na sunkuyar da kaina cikin kunya, ban san abin da zan ce masa ba.




Na ɗan yi shiru, ban san abin da zan ce masa ba. Na ɗaga kaina na kalle shi a taƙaice, sannan na sake sunkuyar da shi.

“Me ya sa ka faɗi haka?” na tambaye shi a hankali.

Ya yi murmushi kaɗan, sannan ya ce, “Saboda na saba da ke, Rammu. Ina jin daɗin kasancewa tare da ke, kuma ba na son ki daina magana da ni.”

Na ji kunya, na kasa kallonsa sosai. Ban san yadda zan amsa masa ba, domin ban taɓa shiga irin wannan yanayin ba.

Sai na ce masa, “Ai ban ce zan rabu da kai ba.”

Da jin amsata, sai ya yi murmushi, yana kallona cikin farin ciki.

“Na ji daɗi da kika faɗi haka,” ya ce.



Ya ce, “Na zo ne kawai in gan ki. Ga wannan  zan tafi.”

Da ya miƙo mini ledar, sai na ji kunya ta kama ni. Na kasa miƙa hannu na karɓa, na tsaya ina sunkuyar da kaina, ban ce komai ba.


Sai na ce masa cikin kunya, “A’a, ka bar shi.”



Farouk ya kalle ni, sannan ya ce, “Rammu, me ya sa? Ai ba wani abu ba ne, na kawo miki ne kawai.”

Na girgiza kai a hankali, ina jin kunya.

“A’a, gaskiya ka bar shi. Ba sai ka ba ni komai ba,” na faɗa cikin sanyin murya.

Ya yi murmushi kaɗan



Sai ya ajiye ledar a gefena, ya ce, “Na zo ne kawai in gan ki. Zan tafi yanzu, ki kula da kanki.”

Na tsaya ina jin kunya, ban ce komai ba. Farouk ya sake kallona, sannan ya juya ya fara tafiya.



Ina tsaye a ƙofar gida, sai ga Aisha ta dawo. Ta tsaya daga ɗan nesa, tana kallona cikin mamaki, sannan ta mayar da kallonta ga Farouk da yake tafiya. Na lura da yadda take binsa da kallo, kamar tana son ta fahimci abin da ya kawo shi gidanmu da wanda yake magana da ni.



Farouk ya yi nisa har na daina ganinsa. A lokacin ne Aisha ta ƙaraso, ta wuce ni ba tare da ta ce mini komai ba, ta shiga cikin gidan. Na bi ta da kallo na ɗan lokaci, sannan na sunkuyar da kaina, na ɗauki ledar da Farouk ya ajiye mini, na shiga gida




Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol