Free chapter · Read without an account

Chapter 9

by Abdulhakim Umar · HANGEN DALA

Page 9

Take tai tsuru tsuru kafin taji duk ta muzanta saboda tsawar da yayi mata tasa hankalin mutane da yawa ya dawo kansu,  
“Ke wace irin wawuya ce da zaki zo inda ba a gayyatokiba ko baki son turakar waye ba da zaki kwaso wani tsumman jikinki kina tsami ki zo kice zaki zauna sai kin mana asarar wannan damar da muka dade muna nema kafin musamu to middin ya daina zuwa nan sai na kulle ki wawuya ƙazama maza ki barnan tun kafin nasa a fitar da ke ” cewar manager wajan wacce macece 
“ wai akan wannan sakaran kuke neman wulaƙantani, wanda banda girman kai da taƙama babu abinda ya iya, shi nan har yanaji yana da abinda za'a dinga bibiyarsa to wallahi babu wanda zai wulaƙantani na barsa ban mai da murtani ba dogo mai kama da shantu. ” 
“ Ke ni kike gayama wannan maganar” ya faɗa afusace yana miƙewa tsaye yana nunata da hannu. 
“ yo angayama ai ba tsoron ka nake jiba daga nazo mu gaisa sai inji ruwan tsawa da zagi bayan kuma kasan duk yawan kuda a nama bai hana asashi tukunya, kayi duk abinda zaka iya kuma na faɗa mai kama da shantu "
Tas ya ɗauketa da mari yana faɗin ” yau zaki san kin taɓa ɗan gidan masu faɗa aji, yau sai kin sheda faɗa da aljani ba daɗi. ”
Ɗaga hannu tai da nufin ta rama amma sai idonsu ya sarƙe waje guda take halara da jazaba suka ksmata jikinta yayi sanyi wani irin shu'umin so ya kawar da damuwarta sai ta ajiye hannunta tana kallon sa cike da shauƙi. 
Hannunta ta ji ankama daga baya ana janta, tana juyawa taga sholy sai batace komai ba ta bita suka shiga motar tai mata key suka bar wajan. 
“Kai bazai yuyuba ni wata ƴa mace zatai ƙoƙarin mari na barta ta tafi bazai yuyuba sai na hukuntata yadda ko nuna ni da yatsa bazata iyaba, kai bama niba ko namiji ta gani sai ta razana sai na gyara mata zama, Ases maza ɗauko mota mubi bayanta” ya kai ƙarshen magana cike da bada umarni don ransa ya ɓaci Sai huci yake kamar tsohon zaki . 
Wanda Aka kira da Ases yayi sautin ɗauko motar ya kawo har inda Areeyan ɗin yake. 
Baɗe motar yai ya shiga batare da yabari anzo an buɗe masa ba ya zauna gidan baya yanata shan kamshi, tuni ya gama ayyana wa aransa yau sai yarinyar nan ta gane kuskurene ta sai yaga waye ubanta sai yaga dame suke taƙama mulki ko sarauta kuɗi ko muƙami, wai me kama da shanntu “ kai dole ta amsa hukuncin ta sai na tozarta ta. 
Duk irin yadda Ases yake zuƙa gudu bai iya ganin inda sukai ba don haka ya juyo yace “ mai gida banfa ga inda sukai ba ”. 
“ kaini gidan gona kawai amma na baka aiki daga yau zuwa gobe duk inda take a faɗin KADUNA a kawo man ita sai ta gwadaman abinda yai kama da shanntu ajikina na tsani yarinyar nan ". 
Sholy 
Tana fitowa daga wajen ta ɗau hanyar unguwar sarki, sai kuma ta tuna da cewa lokacin tashi makaranta bai yiba don haka tai saurin sauya akalar tuƙin nata zuwa wani wajan da ban inda suke zuwa don kallon masu tsuntsaye da ake kawowa duk ranar laraba. 
             
                KATSINA MASANAWA 

sai da mama ta karbo mabuɗin gidan maƙwabta, kafin ta buɗe gidan suka shiga ko hutawa basuyiba mamar ta ɗau waya ta kira layin Samir ta shedamasa cewa auren Ahanah ya mutu kuma suna gida, ko minina biyar cikakku ba a kullaba sai ga Samir ya shigo gidan da alama yana kusa da gidan dama baiyi nisaba.
“ la wai har ka iso ”cewar mama cikin zaulaya 
“ yo ba dole bama bai saurin zuwa na ga sahibata ai ba'a bori da sanyin jiki yanzu zanyi duk abinda ake inyaso tana gama iddah auren kawai za'a ɗaura, don yau sai na kasa bacci tsabar zumuɗi da murna don ba ƙaramin farin ciki nai ba wallahi naji daɗin haka kuma dole na sheda maku naji daɗi don haka mama na biya maki makka sai ki hau shirye - shirye ”. 
“Ni Shamsiyya ni kabiyama makka wai ni yau dole nai rawar murna tun ina ƙarama nake fatan zuwa wannan waje mai daraja amma abi ya gagara yau dare ɗaya ancika mani burina, " sai ta fashe da kuka tana faɗin “ to Ahanah kindaiji gabaki anbiya mani makka to kar inji kar in gani kiriƙe samir hannu biyu biyu don ɗan kirki ne bai da wata matsal, idon har kika saɓa masa ban yafeba Ahanah ki masa biyya don shine mijin auren ki ko bayan raina kika gujesa ban yafeba wallahi ”. 
Sai da ta tsaya ta share hawayen ta da gefen zaninta kafin tacigaba da cewa “ Samir Allah ubangiji yayi maka albarka Allah ya kareka sharrin mutum da aljan, Allah yasa dukiyar ka tai sanadin shigar ka Aljanna, yadda kacika mani burina Allah ya cika maka naka, Allah ya ya kareka daga sharrin makiya Allah ya kareka da shiga wuta na gode na gode ”. 
“Ki dai na wannan godiyar haka mama ai yimaki kamar yima mamatane don kin cancanci fiye da haka, kece wacce zan gode mawa don haka kiman Addu'a kawai ya wadatar , ga wannan ”. 
Yakai ƙarshen maganar yana miƙa mata wani mukulli,  
Amsa tai fuska ɗauke da mamaki kafin tace “ wannan fa na meye Samir?. "
Mulmushi yayi kafin yace “ na sabon gidan da zaku tarene cikin satin manan da ikon Allah yanzu Ahanah zata shirya muje sai ta ga gidan idon yayi in kuma bai mataba sai asake wani anan cikin shagari lowcous ne.”
“Haba mun isa mu fara ai ko yayake yayi mun gode kawai ”
“Kai mama nace adaina mani godiya amma kinki”
“Ina ni ina daina godiya ai yaba kyauta tukwaici bar ni nayi alamar jin daɗice"
Da haka Samir ya zauna suka sha fira da Ahanah kafin ya tafi da nufin zai dawo da da daddare suje har da mama su gano gidan. 
               Gobarau 
Abu kamar wasa wani irin matsanancin ciwo ya baibaye rayuwar Abbas duk wani jiko da ake sai da mahaifiyar sa ta jiƙa ta bashi amma shiru sauƙi sai ga Allah, ganin abin na yine yasa Hajiya Larai ta nemi taimakon samarin unguwar aka kai Abbas Asibitin General, suna ko isa aka bashi gado, hakan yasa Hajiya Larai cikin tashin hankali da tsoro. 
Ciwo fa ya kunno kai abu har da ƙarin ruwa da jini, amadadin abu yai sauƙi sai halhawa yake don duk abinda Hajiya Larai take dashi sai da ya ƙare akan Abbas, ƙarshe dai akace za'ayi masa aikin zuciya, kuma kuɗi ya gagara sai dai gidan Abbas ɗin hajiya larai tasaka a kasuwa aka sai da aka biya kuɗin aikin. 
             Ahanah ko da mahaifiyar ta duniya sabuwa suka shiga don tuni sun koma gidan da samir ya basu, wanda ke shagari low-cous, kuma komai sabo ya saka masu har da ƴar wanke - wanke da shara ya ɗauka masu yana biyanta duk watan duniya, ya buɗe masu bakin Aljihunsa sai fantamawa suke da kuɗaɗe kamar ba neman su akeba, ga wani mugun so da yake nunama Ahanah da riritawa kamar zai mai da ita cikinsa, a haka dai ta gama idda aka ajiye magana sati mai zuwa za'a ɗaura auren kuma a KADUNA za'a kaita inda ya ƙera mata gida, mai girma da kyau, mama da Ahanah sunyi kyau sunyi ƙiba don tuni sun manta da wani abu waishi talauci sun zama masu kuɗi kuma ƴan gayu. 

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol