Free chapter · Read without an account

Chapter 10

by Abdulhakim Umar · HANGEN DALA

Page 10


                 CHARANCHI LOCAL GOVERMENT
 
Ƙauyen fulani Azima da Muheebbah ne zaune agaban kawu Lamiɗo suna kuka da roƙon sa
“ kawu ka taimaka kai wani abu akai karsu kashe baba kaima kasani Babanmu bazai iya aikata abinda sukke zarginsa da shiba sharri ne da ƘAZAFI sukai masa kataimakemu kawu ba zamu iya rayuwa babu Baba ba shi bango ne abin jinginar rayuwar mu kai wani abu kawu”
Azima ce take maganar tana kuka 
“ sharrin da akaima mahaifin ku baƙaramin abu bane zaiyi wuya ya iya fito wa domin abin daga samane yana ma ABUJA ”. Yakai ƙarshen maganar yana mai tausaya masu kafin ya shiga duniyar tunanin inda zai samo mafita. 
Cak tunanin nasa ya tsaya jin cewa Alhaji sulaiman gidan iko zai zo katsina don yima iyayen Alhaji Aliyu muhammad gaisuwa dake nan cikin charanchi a ƙauyen Nufawa, gada cikin akwatin gidan redion dake gabansa yana sauraro don anan nema yaji cewa ɗan uwansa yana ABUJA don tuni labari ya gama rewaɗe gari. 
“ ku daina kuka na samo mafita idon Alhaji sulaiman gidan iko ya zo sai muje mukai masa kukanmu tunda ya samu sheda kowa yasan shi mutunne mai tai mako da tausayin talakawa”. 
Ƙarfe biyar na yamma Kawu Lamiɗo da Azima da Muheebbah suka iso ƙauye Nufawa, suka nemi gidan da ake zaman makokin Alhaji Aliyu muhammad, aka nuna masu sukai sa'a suna zuwa motocin Alhaji sulaiman gidan iko na tsayawa cikin harabar wajen. 
Azima da Muheebbah suka shiga gidan su ka miƙa gaisuwa, kawu Lamiɗo kuma ya tsaya waje cikin maza, sai da Alhaji sulaiman gidan iko ya shiga gidan tare da masu tsaronsa yamiƙa gaisuwa yana kuka tare da yimasu kyautar kuɗi mai yawa, kuma aka hau shigowa da kayan abincin da yatafo dasu, 
Azima ta kalli Muheebbah tace “ Muheebbah ashe babban mutunne kalli yada ake tsaronsa ko ina yayi lallai munyi sa'a da tatafi da ba lallai mu iya ganinsaba, wannan damace Allah ya bamu da rabon zamu haɗu da shi”. 
“Nima dai ban zaci haka yake ba yaya kuma.......”
Cak maganar ta tsaya saboda ganin Alhaji sulaiman gidan iko yana ƙoƙarin tashi, kuma tasan middin ya fita bazasu sake ganinsaba. Atare suka fashe da kuka kowa yajuyo ya kallesu ganin haka yasa suka rarrafa suka kama ƙafafun Alhaji sulaiman suna cewa atare “ Alhaji ka taimaki rayuwar mu Babun mu shine kawai gatanmu bai aikata abinda ake zarginsa da shiba mune yaran da ake zargin Baban mu da alhakin kisan Alhaji Aliyu muhammad ”. 
Au zarginsa ma ake ko, ku saboda tsabar tsaurin ido da rashin kunya mahaifinku yayi kisan kai har ku iya rasowa kuzo nan gidan wai da sunan gaisuwa ko to zaku yayi kanbababbara ubaku, don sai munɗau fansa akan ku don jinin yayanmu bazai tafi a banzaba”. Cewar ɗaya daga cikin wa inda ke zaune wajen da alama ƙanwar mamacince. 
Kukan kura tayo ta cafki huyan Azima tana faɗin sai na kasheki ƴar gidan mugaye dangi matsiyata kawai, Aradun Allah sai na ɗau fansar ran ɗan uwana”. 
Muheebbah take fa ido ya raina fata cikinta ya fara fitar da sautin fitar zaho, sai yanzu suka fahinci kuskuren da sukai na zuwa gidan don kuwa ba lallai a fahimcesuba tunda gaskiyar su ba a goshi takeba , take ita ma wara taja Abayar ta tabaya suka rufeta da duka . 
Da ƙyar Alhaji sulaiman da masu gadinsa suka amso Muheebbah da Azima suka fito dasu waje inda aka sakasu acikin motar da Alhaji sulaiman gidan ikon yazo da ita, ganin haka yasa kawu Lamiɗo ya taso yana faɗin
 “lafiya me yafaru? ”
Ganin mata sun fito suna ihu da faɗin kabarmu da su sai mun hukuntasu, sai mun ɗau fansa ya tabbatar ma kawu Lamiɗo cewa ba lafiya ba kafin ya juyo har Alhaji sulaiman gidan iko ya shiga motar sa sun fara tafiya dole tasa ya hau mashin ɗinsa ya mara masu baya. 
Har ƙofar gida Aka kawosu kafin Alhaji sulaiman gidan iko ya basu katinsa yace “ Gobe kuzo gida na zamu tattauna matsalar ". 
"To ai bamu san gidan kaba"
Kati ya ciro ya basu yana cewa “gashinan akwai komai da ya dangsnceni aciki sai kunzo"
Ko da kawu Lamiɗo ya dawo suka sanar dashi komai sai yace goben zai kaisu. 
       Washe gari tun bakwai na safe kawu Lamiɗo ya kai su har cikin katsina a cikin estate ɗin da gidan Alhaji sulaiman gidan iko yake wato ( sardauna estate) suka shiga shi kuma ya tsaya yana jiransu daga waje. 
Zaune yake yana kalaci asaman kafet ɗin falon suka shigo ɗauke da sallama . 
“ kune har kun iso haka da sauri amma kuna ƙaunar baban nan baku da yawa, to meyasa kuke son na shiga cikin wannan lamari bayan kuma kunsan ba ƙaramin laifi bane ya aikata”. 
Cikin tashin hankali da firgici Azima ta duƙa gabansa tana cewa “ Alhaji wallahi mahaifinmu mutumin kirki ne ko kuɗa bai son cutar wa bare kuma ɗaukar rai ranma na ɗan adam bai aikata ba, don ranar da abin ya faru muna gida zaune bai je ko ina ba, kuma munji ance kai mai temakone kana son Talakka shi yasa muka zo ”, sai ta fashe masa da kuka 
“ ya isa ya isa haka dai na kukan ". 
Sai tai shiru tana sauraronsa 
Maida kallon sa yayi inda mai masa aiki yake yace “ aƙaro madara". 
Mai aikin na fita yace “ ni ne sai Alhaji sulaiman gidan iko, kuma nine zan ɗaga waya ko ina asaurareni zan iya komai idon har naso domin kuwa ina da alfarma ”. 
kuka mai rauni Azima ta fashe da shi tana cewa “ To me kake buƙata "
Ita dai Muheebbah tana tsaye ra kasa cewa uffan 
“ Abinda zan buƙata ba wani babba bane tunda kina da shi nasan ke wayayyace idon har zaki amince man to mahaifinku zai dawo ”. 
Duf kukanta ya tsaya saboda kalaman da taji daga garesa ta fara kallon sa kallon ƙyama da kaico kallon jin haushi da tsana bata sake cewa komai ba ta kama hannun ƙanwarta suka bar gidan, ko da suka iso inda kawu Lamiɗo yake sai ta fashe da kuka ta sheda masa abinda mutumin ya buƙata, zuciya kawu Lamiɗon yayi ya nufi cikin gidan da nufin ya ci mutuncisa amma masu tsaron gidan suka hana sa dole ya haƙura suka koma gida. 
Dare ya tsala amma Azima da Muheebbah sun kasa yin bacci sai Azimar ce ma take iya lallashi Muheebbah da kwantar mata da hankali ta hanyar cewa “ ki daina kuka gobe baba zai dawo "
“ taya ya zai dawo ” 
“Kawune zai dawo da shi kinsan idon na sanar dake abu yana tabbata "
“ To Allah yasa basu jimasa ciwo ba "
Amin ƴar ƙanwata 
Da haka dai Azima ta samu Muheebbah tai bacci, ita kuma ta tashi ta fita tsbar gidan batare da sanin kowaba don kowa bacci yake, da ƙafa tazo charanchi tun daga gidan kawu Lamiɗo dake ƙauye fulani anan ta samu mashin ta hau tana shiɗa ƙofar gidan aka fara zuƙa ruwan sama duk ta jiƙe ta fara rawar sanyi kafin abuɗe ƙofar gidan, ganin itace yasa Alhaji sulaiman gidan iko sakin murmushi yace tafo, ta shiga gidan tanata kyarma da makyarkyatar sanyi ga tsoro da yagama mamaye zuciyarta, tana ihu tana kuka ya rabata da mutuncinta har sai da ta suma. 
Sai washe gari ta farfaɗo ƙasanta na mata zafi kamar anyanka da wuƙa, cikin ƙarfi hali da juriya ta gyara jikinta ta bar gidan, inda Alhaji yayi mata Alƙawarin yau mahaifinta zai dawo. 
Tana isa gidan ta samu suna ta kuka saboda tashin hankalin da suke ciki na mutuwar malam Giɗaɗo, wanda yanzu aka gama nuna ma duniya anyanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya, har yadda hukuncin ya fita sai da aka nuna, wannan dalili yasa babu wanda ya tanbayi inda Azima taje. 
Ita ko komai na duniyar ya fita ranta babu komai acikin zuciyarta sai baƙin ciki da tarin kaico, tuno da Sadaukarwa da tayi na budurcinta yafi komai ɗaga mata hankali ji take inama ace duk abin da ya faru Amafarkine ba zahiriba, ina ma ace tana da yadda zatai ta maido da lokacin baya, sanin tunaninta ba mai yuyuwa bane sata fashe da kuka kafin ta fara shawarar raba kanta da wannan duniyar da zalunci ya zama abin ado ga wasu Al'ummar cikin zarafi da ƙeta suka mamaye zuƙatan mutanenen cikin ta, 
“ Allah ka yafeman zunubbaina Allah kasa baba da mama su kasance ƴan Aljanna Allah kasa cen ta fiye masu nan, " sai ta ɗauko maganin ɓera ta buɗe bakinta ta shanye. 
Cikin ƴan mintoci cikin ta ya hautsine da mugun ciwo, aka duƙufa kanta ana tai mata addu'o'i, kafin aka ɗauketa zuwa Asibiti sai dai kafin aje tace ga garinku nan, ta amsa kiran mahalicci, 
Faɗar irin tashin hankalin da Muheebbah ta shiga ɓata lokaci ne don harda suma ta dinga yi ta daina komai sai kuka babu chi babu sha har tsawon wani lokaci mai tsayi. 
     
  BAYAN WATA ƊAYA


Ahankkali komai ya fara sakin Muheebbah na damuwa da rashin da tai ta soma sakin jiki tana wasu ayyukan amma ba komai take iyayi ba, taji wa'azin da malaminsu na makaranta yayi mata na nuna mata cewa kullu naf'sin za'ikatul maut kowa lokaci yake jira don mutuwa tana wuyan kowa, don haka ba sauri sukai ba abin da zatai masu ɗayane na nuna ƙaunar da take masu shine tai masu addu'a 

Ta ɗau haƙuri da Ƙaddara ta saki jikinta a gidan kawu Lamiɗo ta koma makaranta, cikin wannan yanayi ta kammala karatun ta, ta zauna gida jiran sakamakon jarabawarsu ya fito ta WAEC da NECO, kafin ta samu taci gaba da karatu, inda kawu Lamiɗo ya shiga nema mata mijin aure don a ganin sa auren ne rufin asirinta, sai dai abu kamar saka hannu duk da kasancewar ta kyakkyawa amma babu wani saurayi ɗaya da zata nuna amatsayin saurayin ta.
 
Ana tsaka da haka wata ranar laraba da yamma wata ƙawar matar kawu Lamiɗo ta zo mai suna Atika, bayan anshifiɗa tabarma sun zauna, Muheebbah ta kawo mata ruwa, ta sha suka gaggaisa kafin ta ɗaura da faɗin “ kawata shawara nazo da ita idon har zaku amince da ita akan Muheebbah, akwai wata ƙawata da ke aiki a wani gidan marayu a ABUJA tace sun son ƙarin ma'aikata guda ukku saboda sabone wasu matane suka buɗesa don samun sauƙin rage yara masu gararanba akan titi, har ansami mata guda biyu, shiyasa nace bari nazo naji ko zaku iya bada Muheebbah akai ta, abinda yasa ban saka sunan ƴataba batai boko ba kuma suna son wacce take da boko ko da matakin sakandare ne saboda zasu bama yara tarbiyya kuma tarbiyya sai mace mai ilimi duk watan duniya za abiyata kuɗi dubu talatin, shine nace babu yarinyar da zata iya wannan aiki a ƙauyen nan sai Muheebbah idon har kun amince zan kira na sanar ansammu amma kuyi shawara tunda dai yarinyar nan marainiyace. ”
Haka Atika tai ta nuna ma matar kawu fa'idar abin har ta yadda zata sanar da kawu Lamiɗo idon ya dawo. 
Gada ƙarshe sukai sallama ta tafi. 
Baƙaramin daɗi kawu Lamiɗo yajiba da wannan zance domin tunaninsa kenan ya fara nema mata aiki tayi da zaman da rake ba karatun babu auren to gashi dare ɗaya ta samu aikin kuma a waje mai daraja don kula da marayu ai ba ƙaramar lada ke akwaiba, kuma ko babu komai burin mahaifin ta zai cika na ganin tayi karatu tai aikin gwamnati. 

Da kwarin gwiwarsa yayima mahaifiyar su bayani, sai da ta amince kafin ya shiga bincike duk iya binciken da yayi baiga wani aibun haka ba da wannan ya sanar da Atika sun yarda sun amince, nan take aka fara shirye shirten tafiyar Muheebbah ABUJA. 

Bangaren Muheebbah kau batai musuba kuma bataji komai akan haka ba don babu abinda yake burgeta yanzu a duniya, zataje ko don samun farin cikin da ta rasa tunda iyayenta suka tafi tafiyar da ba' a dawowa, tunda taji cewa aikin kula da yara ne kuma marayu ta fara ɗoki da son tafiyar don itama ta samu ladar da ake samu, domin kuwa akwai wata rana da malaminsu yayi masu tuntarwa akan ciyarwa da kula da maraya, wani bawan Allah ne da manzo Allah (S. A. W) yace da shi ranar lahira shi makwabcin sane, kuma sai mutumin ya kasance ɗan shaye - shaye yana aikata aiki na sabon Allah, mutane da yawa sunyi mamaki akan wannan lamari har suka shiga bincike, kuma suka gano cewa aikin Alkhairi ɗayane yakyi wanda yasa aka wanke masa zunubbansa har ma manzon Allah yace da shi zai kasance makwabcinsa ranar Lahira, aikin da wannan bawan Allah yake shine akwai wata mata da mijinta ya rasu ya barta da yara komai nasu ya ƙare matar ta fara yin bara don samun abinda zataci ta kuma ciyar da yaranta, da wannan bawan Allah ya gani sai yace da ita bai kamata ace kamar shi suna unguwa gudu, ya ganta tana bara ya barta sai yace ta koma gida ta zauna duk sadda ya kwashi albashin shi zai kawo mata, haka kuwa akai ya hanata bara ya dinga ciyar da su da albashinsa shi kuma yana buga buga yana biyan buƙatarsa ta yau da kullum. 

Wannan ne aikin da yayi har manzon Allah S. A. W yayi masa bushara da zama makwabcinsa a Aljanna. 
Aikin Alkhairi ɗaya ya goge dubban zububbansa kuma yayi sanadiyyar shigar sa Aljanna . 

Inko hakane to ta shirya zuwa ko da baza abiyata ko sisiba don ita ma tai sa'ar samun wannan ɗunbin lada da ake samu idon aka ciyar da maraya.

       Bayan anyi duk wani abu da yakamata ayi Atika ta zo da kanta don tafiya da Muheebbah ABUJA, Muheebbah na zaune gaban kawu Lamiɗo kamar mai neman gafara ta na hawaye na rabuwa saboda shakuwar da sukai bakuma ta san wacce irin rayuwa zata taras acanba, mai daɗi ce ko akasin haka mai wuyace ko mai armashi bata saniba amma zataci gaba da addu'a Allah yasa alkhairi ne tafiyar tata. 


“ kiyi haƙuri Muheebbah karki ɗauki hakan a matsayin musgunawa gareki nayi bincike sosai kuma na gane babu wata matsala aciki sai alkhairi don zaki cika wasiyyar mmahaifinki ta hanyar yin aikin nan ko don ki taimaki mahaifiyar sa da ya bari a doron duniya tana tsaka da neman bango abin jingina, kuma ko babu komai aikin ladane da samun rabauta, ki kama kanki banda shirme kiyi abinda yakaiki ki zauna lafiya da kowa banda fariya ko girman kai banda faɗa, kima kowa biyayya marayu ne zaki kula dasu ki zauna da kowa zaman amana da riƙon gaskiya ki zama mai ƙoƙari akan komai kizama mai haƙuri da rayuwa, riƙon amana juriya da jajurcewa da haƙuri da ƙaddara sune matakan nasara akan kowane lamari na rayuwa kar abin duniya ya burgeki domin ƙyale -ƙyale ne kawai na banza mai faruwa da ƙarewa kiyi aiki na gari kiyi koyi da mutanen kirki zaki samu komai na rayuwa da ikon Allah, Allah yayi maki albarka. "

“Amin kawu , na gode kuma insha Allah zaka sameni mai bin umarninka zaka sameni kamar yadda kakeso da iko Allah ”. 
Haka taje wajan kakarsu sukai sallama suna kukan rabuwa, itama sai da tai mata nasiha mai ratsa zuciya da shiga rai kafin sukai sallama, har ƙofar gida ƴan gidan suka fito suna mata baibai kafin, kawu ya rakasu har tasha suka hau motar ABUJA sai da yaga tashin motar su kafin ya dawo gida. 
Ƙarfe bakwai na safe motar su ta tashi suka hau hanya, tafiya mabuɗin ilimi, suna barin charanchi suka shiga Kankiya, Muheebbah ta gane hakan ne ta hanyar fastocin ƴansiyasa da aka lilliƙa akan titi, suna fita kankiya suka shiga Matazu, inda makarantun firamare ne suka shedama Muheebbah suna Matazu saboda taga hakane ta adireshin maakarantar, sosai Muheebbah ta ƙara mai da hankalinta akan titi don ganin garuruwan da zasu wuce har bata sanma sunshiga Musawaba sai da suka tsaya wani gidan mai suka sha mai kafin ta gane Musawa suke akan sinbod ɗin gidan man, suna shiga Malunfashi ta fahimci nan ma wani garin ne saboda Malufashi ta sha banban da sauran garuruwan da suka baro don ita birnice sosai don harda barikin sodoji ke akwai akan hanya ga gidajensu duk ginin bulone da siminti kuma ƙasar su yashine bakamar charanchi ba da duk jar ƙasa ce, bata san sun shiga Ƙafur ba sai da taji wata tsohuwa tana waya tana cewa " muna Ƙafur mun kusa isa Zaria ”. 
Tafiya mai tsawoce sukai kafin suka shiga Zariya yanayin garin ya tabbatar mata da haka don matane zaka gani yara da ƴan mata suna tsayawa wajen kabarin mai tashine suna saida mazankwaila wasu kuma kabeji manya - manya wasu kuma Albasa wasu mangwaro. Tafkeken titin da suka hau ya sheda mata cewa sun shiga Tsakiyar garin Zariya ganin yadda manyan motoci keta jeka kadawo, wata ( flay over.) suka hau mai tsayi sosai don hanyar jirgin ƙasace ƙarƙashin titin, kana iya hango gidajen mutane da unguwanni da duk yadda mutane suke mu'amularsu saboda yadda titin ya ɗaga, manya -manyan Duwatsu ne suka fara gani masu ban mamaki domin kamar zasu waɗone haka suke sunyi tsini sosai har ana ganin kamar da anyi iska mai ƙarfi zasu faɗo amma basauyin komai da izinin Allah. 
Ƙamshin furanni da manyan itacen dake kan titi shine ya fargar da Muheebbah cewa sun shiga KADUNA, Acikin Legos garej sukai burki wanda ke anan cikin Kawo , wasu da yawa daga cikin mutanan anan KADUNA suka sauka , su kuma sauran sukai sallar Azahar da La'asar kafin suka sake hawan hanya har ABUJA birnin tarayya, sun isa ABUJA daf da Issha'i Atika ta kira wayar Anty Ainah ta sheda mata sun iso suna tasha. 

Cikin lokaci ƙalilan sai ga wata mota ƙaramar boss tazo ɗaukarsu mai ɗauke da Tanbarin gidan marayun suka shiga suka hau hanya har Unguwar Kubwa inda gidan marayun yake. 
              HALAL CHINDENT'S HOME, shine sunan da ya fito ɓaro ɓaro asaman gate ɗin dakuma kan wani sinbod na ƙarfe dake kafe a gefen gidan daga can kusa da titi, sai da sukai fakin suka fito suna bin gidan da kallo mai kamar wata ma'aikata Akwai masallaci da makarantar boko da Islamiyya aciki akwai (clenic ) da wajan koya sana'o'i, kai tsaye Office ɗin shugabar wajan suka nufa ɗauke da jikkunan kayansu. 
Suna shiga cikin Office ɗin suka samu wasu mutane da ban ankawo yara jarirai guda biyu mace da namiji, macen babantane ya kawota da kanshi wai gobara gidan sa yayi ranar sunan kuma mahaifiyar yarinyar ta rasu dama wasu daga cikin dangi, wasu kuma suna Asibiti ana kula dasu, ido har ya samu inda zai kaita zai dawo ya ɗauketa bayan komai ya lafa. 
   Shi kuma namijin wasane suka tsincesa abakin tafki an jefar abin duk na ban tausai. 

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol