Free chapter · Read without an account
Chapter 11
Page 11
KADUNA STATE
Hankalin Namsiyya ya tafi akan tsuntsayen dake ta wasa da ƴan uwansu, a zahiri kenan, amma a baɗini hankalin ta yana kan tunanin abinda zataima Areeyan ta wuce don middin bata ɓata ransaba to yau bazata iya bacci ba, dafa kafaɗarta Sholy tayi kafin tace “ bafa don kallon tsuntsaye na kawoki nan ba nazo ne kawai don mu tattauna matsala mu , yanzu mi kika yanke akan marin da Areeyan yayi maki ya mari banza ko zaki ɗau fansa? " takai ƙarshen maganar tana nuna alamar tanbaya a fuskar ta
" Rama cuta ga macuci ai farillah ina nan ina tunanin irin abinda zanmai wanda zai kaini ga samun nasarar aure sa domin kuwa ni da shi muka karaba ”.
“ Ke Namsy har kinga abin aure ajikin Areeyan kin shirya zama cikin wulakanci kenan don duk wadda tacr Areeyan mijine to zata kwana cikin uƙuba don haka bani baki shawarar aurensa don bai dace ba”.
“ Aiko Areeyan shine ya dace don ya haɗa duk abinda nakeso don ni zan jefi tsuntsu biyu ne da Dutse ɗaya yana da kyau yana da kuɗi kuma ina sonsa, kinga ko shine ya dace tun da farko don kuɗi zanyi auren na huta da ɗawainiya da Talauci yanzu kuma gaso ko ba kuɗi akwai ƙauna don haka shine ya dace, bani kunnanki kiji abbinda na shirya akai, ” ta kai ƙarshen maganar tana yima Sholy raɗa a kunne
Da wani irin mugun mamaki Sholy ke kallon Namsiyya kafin cikin faɗa ta fara faɗin “ Namsy ashe baki da tunani ban sani ba taya zaki aikata wannan abun akan Areeyan, kin kuwa san zasuyi bincike idon suka gane gaskiya kuma kiyi yaya baki san waye Alhaji Abdurrahman Na'adami ba da alama wallahi yayi bincike ya gano sharrine har gidan yari sai kinyi idon ma anbaki raye kenan don haka wannan ba abin yi bane zokiji na sanar dake abinda ya dace ”.
“Ni babu abinda zaki gayaman ki rusaman plan na rasa mafita, abinda nace zanyi to shi zanyi sai dai duk abinda zai faru ya faru amma sai na aikata wallahi "
“ To wallahi badani ba don bazankai kaina ga mutuwaba inaji ina gani don haka dole zaki firar da zaɓi ko dai kiyi abinda zance mu zauna lafiya muci gaba da ƙawance ko kuma kiyi abinda kikke so mu raba hanya kuma rabuwa ta har abada ”.
“ yo sai mi idon na rabu dake Sholy babu abinda zai faru don bamu tare duk abinda nace zanyi kuma zanyi nasara zaki gani sai wata rana kinzo kina lallashina akan mushirya don zan samu maɗaukakiyar nasarar aure cikin daula ”.
“ Dama ance ɗan Adam butulune mai mannce alkhairi har kin mance lokacin da kike zuwa gidan mu kina mani magiya ke yunwa kike ji na ɗau abinci mai rai da lafiya na baki yanzu niki cewa zaki iya rabuwa da ni akan ɗan Namijin da bai san kina sonsaba ko, aini soyayyace tasa nake son ki gane gaskiya kiyi abinda ya dace, ƙauna ce tasa nake gaya maki gaskiya amma tunda kin kasa fahinta ki duk abinda kike so bazan hanakiba sai dai duk abinda ya faru daga ƙarshe kiyi kuka da kanki kar ki saki kice zaki nemeni don bszan saurarekiba, "
“ Dama ai bance ki saurareni ba, Sholy kin bani mamaki yau ni kike ma garin kina bani abinci ko to ki shirya karbar abincinki da zarar na auri Areeyan don duk abinda kike mani garin kinyiman zan biyaki alokacin da na zama sarauniyar gidan Na'adami. ”
Wani dogon tsaki Sholy tai ta miƙe cike da takaici ta bar wajan, tana mai kaico da tur da irin tunanin Namsiyya.
Ita ko Namsiyya sai da ta gama tunanin abinda zatai duka kafin ta bar wajan, Abakin kogi na Unguwar rimi ta tsaya tai bidio kafin ta ɗaura midia irin TikTok, Facebook, group - group na WhatsAp, Kafin ta nufi gida ranta wasai.
Alhaji Abdurrahman Na'adami babban ɗan kasuwa ne da ya shahara yayi ƙaurin suna akaf faɗin garin KADUNA yanada manyan shaguna acikin kasuwar central market na saida kayan abinci da na saida kayan sawa Atanpopi da lasa lasai manya na ƙasashen ƙetare , yana kuma da shaguna na sayar da kayan na'ura irin su computer wayoyi, injinan wanki, dana printing , gaskuka da firij -firij da Talvision da su Home tiyata da sauran kayan wuta, yana kuma kasuwancin motoci tsakani kwatano da Nigeriya Togo da Ghana mali da sauran ƙasashen Africa da ma wasu na ƙetare.
Matan aure guda biyu ne Agidan Hajiya Zainab da Hajiya Wasila sai yara ukku wanda duk Hajiya zainab ce ta haifesu kasancewar ita ce uwar gida, Areeyan shine babba yayi karatunsa tun daga keji har zuwa digree ɗinsa da yayi A ƙasar America yanzu shine mai kula da shagunan mahaifin sa na sai da kayan electronic.
Asiya itace ta biyu tayi karatun ta anan KADUNA cikin jami' ar. KASU wato ( KADUNA STATE Universty). ta kammala karatun ta akan Accouting tana aiki da wani banki anan kaduna tayi aure har da yara biyu tana zaune A malali cikin jerin unguwar Dosa,
Lateefah itace auta kuma ƴar lelan babanta shagwaɓaɓɓiya mai son nuna isa da gadara ƴar wulaƙanci da to zarta Al'umma mai taƙama da cewa ita fa ɗi yar wani ce tana da faɗa da masifar tsiya don batason zaman lafiya kusan kullum sai anyi faɗa da ita ko a hanya ko a school ko a gida ta hayyaci kowa sai abinda taso shi takeyi, shekarunta ishirin da biyu tana karatu a (A. B. U. Zaria).
Wannan sune yara ukku da Allah ta azurta Alhaji Abdurrahman Na'adami da su kuma duk sun fito ne a tsatson uwar gidansa Hajiya Zainab, ita ko Amarya Hajiya Wasila bata da yaro ko ɗaya bata haifaba.
*** ***
Wace ce Namsiyya, Namsiyya ƴace ga malam Garba maƙeri ɗan Asalin garin dogon dawa, malam Garba maƙeri ne anan cikin maƙera yake kasuwancinsa wanda ya gada a wajen mahaifin sa yana haɗa kuba da mukullai da turke na ɗaure dabbobi da wuƙaƙe da shebir da diga da haiwa sa dai sauransu, tunda zaman lafiya ya ƙaura acikin Dogondawa suka taso suka dawo cikin KADUNA yana kula da mahaifiyar sa don shi ɗaya ta haifa mahaifiyar sa ya jima da rasuwa sanadin ciwon ciki.
Malam Garba yana da mata ɗaya Karima da ya auro acan unguwar Rigasa suna da yara Taskwas maza da mata Amma duk ciki Namsiyya ce babba, da kyar ya samu ya taƙarƙara ya gina ɗan ƙaramin gidan sa mai ɗaki ukku da kicin da makewayi a nan zafin guza.
Malam Garba Talakka ne sosai don wani bin sai a kwana ayini ba a aza tukunya agidan sa ba hakan yasa babbar ƴarsa Namsiyya ta ɗaurama kanta rayuwar ƙarya da son abin duniya bata da abokai sai ƴaƴan masu kuɗi, har takai idon an turata makaranta bata zuwa sai biɗiɗi da bin lungu da saƙon unguwannin masu kuɗi tana ganin Aljannar duniya, kuma hakan babu abinda yake ƙara mata sai kwaɗayi da son yawan ƙarya, har ranar da Allah yasa Sholy ta kusa bugeta da mota, kumaa wannan haɗuwa tai sanadiyyar kulla ƙawancesu, Sholy tana son Namsiyya kuma bata son dalili ba kawai dai tasan Allah ne ya haɗasu don haɗuwasu gamon jinine, Sholy tana taimakama Namsiyya da kayan sawa wanda ta gama dasu da abinci harma da ƴan kuɗin kasshewa, saboda ita Sholy gidan su suna da iko da rufin asiri sai dai hakan bai rage wani abu ba da ga tarin son abin duniyar dake cikin zuciyarta ba, halinsu yazo ɗaya da Na Namsiyya na son ƙarya da ɗararma tsara da komai na more rayuwa.
Alhaji Abdurrahman Na'adami zaune a katafaren falonsa na alfarma na cikin gidan sa dake a unguwar Miloniyan city, yana karatun jarida sai ga Hajiya Zainab ta fito daga ɗaki arikice tana kiran" Alhaji kaga abinda ke faruwa a midia "
“ me nene ki ka gani har ya ɗaga makin hankali haka lallai ba lafiya ba ”.
“Gashi ka gani Alhaji wallahi sharri suke ma ɗana Areeyan ba zai aikataba ” takai ƙarshen maganar tana mai nuna masa bidion dake yawo a cikin wayarta dama sauran wayonin duniya kamar zatai kuka.
Amsar wayar yayi ya fara kallon bidion
Namsiyya ce ta bayyana acikin bidion tana kuka tana bada labari kamar haka " suna na Namsiyya malam Garba mubtala kawane sosai wata rana zani makaranta muka haɗe da Areeyan a titi har ya kusan bugeni da mota sai nai saurin kaucewa har ina faɗuwa don gujema bugun motar tasa, da sauri ya fito yana tanbayar ina lafiya.
Na tabbatar masa da lafiya lau nake sai yace
ƴan mata kina da kyau ko zaki bani lambar wayarki,
Sai na sunkuyar da kai na ina mai jin kunyarsa kagin na sheda masa bani da waya.
Nan take ya bani waya sabuwa ƙaramar (itel)
Amma sai nace ni bazan amsaba don ban san saba sai yace nayi masa kwatancen gidanmu.
Babu musu nayi masa kwatancen , muka babu cikin dariya da walwala.
Da dare ina zaune muna fira da mahaifiyata aka aiko kirana ko da na isa sai na samesa.
Na gaidashi har ƙasa kafin mukai fira mai yawa har ya shedaman sunansa Areeyan Abdurrahman Na'adami, bayan mugama firar yayi mani kyautar kayan ci na maƙulashe irin coculet da biscuit masu daɗi, dafari naƙi amsa har sai da ransa ya ɓaci, cikin sati ɗaya da mukai da Areeyan na fahici mutumin kirki ne ya da wasa da dariya da son yara yana da kyauta nuna karamci ga wanda yake tare da shi, a haka na kamu da sonshi.
Ranar da abin ya faru ranace da bazan taɓa mancewa da ita ba ranace da zan iya kira da baƙarrana, ranace da nai ma laƙabi da ƙaddara ta.
Ganin yayarsa mukaje da ya sanar dani bata sa lafiya a wani gida, sai dai muna shiga gidan kafin mu fita motar ya ciro wani ƙyalle ya kangasa a saitin hancina ina shaƙa hankalina ya gushe sai samun kaina nai a kwance saman gado jikina duk jini ya keta mani haddi.......
Tana zowa nan a bidion sai ta fashe da wani irin kuka mai riktarwa da ratsa zuciyar mai sauraro cikin da iya sharri da sanin makamar ƘAZAFI kafin ta cigaba da cewa ya bani kuɗi mai yawa ya roƙeni akan abinda ya daru ya zama sirri a tsakaninmu karna saki na sanar da wani don ko na faɗa kaina abin zai tsaya don yasan yadda zaiyi ya wanke kansa, da fari nayi shiru don nima na fahimci kai na abin zai tsaya idon har ya fita bazab samu mijin aureba kuma duniya zata tsaneni da yiman kallon mazinaciya bayan ba da yadda ta hakan ta kasance ba.
Daga baya nayi tunanin idon har nayi shiru to rayuwar ƴan mata da yawa tana cikin hatsari don haka na yanke shawarar gayama duniya don ƴan matan garin KADUNA su hankalta da shi kuma nasan za'a biman haƙƙina, don tunda abin ya faru na gaza bacci bare cin abinci sai kuka ina cikin tashin hankali da ƙuncin rayuwa. "
Kashe wayar Alhaji Abdurrahman Na'adami yayi yana kallon Hajiya Zainab kafin ya fara karanta inna lillahi wa inna ilaihir raju'una a zuciyar sa
“ amma Areeyan ya bani mamaki taya duk tarbiyyar da nai masa da abinda zai sakamani kenan ”.....
“ Haba Alhaji Abinda zakace kenan kama yarda da abinda ka gani ko shakka da kokwanto bakai, kawai ka amince to wallahi sharri ne akema Areeyan ban yadda ya aikataba sai dai idon makiyane suka bata kuɗi domin ta ɓata mana sunan zuri'a, kuma wallahi sai na ɗauki mummunan mataki akanta. ”
“ kuma fah haka ne zai iya kasancewa ƘAZAFI akai masa, ya zama dole na tsananta bincike akai inko har ya zamana sharrine to sai yarin yarnan ta gane kuskurenta don ni ta tozarta ba Areeyan ba, sai na ɓaddata a doron duniya ko ɗuriyarta sai anbajji. ”
“ haba ko kaifa Alhaji yanzu naji zance, yanzu kai magana, yanzu nasan akwai sauran so da ƙaunar Areeyan a cikin zuciyarka ”.
Wayar sa ya ɗauka da ke akan Table ɗin gabansa ya danna kiran layin D. P. O, bugu ɗaya aka ɗauka tare da sallama
“ Alhaji barka da rana da fatan kana lafiya,,? ”
“ lafiya ba lafiya ba zan tura maka wani bidio yanzu a tabbatar da an kama mani wannan yarinyar da tai bidion akawo man ita don ina son ganinta ina son mu tattauna da ita”.
“ Angama Alhaji dazar munganota zankiraka, ”
Batare da Alhaji Abdurrahman Na'adami yace komai ba ya katse wayar saboda yadda zuciyarsa take masa wani irin zafi da wannan lamari.
Areeyan
Yana zaune a gaban sweeminfull ɗin gidan gonarsa dake unguwar Rigacukun ya saka ƙafafuwansa aciki ruwan yana wasa da su yaji messagge ya shigo wayarsa da sauri ya ɗauka ya buɗe ,
bidion da ƙanwarsa Lateefah ta turo masa ya soma kallo,
Dam ! Dam!! haka gaban Areeyan ya shiga dukan ukku ukku take idanunsa sukai ja kamar garwashi zuciyarsa ta fara tafarfasa ya jefa wayar da ƙarfi ƙasa ta watse lokacin da bidion ya zo ƙarshe“ kai bazai yuyuba ni wannan yarinyar zataima haka ” ya faɗi yana miƙewa tsaye cike da ɓacin rai da zuciyar da ta tunzutosa, ya fara safa da marwa a wajan yana kaima hannun sa duka da gudan hannun, sai kuma ya yi saurin ɗaukar waya ya kira lambar wani gaye yana cewa
“ Ɗan kasada ina son wani aiki na gaugawa yanzu ba sai anjima ba zan tura maka poton yarinyar nan ka kawoman ita yanzu- yanzu don zanhukuntata”.
“ To mai gida aikin mai tsada ne ko mai sauƙi ? ”.
“Karka damu da wannan ko nawa kakeso zan baka kai mani abinda nace kawai aikin sirri ".
yana kaiwa ƙarshen maganar ya tura masa poton yarinyar ya ajiye waya, yana cizon yatsa da leɓensa na ƙasa.