Free chapter · Read without an account

Chapter 12

by Abdulhakim Umar · HANGEN DALA

Page 12



              Namsiyya tana isa gida ta samu mahaifiyar ta tana jefa ɗanwake acikin tukunya saman murhu, sai ƙanwarta na shara wata na wanke - wanke, 
“Daga ina kike? ”. 

Itace tanbayar da mahaifiyarta tajefa mata tana kafeta da ido 
Dam! Dam!! Gaban Namsiyya yayi wani irin mugun bugu don ita tuni ta manta da kayan makarantar ta dake can sabon kawo gidan kakarsu Sholy, sai ta dabar barce ta hau kame kame da tunanin abinda zatace da mama ta yadda da ita, dan danan zufa ta fara karyo mata tarasa abin faɗa. 

“ Dake fa nake nace daga ina kike ”

Mama tasake mai mai ta tanbayar cikin ɗaga murya 
Da sauri Namsiyya ta zabura har sai da taja da baya sanin halin mamarsu yanzu zata rufeta da duka “ Daga Daga Daga maka, sai ta kasa ƙarashe maganar da take sakamakon shigowar Baba gidan wutsiya zage yana kwalama Namsiyya kira 
“ Lafiya malam meke faruwa ne haka kake ta kiran ta kamar zaka tsaga gidan ”. 
“ Babu lafiya Karima ƴan sanda sun zagaye garin nan da neman Namsiyya yanzu haka suna kan hanyar zuwa gidan nan ”. 
“ mun shiga ukku malam mita aikata masu wane irin laifi tayi? ”
“Yanzu ba lokacin wannan tabaye tanbayen bane don basu da amfani” , ya bata amsa yana mai da kallon sa kan Namsiyya yana cewa

 “ maza ki gudu gidan Kakarku Rigasa idon komai ya lafa kin dawo, maza bi ta katanga ”. 
Haka babansu Namsiyya ya tintiɗata ta haura makwabta kafin ta fita da gudu ta saka Niƙab ta hau kekenapep sai Rigasa, Tafiya suke kamar zasu fita gari saboda ba ƙaramin nisa ke akwai tsakanin Rafin guza da Rigasa ba, lokacin da suka isa har yamma ta fara hakan ya haifar da gosilo, kasantuwar titi gudane a unguwar mai kwalta, duk wanda ya kwana ya tashi a Rigasa yasan idon yamma tayi baƙaramin gosilo ake a wajan ba ga lunguna da yawa kuma matsattsu, don haka Namsiyya ta fita ta sallami mai kekenapep ɗin ta fara shiga lungu da saƙo da ƙafarta cike da tsoro a zuciyar ta, fatanta ta Samu ta isa gidansu mahaifiyar ta lafiya batare da wani ya taretaba kasan tuwar unguwar akwai tarin ƴan iska da kauraye daddaɓe da ita sun addabi unguwar hakan yasa suke jimawa basu kawoma kakarsu ziyaraba, unguwar Rigasa unguwa ce da tai shura kuma tai fice wajen tara marasa ji da ƙauraye a garin KADUNA duk wanda ya kwana ya tashi a kaduna to yasan halin mutanan Rigasa, ga unguwar da yawan jama' a kamar kwari kuma cunkushe suke da juna, tana shiga gidan kakar tasu da ya kasance ƙaton gida mai cike da ƴan haya kala -kala ta samu mahaifiyar mamar tasu tsaye a zaure hannunta riƙe da botiki da alama yaron da zata aika ɗibar ruwa take nema, 
“ kaka lafiya na ganki anan tsaye? ”. 

Dayake kaka suke kiranta harma da jama'ar unguwar kowa kaka yake cemata 
“ wai yaro nake nema yazo ya ɗebo mani ruwa na biyashi amma shiru duk babu yaran kuma babu almajirai duk sun koma gida dama kinsan ido damina ta kawo tsakiya ana wahalar almajirai ”. 
“ yo kaka duk ruwan da akai jiya baki tarba ba? ”. 

“ Na tara wanki nai tunda safe”
 ta bata amsa tana kallon ta
“ To bari na ajiye kayana nazo na ɗibo maki ”
 tana maganar tana shigewa gidan mai ɗauke da mutane da yawa don ɗakunane zasu kai ishirin kowa haya yake akwai ibo akwai yarbawa da hausawa da kiristoci kowa akwai a gidan kuma duk haya ta haɗasu waje guda, ɗakin kakarsu taje ta ajiye ledar hannun ta da niƙab ɗin dake fuskarta kafin ta fito ta amsa botikin tai waje daniyyar ɗebo ruwa, tana fita ta shiga kwanar bayan gidan ta miƙe tana sake shan kwanar da zata sadata da layin da fanfon yake tai karo da wasu gwarazan samari su biyar sanye da kayan ƙauraye Duk tabunna a fuskokinsu, da layoyi da suka rataya wasu a wuya, wasu a gulamar hannu, hannayensu ɗauke da manyan makamai gatari da wuƙa ƴar kugu da zarto da gorori, kallo ɗaya zakai masu ka gano cewa manyan kwarine kuma ƴan bakin rai. 

Cikin tsoro da ruɗewa Namsiyya tai gefe don basu hanya su wuce amma sai suka kafeta da ido kamar masu neman wani abu a fuskar ta, Rudududum! Gabanta yayi wata mummunar faɗuwa ganin yadda suka tsareta da ido. 
Wani daga ciki ya kalleta yace “ Ɗankasada wallahi itace aka bamu aikin ta ashema a unguwar mu take ”. 
“ kai bari dai nasake dubawa karmu kama wata a matsayinta ” wanda aka kira da ɗan kasada ya faɗa cikin muryarsu ta ƴan shaye - shaye yana ciro wayarsa ya duba, “ lah wallahi itace ko kayama bata sauyaba, amma kura kana da basira, ku kamata karta gudu ”. 
Namsiyya
 tsakanin ku kamata karta gudu da kuntun fitsarin da ya zuboman bansan wane ya riga fitowa ba take Tsoro ya kamani zullumi da firgici sukai mani ƙawanya a zuciya, tunani na ya tsaya cak na wucin gadi, na nemi natsuwata na rasa sai jikina kawai naji ya ɗau mazari, yo ashe haka kyarma take jiki da kansa keyinta ba wai mutum ba, so nake na cira ƙafata na ruga amma na kasa tsabar ruɗani. 
Da sauri samarin sukai mata zobe suka kamata, ta buɗe baki da nufin ihu taji saukar marin da sai da tai taga taga zata faɗi, sai taji antarota ansakata acikin kekenapep, tana ji tana gani amma ta kasa magana saboda tsoron duka irin nata don taji marin har cikin kwanyart, don haka tai lamo tana jiran ajali ya risketa don tuni ta sadaƙat yau ƙarshenta ya zo. 
Ƙofar wani katafaren gida suka tsaya dake a cikin Rigacukun , Ɗan kasada ya ciro waya yakira Areeyan yana tabbatar masa sun iso ƙofar gidan, 
“Ku shigo da ita”. shine abinda kawai ya iya furtawa   
Har cikin harabar gidan suka shigo da kekenapep ɗin kafin suka taso ƙeyar Namsiyya gaba har gaban Areeyan, tana ganinsa taji wani sanyi aranta don azatonta sai da ita zasuyi, sai kuma ta koma cikin tashin hankali tuno abinda tai masa, gabansa ta duƙa tana faɗin “ Don Allah don Annabi kace karsuyi mani komai na tuba bazan sake ba, wallahi zan koma na sanar da kowa ƘAZAFI nai maka bakai mani komai ba”. 
“ yo ashe ke ƙaramar ƴar balaja'u ce har kin karaya tun kafin na ɗau hukunci akanki , kinyi kuskure mai muni a rayuwar ki don sai na ɗai ɗaita rayuwar ki sai naga waye gatanki a faɗin duniyar nan, tunda fyaɗe da keta haddi kike so za ai maki yanzu ba sai anjimaba ” ya faɗi yana cire rigarsa ta sama, take singilet ta bayyana ajikinsa. 
Inda ita kuma tsoro da fargabar ta suka ƙara tsananta hankalin ta yayi mummunan tashi, 
Inda take ya fara tunkarowa yana wani shu'umin murmushi, sai kuma ya tsaya yana kallon ta kafin yace 
“ ko da yake nai ma babana alƙawari zan nisanta da zina kuma zan tsare kaina har lokacin da zanyi aure, kuma bayan haka ni mai darajane kuma mai tsada jikina yafi ƙarfin yazo gareki, bazan iya haɗa jikina da ƙazamin jikinkiba, kuma hakan ba yana nufin zaki tsiraba yau sai an mani kaca -kaca da ke, waɗan nan zaratan samarin sai kowa ya kwanta da ke inya so na koma gefe nai maki bidion da zaki sami damar ɗaurawa midia, sai naga menene zai faru tunda ke ƴar tashace yau zaki kwana a gareji. ”
“ inna lillahi wa inna ilaihir raju'un na shiga ukku ni Namsiyya don Allah kayi haƙuri wallahi bazan kumaba dama sai da Sholy tace kar nayi amma kuma na aikata gashinan nagane kuskurena tun ba'aje ko ina ba. ”
“ samari a motsa ba wannan magiyar tasa nace ku kawo man ita ba maza kuyi mata fyaɗe ɗaya bayan ɗaya don hukuncinta kenan ”. 
Tashin hankali wanda ba'a sama rana take Namsiyya ta rikice ta rasa inda zata saka kanta. 
Kafin tai wani yunƙuri, Ɗan kasada ya fincike hijabinta ya tillar gefe ya na ƙare mata kallo, take gashin kanta ya balbaje akafaɗarta tai saurin dafe ƙirjinta ta na fashewa da kuka. 
“Duk wanda ya motsa sai na harbesa”. 
Kalaman da sukaji kenan ana faɗa daga hanyar shigowa gidan, kusan atare suka kai kallonsu wajan da sukajiyo maganar, 
Ƴan sanda ne suke shigowa ɗauke da bindigu a hannun su duk sun saita inda su Ɗan kasada suke da shirin harbin duk wanda yayi ƙoƙarin guduwa, dan danan hankullasu suka ƙara tashi ganin yadda ƴan sanda sukai masu zobe. 
“ ku kuma daga ina waye ya baku ikon shigaman har cikin gida bada izininaba, ” cewar Areeyan cikin gadara da nuna alamar ɓacin rai don shi aɓangarensa babu wani tsoron da yaji. 
“ Ni ne na basu izinin shigowa kuma don na isa nai hakan ”. 
Atare suka kalli hanyar gate ɗin inda sautin maganar ya ke fitowa 

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol