Free chapter · Read without an account

Chapter 13

by Abdulhakim Umar · HANGEN DALA

Page 13


Dam!! Dam!! Haka gaban Areeyan ya yanke ya faɗi tsoro ya kamashi ganin mahaifinsa awajen kuma fuskarsa ɗauke da ɓacin rai. 
“ Areeyan dama irin abinda kake aikatawa agidan naka kenan sawa akawomaka mata kai masu fyaɗe ko kasa wasu marasa imani su keta masu haddi kana kallo, amma ka bani mamaki Areeyan bacci nazo kuma naji komai da bazan taɓa yardaba,, ina ka baro karatun da kai, ina ka ajiye addinin ka, ina ka ɓoye tarbiyyar da nai maka, me ribarka acikin aikata zina, bayan kana da gata kasan da cewa idon mace hudu kai niyyar aura a rana ɗaya alokaci guda zan aura maka ko da kuwa ranar ta kasance yau ɗin nan da muke ciki........ ”
 “ wallahi Dady bantaɓa aikata zina ba kuma bana fatan na fara, aikata abinda Allah da kansa yace nu nisanta, banyi komai ba Dady ka saurareni kaji abinda zan faɗa..... "
“ bazan saurare kaba Areeyan domin baka da abinda zaka faɗaman na aminta da kai domin ganinai baji naiba kuma ba labari aka baniba zahiri na gani don haka zan yanke maka hukuncin da ya dace da kai, "
Sai da Dadyn ya haɗiye wani yawu mai ɗaci kafin yacigaba da cewa “ police akulle mani yaran nan don sune suke bada gudummuwa akan lalara mani yaro, ke kuma yarinya kije kizoman da mahaifinki gidana dake Miloniyan city don magance wannan matsalar. ”
Ya kai ƙarshen maganar yana kamo hannun Areeyan ya fara jansa suka nufi hanyar fira
Da wani irin sauri da azama Namsiyya ta tashi ta sha gaban Areeyan da Dadyn sa kafin ta zube ƙasa akan guyagunta ta dafa ƙafafuwan Alhaji Abdurrahman Na'adami tana fashewa da kuka kafin ta fara magana cikin muryar bantausai
“ Dady ka taimaki rayuwa ta kai man adalci duk faɗin garin nan yanzu kowa ta san abinda ya faru ga rayuwa ta kuma babu wanda zai iya aurena a haka, kai man adalci na tabbata da ƴar kace wani yayima haka da dole ka ɗau hukuncin da ya fi wannan ”. 
 kallon ta yake amma kuma tunaninsa yanacen wani wajan da ban sai kuma ya kalleta yace “ To dama ai zan hukuntashi amma da kai na don bazan iya barin yarona ya kwana sitasion ba ko mai ya aikata middin ina raye to jini na yafi ƙarfin prision ”. 
“Ni dama bani fatan ya je sitasion amma ina fatan ya aureni domin shine adalcin da za'ayiman don ya yalalata mani rayuwa duk inda zanije sai anyiman gari wata ƙilama aranar za a sakeni kaga zaman aure ba zai yuyuba a wajana...... Sai ta fashe da kuka mai cike da sinadaren narkar da zuciyar wanda akemmawa. 
“ ke amma yarinyar nan ki cika makira to bara kiji wallahi ko kukan jini zaki bazan aureki ba ke ko amatsayin ƴar aiki bazaki zo gidana ba don bakikai wannan matsayin ba ". 
   “ Dama dole kace haka tunda kana taƙama da kuɗi da matsayi da gata, amma kuma abinda baka sani ba shine za a mutu akwai hisabi akwai tsayuwa gaban ubangiji ranar da kuɗi, ko mulki sarauta ko miƙami alfarma ko gata basa da wani tasiri sai aiki na gari da riƙon gaskiya da amana ranar zakayi kukan cin zarafina da kai ranar zan mori haƙƙina da ka tauye domin bazan taɓa yafemakaba middin baka aureniba " takai ƙarshen maganar tana share hawaye ta
Wani irin abu ne mmarar daɗi yake ma Alhaji Abdurrahman yawo acikin zuciya tabbas idon ya bar abin a haka bai yima yarinyar nan adalci ba kuma tabbas yaron sa zai iya shiga huta akan haƙƙinta kuma don haka dole Areeyan ya aurera tunda har ya iya kai jikinsa a nata to zai iya zaman aure da ira, sai da ya saki ajiyar zuciya kafin ya kalli Namsiyya yace “yarinya ya ya sunanki? "
Bakinta har rawa yake wajen furta “ Namsiyya ”
“ kije ki sanar da mahaifin ki kinsami miji sati mai zuwa za a ɗaura maki aure da shi ”. 
Bai sake cewa komai ba ya kama hannun Areeyan dake ta buɗe baki alamar yana son yayi magana amma babu damar hakan har suka iso ƙofar gidan inda Dady yasakashi motar da yazo da ita, sai da ƴan sandan suka sanya su ɗan kasada mota suka tafi kafin Namsiyya ta fito daga gidan ranta fayau zuciyarta wasai da alamun nasarar da tai tasata farin ciki. 
Sai da Dadyn ya kulle gidan da wani ƙaton kwaɗo kafin ya koma motar ya shiga ya ja yabar wajan. 
Namsiyya kai tsaye gidan su ta nufa dake Rafin guza ta sanar da mahaifinta za a zo neman auren ta da ikon Allah. 
     Areeyan har cikin ƙaton falon dake gidan mahaifinsa ya jashi inda suna shiga falon ya ɗaukessa da maruka haggu da dama cikin ɓacin rai ya soma magana “ Areeyan ashe sakarai ne kai kuma shashasha me ka nema ka rasa a rayuwa da har zina zata burgeka, kana da hankali , kana da ilimi, kasan aibu da illolin da zina ke haifarwa Amma ka biyewa sheɗan ka ka aikata bayan kasan da cewa ko mace hudu kace zaka aura ayau sai na aura maka su amma ka kasa sanar mani kaje ka aikata kuskure to nayanke hukuncin da ya dace idon har bai makaba sai ka shiya abin yi amma kafin nan ina mai jaddada maka bijirema umarnina kamar bijirema zamanka a gidana ne don wallahi middin bakai abinda nake so ba, to wannan karon sai dai kasake uba amma baniba. " yana kaiwa ƙarshen maganar ya hau saman bene ransa ɓace. 
Duƙewa Areeyan yayi a tsakiyar falon yana zubda hawaye, zuciyarsa na masa wani abu irin zafi, yanzu da gaske Dady zargina yake da aikata zina lallai Wannan yarinyar ta cuceni amma kuma zan sheda mmata cewa ba matane kawai suka iya ƙulla sharri ba suma mmazan sun iya yanzu wasan zai fara sai ta raina kanta sai tayi da nasanin sanina da tai arayuwar ta zan ɗauki hukuncin da Dady ya yanke mani amma kuma sai na tabbatar mata da cewa HANGEN DALA ba shiga birni ba ganin ɗaula da shigarta ba yana nufin jindaɗiba..... 
Dafashin da akainne ya katsemasa tunaninsa ya kalli mahaifiyar sa da kuma Hajiya Wasila dake tsaye gabansa da ƙanwarsa Lateefah. 
Rungumosa momy tayi ajikinta tana faɗin “ daina hawaye yarona kafi gaban kuka middin munnna tare waje guda idon mahaifin ka ya kasa fahimtarka ni zan fahimceka kuma zan sama maka mafita da ikon Allah ”
Sai da ya saka tusho ya goge hawayen nasa kafin yasaki wata ajiyar zuciya ya fara nazarin ta inda zai sanar da mahaifinyarsa abinda ya faru domin baya ɓoye mata komai da ya shafesa yana sanar da ita gaskiya ne koda zatai fushi da shi, yasan kwana kadan zata sakko kuma zata bashi mafita bai iya ƙaryaba tun yana yaro komai ɗaci da baurin gaskiya faɗarta yake inyaso ayi masa hukuncin abinda ya yi dai dai da laifinsa, wannan dalili yasa momy ke ƙara ƙaunnar ɗanta don duk sadda yayi mata ƙarya sai ta gane tunda bai sababa kuma bai iyaba. 
Sai da tayi gyaran murya kafin ya sanar da Mahaifinyar sa komai da ya faru a tsakaninsa da Namsiyya har zuwa hukuncin da Dady ya yanke akansa. 
“ kai yaya kace man za'ayi bala'i da lilliɓi a gidan nan wallahi bazata saɓuba bindiga aruwa, idon raƙamarta makirci to tazo wallahi sai ta nemi hanyar guduwa ta rasa don ni ɗin nan kawai na isheta sai na gwada mata ni dafin kunamace ko ba a mutuba za'a sha jinya sai ciwon zuciya yayi ajalinta....... 
“Ke bana son shirme da shashanci maza ɓacceman da gani tun kafin ranki ta ɓace" cewar momy cikin faɗa-faɗa. 
Sama ta haura tana gunguni da baki, ko da ta isa ɗakin sai ta kasa zama zuciyarta nata ingizata taje ta nemi yarinyar nan tai mata cin mutunci da gargaɗin da zai saka ta fasa aure yayan nata ta janye da kanta, ta kasa tsaye takasa zaune sai safa da marwa take acikin ɗakin nata sai kawai ta zari gyalen ta da key ɗin motarta ta fice ba da sanin kowaba ta nufi Rafin guza don idon har bata ja kunnen Namsiyya ba to yau bazata iya bacci ba don bata barin sai ta kwana ƴar fitinace ta ƙin ƙari ta bugawa da yaɗawa ajarida. 
Momy cikin wata irin murya mai sanyi tace da Areeyan “kayi haƙuri yarona zan shawo kan Dady dole a soke maganar auren nan tun da har baka aikataba, ” nan tai ta lallashinsa har ya manta da komai don yasan momy bazata bari auren ya kasanceba. 
Lateefah tana ƙutsa kai da morar ta ƙirar Lexus cikin layin gidan su Namsiyya aka fara kiran sallar Issha'i 
                
                     ABUJA
Yahaya madaki way, Kubwa , 
Da misalin ƙarfe goma na dare wata hamshaƙiyar motace dock blue ta kanfanin sport take ta sheƙa uban gudu kamar zata tashi sama, ƙara gudun motar matuƙin yayi ganin ya iso gate na ƴan sanda , wanda aka aza wani dogon ƙarfe mara nauyi aka katange wajan dashi don rage gudun motocin da basa tuƙi cikin ƙa'id, bai tsayaba kuma bai rage gudun da yakeba haka ya yi ciki da ɗan yalolan gate ɗin, ganin haka ya sa sauran ƴan sandan matsawa da azama suka waske suka bashi waje don tsira da rayukansu, sai dai yana wucewa suka shiga motar su ta ƴan sanda wato (Hilux ) suka mara masa baya. 
Bai damu da ganin an biyoshiba don hankalinsa kwance yake kamar bai aikata komai ba sai ma ƙara ƙure bolum ɗin rikodar motar sa da yayi inda yake sauraron sabuwar waƙar ( Nairamaley). 
Babu shiri ya taka burki sakamakon ganin hilux agabansa 
Da sauri ƴan sandan suka shiga fitowa hannayensu riƙe da bindigu, sai dai sunayin tozali da fuskar matuƙin motar suka ja baya da sauri suka koma motar su suka bashi hanya ya huce batare da ya ce uffan ba kasantuwar shi ɗa ɗaya tilo ga wanda yafi kowa kuɗi akaf faɗin garin ABUJA wato Alhaji sulaiman Bara'u gidan iko , ɗaga masa hannaye suka hauyi alamun Allah ya tsare. 
Shima kaɗa kansa kawai yayi yaja matar sa ya cigaba da tafiya bai tsaya a ko'ina ba sai a ( TJ club), yana shiga cikin holl ɗin aka sakar masa sautinsa na musamman tare da sakin hasken kwayakwai masu launin ja blue da green, dan da nan waje ya hautsine da rawa da ƴan bushe bushen hayaƙi da shaye - shayen kayan maye. 
Yarinyarsa na hangosa ta iso wajansa hannunta ɗauke da kofin barasa ta rungume sa suka soma rawa mai kama da rangaji. 
Tahteef kenan ɗan gayu kuma ɗan kwalisa, kazaslika ɗa ga wanda yafi kowa dukiya a cikin birnin tarayya. 
Tahteef dai fari ne tas dogo mai ingarman jiki yana da kyawon fuska da na fata yana da son more rayuwa da zuwa club, fuskar sa mai tsawoce wacce ya ƙawata da saje mai kyau wanda ke ƙara masa kwarjini da haiba da zati yana da zuciya sosai da matsanancin kishi yana da ƙarfi na jiki kamar wanda akaima Allurar doki, yana shan taba kuma yana shan shisha harma da kokin yana shaƙawa wacce ke shirin zautar da kwakwalwar kansa,yana da son mata kamar zai haɗiyesu domin kuwa tun yana da shekara sha ukku ya kashe wani malamin makarantarsu dalilin cakama malamin ƙarfen masat da yayi a ciki saboda ya dokai, kuma wata yarinyace tai ƙarasa wai yayi mata kiss da yake ubansa sune ƙusoshin ƙasar sai aka wofintar da abin da cewa yaro ne, kowa shakkarsa ya ke saboda ƙarfinsa da zuciya, gefe ɗaya kuma ga muƙami da dukiyar ubansa duk abinda ya so to sai ya aikata babu mai iya hanasa, wannan dalilin yasa ake mugun shakkarsa a kaf faɗin garin, Tahteef zaki ne mai zafin nama irin na Damisa ga himma kamar Gadah, babu abinda Tahteef yake tsoro ko shakka a duniya komai ya zo masa to zai tunkara kuma yayi nasara, akwai soyayya da shaƙuwa sosai tsakannninsa da mahaifin sa wacce take hana mahaifin nasa sukuni idon har yayi nisa da shi. 
 
Sai ƙarfe ɗaya na dare kafin ya bar club ɗin ya nufi gidan mahaifinsa dake javi. 

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol