Free chapter · Read without an account
Chapter 14
Page 14
. Gidan maraayu
Da misalin ƙarfe bakwai na safe Muheebbah na tsaye abakin wani waje da aka tanadar don yin alwallah ga yara, tana wankema wani yaro baki da brosh sai ga Anty Ainah shugabar masu kula da wajan ta shigo a rikice tana kiran Atika kafin kace tak tuni ma'aikatan wajen da yaran sun taru waje guda don sun san ba lafiya ba, Anty Ainah ta fashe da kuka kafin ta sheda masu ƴan fashine suka shiga gidan Hajiya Babba suka kwashe komai kuma sukai mata dukan mutuwa yanzu hakka tana kwance a gadon Asibiti.
A take kowa ya sami kansa acikin baƙin ciki da jimamin wannan lamari da yima Hajiya babba fatan samun nasara, da addu'ar Allah ya toni asirin waɗanda sukai wannan aika aikar, domin kuwa hajiya babba itace bango abin jingina ga rayuwar yaran gidan saboda itace kinsu da shansu da suturarsu dama komai na rayuwar su kasantuwar gidan marayun bana gwamnati bane nata ne na ƙashin kanta ita ke biyan ma'aikatan albashi da ɗawainiyar komai ta gidan.
Cikin abinda baifi wata guda ba rayuwar gidan ta sauya saga walwala zuwa ƙunci daga jindaɗi zuwa baƙin ciki saboda komai na gidan ya ƙare babu abinci babu sabili babu duk wani abu da za'a buƙata ya ƙare, hakan yasa mutane da yawa daga cikin ma'aikatan wajen guduwa suna komawa inda aka ɗaukosu, cikin mutane ishirin da biyar mutum ukku ne suka rage daga Anty Aina sai Muheebbah da wata ƴar garinsu mai suna kuluw, tuni aka fara shawar kulle gidan saboda rashin mafita Muheebbah ko tace bazata bari rayuwar yaran da suka fara gyara ta koma baya ba su tashi a gidan marayu su koma kan titi hakan zai haifar da gagaruar matsala don haka ta fara rubutu a takarda tana zagaye unguwannin masu kuɗi domin neman taimako, ganin haka yasa ita ma Anty Aina ta fara irin nata neman taimakon akan intarnet, fecebook da TikTok da whatsapp da sauran kafafen da tasan za'a sami wani abu.
Da haka suke kula da tarin yaran dake rayuwa a ƙarƙashin kulawarsu.
RANAR TALATA
Da misalin ƙarfe shabiyu na rana Muheebbah na zuba dakakken kuli acikin garin kwakin da ta jiƙama yaran don suci, Kuluwa ta zauna aa gabanta tana cewa “ Muheebbah naji labarin wani hamshakin ɗan masu kuɗi wanda idon har muka samu ya ji kukanmu to wallahi zai bamu kuɗi bana wasa ba kuɗi mai yawwa wanda zai isa rayuwar yaran nan har zuwa wani lokaci mai dama wanda kafin sannan an sami mafita mai yawa da ikon Allah ”
“ To Alhamdulillah yanzu yaushe zamuje ”
“ ba zuwan bane aikin samun kansa shine aikin domin mutum ne wanda kowa yake shakkarsa don yana da hatsari kuma ba lallai bane ya sauraremuba”.
“Firar me kuke anan bandani" cewar Anty Ainah tana zama kusa da Muheebbah kafin ta ɗaura da cewa “ yanzu wallahi ina zaune saƙo ya shigo man ta fecebook kunga poton wannan gayen” ta kai ƙarshen maganar tana nuna masu poton matashin kafin ta ɗaura da faɗin wani ne ya turoman da poton yace munemi taimako a wajansa zai taimaka sosai don mahaifinsa yafi kowa kuɗi a garin nan sunan sa Tahteef kuma a club ne kawai zamu iya iskesa, ”
“ To menene wahalar indai zamu sami abinda muke nema ai rai ba komai ba inda biyan buƙata inji ƙuda, ni ai tuni na shirya fuskantar kowane irin ƙalubali akan tallafama waɗan nan yara don haka yaushe zamuje? " cewar Muheebbah inda ta kai ƙarshen maganar da nuna alamar tanbaya
“ yau zamuje don ba'a bori da sanyin jiki, bayan sallar la'asar zamu iskesa ”
To Allah ya kaimu suka faɗa atare kafin suka hau kason garin kwakin da suka jiƙa da ƙuli ga yaran .
Bayan sallar la'asar Muheebbah ta fito cikin shirin tafiya ita da Anty Ainah kaya kala guda suka saka, dogayen rigunane irin na kanti sai dai su waɗanda suka saka bana kwalliya bane don ɗauke suke da tanbarin ( HALAL CHINDENT'S HOME ), suka bar kuluwa ta kula da gidan sukuma suka fita basu zame a ko'ina ba sai inda akace zasu iske Tahteef wanda gidan Abinchine dake unguwar jabi.
Mai tasi na sauke su suka fara bin wajan da kallon don wajene na alfarma mai kyau da ɗaukar ido kamar a kasar turai, ko ina ka kalla sai walkiyar gilassai ke yayo saboda yadda rana ta haska wajan ga walƙiyar sabon fati da ƙamshin sa domin kuwa kana tunkarar wajan zaka sheda sabon wajene.
Cikin yaren turanci Anty Ainah tai ma mai gaɗin wajan batani ataƙaice kafin ya barsu suka shiga,
Dam! Zuciyar Muheebbah tai wani irin bugu sakamakon ganin wanda sukazo wajansa don kuwa take ya burgeta, bakuma burgewa irin ta so ko ƙauna ba, ba kuma burgewa ta matsayin da yake da shiba a'a burgeta kawai yayi burgewa irin wacce kowane Talakka yakema mai kaɗi, sai da suka shiga linter zuwa hawa na ukku wanda zai kai su har mazaunin da yake.
Muheebbah ko ina suka shiga sai tabi wajan da kallo domin karo na farko kenan da ta shigo waje mai kyau irin wannan wanda harda lintar ake hawa.
Inda escord ɗin sa suke tsaye abakin ƙofar shiga suka tsaya Anty Ainah tace “ pleass munzo wajan Mrs Tahteef ne muna son zamu shiga ”
“ ok kuna da Aportement da shi ”
“ A'a munzo ne kai tsaye ”
“To ku koma dan bazaku samu damar ganin sa ba ”
Don Allah ka sanar da shi yayi baki daga HALAL CHINDENT'S HOME muna son ganinsa sosai domin kuwa haɗuwarmu da shi tana da muhimmanci”
Bai ce komai ba ya tura ƙofar ya shiga da alama mai tausayine don tunda yaji cewa daga gidan marayu muke yanayin sa ya sauya yayi kalar tausai.
Muntina kaɗan sai gashi ya fito yana cewa “ cewa yayi kuyi haƙuri baya acikin yanayin da zai iya haɗuwa da kowa kuma majorety irin wannan buƙatun yana amsa sune a gobe da ƙarfe biyu na rana a gast hause ɗinsa dake unguwar katampe ”.
“ To mun gode ” cewar Anty Ainah cikin sanyin murya jiki babu ƙwari suka sauka ƙasa suka koma gida batare da samun nasaraba.
Washe gari ma sunyi sakkon fita zuwa katampe domin kuwa suna cen akai sallar Azahar sai dai duk irin zuwan da suke ganin sunyi da wuri sai da suka samu layin mutane sosai ana jiransa haka suka hau layin da addu'ar Allah ya sanya su sami ganin sa kuma suyi nasarar samun abinda sukazo nema sai dai kash suna daf da shiga labari marar daɗi ya ruskesu, cewa wai yayi baƙi su tafi kuma sai gobe.
Babu irin magiyar da Anty Ainah batai masu ba amma suka hana su shiga, yau ma haka suka tafi jiki babu ƙwari, sai da sukai sati ɗaya suna zarya amma abin kamar ƙin jini ko da gayya ake masu domin kuwa har yanzu basu sami damar ganin saba, fidda rai da Anty Ainah tai da neman taimakon sa shine abinda ya yima Muheebbah ciwo a zuciyarta har ta ɗauri aniyar yau ko me zai faru sai ta iske sa sai ta haɗu da shi ko mai zai faru tai alƙawari kuma taci alwashi.
Da dare misalin ƙarfe sha ɗaya Muheebbah ta tashi tai shirin fita batare da sanin kowaba ta saka Aftar dress baƙa ta yane kallabin a fuskarta, sai tai wani irin kyau na ban mamaki domin kuwa ba kwalliya tai ba amma duk wanda ya kalleta sai ya sake kallonta, saɗaf - saɗaf tai ta fice batare da sanin kowa ba ta bar gidan aƙafa ta isa har ( Tj club) inda ta san zata samesa babu wanda tare ta bare har atanbayi wajan wata zo ganin irin kayan da ke jikinta da kuma lokacin da tazo.
Tayi nasarar shifa har cikin Holl ɗin inda matasan samari maza da mata keta tiƙa rawa an ƙure bolum na spekun dake wajan, gefe ta tsaya tana jiran ya gama tiƙar rawar da yake ta kumayi sa'a don ko mintina biyu batai ba taga an tsayar da kayan kiɗin inda shima uban gayyar ya nufi wajen wani tebur na musammanma ya zauna sai nasu tsaronsa da suka zagayesa har su biyar kuma majiya ƙarfi inda ya zauna ba cikin Holl ɗin bane cen nesa da wajanne don haka ta taka tana mai addu'ar samun nasara a zuciyarta.
Tana daf dashi escord ɗin suka tareta suna ƙoƙarin korata.
Karaf sukai ido biyu da ita kuma ido cikin ido take wani abu da baisan da shiba a zuciyar sa ya motsa wani irin felling ya shige sa wani abu da ake kira da shauƙi ya bayyana a ransa ya kafeta da ido yama mata kallon ƙurulla kafin yaji zuciyar sa tai masa wani irin bugu da ƙarfi ya shiga cikin jazabar da masoya ke shiga a haɗuwar farko, babu abinda yake kallo sai siraran laɓɓanta da suke jajurur kamar tufa, inda hancinta ya kasance dogo kuma siriri mai jan hankali, yayin da kwayar idon ta suka kasance farare tas masu kamar madara gani irin sanyin kyau da kwarjini da yake fitowa daga cikin su, haka yake ƙare mata kallo tun daga ƙasa har sama yana ayyano abu buwa da dama aransa yadda take magana tana masu magiya kawai yake kallo yana shauƙi, ganin yadda wani yake ƙoƙarin jan hannunta ya korata yasa ya dawo hayyacinsa cikin wata irin murya da shi kansa bai san yana da ita ba yace “ kubarta tazo ”.
Jin hakan yasa suka kauce da sauri, ita kuma ta ida takowa har inda yake ta ja kujerar dake saitinsa ta zauna tana faɗin.
“ Barka da dare ƴallaɓai sunana Muheebbah ni ma'aikaciyace a HALAL CHINDENT'S HOME wani ibtila'ine ya afka mana "nan tai masa bayanin abinda ya faru da mai wajen kafin ta ɗaura da cewa“ yara da yawa sunkamu da olser saboda zama da suke da yunwa, idon har ka taimaka, yara da yawa ne zasuyi farin ciki da haka, wasu suna karatu wasu basayi saboda rashin gata mutane irin ka sune kawai zasu iya taimakawa da abinda zaya wadata ka taimaka ƴallaɓai, "
Bayani take amma dukka illahirin hankalinsa da tunaninsa baya jikinsa yana cen wata duniyar har ya fara hangosu a bakin ruwa matsayin mata da miji suna nishaɗi tsabar sauƙi da soyayyar dake ƙoƙarin shiga zuciyarsa.
Sai da wani makusancin sa acikin yaransa ya taɓoshi yana cewa “ lafiya dai ko ƴallaɓai ".
Firgigit ya dawo hayyacinnsa yana ƙoƙarin saita natsuwarsa yace “ Afif a bata ko nawa zai isa ”.
Take Wanda aka kira da Afif ya buɗe wani ƙaramin madai daicin akwatin dake gabansa inda kuɗi suka bayyana cike da akwatin kuma Dalos na America
Dam! Dam!! Gaban Muheebbah ya yanke ya faɗi ta ɗago da sauri tana kallon sa idanuwa waje, cikin in ina tace “ me me meye wannan " takai ƙarshen maganar tana mai nuna tsabar tsoron dake kwance a zuciyar ta.
“ kuɗine ko sunyi kadan ” ya faɗi da sigar zolaya
Nuna kuɗin tai kafin ta nuna kanta tace duka nawane wannan
Baice komai ba sai kaɗa mata kai da yayi alamar eh
Da sauri ta kai hannun ta tana toshe bakinta da wani irin murmushi da ya subuce mata tsabar jin daɗi kafin tace “ amma ƴallaɓai duka wannan kuɗi sunyi yawa ni da nazo ka taimaka da ɗan wani abu amma sai kabada wannan makudan kuɗi na gode sosai Allah ya ƙara arziƙi da wadata Allah ya baka abinda kake so ”
Ai yama bani tunda ya haɗani dake ina son ki, abinda ya furta kenan a zuciyar sa inda a fili kuma ya amsa da Amin.
“ zan iya zuwa naga gidan marayun ”
“ Eh mana me zai hana ƴallaɓai ”.
“To muje sai ma mu saukeki tunda dare yayi, saka mani phone nuber naki idon wata buƙata ta tashi sai ki kirani bama sai kinzoba ".
“ kayi haƙuri ƴallaɓai amma bani da waya ”.
“Is ok ba damuwa muje kawai ”
Haka suka fito harabar wajen inda wata hanshaƙiyar mata ke jiransu baƙa mai lumfashi sai sheƙi take tamkar gilas ɗin da rana ta haska PRADO ce mai kyau da ɗaukar ido har bakin gate ɗin gidan suka ajiye ta inda suka kama hanyar gida.
Tana shiga ta samu Anty Ainah da kuluwa a tsaitsaye sunata kai kawo a harabar gidan, kusan atare suka sauke ajiyar zuciya kafin Anty Ainah ta iso inda Muheebbah take tana cewa “ Daga ina kike Muheebbah kin tayar mana da hankali mun kasa bacci muna nan muna zullumi ko ina kika shiga”
“Muje daga ciki muyi magana domin ina lafiya kuma fitar da nai arziƙi da rabo ne suke kamuwa rana domin kuwa nayi nasar haɗuwa da Tahteef kuma yabada kuɗi mai yawa da zai isa ”
Kama hannun Muheebbah Anty Ainah tai suka shiga ɗakinsu suka zauna suna fuskarta juna, inda suna zama Muheebbah ta sanar da su inda taje da kuma Alkhairin da ra samo.
Dam! Zuciyar Anty Aina da kuluwa tai wani irin mugun bugu wanda har sai da Muheebbah taji sautin a fili, kafin Anty Aina ta soma magana cikin ruɗani da firgici
“ Muheebbah wannan uwayen kuɗin ya baki a matsayin taimako wallahi ban yarda da ke ba ki yi hanzarin sanar dani abinda ya faru don kai na bazai ɗaukaba ”.
“ wallahi Anty Aina shine ya bada kuma yace zai zo yaga abinda mukai da su ban aikata ko mai kuma bazan taɓa aikatawaba ”.
Nan take ta sanar masu da komai har irin kallon da yake mata sai a sannan Anty Aina ta saki ranta tace “ Lallai Muheebbah ke mai sa'a ce domin kuwa babu shakka ya kamu da soyayyar ki ".
“Haka dai kikace Anty Aina amma ni banga alama ba taya mma za'ace mutum mai daraja da girma da matsayi kamar mrs Tahteef ace wai yana sona kai abin da kamar wuya ”.
“ Babu wata wuya idon har Allah ya Amince ke dai ki nemi zaɓin gaskiya A wajan ubangiji Allah ya tabbatar da Alkhairin sa marar adadi acikin labarin. ” cewar kuluwa wacce sai yanzu tayi magana
Da haka kuma suka sauya aakalar firar tasu zuwa yadda zasuyi amfani da kuɗin da kuma sana'ar da za'a fara domin samun kuɗin shiga don sama ma yaran sauƙi a rayuwarsu.