Free chapter · Read without an account

Chapter 16

by Abdulhakim Umar · HANGEN DALA

Page 16


Banɗaki ya shiga ya rage kaya ya sakarma kansa shawa, sai da yayi kusan mintina ishirin kafin ya fito ɗaure da tawul ya saka jallabiya ya hau gadonsa ya kwanta, domin babu abinda ya ke da buƙata a yanzu kamar yagansa yana hurawa, kwanciyar sa ke da wuya Tunaninta yayi masa sallama a zuciya komai nata biresa yake yana mata wani irin sone da zai kira hakan da masifar so, don ya huce yace masa ma haukacin so, sone yake mata irin son da kowacce gangar jiki takema ranta, sone irin wanda kowanne ɗan Adam yakema Aljanna, sone irin wanda kowacce uwa takema ɗanta, sone da bai san yadda zai iya faɗarsa abakiba, a yadda yakeji ko zai rasa ransa akanta to a shirye yake , ya shirya zama da ita aduk inda ta keso koda a gidan marayu ne, baijin akwai wani abu aduniyar nan da zai iya hanasa ya mallaketa , wani irin so yake mata da dukkan nin ransa da zuciyar sa da gangar jikinsa, haka kawai yake jin sonta a matsayin jarabta daga Allah, don bai taɓa jin son wani abu ba irin yadda yake ji akantaba. 
Ahaka bacci ya yi gaba da shi cikin shauƙi da walwala, inda yayi mafarkin gasunan a zaune cikin wani irin ƙawataccen lambu mai cike da korayen gayyayaki suna zaune yana bata Apple a baki tana ci tana masa murmushi. 

Muheebbah sai da taci kuka mai isarta kafin tai shiru don kanta, babu abinda take son sani a yanzu sai cewa da gaske Tahteef ɗan gidan iko ne ko ko dai wani Alhaji sulaiman ɗin ne aka samu da ban, inda ta ɓoye wayar da ya bata ta nufa ta ɗauko ta kunna, tana gama dai daituwa ta buɗe data tai sa'a kuma layin cike yake da kati da date don haka ta fara googling tarihin Tahteef ta fara bincika sai dai na mahaifin sa ne ya bayyana, inda anan ta gane cewa Alhaji sulaiman gidan iko yafi kowa kuɗi a ABUJA birnin tarayya kuma anan ta fahimci irin mugun son da yakema ɗan sa kuma shine dai maci amanar nan da ya keta haddin ƴar uwarta har baƙin ciki yasa ta kashe kanta ta bar duniya, kuma shine dai mutumin da yayi ma mahaifin ta ƙazafin da akayanke masa hukuncin kisa taya zata iya mancewa da shi taya ɗansa zai zo garta da sunan soyayya, wani photo ta danna wanda Tahteef ne aciki tare da ƴan sanda tari guda sun zagayesa, a she alokacin da ya karya wani mutum ne kuma tunda aka gane ko ɗan waye aka lalata zancen, gama karanta tarihin Tahteef keda wuya kuka yaci ƙarfin ta tsoronsu ya kamata, atake ta fara tinanin guduwa don tsira da ranta domin kuwa ta tabbata da cewa suna sanin ko ita wacece zasu aikata ƙiyama, sai ta sulale ta zauna akan katifarta tana kuka mai sauti tuna abinda ya fara wanzuwa a tsakaninsu,ji take duk ta tsani kanta saboda sakin jiki da tai da Tahteef ji take kurwar Ahalinta bazata taɓa yafemata ba, dole inbar garinan nan kusa tunkafin ƙarshena yazo. 
Babu inda zakije domin kuwa wannan wata damace kika samu ta ɗaukar fansa akan maƙiyanki, wannan son da Alhaji sulaiman gidan iko yakema ɗannsa da shi zakiyi anfani wajen ɗan ɗana masa irin abinda ake ji idon aka rasa masoyi, da wannan damar zakiyi anfani kisakashi kuka makamancin wanda yasaki a baya, dole ki nuna masa kuskuresa, tabbas an zalinceki amma ga dama kin samu ta rama ma kura aniyarta, 
Waɗan nan kalamai sune suka fito daga wani yanki na zuciyar Muheebbah, kuma sune suka ragemata kashi saba'in cikin ɗari na zugin da zuciyarta ke mata, suka kuma yi nasarar sakata murmushi, ta fara tsara yadda komai zai kasance daga yanzu. 

Alhaji Sulaiman Bara'u Gidan Iko zaune a harabar kanfaninsa na sarrafah audiga, yana murmushi gami da walwala saboda haɗuwa da yayi da abokansa wa ɗanda suka jima basu haɗuba tun bayan kammala zaɓe, a yanzu Alhaji iro mai kaita shine ministan ilimi na ƙasa baki ɗaya, shikuma Alhaji Nuhu Dutsi shine ministan lafiya na ƙasa, inda Alhaji Ado kurfi ya kasance mai kula da shige da ficen komai da yake wanzuwa a cikin garin Abuja dama ƙasa baki ɗaya .
****** **** 
KATSINA STATE  
General Hosbital, hajiya Larai ce zaune akan kujerar roba tayi tagumi tana kallon ɗanta Abbas dake kwance yana ta sharar baccin sa wanda Allurar bacci akai masa domin gobe ake saka ran za'ayi masa aikin zuciyar da ikon Allah, ƴar ƙaramar wayarta da ke hannunta ce ta hau ruri alamar ana kira da sauri ta kalli wayar amma lambar babu suna har sai da ta kusa katsewa kafin ta ɗauka tana karawa a kunnanta dare da yin sallama, da cen ɓangaren ma sallamar akayi dole ta tsayar da tata ta amsa ta wanda ya kira domin taji muryar namijin ne wata ƙila abokin Abbas ɗin ne zaiyi masa yajiki, 

“ ina huni mama” aka faɗa cike da girmamawa daga wancen ɓangaren cike da girmamawa 
“ lafiya ƙalau ɗan nan, amma wake magana ban ɗau murya ba ”
“ Alhaji AHMADU ne mamallakin gidan man da ɗanki yake aiki, nakira ne zan masa yajiki kuma ina son sanin wacce Asibitin yake kwance ina son nazo na duba sa domin bansan baya da lafiya ba sai yau da safe ”. 
“ To Alhaji mun gode da kulawa, muna Asibitin General. ”
“To Allah ya bashi lafiya Allah yasa kaffarane sai mun shigo zuwa yamma ”. 
“To Allah ya saka da Alkhairi sai kunzo ɗin” 
Daga haka sukai sallama ta ajiye wayar tana ƙare ma Abbas kallo wanda bai san tanayiba sai taji hawaye sun fara bin fuskar ta afili kuma a bayyane tace Allah ya baka lafiya Allah ya sakamaka idon har ancutar da kai. 

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol