Free chapter · Read without an account
Chapter 17
Page 17
KADUNA
Rafin guza sai da aka fito daga masallaci kafin Lateefah ta tanbayi wani inane gidan su Namsiyya take ya nuna mata saboda sunan ba wani boyayye bane saboda shurar da tayi wajen son ƙarya da rayuwar hutu kuma daɗin daɗawa ita kaɗaice mai suna Namsiyya kaf faɗin unguwar, ɗaure fuska Lateefah ta ƙarayi lokacin da ta isa ƙofar gidan don rashin mutunci zatai masu da ruwa ruwansa sai taja masu kunne ta yadda zasu dinga shakkarta har suji tsoron ganinta, rashin mutunci ta zo da niyyar yimasu irin rashin mutuncin da ko sunan ta sukaji sai sun razana, sai sunji shakkar yadda da maganar auren da mahaifin ta ya yanke akan rashin sani, yau sai tayi masu rashin mutunci mai kalar ruwan omo.
Kallon tsakar gidan take tana yatsine fuska ta jinjina irin talaucin da suke ciki tabbas zata iya aikata komai akan ɗan uwanta don ta samu abin duniya, yaran gidan ne daga can bakin ƙofar wani ƙaramin ɗaki suna ta wawason tuwo miyar kuka inda ita kuma uwar take zuƙunne bakin murhu da alama yanzu take rabon tuwon sai wata budurwa mai kama da Namsiyya tana gefe guda tana ɗaura gyaɗa amaro da alama sai da ita take, inda mamar take Lateefah taje ta tsaya mata ƙerere akai batare da tayi mata sallama ba.
Ganin inuwar mutum akanta yasa ta ɗago tana cewa “ lafiya baiwar Allah daga ina meye haka? Zakiyiman tsaye akai babu ko sallama ko ba musulma bace ke ”....
“Keeee! ya isheki karki nemi kice zaki kafurtani don yanzu zan maki rashin mutunci bana wasa ba ”
“ To ” mama ta furta fuskarta ɗauke da matsanancin mamaki kafin tai wata magana Lateefah taci gaba da cewa
“ Tsohuwar guzuma ba wajanki na zoba wajan ƴarki na zo na jamata kunne don gidan mu kamar kabari yake ga bare , kabarin ma na wanda bai dace da samun rahamar ubangiji ba, kabari irin na wanda yake tsaka da shan ukubar aikin sabon da yayi a duniya, ki sanar da ƴarki taje ta warware mugun ƙullin da tai na ɗaurama ɗan uwana ƙazafin da tai tun kafin waje ya ƙure mata don ko wallahi mun shirya tsaf sai mun zamar mata ƙadan garen bakin tulu, balle shima Areeyan ɗin ba kanwar lasa bane don shima sai ya zame mata wuƙa a maƙoshi. ”
Mama ta kasa magana sai kallon Lateefah ta ke tundaga ƙasa har sama tana kaɗa kai cike da al'ajabin kalaman dake fita abakin Lateefahn
“ To mamaki kike naga kina wani kallon sama ”
“Dole nai mamaki ƴar nan dole na kalli sama ”
Murmushi Lateefah tai tace “ ai ba ayi komai ba cikin tujarar da na tanazar ma ƴarki naga kamar bata nan, idon har ta dawo ki gayamata na zageki naci maki mutunci....... ”
“Dakata ƴar nan baki zageni ba kuma karki yarda ki soma don zan gwadamaki nima na iya tujara....... ”
“Kwantar da hankalinki mama ai ina gidan kuma kin haifeni, don haka babu wat ƴar iska marar tarbiyya da zata zo tace zata nunaki da yatsa ban karya shegen yatsanba ” cewar Namsiyya tana fitowa daga cikin ɗakin su
“ au dama kina cikin gidan kikai mukwi, ko da yake ga alamu nan sun bayyana razana kikai kika buya don kinsan baki da gaskiya munafukar banza da wofi ”
Wani irin kallon tsana Namsiyya taima Lateefah kafin ta ɗaura da cewa “ har gaban abada ba ayi ƴar da zanji tsoron taba, babu ita kuma bama za'a yitaba.........
Takowa Lateefah tai har inda Namsiyya take tace“ BA wannan gardamar ta kawoniba jankunne nazoyi maki da gargaɗi don ke baki isa nayi gardama dake ba sai dai nai maki kashedi na sanar da ke abinda kike ƙoƙarin kullawa ba abune mai yuyuwa ba don yaya Areeyan yafi ƙarfinki ko ta ina, ki duba jikin ki kigani jibeki don Allah kamar wata mahaukaciya, ke inbaccin jarabawa ya za'ai ki iya ganina bare har na shigo cikin wannan matalaucin gidan mai kama da bola, ki sake buɗe kunnuwanki da kyau jini yaya na ɗan gatane kuma ɗan masu kuɗi ko a matsayin mai masa shara kinyi kaɗan bare matar aure , mutane sai kwaɗayin bala'i da burin da bai da wani amfani, inba kwaɗayi ba inake ina yaya Areeyan tun yana yaro da madara aka rainesa ya tashi cikin kwai da bota ya rayu da cin naman kaji da bounbiter, ɗan gidan gate da mai gadi ke ko mota sai anbuɗe masa yake hawa, ɗan gayune na ƙarshe, kefa ki duba yadda ƙannanki suke wawason wani irin abin ƙazanta ko menene ma sunan sa na manta, wai ashe tuwo sunansa miyar kuka bansaba ganiba, ko da yake muna ganin yadda kuke rayuwarku acikin film rainon kwakko kiwon garin kwaki da ƙanzo, taya wannan haɗin zai yuyu yo ai ko makaho ya laluba ya san da banbanci don wutsiyar raƙumi tai nisa da ƙasa kuma bakin rijiya ba wajan wasan makaho bane, don haka kije ki warware komai ki zauna lafiya inko ba haka ba sai kinyi nadama da dana sanin haifuwarki da akai a garin kaduna don munyi maki tanajin komai irin yadda kike so kuma kika zaɓa. ”
Murmushin takaici Namsiyya tai don tana baƙin cikin taji an cimata mutunci gashi kuma inda ba za'a ta iya kai dukaba amma zata rama ko da fatar bakin don haka ta cigaba da faɗin
“ bana yafiya kuma banbari abiyoni bashin magana don haka dole kema kiji ɗaya da kunnanki, da kike cewa kiwon ƙanzo da garin kwaki, ahaka bunsurun yayaki ya bini ina kaɗa masa bindi kuma ki sani ki sheda da cewa duk irin yadda kuda yayi daddaɓa akan nama bai hana asashi tukunya kuma adafa aci har alashe hannu, kuma duk abinda mukecu ai shi Alhaji ku yaci ya rayu don naji ance bakwauyene ya samu ɗaukaka garama mu muna da galihu don ruwan da buke sha fararene bana ƙorama ko na tafkiba, kuma ko babu kuɗi cikin birni aka haifemu kuma aka rainemu don haka munfi baƙauye daraja tunda tuwon da mukeci farine niƙan inji ba baƙin tuwo da baƙar miyaba dakan hannu da dutsi. ” takai ƙarshen maganar tana murmushin mugun ta da yin fari da ido.
Duk wani abin da ake kira fusata to shine ya cika zuciyar Lateefah tunani take na abinda zatace ta huce daga zafin da ƙirjinta yake mata ita da tazo jankunne faji ita anjamata an kuma gaya mata baƙar maganar da bata taɓa zaton wani mahaluƙi zau iya faɗa mataba, don ita dai tasan tun tana yarinya duk inda suka shiga girmamasu ake na karramasu ko don kuɗin ubansu wanda dashi suke taƙama suna alfahri su bigi ƙiji a ko ina suna faɗar ubansu mai arziƙi ne to gashi yau an ci mutuncin mahaifin nata to me kuma yayi saura me zatayi ta huce, take kuma ta saki wani shu'umin murmushi tono da abinda zatai yasa afasa auren don haka da sauri ta ɗaga hannu ta gallama mama mari.
Mama so take ta fara bama Lateefah haƙuri race ta tafi dob ita batasan me ye maƙasuɗin faɗanba batasan me ya ke faruwaba ta buɗe baki da niyyar magana taki tas ƙarar saukar wani irin mari a kuncinta wanda rabon da amareta tun tana budurwa don kuwa tunda tai aure tsabon shekara ashirin kenan mijinta bai taɓa daga mata hannu da sunan dukaba.
Ƙanwar Namsiyya dake gefe tana kallo itace tai saurin daka tsalle da yin kukan kura tanufi Lateefah zata mara, cikin wani irin ƙarfi da kuzari Namsiyya ta janyeta gefe rana faɗin “ na shiga ukku baki da hankali marin ta zaki kijawoman abin kunya ace anfasa auren to wallahi babu wanda zai taɓata ”.
Ba Lateefah ba hatta mama mamaki take tayyada za amareta gaban ƴarta amma ta kasa aikata komai kuma mai kishi da sonta tazo ta rama amma ta hana to meye dalilinta na yin hakan.
Itako Lateefah ba haka tasoba sotai su mareta koma su daketa ta yadda mahaifinta zai fusata yace a fasa auren domin kuwa yana matuƙar sonsu kuma babu abinda ya tsana a duniya sama da yaji cewa wai an dakesu don ko mominsu ta dakesu sai taga fushin shi bare kuma wani bare, Lallai Namsiyyar nan bata da zuciya a daki uwarta gabanta ta kasa aikata komai kuma ta hana masu zuciyar aikatawa lallai ta shirya ta ko ina.
“ Ki barni yaya kibarni na daketa naga ƙaryar iskanci, don wallahi bata fita gidan nan lafiya mama fa ta daka, to wallahi bata daki banzaba sai mun bugi shegiya,.
“ yo dama ai bata daki banzaba kuma babu mai bugunta ya ja afasa aurena da ɗan masu arziƙi, sai dai kawai zan sanar mata ta daki kuɗin ubanta don ina shiga gidan zan kawoma mama million ɗaya shine fansar marin da akai mata dole kuɗin ubansu su jijjiga ”.
“Babu wata million ɗaya sai na ci ubanta wallahi sai na gwadamata cewa kuɗi ba hauka bane don basu isa su saiyi martaba da kimar uwataba dole sai na ɗau fansa, Ahmat Auwal saude kuzo mu bugi shegiya, yo ai da wani irin sauri Lateefah ta fita tabar gidan ganin yadda suka yo mata ca hannuwansu duk sunyi faca faca da miyar kuka jikinsu duk dauɗa ga majina tai masu kaca -kaca da alama sunyi kwana biyu basuga ruwaba, wannan dalilin shi yasa tai saurin fita ba wai don tsoron dukan da zasuyi mataba, don zata shsnye amma barata bari su taɓataba don ƙyamarsu take, wata ƙila sai tayi sati taba amai middin suka raɓi jikinta .
Hawayene suka fara bin fuskar mama kafin cikin wata irin murya mai rauni tace “ yanzu Namsiyya har son abin duniya yakai ki bari amareni gabanki kuma zaki ɗau matakiba yara masu son ɗaukar matakin kuma ki hanasu, amma kinyi asarar rayuwar ki nayi nadamar haifarki da nai ga ki ga duniyar nan kici abinda ke cikinta bazan maki bakiba amma zakiga abinda baki tsammani ba arayuwarki don hangen dala ba shifabirniba kuma duk wanda yace duniya ya zaɓa to ta ishesa riga da wando har da ɗankwalin ɗaurwa, tunda kin zaɓi rayuwar hutu gaki ga ɗan masu kuɗin ki zama Ealezerbet ƙarshen mulki da kuɗi. ”
Mama na gama faɗar haka tai hanyar ɗakinta.
Washe gari sai ga Alhaji Abdurrahman na'adami da ƴan uwannsa biyu da limamin masallacin unguwar su sunzo neman auren Namsiyya, bayan fira da neman sanin juna aka tsaida ranar biki sati mai zuwa da izinin Ubangiji kuma Alhaji Abdurrahman ɗin shiya ɗau nauyin komai na bikin, kuma anan take suka bada sadaki da kuɗin da zasu isa ayi lefe har naira million biyu.
Babansu Namsiyya ruɗewa yayi ganin tsabar kuɗin da ko a mafarki baitaɓa tozali da suba bare kuma zahiri, banda nabaku ita Allah yasa albarka babu abinda baban yake iya faɗi haka aka watse ran baba fal ƴasa tayi goshi, yana shiga gidan tun daga zaure ya fara faɗin “ke Namsiyya ina kika samo mana irin albarka wannan ɗan kirki ɗan waye a KADUNA. ”
Jin muryar mahaifinta na amsa kuwa tundaga zaure ta sheda cewa yana cikin farin ciki don haka ta fito da murna ta rarbi baban ta faɗin “ Baba ɗan gidan Alhaji Abdurrahman Na'adami ne ”.
“Wai wai wai kace zan zama babban mutum kuma sirikin manyan mutane masu arziƙi da wadata a KADUNA amma ƴar nan Allah yayi maki albarka ”
“ Amin” tace ranta wasai zuciyar ta fayau jin zancen aure ya tabbata da ita da ɗan gidan Alhaji Abdurrahman Na'adami zata zama matar mai kuɗi wacce za a rinƙa tuƙawa a cikin jibgegiyar mota, zagewa tai ita ma tasanar da baba labarin ƙarya akan cewa Areeyan ya mutu kanta yana mata mahaukacin so da irin shaƙuwar da sukai amma bata sanar da kowaba har sai magana ta kankama.
Banda Allah “ kaji ƴar Albarka irin Arziƙi ” babu abinda baba yake faɗa, haka ya damƙa mata kuɗinta a hannu yace taje ta sai duk abinda yayi mata domin kuwa mama ta rantse ta maya babu abinda zatai acin wannan aure, don yanzu ji take tsar ƴarta na mata yawo a zuciyarta musammanma ma da tai bincike taji yadda akai Alhaji Abdurrahman ya yanke hukuncin auren don haka babu ruwan ta aciki, yadda mama tai zuciya haka suma sauran yaran gidan suke zuciya da baikin banda Namsiyya da Baba babu mai maraba da auren.
Namsiyya kwance take asaman yaloluwar katifarta wacce bata da maraba da tabarma saboda yadda ta zama kamar zani, banda nishaɗi babu abinda take, tana ma ɗakin kallon bankwana tana kuma murnar zata rabu da kurkuku ta shaƙi iskan ƴanci na gidan kuɗi mai garwaye da shukokin filawoyi, so take ta sanar da wani wannan abin farin cikin da ya sameta so take ta sanar da wani wannan labari amma bata san wanda zata sanar mawaba don haka ta yanke shawarar kiran Sholy ta bata haƙuri su shirya ta zamemata jagora akan wannan fidimar bikin da za'a gudamar tunda abin ya tabbata manya sun shigo cikin maganar ai sai su hau shi tanda sati ɗaya kamar gobe ne zai zo ”.
Wayarta ta ɗauka ta danna kiran lambar Sholy sai dai kuma bata shigaba sakamakon maganar da madan tai mata koda batajin turanci amma tasan babu kati akace saboda sabawa da tai da jin kalmar idon har babu kuɗi kira a wayar tata, buɗe baki tai da nufin kiran Auwal ta aika sai ta tuno gargaɗin da mahaifiyar ta tai mata akan ta fita daga harkar kowa na gidan middin rana son su zauna lafiya, dole ƙanwar naki tasa ta ɗau mayafinta ta shiga saka takalman roba a ƙafarta ta fice, katin kawai ta sawo na dubu ɗaya ta dawo da farin cikin sauyin da ta fara samu tun tana gidansu, domin da idon zata saka kati sai dai sholy ta turomata ko taci bashi tasa na ɗari sai ranar da rabo ya rantse aka bata kuɗin makarantar boko sai ta biya ko kuma idon mamarsu tai wawuyar ajiya sai ta ɗauka ta biya buƙatar kanta, sai da ta koma ɗakinta sannan ta saka katin tana murna don ji take kamar na dubu goma ta sa abu ga wanda bai sababa.
Tana gama saka katin ta kira Sholy bugu guda tai ta ɗauka kamar dama jira take, “yauwa ƙawata ashe ina cikin ranki har yanzu don ina nan ina zullumin ko bazaki ɗaukaba sai kuma naji kin ɗauka da sauri ”. cewar Namsiyya cike da ɗoki muryar ta wasai babu wata damuwa
“ wayar tana a hannu na dama yanzu zan kiraki don har beep ya shigo , sai kuma ga kiranki kashe sai na kiraki muyi magana”.
“ A a ba sai na kasheba don ina da wadataccen katin da zai isa ko kwana zamuyi ”.
“ To faɗi abinda kike son faɗa ina jinki ”
“ Dama na kira ne na baki haƙuri kuma na yimaki albushir ”.
“ Bar zancen ban haƙuri don ni tuni na haƙura domin da ban haƙuraba ko wayarki ma bazan ɗaukaba bare har na saurareki ”.
“ To ai Albushir ɗin babbane mai girma sai kin bada garon tukwici me zaki bani ”.
“ ke Namsy nifa inada abin yi idon bazaki faɗaba zan kashe wayata ” cewar Sholy cikin ƙaguwa da son jin abinda Namsiyyar zata sanar da ita
Sai da Namsiyya tai murmushi ta gyara zama kamar suna tare kafin tace “ zancen aurena da Areeyan ya tabbata sati mai zuwa za'a ɗaur aure kuma........
Take sauran maganar da take yi ta koma cikin cikinta babu shiri saboda yadda taji tari ya sarke Sholy cikin wayar kafin taci gaba da magana taji ankatse wayar daga can.
Sauke wayar tai tana binta da kallo kamar zataga Sholyn aciki, mamaki da al'ajabi sun hanata aikata komai, kawai sai ta shiga kallon kuɗin dake hannun ta da wanda ta ajiye acikin leda wanda Baba ne ya bata tanajin sanyi a zuciyarta, tana nan tana ta tunanin yadda zata kashe kuɗin har tsawon wani lokaci amma ta rasa meyema rake buƙata kamar daga sama taji an ɗaga labulai anshigo.
Da wani irin sauri da azama ta ɗago ta kalli hanyar shigowar sai tai tozali da fuskar Sholy
“ Ah wai kece da gaske ko kuma idona gizo yake mani ”
“ nice Namsiyya ai na huce daga fishina zowa naina tabbatar da zancenki da gaskene ko kuma wasa kike kinyi ne don mu shirya ” cewar Sholy tana mai zama a gefen katifar da Namsiyya ke zaune.
Gyara zama Namsiyya tai cike da farin ciki da ɗauki na ganin Sholy gaban ta kafin ta washe baki tana cewa “ Babu wasa kuma babu ƙarya a cikin zancena ranar Asabar mai zuwa zan mallaki Areeyan Abdurrahman Na'adami a matsayin mijin aure na ”.
Wani dogon lumfashi Sholy ta sauke kafin ta fara goge zufar da ke bin fuskar ta tana cewa “ lallai ke Namsiyya abin tsoro ce taya daga shiri abin zai kasan ce gaske ina son sanin yadda komai ya wakana kuma ki yiman dallah dallah yadda zan fahinta da kyau don haka inaji me ya faru? ” taki ƙarshen maganar da sigar tanbaya.
Nan take Namsiyya ta kwashe komai yadda ya wakana ta sanar da Sholy har zuwa yanzu da sukai waya
Mulmushi Sholy tai mai sauti tana cewa “ Lallai Namsy dole asara maki kin kai shu'umar mace ko nace kina da sa'ar rayuwa Allah yasa ace gara da akai yanzu me ake ciki, so dame dame zamuyi? ”
“ wannan dalilin shiyasa na kira ki don mu tsara komai ya yi yadda ake so amma kafin muje ki tayani bama mama haƙuri don ta hayaƙa sosai tayi zuciya bataji bata gani”.
Sholy wata irin macece mai tsananin iya magana idon tana tsara zance kamar ana mata wahayinsa don tana bama mutane mamaki sosai kamar suda haka take da magana, wannan dalilin yasa basu sha wata wahala ba wajan sauya ravayin mama har ta haƙura ta sakko daga dokin zuciyar da ta hau, aka hau shirye shiryen biki babu kama hannun yaro sai dai abu ɗaya yake damun su shine yadda zasu shawo kan Areeyan ya sakai jiki suyi komai yadda ya dace batare da mutane Sun zarfi wani abu ba don gudon tonuwar Asirin su afasa bikin, duka kuɗin da aka bama Namsiyya haka Sholy ta tsaya akansu akai masu kisan gilla a wajen fati da shagulgulan sa suka tsara zasuyi, bata bata shawarar sayen ko cokali ba don acewarta ita da zata gidan kuɗi me zata buƙata hatta buta akwai a cikin gidan don haka kawai su fita kunyar ƙawayensu da zasu gayyata ƴan ƙarya.
Anyi duk abinda ya dace kuma anyi komai cikin wadata da kwanciyar hankali ranar Asabar aka ɗaura auren Namsiyya da Angonta Areeyan Abdurrahman Na'adami, kuma aranar a ka kaita inda kuma aranar ne Al'amurra da dama suka wakana.
Da misalin ƙarfe shabiyu na dare, Namsiyya dake zaune asaman gadon ta ta ɗago ta kalli agogo, sai da gabanta ya yanke ya faɗi saboda tozali da tai da abu biyu wato kyau da tsaruwa irin na agogon mai kama da ta zinare, sai kuma lokacin da taga yayi nisa amma angon nata bai shigoba, a hankali ta sauke mayafin dake kanta ta tana ƙarema kanta kallo, sanye take cikin wani ɗan karen leshe mai kama da matiriyal ja da fari anmata ɗinki mai kyau wanda ya amshi jikinta tsaf tsaf, ƙafarta da tasha jan lalle ta sakko ƙasa ta mike tsaye rana kallon ƙofar da take tunanin Tolet ne, tana isa ta buɗe handdile ɗin ƙofar ta shiga da bismillah,
Yo ai da wata irin azama tayo baya tana mai rafka wata irin uwar tsawa wace ta garwaye gidan baki ɗaya, idanu waje take kallon macijin dake ta wanka cikin kwamin wankan dake Tolet ɗin, take jikinta ya fara rawa tsoro ruɗewa ɗimaucewa sukai mata dirar mikiya a cikin zuciyi, jawo ƙofar tai da wani irin ƙarfi ta bugu bam ta daka wani uban tsalle zata hau gadon sai akai rashin sa'a gyalen da ta cire ya taɗeta ta faɗi ƙasa tum!, ƙas ƙafarta ta bada wani irin sauti mai tabbatar mata tayi targaɗe ko ta goce, ga kanta da ya haɗe da ƙaramin kan gadon na wajan hawa, take goshinta ya hau yayi suntum kamar ansaka mata dutse aciki, baiyi jini ba amma ya tashi sosai ga kuma wani irin zafi da yake ratsawa har cikin kwanyarta wanda take ya sakar mata ciwon kai, ƙafarta ko ji take kamar an buga mata taɓarya don ji take kamar ta karye, yunƙurawa tai da nufin tashi wani irin zafi ya ratsata har cikin zuciyarta, don haka babu shiri ta koma ta zauna tana mai rafka ƙarar da take saka ran wani zai jiyota azo abata agaji da ɗaukin gaugawa .
Tayi sa'a don ko rufe bakinta batai ba aka turo ƙofar aka shigo Lateefah ce ta shigo tana cewa “ lafiya zaki cika mana gida da ihu saboda tsabar iskanci ”.
Ganin yadda Namsiyya ta tsure a waje guda tana ta kyarma fuskar ta har da hawaye yasa ta kwashe da dariyar mugunta aranta tace ɗaya kenan bom ɗaya ya fara tashi sauran na nan tafe.
Namsiyya bata lura da yanayin Lateefah ba kamar yadda tashin hankali bai bari taji dariyar da take mataba tace “ ki taimakan don Allah zan mutu yau naga ta kaina maciji a banɗaki ” takai ƙarshen maganar tana jan ƙugu tana nufo inda Lateefahr take tana mata nuni da ƙafarta don wajan har ya fara kunbura,
Da gangan Lateefah ta take ma Namsiyya yatsun hannu amma sai ta nuna bada ganganba,
Itako Namsiyya sai da saki guntun fitsari a wando saboda azabar da taji har cikin kwanyarta, da sauri ta ɗago yatsun tana mai turasu cikin bakinta tana tsotsa saboda yadda sukai ja,
Hanyar Tolet ɗin Lateefah ta bi ta tura ƙofar ta shiga tana murmushi tasaka hannu ta ɗauko macijin wanda ya kasance na roba ne dama tarko taima Namsiyya dashi, ta gaban Namsiyya tazo ta huce ɗauke da macijin a hannun ta har rae kai bakin ƙofa sai ta juyo ta kalli Namsiyya tace “ Anty a rage tsoro don snake ɗin na roba ne asha jinya lafiya, ” sai ta fashe da dariya kafin ta fice tana dafe ciki.
Mamaki da al'ajabi sun hana Namsiyya faɗar komai sai wani irin mugun tunanin da ya mamaye zuciyarta taya zata fara zama a haka tun ranar farko ta fara fuskantar haka to wane irin zama zatai da su kaddai ace suma da nasu shirin a kanta lallai ko akwai lauje cikin naɗi akwai Badaƙala a zamanta cikin gidan nan.
Lateefah tana fita tai karo da yaya Areeyan tana faɗin “yaya ka dawo ".
“ Na dawo Lateefah zanje na amso wayar waccen ƴar duniyar tun kafin ta sanar da wani irin zaman da zata fara a gidan nan don sai ta kwammaci kiɗa da karatu ”.
Yana kai ƙarshen maganar ya tura ƙofar falon ya shiga yana faɗin “ jirani minti ɗaya Lateefah ina zuwa ”
Yana shiga ɗakin ya sami Namsiyya zaune a ƙasa tana latsa waya da alama wani zata kira ta sanar da shi halin da take ciki, don haka da azama ya matso gabanta yace “ Bani wayar ”.
Sai ta miƙamasa tana fashewa da kuka cikin kukan tace “ Dama kai zan kira kazo ka taimakaman tun kafin azaba ta kai ni ƙiyama faɗuwa nai wallahi a hanyar Tolet ”.
“ To ai gani nazo me zan maki,? ”
“ka kaini Asibiti a dubaman ƙafata, wata ƙilama na goce koma ince na karye don ni kaɗai nasan irin azabar da nakiji ajikina. ”
“ Aiko da na kaiki Asibiti gara nai sadaka da kuɗin don ina mai tabbatar maki sai na nuna maki cewa HANGEN DALA ba shiga birni ne ba, ke da samun farin ciki wata ƙila sai a lahira don zamanki a gidan nan kamar zaman mutum a dajin mutuwa ne mai ɗauke da zakuna da kuraye, farin ciki ya fita daga rayuwar ki kin barosa a can waje, bakin ciki kika aura ba wai Areeyan ba don sai na gwada maki kuskurenki don duk lalacewar tsohon zaki yafi ƙarfin kare ya nunashi da yatsa, kuma ko anci birnin kura ba'a bama kare dillanci gida dai gashi kin shigo sai dai bayadda kike zato zaki samesaba, wawuya kawai ƴar kauye mai kama da mayu.
Yana kai ƙarshen maganar ya tura ƙofar falon ya fice batare da saurari maganar da take masa ba