Free chapter · Read without an account

Chapter 19

by Abdulhakim Umar · HANGEN DALA

Page 19




“ lah kama ma nai da gwanin iya soyayya to kiyi gaggawar cire kama don ni gwanine akan soyayyarki, bani da babban burin da ya huce inji kalmarso ta fito daga bakinki kina furtata gareni ”. 
Haka sukai ta fara cikin raha da nishaɗi har suka iso bakin gate ɗin HALAL CHINDENT'S HOME, kansa tsaye ya danna kan motar cikin gidan ya faka inda aka tanaza don Ajiye motoci, suna tsayawa Muheebbah ta fara kiciniyar buɗe marfin motar amma ta kasa saboda motar a kulle take, take ta zuba masa kyawawan idanun ta tace “ mun iso fa me kuma yayi saura ”
“Ina sone zamuyi magana da ke ”
Kafin ta bashi amsa wayar sa ta hau ruri yana dubawa ya ga sunan Dady don haka ya ɗaga da sauri yana karawa a saitin kunnansa 
“ ok Dady, to gani nan yanzu zan iso insha Allah ”. 
Yana sauke wayar ya kamo hannun ta ya yi mata kiss, kafin ya furta “ki kula mani da kanki”
Yana sakinta ta fice da sauri, shi kuma yayi ma motar key yayi ribos ya fice tana tsaye rana ɗaga masa hannu har ya ɓacce ma ganinta, tana juyawa da niyyar shiga cikin gidan taji ance Muheebbah, cak ta tsaya tana kallon mutanen dake tsaye suna mata wani irin kallo mai kama da na zargi, Anty Ainah ce tsaye da Atika da wannan mutumin da akace ƙanen mai gidan ne wato Yahuza sai wata hanshaƙiyar hajiya dake kama sosai da yahuza ɗin da alama dai ita ce mai gidan marayun, 
Dam! Gaban Muheebbah ya yanke ya faɗi don irin kallon da suke mata bana lafiya bane haka kawai sai taji wani irin tsoro ya shiga cikin zuciyarta wanda batasan dalilin saba. 

Takowa sukai har inda Muheebbah ke tsaye su duka huɗun suna mata wani kallo mai cike da ma'anoni Alhaji da akace ƙanin mai gida ne ya fara magana cikin zafin rai 
“ Muheebbaht kin bani kunya kuma kin bamu mamaki don abinda kike yi ko wani yace zakiyishi a nan gidan to zamu ƙaryata soyayya a matsayin ki na mai bada kula da tarbiyya ga yara, kuma soyayyar ma ta shan minti har acikin gidan nan to ya yaranmu zasuji idon suka ganku a haka bama suganine abin damuwaba idon suka aikata abinda suka ga kunayi to wa gari ya waya. ”
Anty Aina ce tace “ wata ƙila don ya bata taimakone abin bazai huceba sai bibiyarta yake ita kuma taƙi ta taka masa birki ”

“To inma saboda taimakon da yayine take jin nauyinsa to ashirye muke da mu mayar masa don ba shi kaɗai yake bayar da wannan taimakon ba ”. 
“ Taya zata iya ce mai ya daina zuwa bayan ya mayar da ita ƴar gata tana hawan mota mai Ac ya kaita inda ranta ya so kunfa ga harda saloon aka kaita Allah kaɗai yasan irin abin da suka aikata. " Cewar hajiyar da ke da wajan 
Wani irin abune yake yawo a zuciyar Muheebbah marar da ɗi take wasu siraran hawaye suka fara bin kumatunta so take tai magana amma sunƙi bata dama abin da ciwo adinda dangantaka da wani bakin wali na marassaji ko da kana acikin masu halin bare kuma ita da baccin yau da tsotsai ya saka yayi mata kiss da hannu babu wani abu da ya taɓa haɗasu, 
“ zan buge maki kashedi ne a yau shima saboda yadda naga kina maida hankalinki wajan aikin shiyasa amma da sai na koreki kuma ko yanzu kika sake yadda kika aikata wani abu makamancin wannan sai na sallameki, don haka ki kama kanki da matsayinki ki zauna lafiya”. 
“ insha Allah zaku sameni mai biyayya a gareku ba zam sake aikata wani abu maka mancin haka ba na gode da tunatar da ni kuskurena da kukai ” Muheebbah takai ƙarshen maganar tana goge hawaye dake kwance a kan kumatunta.
Kamar wacce akace ta kalli ƙofar shigowa sai ga Tahteef ya bayyana ya nufo inda suke a fusace yana huci kamar kumurcin zaki, Dam! Dam!! Zuciyar Muheebbaht ta hau luguden dakan ukku ganin sa a lokacin da batai zatoba ya ma akai ya dawo mantuwa yayi ko wani yasanar masa to wayema zai sanar masa kawai dai dai toni akai ya na isowa ya damƙi hannun ta da ƙarfi inda wani irin shoking ya ziyarci jikin Muheebbaht wanda har yafi na hutar lantarki ratsa jiki. 


KADUNA STATE. 
MiLounion CITY UNGUWAR Tayi tsit bakajin kukan komai sai na police Dock duk da dama ba unguwar da ake hayaniya bace amma wannan tsit ɗin ta wanzu ne saboda yadda dare ya tsala don ƙarfe biyu da mintina a lokacin pm, 

Namsiyya zaune take atsakar ɗakinta ta dafe ƙafa tanata rusa kukan azaba saboda yadda ƙafar tai mata tsami tana ta zugi mai kama da na jan ruwa da kowane sabon ciwo yake mai alaƙa da haka, idon ƙafarta yayi suntum kamar an tura dutse aciki ga yunwa don rabonta da abinci tun kalacin safe don darana ma da aka bata loma biyu tai tace ta ƙoshi saboda yadda tunaninta ke hasko mata ƙatuwar kazar da za'a kawo mata taci alwashin kafa tarihin ta na Amarya da tacinye kaza bata rageba saboda ta dade da cin alwashi duk ranar da ta auri Areeyan to har ƙasusuwan kazar sai ta taune saboda farin ciki akuma kalleta a matsayin Amaryar da tacinye kaza guda babu ragi, to sai gaashi kuma taji kunya domin ita duk tanajin da tai sai gashi ko ɗan kurciya ba akawo mataba bare kaza, shin haka aure gidan kuɗin yake ko kuma ƙiyayya ce tasa ita ba'ayi mataba so take ta fito falonta taga yadda yake da kalar kujerun da akai mata amma ƙafarta taƙi bata dama, ɗan ƙullin tasshin da ke gefenta ne ya faɗo, sai ta kallai ta sake fashewa da wani sabon kukan saboda tuno wahalar da tasha wajen sawo tafarnuwar da tasamasa don acewarta idon ta daka yaji mai tafarnuwa sai yafi daɗi da kazar sai gashi kuma ta Allah ta kasance akanta duk wani hasashenta da tsammaninta ya zama tarihi, kugunta ta fara ja don ɗauko wayar ta ta kira Sholy ta sanar da ita halin da take ciki sai kuma ta tsaya cak tuno da cewa Areeyan ya amsawar sai ta sake Aza hannu aka ta fashe da kuka, sai dai ganin kuka ba nata bane yasa ta fara rarrafe har ta iso falon duhun da ke akwai da kuma rashin hankalin da take ciki ya mantar da ita kallon kujerun da komai ma na falaon don idon ta ya rufe abinci kawai take son gani, inda aka jera kujerun Dany ta nufa da fata kala- kala a ranta, amma ko da ta isa sai ta samu kujerun ƙal suna ta ƙamshin sabinta kamar yau aka kafasu, hanyar kicin ɗin tanufa da rarrafen nara ta tura ƙofar amma sai taji kofar a ƙulle, dogon tsaki ta ja tare da kaima ƙofar duka da ƙarfi wanda dukan yasa mukullen dake jikin ƙofar faɗowa tai saurin ɗauka da hamdala abakinta, hannu na rawa jiki na kyarma haka ta samu ta buɗe kicin ɗin ta shiga sai da tasaki wani shu'umin murmushi gani kyau da taruwar kicin ɗin nan duk natane mallakin ta aurene kuma ya bata sai ta ƙarayin handala tana mai fara dube-duben abinda zata samu ta sama hanjinta, takai tsawon minti talatin tana bincikar kicin ɗin amma komai babu naci ko na sha sai dai duk wani abu na buƙatar gida to ta gansa a ciki wani abin amfanninma sai a gidansu Sholy ta taɓa ganinsa da cikin facebook idon ansaka tallarsa na yin kayan zamanin da ake birga ta ƙarya da su, to ita dai komai zata iya cewa akwai indai na amfanin kicin ne har ma da abinda bata taɓa ganin irin saba dama wanda batasan amfaninsaba. 

Jiki asanyaye babu ƙwari ta baro kicin ɗin ta nufi hanyar fita daga falon ta murza amma sai tajita a ƙulle dole ta dawo saman doguwar kujera ta kwanta tana kukan zuci da na fili, take ta fara tunani a zuciyarta kala kala wai ko dai ban shigo da Bissimillah bane acikin gidan na ranar farko a gidan aurena aceman tazo mani a haka babu wani sauki ta ko ina kar wacce ta zagi sama wannan wacce irin kaddarace mai kama da gahurtaccen yaƙin yunwa da ƙishirwa, Allah kana gani Allah ka sauya masu ra'ayinsu a kaina su rungumeni a matsayin mata sai hawaye zar-zar sai kuma kukan da cikin ta yake shima ya ƙaru wanda ƙugin yunwane, a wannan dai Namsiyya batai bacci ba har aka fara kiran sallar assalatu, da kyar ta samu ta bi sallar a jam'i tunda anaji har cikin falan duk da bata san tawane ɓangare masallacin yakeba ko da aka gama sallar sai ta malale akan kafet ɗin tai lamo kamar mai bacci ba kuma bacci takeba ukubar yunwace kawai tasatayin laushi, sai wajan ƙarfe bakwai da rabi kafin Areeyan ya shigo gidan ɗauke da jok mai kyau dai dai gwargwado da ƙaramar baƙar leda a hannu ya yi sallama ya shiga ɗakin. 

Ta amsa sallamar amma kamar bata amsaba saboda babu wani sautin da ya fita waje bare har mai sallamar ya ji cewar an amsa masa, bai damuba ya ajiye mata kofin da leda a gabanta kafin ya koma a kan gadon ya kwanta ya fito da wayarsa ya kunna Data ya shiga whtsapp, take ko saƙwanni suka shiga tururuwar shigowa wanda mafi yawa ana masa Allah yasa albarka yabada zaman lafiya da zuri'a ɗayyaba acikin auren da yayi, yayi mamakin yadda mutane da yawa suka san da bikin duk da ba gayya akaiba amma sai gashi mutane da dama sinji harma da wanda baiyi tsammanin jin nasuba,. 
Namsiyyah jiki na rawa ta tashi zaune ta hau kiciniya buɗe jok ɗin sai dai tozali da koko ya sare mata duk wani kwarin guwar da tatashi da shi, bakar ledar kuma ƙosaine ciki wanda baifi na ɗari biyu ba, kwakkon ta fara kaiwa bakinta sai dai da sauri ta ajiye kofin tana kallon Areeyan da baima san tanayiba sai ta hau magana a hassale 
“ Haba Areeyan kamar dai babu ɗigon imani a zuciyar ka tun jiya ka fita kabarni baka dawoba da da ƙarar kwana da yunwa ta ga bayana sai dai ka iske gawata, yanzu kuma sai ka kawo mani ruwan kwako haka tsurarsa baba ko sugar, yo ai duk talaucin mutun yayi sabon aure Allah na buɗa masa asha tea da bread a gidan sa bare kuma kai da kake da arziƙin ciyar da duk unguwar nan batare da kaji komai ba ace sabida Allah kwakko zan sha kwakkon ma babu sugar ”. 
“ To ko ba zaki shaba ”. 

Take mamaki ya kama Namsiyya kallon sa take kallo mai ɗauke da ma'anoni, kamar bashi yayi maganar ba ba kuma zata ce bashi ɗin bane,saboda su kadaine bai kuma bar wata alama da zata nuna cewa shi yay maganar ba, 

“ in ban shaba ai sai yunwa tai mani lahani amma kasani ka shiga haƙƙina kuma sai Allah yayi mana hisabi ”. 
Sai ya tashi zaune daga kwancen da yake kamar wanda maganar ta girgiza, amma sai ya hau faɗin “ Alhamdulilllah ashe kinsan cewa Allah zai mana hisabi kinsan da cewa Allah bai yafe haƙƙin wani akan wani amma kika zaɓi ki yiman sharrin da duniya zata tsineman don cikar burinki kawai, kin bani mamaki kuma kin azabtar da zuciyata don haka dole nai amfani da wannan damar ni ma wajen ɗaukar fansar abinda kikai man sai na azabtar da zuciyarki dama gangar jikinki ”. 

Yana kaiwa ƙarshen maganar sai ya tashi ya bar ɗakin 
Maganganun da tai niyyar yi da shi sune suka koma suka bugi zuciyarta sakamakon fitarsa batare da ta gama furicin taba, wani irin abu takeji yana mata yawo a cikin zuciya , hakan yasa ta kasa cin ko ƙosan da ƙamshin shi yake mata shigar burgu a cikin hanci, tana nan a haka har tagaji ta sakko ƙugin da cikin ta yake mata yasa ta jawo ledar ƙosan ta haɗa da kwakkon da babu sugar ɗin taci don kare kanta daga cutar olser, wani murmushi ne ya subuce mata tuno da yau ne ƙawarta Sholy zata kawo mata ziyara da kuma ƙanwarta da zata kawo mata sauran kayanta, Zumuɗi ta fara tare da jiran jin kwankwasa kofa amma shiru har shabiyu ta rana ta gota babu wanda yazo, tana Ahaka Areeyan ya shigo duk fushin da takejin tanayi da shi sai ta nemesa ta rasa saboda wani irin turare da ya saka mai sanyaya zuciya da duk ran wanda ya shaƙi ƙamshin ya yi kyau sosai kyau irin wanda ba sai anfito ance masa yayi kyauba saboda abin afili yake kuma a bayyane, sanye yake cikin wata dakkakkiyar shadda kalar kwaiduwar kwai ɗinkin ya amsheshi yasaka hula ƙube mai kalar shaddar amma ita ansaka wasu nau'ikan zaruruwa don ƙawata hular da su ya saka takalman fata na (Bunfalo) baƙaƙe masu gidan ɗan yatsa ba wata kwalliya yayiba ta azo aganiba amma kuma sai yayi kyau na azo agani har aɗau photo, ta shagala da kallon sa har bata san sadda ya isa wajantaba ya tsaya gabanta, yana mai kallon nata shima wai don taji kunya ta ɗauke idonta amma bata samma yanayiba sai da ya fura mata iska a cikin idon ta kafin ya samu taja wani dogon lumfashi tana kallon sa tace “ mijina na kai na Allah ubangiji ya kyaremaka kyanka kana da kyau kuma kana da kudi kaji daɗin duniya ”. 

“ ke ya isa ba abinda nazo ji kenan ba zowa nai na sanar dake zan huce mixeco zanyi waya guda ne acan idon na dawo zan biya ta ghana don canma akwai wasu kaya da zani ɗaudo ta jirgin ruwa zuwa legas, ko mai zaki buƙata ki nemi Lateefah zataji da komai ”. 
Yana gama faɗa ya juya da niyyar ficewa 
“A'a Areeyan karkayiman haka wallahi ni ina sonka zan zauna da kai ko a ina ne duk abinda nayi nayine don na sameka ka kalleni da idon rahama ka zauna mu fuskanci juna. ”

“Bani da wannan lokacin yanzu don haka idon na dawo munyi magana sai na dawo ayi man addu'a ” ya kai ƙarshen maganar yana murmushi mai nuna ma'a noni da dama atare da shi kafin kuma daga bisani ya fice, 
Yana barin gidan motar Sholy na faka wa a bakin gate ɗin, takeko suka fara hayaniya da masu gadin gidan don ance dasu kada kowa ya zo subarshi ya shiga ko waye, Lateefah dake zaune a harabar gidan tana waya da sabon saurayinta taji kamar hayaniya abakin gate , “Ina zuwa don Allah zan kiraka yanzu one minit, " tana gama faɗa ta katse wayar ta fita tana faɗin wai ƴar wane shegence take mana hayaniya yanzu da fara Safiyya a ƙofar gida......
 
Ganin danƙareriyar mota ya shedama Lateefah cewa badai daga gidan su Namsiyya ba sai dai ko daga wani wajan suke don haka sai ta sassauta kamannunta na rashin mutunci tace “ baiwar Allah daga ina ban wayekiba?, " tai tanbayar tana ƙarema Sholy kallo ita da motar da ta hau don bata taɓa kawowa aranta Namsiyya na da kawa mai hawa mota ba don kamanninta basu yi kama da hakan ba 
“ yau wa baiwar Allah gara da kika zo don naga da alama masu gadin nan naku duk ƴan wahala ne wajan Amarya nazo amma sun hanani shiga sunana Sholy kuma babbar aminiyar Namsiyya ”. 

Ɗaure fuska Lateefah tai jin abinda Sholyn ta faɗa don haka sai ta wayance da cewa “ Ayya nasan bakuyi wayaba ai da ta sanar dake yau ƙarfe biyar motar su ta fita kuma filin jirgi suka nufa yanzu ai sun hau hanyar maxico ”. 
“ maxico kuma ” Sholy ta furta fuska ɗauke da matsanancin mamaki tana mai saƙa abubuwa sosai a ranta 
Ganin ta hau duniyar tunani Lateefah tace “ honymoon suka tafi sai nan da wata guda zasu dawo don haka a gaida gida ” tana gama faɗa ta koma ciki mai gadi kuma ya sake kulle kofar ya koma mazauninsa . 
Sholy ko sai ta sami kanta acikin farin ciki jin cewa suna honymoon amma kuma tuna wa da jiyafa suka kawo Namsiyya gidan nan kuma kowa yasan Areeyan bai sonta yanzu kuma ace suna honymoon to yaushe ya siya masu visi ɗin yaushe komai yau shirhu tsakaninsu da har zai kaita honymoon kai gaskiya ban yarda ba da sake sai dai idon wani abun ne yake faruwa, amma yadda nake da Namsy dole zata sanar mani idon zasuyi tafiya bare kuma tafiya irin wannan mai daɗi ta farin ciki ta gayama dangi suyimaka addu'a gaskiya da sake, amma zata koma gida ta sake shiri ta dawo don tasan gidan nan ba lafiya ba, musamman ma da ta tuno da irin alƙawarin da Namsiyya ɗin tai mata ranar farko idon anwatse anbarta, uhmmm! Tai wani irin yanayi da bakinta kafin ta koma cikin motar ta ja tabar wajan. 

Sai da akai sati Lateefah na Azabatar da Namsiyya da yunwa babu wani sauyi kafin zuwan wata rana da sukai faɗa ranar Namsiyya na zaune A ɗaki tayi tagumi tana tunanin duniya sai ga Lateefah ta shigo tana faɗin ga abinci 
Jiki na rawa Namsiyya tai caraf da hannun Lateefah ta karɓi abincin tana ƙare masa kallo garin kwakine akajiƙa baima ko jiƙuba aka zuba yaji da gishiri ko mai babu, wani irin kallo Namsiyya taima abin da ake kira abinci kafin ta kalli Lateefah tace “ yanzu tsakanin ki da Allah idon aka baki wannan abincin zakici ”. 
“Aaa wace ni ai wannan abinci yafi ƙarf na sai dai ku ƴaƴan malam shehu, don ni wallahi naci wannan abincin sai na kwana medecal center ansaman ƙarin ruwa ”. 
“Amma saboda rashin imani sai ki bani. ”

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol