Free chapter · Read without an account

chapter 22

by Abdulhakim Umar · HANGEN DALA

Page 22



            ABUJA 
Gidan marayu sai da Tahteef ya haɗe jikinsa da na Muheebbaht ya rungume kafin ya soma faɗin “ kina lafiya babu abinda ya sameki ko? ” 
Eh ta faɗi a hankali tana kallon sa cike da tausayawa saboda tsabar sonta da take iya gani a cikin idanunsa, saboda ba ya ɓoyuwa ko ba ita ba mutane da yawa za su iya gane hakan ta hanyar kallon ƙwayar idon sa idon yana tare da Muheebbaht . 
Mai da kallon sa yayi inda su yahuza suke kafin yace “ ita ɗin rayuwa tace kuke son tozartawa, don haka dole ku karɓi hukuncin dai dai da Abinda kukai Acp maza ku shigo ”. 
Tun Kafin ya ida rufe bakinsa motocin ƴan sanda biyu suka shigo suna gama paking suka tunkari inda su Tahteef ɗin suke a tsaye. 
“ Ga sunan sunci zarafin matar da zan aura a tabbatar da an hukuntasu ni banma san wane irin hukunci ya kamata da suba Amma kai kasani kayi abinda ya dace domin wallahi suka sake aibanta mani mata sai na datse masu harsuna ta yadda ba zasu sake maganaba bate kuma har suyi ƙoƙarin aibata wani ”…

“ Angama ƴallaɓai” Acp ɗin ya faaɗa yana tunkarar su Anty Ainah da Atika da yahuza hannunsa riƙe da hangcock. 
“ A'a idon hakan ta faru bazsn yafema kaina ba suna da daraja da kima a wajena ko sunyi mani abinda yafi haka basu cancanci hukunci ba don sun isa suna da iko dani don haka ka hanasu taɓa kowa a nan. ”
Cewar Muheebbaht cikin kuka 
“ A'a Muheebbaht ba su cancanci a barsuba dole sai an hukuntasu, ai sun mayi sa'a na raga masu saboda ke idon da wani ne can da ban da da hannuna zan sare masu harsunansu kuma duk da haka zasu san ko ni waye anan gaba don bana yafe cin zarafi akai na ”. 
Da sauri Muheebbah ta duƙa a gabansa tana faɗin “ zasu gyara amma ka barsu ko don ni ”. 
“ zan rabu da su akan sharaɗin ba zaki sake ko minti Daya a nan ba bare kuma kwana zaki bini mu tafi gidan mu”
Wani irin kallo Muheebbah tai masa tana miƙewa da sauri tana faɗin “ me hakan yake nufi kenan ban fahimtaba ”. 
Zaki fahimta yanzu da zarar bayi maki bayani yanzu zan kaiki ki gaida iyayena daga nab kuma zan kai ki garinku da kaina har gida daga bisani kuma sai na zo da kuɗin aure don ba zaki sake ko sati guda batare da kin zama mallakina ba don haka muje ”. 
Yakai ƙarshen maganar yana kama mata hannu yasakata a motarsa da ta kasance Bugatti veyron wacce kuɗinta zai kai $3.4 million a kuɗin naira kuma zata kai ( N1,290,400,000) ko a mafarki Muheebbaht bata taɓa mafarkin mota mai kyau da tsada irin wannan ba bare har tasaka ran zata hauta. 
Shigowa yayi a mazaunin direba ya zauna ya ja motar sukabar wajan dama jikin Muheebbaht a gyare yake don haka wani super market ya nufa da ke 27 Alexandara street ABUJA ya siya mata doguwar riga dock blue da Hijabi itama dock blue acikin wajan akwai ɗakin sauya kaya don haka a nan ta sauya kafin ta fito suka sake hawa hanyar gidansu Tahteef dake JABI. 
Da misalin ƙarfe biyu na rana suka isa ƙofar gidan, tun da suka shigo unguwar hankalin Muheebbaht ya bar jikinta ya koma akan manya manyan gine ginen dake yankin har suka shuga harabar gidan inda ma 'aikata keta sintiri ɗauke da bindigu a hannayensu, babu kowa a cikin falon sai Sanyin Ac da kwanshin turaren wuta ko ina shaf sai sheƙi da walainiya wajan yake tamkar da zinari aka ƙera kayan adon falon. 
“Zauna bari na fito da mamana ku gaisa ” ya kai ƙarshen maganar yana hawa stop ɗin da zai sadashi da saman benan dake falon, kafin ya fito tuni wata mai aiki ta cika gaban Muheebbah da kayan ciye ciye tun daga kan abinsha har zuwa farfesun kaji da na ƴan ciki ga abinci har kala ukku masu kyau a ido. 
“ lale-lale maraba da matar ɗana ” cewar wata hamshakiyar hajiya dake sakkowa akan benan tana ta washe baki fuskarta ɗauke da fara'a da kwalliya ta alfarma tana sanye cikin wata irin shadda kanfala ɗinkin agadaz tasha sarƙa da ƴan hannu da ƴan kunne duk na gold sai walainiya take musamman ma haƙorin makkar dake manne da haƙorinta mai sheki da ɗaukar ido. 
Sinne kai ƙasa Muheebbaht tai tana wasa da yatsun hannunta 
“ Ankawo maki lemu ko basuyi maki ba a canzo? ”
Hajiyar ta faɗa tana mai zama akan ɗaya daga cikin kujerun dake falon. 
“ A'a komai yayi Hajiya ” cewar Muheebbah tana saukowa daga kan kujerar ta zuƙunna ƙasa tana faɗin “ Barka da wuni hajiya da fatan mun sameku blafiya ” 
“ lafiya lau yarinyar kirki, koma akan kujerar ki zauna ”. 
“ Lafiya lau hajiya zan zauna a ƙasa ”. 
“Amma me yasa ?, ki daina jin kunyata domin uwa nake a wajanki ”
Nima uwa na ɗaukeki hajiya shiyasama na zauna a ƙasa domin tarbiyar da akai mana kenan idon babba na sama to mu ƙasa muke zama. 
“ kaji ƴar kirki amma Tahteef na tayaka murna da kasamo yarinya mai tarbiya kamar wannan Allah ya tabbatar mana da Alkhairi. ”

“ eh inajinka, ok to yanzu mitina kaɗan sun isa na zo inda kake gaisawa kawai zanyi da surukata ”. 
Yana isowa nan ya kashe wayar ya zauna kusa da hajiyar yana mai saka wayar a cikin aljihun rigarsa ta shadda kalar kwaiduwar kwai 
“ Muheebbaht ga mahaifina da najima ina baki labari ”cewar Tahteef yana maida kallon sa kan mahaifin nasa yace “ Baba ga Muheebbaht ita ce wacce zan aura ”. 
“ Barka da zuwa yarinya ya hanya ”
Zumbur Muheebbaht tai ta miƙe tana cewa “ mugu azzalumin banza ashe zan sake sakaka a ido na mayaudari maciyi amana amma dai kaji kunya wallahi. ”
“ mene? Cewar Tahteef yana miƙewa tsaye gami da zaro ido waje cikin mamaki da al'ajabi yace kina a hayyacinki kuwa shiɗin mahaifina ne. 
“ ni ko nasan abinda nake faɗa kuma kasani waɗannan kalmomin sunyi kaɗan wajan jifar mahaifinka da su don shi ba mutun bane azzalumi ne marar imani da tausai na tsanesa kuma kaima na tsaneka nayi nadamar saninka da nai a rayuwa ta Tahteef ”. 
Sai ta fashe da kuka 
“ Tahteef mahaukaciya ka kawo mani gida da sunan matar da zaka aura ”. 
“ Ni ba mahaukaciya bace ina da hankali kuma nasan ban zalunci kowa ba kai kuma fasiƙine...... 
Da sauri Tahteef ya toshe mata baki yana faɗin “ na gaya maki shiɗin mahaifina ne ”. Ya ƙarashe cikin ɗaga murya yana huci don har idanuwansa sunyi jajur da su 
“ Naji shi mahaifinka ne amma ai uba bafin uba yayi ba ko don bakasan abinda ya faru da nawa mahaifinba, mahaifinka shi ya rosa farin ciki da walwalar gidan mu don haka wannan bai cancanci a kirashi da ubaba, ” nan take ta sanar da Tahteef abinda ya faru a garinsu charanchi.
Sai ta kalli Alhajin ta ɗaura da faɗin “ kaimana alkawarin baba zai dawo yana ina yanzu kasa anyenke masa hukuncin kisa akan abinda baisan an aikataba ka salwantar da rayuwar ƴar uwata Azima me mukayi maka ka cutar da mu don haka na tsaneka kai da Ahlin naka kuma Allah zai sakamana don Haƙƙinmu ba zai barkaba ”. 

Wata irin zufa ce ta fara karyoma Alhaji sulaiman gidan iko tabbas ya shedata sai dai baisan yadda zaiyiba a wannan gabar don haka zaro idanuwa waje kawai yake yana gumi kamar wanda ya haɗiyi kunama. 

Inda Tahteef yake tsaye Muheebbaht tazo ta tsaya ta kallesa tace “ wannan shine mahaifinka kuma wanda yafi so kai ne, zan iya cewa bakasan tsanaba sai so don haka yau zakasan meye tsana kuma meye ƙiyayya, bana son ka na tsaneka kuma bazaka sake sakani a ido ba har tsawon rayuwarka ka manta da ni ”. 
Tana gama faɗar haka ta nufi hanyar fita 

Da wani irin sauri Tahteef ya sha gabanta yana cewa 

“ Muheebbaht ki saurareni kiji Laifin ba nawa bane na mahaifina ne karki hukuntani akan laifin da ban aikata ba kinsan ina son ki ina ƙaunar ki a kusa dani..... ”

“ ya isa haka Tahteef laifin da kake cewa ba nakaba to irin haka ce ta faru ga mahaifina da wannan tabon aka binnesa, saɓanin kai da mahaifinka ne yayi laifin muna san iyayen mu so mai tsanani muna karesu da dukkan ƙarfinmu babu wanda zai so hakan ta faru da shi sai dai ƙaddara, amma kai m”ahaifinka ne kuma jininsa yana gudana a naka jinin don haka ko kaso ko baka so ba akwai alaƙa mai girma da ta haɗaku kuma babu wanda ya isa ya raba kai da shi abu ɗaya ne. ”

“ Naji ni da shi abu ɗaya ne ki hukuntamu yadda ranki yayi maki Muheebbaht zan tsaya a bayaki har na tayaki ɗaukar fansa domin kuwa zahiri an zalunceki, ki zama mai adalcin a rayuwa kar ki tafi ki bar zuciyar da ta mutu akanki zan ɗau ko wane irin hukunci da zaki gudanar a kainaa amma ba zan jure rabuwar mu ba, don bugun zuciyata da naki yake tafiya, ki taimakama ruhina kar ki barni da ciwon sonki ”. 

“ kayi haƙuri Tahteef bana son ganinka kana tuna mani da abinda ya huce na barka da mahaifinka yana da kuɗi kuma yana da iko da matsayi zai iya sayamaka farin ciki idon yaso ”. 
“ A'a Muheebbaht karkice zaki gujeni ina buƙatar ki a cikin rayuwata ”. Ya faɗi yana marairaicemata kamar zaiyi kuka 
“Na tsaneka na tsaneka Tahteef ka rabudani ”
Sai ta fice daga cikin gidan aguje tana kuka 
Kasa binta yayi ya tsaya tana kallon mahaifin nasa kafin yace “ Dady kaga abinda son zuciyarka ya haifar Ko ”. 
Dadyn ya kasa cewa uffan sai zare idanuwa kawai yake jikinshi yayi sanyi 

Muheebbaht na fitowa daga cikin gidan ta nufi titi a guje tana share hawaye 
Keeyy! Kakeji ƙarar jan birkin wata ƙatuwar mota PRADO da ta kusa yin karo da Muheebbaht don ma Allah ya kiyaye mai motar ba gudu yake ba, da sauri Abbas dake tuƙin motar ya fito waje yana kallon inda Muheebbaht take tsaye tana zare idanuwa, ya isa wajan tare da faɗin “ sannu baiwar Allah kina lafiya dai ko da fatan babu wani abun da ya sameki. ”
Madadin ta bashi amsa sai ta fashe da kuka cikin kukan take cewa “ pleass half me ” 
“Da wane irin abu zan taimakeki ”. 
“ so nake ka kai ni tasha ban san hanya ba ”. 
“ Amma me yasa zaki bar garinku me ya faru da ke ne? ”. 
“ kaga malam bani da lokacin amsa wannan tanbayoyin naka ina da abinyi idon ba zaka iya kai ni ba kabarshi ka tafi zan nemi wani ”. 
Sai da ya ƙare mata kallo daga ƙasa har sama baiga wani abin aibu a tare da ita ba don haka ya buɗe mata motar yana yi mata nuni da hannu alamar ta shiga. 
Bata bata lokaci wajen yin wani tunani ba ta hau motar ta zauna a gidan gaba inda ya yi mata nuni da ta shiga. 
Shima zagayawa yayi ya zauna a gidan gaba yayima motar key suka nausa a kan hanya suna fara tafiya ya rage sautin rikodar motar dake tashi da karatun suratul ma'idah, sai da yaga alamar sanyin Ac ɗin motar ya fara tasiri akan Muheebbaht kafin ya kalleta yace “ Baiwar Allah ya sunan ki? "
Muheebbaht ta bashi amsa atakaice. 
Sai da yayi shuru na wani lokaci kafin yace “ wane gari zaki je kuma me yasa? ”. 
Ganin yadda yayi maganar da wani irin salo mai ratsa zuciya da sanyaya rai yasa ta sami kanta da bashi amsa
“ Katsina zani kuma dalilin zuwa can ne ma haifata?. ”
Zaiyi magana ta tari lumfashinsa da faɗin 
“ pleass ka ajiye ni anan zanje na ɗauki kayana ”. 
Sai da ya tsayar da motar ganin zai wuce inda take nuna masa kafin yace “ A gidan marayu kuma zaki ɗau kayan? ”. 

“ Eh anan zani ɗauka kafiye tanbaya kamar ɗan jarida”. 

Sai da yayi murmushi kafin yace “ kuma ni ba ɗan jarida bane ki yi sauri ki fito domin nima ina kan hanya yanzu garin zan bari ”. 

Sai da ta ɗan ƙago murmushi wanda bai kai cikin zuciyarta ba kafin tace “ kayi haƙuri na ɓatamaka lokaci kuma ban san uzirin ka ba ka gafarceni zaka iya tafiya zan hau tasi ta kai ni idon na fito na gode sosai da taimakon da kayi mani ”. 

Dam! Zuciyarsa tai wani irin bugu da bai san dalili ba haka kawai sai yake jin abin da ta faɗa bai kamata ba to ya zaiyi shifa wani abu yake ji a ruhi da zuciyarsa kuma duk a kanta ba wannan bane karo na farko da ya fara son mace ba hakan yasa ya ɗau haske akan son tane yake ƙoƙarin shiga zuciyarsa sa. 

“ zan jiraki babu damuwa amma kiyi sauri ”. 

To kawai ta faɗi tana mai fita daga motar ta shiga cikin gidan marayun bata sami kowa a harabar wajen ba sai da ta gama haɗo kayanta tas zata fito kafin tayi kayo da Atika. 
Nan suka yi bankwana tai mata sallama ta fito tana shiga motar ya ja suka nufi hanyar KADUNA STATE . 
Kasantuwar Abbas mutane mai kirki da barkwanci yayi nasarar saye zuciyar Muheebbaht har ta Amince suka tafo a tare yana tayi mata fira har ta saki jiki da shi, sai da suka shigo garin KADUNA ta tsaya a gidan mai na Shema ya ƙara mai kafin ya sayi kayan tsaraba irin su Abarba gwanda da Ayaba da mangwaro masu yawan gaske, duk da haka sai da ya tsaya a zariya ya sayi mazan kwaila tunawa da yayi da cewa mahaifiyar sa hajiya Larai tana son mazan kwaila. 
Bai sake tsayawa ba sai a garin Charanchi yaso ya kai Muheebbaht har gida amma tace dole ya ajiye ta a AKah don bata son ƴan garinsu su giskanci wani Abu game da wannan danƙareriyar motar, sai da ya azamata duka kayanta a Cikin wata kekenapep da zata kai mata har ƙauyen fulani, sai da suka koma gefe ɗaya sukai magana kafin taimasa godiya sosai sukai sallama bayan yabata duk wani abu na tsarabar da ya saya da sunanta. 

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol