Free chapter · Read without an account
Chapter 24
Page 24
KATSINA STATE NIGERIA
Ba ƙaramin farin ciki Abbas yayi ba ganin Muheebbahr da ya fara kamuwa da son ta a matsayin zabin mahaifiyar sa, kuma ita ma haka a wajanta ta yi farin cikin samunsa a matsayin miji.
Labarin Abinda ya faru da su Tahteef ya riskesu, Muheebbaht tayi farin ciki da Allah ya bi masu haƙƙin mahaifinsu tun a duniya, kuma gefe ɗaya wata shari'a nace tana jira wacce zance sai A lahira.
Ba ayi wani sa biki ba kawai rana aja aka sha shagalin biki na Alfarma kuma na manya domin kuwa har da mabuɗin mota a cikin lefen Muheebbaht, bayan biki suka tare a katafaren gidan Abbas dake Abuja Acikin estate ɗin Ɗantata da ke kubwa.
Shagari lowcous
Mahaifiyar Ahanah tana zaune tana kallon tashar TRT sai ga wani mummunan labari ya fara gudana a cikin TV ɗin kamar haka.
A yau Alhamis 25 ga watan September na shekarar 2025 gwamnatin ƙasar Sweethearland ta yanke ma wata ƴar Najeriya mai suna Ahanah Idiris hukuncin zama a gidan kurkuku na tsawon shekara goma sakamakon kamata da akai da laifin safarar miyagun ƙwayoyi A filin jirgin ƙasar. sai kuma labari na gaba mun samu gawar...
Jigib ta yanke jiki ta faɗi don jininta yayi mugun hawa, da taimakon yaranta maza manya aka kaita Medecal CENTAR.
Ko da ta farka babu abinda take sai kukan nadama da dana sani wanda ba zai haifar mata da komai ba faɗi take “ oh ni maman Nura naga takaina, kaico da uwa irina, da kai na na jefa rayuwar ƴata cikin masifa da bala'in da bazata iya fitar da kanta ba haka kawai tana zaune ɗakin mijinta tana bautar aure son duniya da neman hutu ya jefani a masifa, gashi sai nadama nake marar amfani, tabbas na yadda wani jin daɗin masifa ce kuma na aminta da cewa kaddara darasi ce, Allah, ka fito man da ƴarta..... ”
Sai kuka ya ci ƙarfin ta.
Damuwa da tunani sukai mata yawa hakan yasa ciwon ko sauƙi baiyi ga ciwon zuciya ga na hawan jini, yaronta Nura shine yake kula da ita kuma da kuɗin hannunsa ya ƙare babu yadda za suyi dole ya kwasota suka koma gida, tunda babu wani sauyi a jikinta kamar ba Asibiti suke ba babu wani cigaba sai asarar kuɗaɗen da akeyi kawai.
Ko sati basuyi da dawowa gida daga Asibiti ba Aka kawo masu notis na tashi daga gidan don kuɗin hayarsu ya ƙare, sati na cika a kazo da samari suka watso da kayansu waje suka kulle gidan cike da rashin mutunci.
Nan maman Ahanah ta sake shiga wata damuwar saboda ta sayar da tsohon gidansu a bikin Ahanah da yaƙinin zata mayar da wani bayan Ahanahr ta tare ita kuma sannan ta dawo daga saudiyyar da ta fara shirin zuwa, wacce aka aje magana bayan biki fa sati ɗaya za a fara shirin tafiyar gadan gadan, ashe ashe babu rabon zuwan.
A wani gidan makwabtansu suka kwana kafin kuma da safe mai gidan ya sanar da su su nemi mafaka don shi ba zai zauna da irin su ba.
Rasa mafaka da wajan zama yasa maman Ahanah fashewa da kuka mai ban tausai sai dai kafin wani ya lallasheta sai ga ƴan sanda sun zo neman nura bagatatan, suka kuma yi nasarar kamashi suka tafi da shi.
Cikin tashin hankali da ruɗani mama ta bi bayansu,
Sai bayan da taje Sitation jin ba asin abinda ya yi aka shedamata cewa ankamashi yana sayar da kokin wato ( powder iblis) kuma baiyi gardama ba ya amsa laifinsa.
“ kai ba dai ɗana ba wallahi sai dai idon sharri akai masa” ta faɗi tana isowa bakin kofar sell ɗin da Nuran yake ciki tana kuka.
“ Babu wanda yayi mani sharri mama na aikata kuma amsa laifina don nasan gara zaman gidan yari da irin rayuwar da zamu shiga a nan gaba, kuma ina mai sheda maki cewa samir ne ya sakani a harkar bayan na tanbayesa wai ina yake samun kuɗi haka da yawa cikin ɗan lokaci sai yaceman nayi masa aƙawarin babu wanda zan sanar mawa kuma idon ya faɗaman nima zan taya shi sayarwa nan take nayi masa alƙawari, kuma ko da naji cew sayar da koƙin yake ban razana ba saboda nasan zan sami kuɗi, mama komai ya faru a rayuwar mu ke ce sila tunda baki mana tarbiya da komai ba sai san duniya da abin cikinta ga shi munbi duniyar ta hau saman mu ta kashe mana rayuwa, don dama masu iya magana sunce duniya kamar dokice idon ka hau kanta zata kaika inda kake so inko ka bari ta hau kan ka to zata kasheka gashi da da fari munji dadi kuma munyi dariya amma daga ƙarshe bakin ciki da kunci sune suka wanzu ga rayuwar mu kije ki sauya halinki ki sake ma sauran yaranki maza hali idon har zaki iya don abinda ya samemu darasi ne ga mai hankali kuma iznah ga mai hali irin naki kaico da uwa irinki ”.
Sai ya kalli gabas yana ƙoƙarin mayar da hawayen dake bin fuskarsa.
Jiki babu kwari mama ta baro sitation ɗin tafiya take tana kuka tana tunanin yadda ta zama hanyar tarwatsa rayuwar yaranta, a haka har ta iso bakin titi bata dubaba ta kutsa kai, duk ƙoƙarin da mai motar zaiyi yayi amma bai iya kaucemata ba dole yabi ta kanta inda ko shurawa batayi ba ta ce ga garinku nan, ta tafi da tarin buruka a rayuwarta, ta tafi da tarin damuwa a zuciyarta, iyakar ta duniyar kenan ta ta taƙare sai girbar abinda aka shuka a lahira.
Sweetherland
Daga kotun ƙasar dake babban birnin ƙasar Sweetherland wato Zurich Ahanah ce take fitowa hannayenta saƙale cikin hangcock gandirobobi guda biyu sun tasata gaba, sai ga wani police yazo kusa da su yana cewa ga wannan sakon in kin isa masaukin ki sai ki karanta.
Amsar takardar tayi batare da tace komai ba ta riƙe a hannun ta har suka isa inda motar take, da kyar take iya buɗe idanuwanta saboda tsabar kukan da tasha ta fara karanta takardar a cikin motar kamar haka:
Slm
Barka da zuwa kurkuku
Wannan sakone daga Mijin ki na da wato Samir, ina mai baki haƙuri akan halin da kika sami kanki, ko nace kika jefa kanki, don kar kiyi tunanin wanine ya saki a wannan hali domin son duniyarki ne ya kawo ki a matakin da kike yanzu.
Gaskiyar zance ban taɓa soki ko na daƙiƙaba abunda yasa na shigo rayuwar ki shine A kwai wata matar ubangidana da ake nema saboda safarar miyagun ƙwayoyi, tana ta ɓuya a gari ta kasa samun saƙat a rayuwar ta, ana tsaka da haka na sami poton ki a facebook kamar ku ɗaya sak da wannan matar ubangidan nawa, A gaskiya kanki na fara sanin cewa ko wa na da mai kama da shi a duniya.
Ni na bama wannan ubangidan nawa shawarar a maye gurbin matarsa da ke.
Sai yace ta yaya?.
Na ce masa amin cewar sa kawai na ke so.
Yace ya bani dama kuma yayi mani Alƙawarin kuɗi masu tarin yawa.
Da kuɗin ne na zo gareki don na samu duk wani bayani da nake nema a cikin facebook, don haka na raba ƙuɗin biyu na ɗau rabi rabin kuma nayi fidima da su har na samu kika rabu da mijinki kika aureni.
Ina maki fatan zaman lafiya a kurkuku da kuma godiya akan kuɗin da kika zama sanadiyyar samun su gare ni.
Sai an jima a kwana lafiya mai son duniya.
Da sauri ta duƙunƙune takardar ta jefar da fashe da kukan da ba zai bata mafita ba.
ABUJA NIGERIA
Bayan shekara Huhu.
Abbas ne yake sakkowa daga saman matakalar benen jirgin sama da ya sauka a filin jirgin ( Nnamdi Azikiwe Internasional AIRPORT) dake a birnin tarayya Abuja sai mahaifiyar sa a bayansa tare da matar sa Muheebbaht wacce sai da na ƙura ido sosai kafin na ganeta tsabar fari da ƙibar da hutu da kwanciyar hankali suka saukar mata da su.
Dukkan nin su suna sanye ne a cikin uniform na aikin hajjin da suka gabatar a wannan shekar.
Da gudu ma'aikatan da ke jiransu suka fara gudu wajan buɗe masu motacin da suka zo da su.
Mota biyar ce take tafe akan titin filin jirgin suka nufi hanyar unguwar kubwa inda katafaren gidan Mr Abbas yake.
Duk wata nasara a rayuwa da ake fatan samu to wannan Ahali sun sameta domin Alhaji Abbas shine Maganar na Refineries dake Abuja yana tare da mahaifiyar sa da matarsa Muheebbaht wacce Allah ya azurta ta da haifar yara biyu duk mata aka sa masu sunan Basira da Azama Ana kiransu da Islam da Ikram.
Muheebbaht ta ci gaba da karatu har ta kammala kuma ta samu aiki a gungiyar da ke kare haƙƙin mata da yara ƙanana wato ( UNISEF).
Sau ukku suna zuwa aikin Hajji, Ayanzu haka Ahmat yana saudiyya yana karatun larabci.
Muheebbaht na zaune akan kujerar roba dake a garding ɗin gidan tana shan Icecrem taji an rufe mata idanu ta baya taji hannun na yara ne amma kuma tana juyawa sai taga Abbas yana murmushi, can kuma taji dariyar yaranta suka tashi daga zuƙunnen da suke suka rungumeta suna mata cakulculi, babu shiri ita ma ta fashe da dariyar,
Islam na ganin haka ta amshe Icecrem ɗin dake hannun ta ta ruga ta nufi cikib lambun aguje, ganin haka itama Ikram tabi bayan ƴar uwarta suna dariya cike da farin ciki, ai itama sai ta mara masu baya suka fara zagaye garding ɗin suna wasan tsere.
Kaɗa kai Abbas yayi yana murmushi shima ransa fal farin ciki da annashuwa.
Arziƙi ya sauka garesu talauci kuma ya ƙaura don sun koresa da ƙarfin zuciya da kuma Addu'a.
Masha Allahu lakuwatta illabillah
Ƙarshe
Anan na kawo ƙarshen littafin HANGEN DALA, Darasin da ke cikin sa Allah ya bamu ladar sanarwa Allah kasa ayi amfani da shi wajan gyara rayuwar Alumma, akasin haka kuma Allah ya yafe mana.
ABDULHAKIM UMAR ƊAN BUGAJE ke maku fatan Alkhairi.
�***.
Sai mun haɗu a sabon littafina mai suna ƘAZAFI. Insha Allah nan kusa