Free chapter · Read without an account
MATAR GIDA PAGE 88
by Maimuna Bala · MATAR GIDA
*MATAR GIDA BOOK* 2
*SHUUKRAN* /022
P88
Washe gari da safe misalin ƙarfe goma da wasu mintina su Hajiya Zulfa'u tare da Alhaji Babah suka nufi gidan Mama,Hajiya tare da su Hajiya Biklisu ne suka shiga yayin da Alhaji Babah ya tsaya a soro tare da Baffah kasancewar har sannan Baffah bai koma ba saboda jikin Mama,har cikin ɗakin Mama su Hajiya Zulfa'u tare da Hajiya suka shiga inda suka tarar da Mama kwance gefenta kuma Babah Rabi ce zaune,babu laifi jikin Mama da sauki ba kamar jiya ba,ba a dade da cire mata drip ba,Bakunan su dauke da sallama suka shiga ɗakin,a hankali Mama ta yunƙura ta tashi zaune tana amsa masu sallama cikin muryar ta da bata fita sosai ganin baƙin fuska yasa Babah Rabu tashi daga inda take ta dauki tafurma ta shimfida saman leda dake shimfiɗe kasan ɗakin Mama tana faɗi ''sannun ku da zuwa bismillah ku zauna'' ta faɗa tare da nuna masu tafurma,Hajiya ce ta fara zama kafin daga bisani su Hajiya Bilƙisu suka zauna cike da mutuntawa suka gaisa da juna bayan sun gama gaisawa Hajiya Biklisu ce ta fara magana dakin ya dauki shiru,har Hajiya Bilƙisu ta idah zantuka,Mama ta yi shiru tana sauraron Hajiya Biklisu haka zalikah Babah Rabi bayan Hajiya Biklisu ta gama jero zance,Murmushi mai sauti Mama ta yi kafin a hankali ta buɗe baki ta ce ''tun ba yau ba Unaisa ta sanar da mu komai tabbas Hajiya Bilƙisu kun yi kuskure ke da ƴar'uwarki amma ki sani ban taɓa daura maku laifin abinda Unaisa ta aikata ba sakaci daga gareni ne,na nunawa Unaisa so fiye da ƙima soyayyar da nake mata ya kai bana iya mata nasiha ko na tsawatar mata wanda hakan yasa ta taso a sangarce'' shiru Mama ta yi na wasu ƴan sakanni fuskarta dauke da kunci,a hankali ta kai hannu ta goge hawaye da ya gangaro kuncinta daga haka ta sauke wata ɓoyayar ajiyar zuciya,can ta buɗe baki a hankali ta ce ''duk abinda ya sami Unaisa da ƴar uwarta kaddararsu ce hakan na yarda da Allah sannan kowanne mai rai mamaci ne,mu da muke a raye lokaci muke jira, saboda haka ni ba ku yi min laifin komai ba ko da kun yi min laifi to na yafe maku duniya da lahira'' wani irin farin ciki haɗe da nitsuwa ya ziyarci Hajiya Bilƙisu da Hajiya Zulfa'u lokaci guda, sosai sun ji dadin furucin Mama,ita dai Hajiya ta yi shiru tana ƙarewa Mama kallo tausayin Mama ta cika mata zuciya,a hankali Hajiya ta sauke ajiyar daga haka ta yiwa Mama godiya tare da addu'a samu lafiya,a hankali Hajiya ta kai hannu cikin hand bag ɗinta ta dauki kuɗaɗe masu yawan gaske da ita kanta bata san yawan su ta daura saman tafurma da suka zauna,mayar da dubanta ta yi ga Babah Rabi ta ce ga wannan a ɗan siya mata lemo'' Mama ta ce a'a kuɗaɗen sun yi yawa ta kuma nunawa Hajiya basu bukata amma fir Hajiya ta ce bata san zancen ba,daga karshe dai Mama da Babah Rabi suka yiwa Hajiya giduya,bayan fitarsu daga gida Mama basu tsaya ko ina ba sai gidan Ɗalha,bayan sun isa gidan Ɗalha sun tarar Amirah bata nan ta je kitso tare da su Fauziyya,cikin parlour suka zauna, cike girmamawa Ɗalha ya gaida Alhaji Babah da Hajiya,sai dai ko kallo Hajiya Biklisu da Hajiya Zulfa'u basu ishesa ba tun da suka gaisa bai sake kallon inda suke ba,kamar dai yadda suka saba Hajiya Biklisu ta shiga jerowa Ɗalha bayanai tun daga haduwar sa da Unaisa har izuwa aurensu da kuma sihiri da ta sa aka masa ba da sanin Unaisa ba,Fuskar Ɗalha dauke da wani yanayi ya kalle Hajiya Biklisu na wasu ƴan sakanni kafin ya mayar da dubansa ga Hajiya Zulfa'u,ya dauki a ƙallah sakan biyar yana ƙare masu kallo kafin daga bisani ya sunkuyar da kai ƙasa ya sake wata murmushi da iya karsa lips ɗinsa a hankali ya ɗago ya kalle Hajiya Bilƙisu har sannan fuskarsa dauke da murmushi a hankali ya buɗe baki ya ce ''ribar me ku ka samu da yin hakan,sannan me ku ke bukata daga gareni?me ku ke so na maku?me yasa sai yanzu ku ke sanar dani abinda kuka aikata?me yasa tun sanda take raye baku faɗa min ba?me yasa sai yanzu?" ya ƙare magana cikin dishewar murya daga yadda Ɗalha ke magana su Hajiya Biklisu sun fahimci ransa ya ɓaci kasa magana Hajiya Biklisu ta yi yayinbda Hajiya ke kallon Ɗalha so take ta ce wani abu amma ta ƙasa,wata ɓoyayyar ajiyar zuciya Hajiya Zulfa'u ta sauke kafin ta buɗe baki a hankali tare da kallon ɗalha ta ce ''tabbas mun cutar da ku amma muna roƙon ka da ka dubi girman Allah ka yafe mana ba dan halin mu sai ɗan girman Allah,ƙaddara ce'' Ɗalha ya yi shiru na wasu ƴan sakanni kafin ya saki murmushi mai sauti daga haka ya ce ''so ku ke na yafe muku ki ka ce?" da kyar Hajiya Zulfa'u ta iya furta ''kaddara ce ka yi hakuri ba dan halin mu ba sai dan girman Allah''wata ɓoyayyar ajiyar zuciya Ɗalha ya sauke kafin daga bisani ya ce ''shikenan za ku iya tafiya''yana gama faɗin haka ya tashi tsaye tare da nufar hanyar bedroom ɗinsa ya bar su zaune wajen,parlourn ya dauki shiru na wasu ƴan mintina duk suka yi shiru Hajiya ta yi magana inda ta ce ''ko tasu mu tafi ko ma mene ko ku ka janyuwa kanku,ku godewa Allah tunda ya yafe maku yanzu ya rage tsakanin ku da mahaliccin ku ''ta kare magana tana nufar hanyar fita daga parlourn,jiki babu kwari Hajiya Bilƙisu tare da Hajiya Zulfa'u suka bi bayan Hajiya
Tun bayan tafiyar su Hajiya Biklisu Ɗalha ya shiga ɗaki ya zauna shiru,zuciyarsa tana masa zafi tausayin Unaisa da nadamar wulaƙanci da cin mutunci da ya rika mata su suka riƙa masa yawo a zuciya,tabbas ya cutar da ita harda itama tana da nata laifin na rashin kunya,kusan unin ranar a daki ya yi shi kasancewar su Sudais sun tafi islamiyya Amirah kuma ta tafi kitso da yaran mata,haka Ɗalha ya uni shi kadai a ɗaki misalin ƙarfe biyar ya je ya kwaso su Sudais daga islamiyya bayan dawowarsa da wasu ƴan mintina Amirah ta dawo tare dasu Sumayya,tun misalin ƙarfe biyar da rabi ya tafi masallaci dan sallar magrib bai dawo gidan ba sai da ya yi sallar isha'i,bayan dawowar sa ya tarar da yara zaune parlour suna wasa Amirah na can kitchen tana dafa abincin dare,bai ko kalle inda suke ba ya yi wucewar sa ɗaki zuciyar sa cunkushe da damuwa,bai ko canza kayan jikinsa ba ya samu waje bakin gado ya zauna zuciyarsa tana masa zafi tausayin Unaisa da nadamar wulaƙanci da cin mutunci da ya rika mata su suka riƙa masa yawo a zuciya,tabbas ya cutar da ita harda itama tana da nata laifin laifinta shine tsiwa da rashin kunya,sai yanzu ya fahimci dalilin tsanarta da ya yi lokaci guda ba tare da kwakwarar dalili ba,cikin yanayi na nadama ya rintsa idanunsa murya can ƙasa ya ce ''ya Rabb'' lokaci guda ya ji kirjinsa ta masa nauyi zuciyarsa tana tafarfasa da kyar yake sauke numfashi tausayin Unaisa na ƙara ninkuwa cikin zuciyarsa lokaci guda wani irin zazzaɓi haɗi da ciwon kai suka sauko masa,a hankali ya rintsa idanunsa wani irin jiri na dibansa,tun bayan aukuwar haɗari bai yi kuka ba,sai dai duk sanda ya tuna Unaisa bata duniya ya kan ji wani irin ciwon kai da zafi a zuciyarsa amma ko sau ɗaya bai taɓa zama ya yi kukan rashinta ba,sanin kansa ne ya kan shiga matsanaiciyar damuwa duk sanda ya tuna bata nan ita da yaran da ta haifa,duk sanda ya tuna hakan sai ya ji hawaye ya gangaro masa amma yau ya ƙasa jurewa a hankali ya kai hannayensa duka biyu ya daura ka ya rintsa idanunsa babu shiri ya ji wasu hawaye masu zafin gaske suna bin fuskarsa bai hana kansa kuka ba sai ma ya cigaba da kukan,sosai yake kuka yana tuna zaman sa da Unaisa a Kano da kuma saɓani da suka rinƙa samu bayan dawowarsu daga Kano cikin wata iriyar murya ya ce ''rabbi ka yafe min ba a hayyacina na aurota ba ina da tabbacin bayan hajiya Biklisu ta bata asiri na tsani Unaisa babu ƙwakwarar dalili harda halin rashin kunya da tsiwa irin nata wanda kuruciya da rashin wayo ya janyu mata su''sosai Ɗalha ke kuka bil hakki,ya dauki tsawon lokaci cikin wannan yanayi kafin daga bisani ya ji wani irin bacci yana daukar sa,ga wani irin sanyi dake ratsa gaba ɗaya jikinsa,karfe takwas da wasu mintina na dare Amirah na zaune bedroom ɗinta fitowarta kenan daga wanka,bayan wasu ƴan mintina ta shirya kanta cikin wasu nigth wear masu sauƙin ado,a hankali ta kai hannu ta dauki magani cikin kwali ta buɗe ta cire guda daya daga haka ta dauki ruwa cikin glass cup ta sha maganin,tun bayan faruwar haɗari Amirah ke fama da wani irin matsanancin ciwon kai kusan kowanne safe in ta tashi bacci da ciwon kai take tashi,ba tare da sanin Ɗalha ba ta tafi asibiti bayan tafiyarta asibiti likita ya tabbatar mata cewar cutar hawan jini ke son kamata dalilin yawan tunani da take,daga haka ya rubuta mata wanna maganin duk dare take sha cikin hukuncin ubangiji tunda ta fara shan maganin take samun sauƙin ciwon kan sosai,tun bayan faruwar haɗarin kullum cikin kwantarwa Ɗalha hankali take da ta ga ya zauna zai fara tunani take kawar masa da tunani ta hanyar yi masa hirar kasuwancinta ko wajen aiki ko ma dai wata hira ta daban wanda zasu dauki lokaci mai dan tsawon suna tattaunawa,sai dai duk irin kokarin da take wajen kwantarwa Ɗalha hankali da kuma kawar masa da tunani,ita bata iya hana kanta tunanin rasuwar Unaisa wani sa'ilin ta kan kulle kanta cikin bathroom ta ci kukanta ta koshi,sai dai bata wasa da yiwa Unaisa addu'a,bayan ta gama shan maganin ta dauki hijab ta zura daga haka ta fita daga ɗaki zuwa kitchen inda ta haɗawa Ɗalha abinci ta jera saman tray ta nufi dakinsa,Sallama dauke a bakinta ta shigo ɗakin shiru ta ji bai amsa ba hakan yasa ta yi tunanin ƙila ya shiga bathroom,a hankali ta kai hannu handle ɗin kofar ta tura kofar dakin ciki tare da cusa kai ciki bayan shigowar ta ganinsa ta yi kwance kan gado idanunsa rufe a hankali ta ajiye tray ɗin abinci saman stool dake dakin daga haka ta nufi gadon,a hankali ta kai hannu ta fara tashin sa tare da kiran sunansa,ga mamakin Amirah ta yi ta kiran sunan Ɗalha amma shiru baya ko motsi nan da nan hankalin Amirah ya tashi cikin sauri ta shiga bayi ta debu ruwa ta zo ta shafa masa a fuska nan ma shiru bai motsa ba cikin tashin hankali ta fita daga ɗakin zuwa nata dakin,wayarta ta dauko ta kira layin Muhsin Allah ya sa dare bata yi nisa ba, lokacin karfe takwas da rabi na dare,bugu biyu Muhsin ya amsa kiran da kyar Amirah ta iya saita nitsuwarta kafin ta fadawa Muhsin abinda ke faruwa Muhsin yana jin maganarta ya katse wayar ba tare da ɓata lokaci ba ya shiga mota ya nufi gidan Ɗalha,matarsa Hafsah na tamabayarsa ko lafiya amma bai samu damar amsa ta ba ya sa kai ya fita,tare da taimakon Amirah Muhsin ya sa Ɗalha a mota suka tafi asibiti tare da Amirah,Amirah ta goya Fauziyya suka kama hanyar asibiti Muhsin ya so Amirah ta zauna gida tare da yara amma ta ce sam da ita za a tafi asibitin babu yadda Muhsin ya iya haka suka tafi tare,daga tafiyarsu asibiti likitoci suka dukafa aikin ceto rayuwar Ɗalha a daren Amirah ta kira Ammi da Husnah ta sanar masu abinda ke faruwa,Misalin ƙarfe goma da wasu mintina ɗaya daga cikin likita dake duba Ɗalha ya fito sanye da rigarsu ta likitoci fuskarsa sanye da facemask,mayar da dubansa ya yi ga Muhsin da Amirah yana shirin magana Amirah ta yi saurin tarar numfashinsa ta ce ''ya jikin na sa doctor how is he?pls say something doctor'' a natse doctor ya kalle Amirah ya ce ''clam down madam he is doing great'' daga haka ya ce su biyo sa office ɗinsa Amirah kamar jira take ta shiga bin likitan da sauri Muhsin ma ya bi bayansu,bayan shigar su office likita ya nuna masu kujera yana faɗin bismillah Amirah da Muhsin suka zauna,a hankali ya cire facemask dake fuskarsa kafin ya fara magana a natse inda ya ce ''Da fari ina son ku kwantar da hankulan ku,wato ita rayuwa a kullum bawa tafiya yake kan kaddararsa'' shiru likita ya yi na wasu ƴan mintina kafin ya ce ''Alhamdullilah jikin nasa da sauki'' daga haka shiru ya kuma yi a karo na biyu wanda hakan ya sa Muhsin da Amirah kara shiga damuwa a hankali likita ya buɗe baki ya ce ''da fari ina son ku kwantar da hankula ku,sakamakon binciken da muka yi mun gano pateint ya kamu da cutar hawan jini dalilin yawan damuwa da kuma tunani sannan yana daf da kamuwa da cutar ciwon zuciya saboda haka yana bukatar kulawa sosai a kuma sa ido sosai cikin lamurran sa,in da akwai abinda yake so a yi gaggawar samar masa wannan abin,sannan a daina barinsa yana zama shi kadai dan Allah'' likita ya ƙare magana idanunsa kan Amirah da Muhsin,tun sanda ya furta kalmar hawan jini da ciwon zuciya Amirah ta shiga wani irin yanayi ji ta yi jikin ta ya yi sanyi sosai nan take tausayin Dalha ya cika mata zuciya kenan duk kokarin da take dan ganin ta hana sa yawan tunani hakan bai yi tasiri ba,nan take ta kudira a zuciyarta cewar za ta ƙara mayar da hankali kansa fiye da dah,misalin ƙarfe goma da wasu mintina na dare Muhsin ya cewa Amirah ta koma gida saboda yara shi zai zauna da Ɗalha,da fari ta so ta yi masa jayeyya amma daga karshe ta hakura ta tafi gida,misalin karfe biyu da wasu mintina Ɗalha ya farfaɗo daga doguwar suma da ya yi,a hankali ya sauke idanunsa kan Muhsin dake zaune saman kujera yana bacci zaune a hankali Ɗalha ya cire idonsa daga Muhsin ya lumshi su a hankali yana jin yadda kansa ke masa ciwo sosai ga wani irin zafi da idanunsa ke masa,a hankali ya buɗe baki ya lashe lips ɗinsa da suke a bushe ƙishin ruwa yake ji sosai ya dauki a ƙallah mintina uku a haka kafin daga bisani ya buɗe idanunsa a hankali yana ƙarewa Muhsin kallo can ya buɗe baki da ƙyar cikin muryar ciwo ya yi magana da kyar inda ya fara kiran Muhsin yana faɗin ''man..man..man'' Muhsin da ya fara nisa cikin bacci kamar a mafarki ya jiyu muryar Ɗalha yana kiran sunansa a hankali ya buɗe ido tare da gyara zama yana mai kallo Ɗalha ganin Ɗalha ya bude ido ya sa Muhsin tashi da sauri daga inda yake,cikin sauri ya ƙaraso gadon da Dalha ke kwance a kai yana kallon Ɗalha kamar yadda shima yake kallonsa ya ce ''sannu ya jikin?" Ɗalha bai amsa sa ba sai cewa ya yi ''bani ruwa na sha'' Muhsin ya ce ''ok amma bara na fadawa likita in ya ce na baka sai na baka'' yana gama faɗin haka ya nufi hanyar fita daga word ɗin Ɗalha bai ce komai ba sai rufe idanunsa da ya yi yana jin yadda kansa ke sara masa,bayan wassu ƴan mintina Muhsin ya dawo dakin tare da likita inda ya kara duba Ɗalha,bayan ya gana duba Ɗalha ne ya cewa Muhsin zai iya basa ruwa babu matsalah
*SHUUKRAN*