Free chapter · Read without an account
Chapter 41
BIYU A ƊAYA
( Don't judge a book by its cover)
Page 41
Sayyada barrister
YOTA 13
The five ink legends
Sa'eed ya gyara zamansa sosai yana fuskantar ɗan'uwansa tare da cewa
"Ina tunanin Ashfat ce"
"Ashfat! akan me?"
"Kafi kowa sani ai"
"A'a ina ta yaya za ta ɗaukar min waya? Ai ba ta san da Bilqees ba, kuma ko ta sani me ya shafe ta?"
"Oh nice name Bilqees"
Dr Waahab ya sauke numfashi yana ɗan tunani, Sa'eed ya ce
"Ita ke shigo maka ɗaki, bayan ita kuma sai ni, kuma bana nan"
"To amma me yasa za ta yi hakan?"
"So mana"
"So?"
"Dr Waahab ka bata dama ku daidaita sakaninku"
"Kada ka ɓata min rai, Ashfat ƙanwa kawai na ɗauke ta, ban taɓa yi mata wani kallo na daban ba, zuciya ta Angel ce"
"Angel, shi ma sunan ta ne?"
"Yeah"
"To maybe Ashfat taji kana waya ne da Angel naka"
"To ina ruwan ta, menene nata a ciki? Sai na saɓa mata"
"A'a kada ka fara, kyaleta"
"Ya zata goge min number Angel? Yau kusan kwanaki nawa bamu yi waya ba"
Murmushi Sa'eed ya yi, yana kallon ɗan'uwansa yau shi yake kewar mace? A hankali ya ce
"Kaga ka yi bincike ka tabbatar da hakan, sannan ka yi worning nata, don gaba"
"To ɗan'uwa"
Suna hira har aka kira sallah magrib tare suka fito zuwa masallaci suka idar, sai da aka yi sallah ishai sannan suka shigo gida, a ɗakin Dr Waahab suka ci abincin dare, sai da suka raba dare suna hira sannan Sa'eed ya koma bangaren sa. Dr Waahab ya yi shirin kwanciya sai dai bacci ya gagare shi sai tunanin Angel yake yi ko ya take? Amma me yasa bata kira shi ba, da taji shiru bai neme ta ba? Yana wannan tunanin ne bacci ya ɗauke shi.
****************
Washegari Dr Waahab ya shirya kamar yadda yake yi in zai tafi office, sanye yake cikin ƙananan kaya, ya sanya farin eye glass, riƙe da side bag nasa da white coat nasa da ya sha guga ya saɓa a kafaɗa, ya wuce ɗakin Mommie, ya yi nocking Suhaima ta buɗe tare da cewa
"Barka da safiya Ya Waahab"
"Suhaima sannu"
Ya faɗa ya shigo ciki bakinsa ɗauke da sallama, Mommie ta amsa, ya zaune ya dube ta tare da cewa
"Morning Mommie"
"Morning Son, har an shirya?"
"Eh ya ƙarfin jikin?"
"Bana jin komai sai dai wani lokacin nakan ji ciwon kai ko zafin kirji"
"Su ma za su daina ki ci gaba da shan magungunan da kika zo dasu"
"In sha Allahu, Jamila ma tana hanya"
"Ayya Allah ya kawo su lafiya"
"Amin"
Ya mik'e tare da cewa
"Bari na gaishe da Mamie"
"To sai ka dawo"
"Yawwa"
Ya fice, ya iso ƙofar ɗakin su ya yi nocking ta ba shi izinin shigowa ya tura ƙofar ya shigo tana kwance, ganinsa yasa ta tashi ta zauna tare da cewa
"Babangida har ka fito?"
"Eh Mamie barka da safiya"
"Barka dai, ka ganni nan da komawa bacci zan yi"
"Ayya ki kwanta ni ma ina sauri"
"To Allah ya tsare"
"Amin Mamie"
Ya fito, kai tsaye parking space ya wuce ya kunna motar yana ƙoƙarin buɗe wa yaji muryar Sa'eed yana cewa
"Likita bokan Turai"
Murmushi ya yi tare da cewa
"Sa'eed ba ka rabo da tsokana"
"An fito kenan"
"Eh fah gari ya waye, ina ka nufa?"
"Zan je na duba harkokin kasuwanci na ne, kai kam yanzu ka bar business"
"A'a ban bari ba, ina yi fa, amma ban cika zuwa ba"
"Gaskiya ka mai da hankali akan kasuwanci suna da rana"
"Sosai ma"
"To zan wuce ayyuka da yawa a gabana"
"Ba matsala mota ce ake wanke wa ana gamawa ni ma zan wuce"
"To sai mun dawo"
"Morning Ya Waahab and Ya Sa'eed"
Su ka ji muryar Ashfat, Dr Waahab da yake ƙoƙarin shiga mota ya dakata ya amsa da
"Morning"
Bai sake cewa komai ba, Sa'eed ne yake tambayar ta aiki, Dr Waahab ya shige ya tada motar ya fice daga gidan...
Kai tsaye ya iso hospital, ya yi parking ya fito, ya wuce office nasa, yana shiga bayan ya sanya key ya buɗe ƙofar ya rataye white coat nasa ya ajiye side bag da wayarsa ya zauna yana ƙoƙarin kunna system nasa, Dr Faisal ya shigo yana
"Special doctor morning Sir"
Dr Waahab ya sauke numfashi tare da cewa
"Dr Faisal morning gari ya waye mun fito"
"Ai ni da za a bani hutu ina so"
"To ba za a baka ba, haka za ka lallaɓa"
Dariya Dr Faisal ya yi ya ce
"Kasan Allah Sir har yanzu ban huta gajiya ba"
"Duk haka muke, juriya kawai za mu yi"
Ya zauna tare da cewa
"Ina kewar Ghana sai na ji da ban zo ba"
A hankali Dr Waahab ya ɗago ya kalli sa, ya sosa masa in da yake yi masa kaikayi, ya ce
"Saboda me?"
"Garin ya yi ba ƙarya, nayi missing ALAJA SPECIAL RESTAURANT"
Mai da system ɗin Dr Waahab ya yi ya ajiye, ya kalli Dr Faisal, jikinsa ya yi sanyi, a hankali damuwar da yake ɓoyewa ta bayyana kan fuskarsa, ya yi kewar kyakkyawar Aunty sosai, yana son jin muryar ta ya san kuma yanayin da take ciki, wani lokacin ji yake kamar ya yi bukin jirgi ya je ya dawo...
"Sir lafiya?"
"Ba komai, ni ma na tuna da Ghana ne"
"Yawwa Bed tana tambayar wannan yarinyar da suka kwana kwanaki ɗaki ɗaya, kullum sai ta yi min zancen ta"
Dr Waahab ya sauke numfashi tare da cewa
"Na yi losing contact nata"
"Ikon Allah garin yaya?"
"Ban sani ba, kwana biyu ba mu yi waya ba"
"To ka kira waɗan da ka sani acen"
"Bani da contact na kowa sai nata"
"To bari na tambayi Beb ko kuma akwai number ɗaya daga cikin ma'aikatan restaurant ɗin da nake order abinci ta wajensa, amma sim card ɗin yana gida, sai kuma memo da suka bamu da zamu dawo kamar da number a jikin. Anyway zan duba sai na yi maka magana"
Sauke ajiyar zuciya Dr Waahab ya yi da ƙarfi, kamar ma ya samu number, cikin farin ciki ya ce
"Ok koma number waye ne ka bani sai na yi yadda zan yi ya haɗa ni da Angel"
"Okay Sir OG da MD suna neman ka"
"To bari na ɗan kammala wani aiki sai na je"
"To"
Dr Faisal ya fice, Dr Waahab ya samu ƙarfin gwiwar yin aiki...
Sai yamma ya dawo gida, ɗakinsa ya wuce sai da ya watsa ruwa ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya, sannan ya fito a lokacin ana sallah kiran sallah magrib ya fito farfajiyar gidan suka haɗu da Sa'eed da Daddy da sauran suka nufi masallaci dake ƙofar gidansu, sai da suka idar da sallah ishai sannan suka shigo, Daddy ya dube su ya ce
"Yanzu kun girma ya kamata ku fidda mata ayi muku aure"
Dr Waahab ya ɗan sudda kai ƙasa yana sosa keyarsa ya ce
"Daddy"
Shi ma Daddy dariyar ya yi, Sa'eed ya ce
"Daddy ku taya mu da addu'a"
"Muna yi sai dai mu ƙara"
Suna hira kamar sa'annin juna har suka shigo, Sa'eed ya wuce bangaren su, Daddy da Dr Waahab suka shigo nasu bangaren, side na Mamie suka shigo bata ciki, suna hira ta shigo hannunta ɗauke da madaidaicin tray ta ajiye Dr Waahab ya ce
"Mamie ina wuni"
"Lafiya Babangida, ashe kuna tafe da Daddynka?"
"Eh Mamie, ina Hauwa ne ta haɗa min ruwan tea?"
"Tana cen bangaren su Suhaima Jamila ta iso, bari na haɗa maka"
"Haka mommie ta ke sanar da ni yau za su iso, sai in na fita mu gaisa"
"Ya kaga jikin nata?
"Daddy mommie?"
"Eh"
"Jiki Alhamdulillah amma har yanzu abin da ya faru yake zuwar mata, kuma hakan zai sake sanyata cikin wani halin"
"To in ba abinka ba Babangida, ai wannan abin ba na manta wa bane, ko kai yana samun ka"
Ya ɗan girgiza kansa a hankali ya ce
"Mamie lafiyarta ake buƙata, damuwar ba za ta sauya komai ba"
"Haka ne so, ko mahaifinta Abbie har yanzu yana cikin damuwa kullum cikin kwantar masa da hankali nake yi"
Mamie ta haɗa musu tea, suna sha suna hira abinci ma anan su ka ci, sannan Dr Waahab ya fito zuwa side na Mommie yana turo ƙofar tare da sallama ya shigo, ganin Mommie a tsaye akan Jamila ta inda ta shiga ba tanan ta ke fita ba, sai faɗa ta ke yi mata ido rufe, Jamila kuma sai hawaye ta ke yi...
"Ki koma gidan ki, tun da kin zo ne ki tada min hankali, rayuwa da mutuwa duk a hannun ubangiji su ke"
"Subhanallah me yasa faruwa ne?"
Cewar Dr Waahab ya ƙaraso ciki, Mommie ta zauna cike da ɓacin rai ta ce
"Ga ta nan sai ta yi maka bayani, tun da ta girma tana yanke hukunci da kanta"
Dr Waahab bai fahimci me Mommie ta ke faɗa masa ba, ya dubi Jamila cike da son ƙarin bayani ya ce
"Jamila me yake faruwa ne? Wani abu ne ya same ki?"
Da ƙyar Jamila ta haɗiye kukan ta ce
"Wahaab yau kusan shekaru ashirin tana fama da ciwo, kuma an faɗa mata warakarta tana gare ta, muddin bata daina tunani ba, ita da samun sauƙi sun yi hannun riga...
"Likitoci su ba Allah bane, waraka kuma daga ubangiji ya ke"
Dr Waahab ya sauke numfashi a hankali ya zauna kan stool ya ce
"Jamila me ya sami Mommie?"
"Likita sanya hoton Shalele ta yi tana kallo, ta ƙi cin abinci sai cewa ta ke yi ko warhaka an kashe ta? Ko yaya Shafa ta yi da ita? Anya ba juju aka yi da ita ba? Shi ne nayi mata magana"
"Yarona goge hoton ta yi, ina ruwan ta da shi a wayata, ni bana son tashin hankali"
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, shi ne abin da Dr Waahab yake furtawa cikin zuciyarsa, Mommie sai sun koma na Islamic medicine, sai an ci gaba da addu'a da sadaka...
"Muna son ki, ba ma so mu rasa ki, watanni uku da ki ka yi a Egypt bana runtsawa cikin dare, ki duba yadda na koma duk saboda tunanin kada na rasa ki"
Cewar Jamila tana kuka, Dr Waahab ya ce
"Jamila"
Ta ɗago ta kalle shi tana sharar ƙwalla, ya yi mata alamu da ta fita, ta mik'e ta fice cikin damuwa...
"Yarona kaga fa yarinyar nan wai ni take yi wa faɗa"
Ya tsiyaya ruwa a cup da ya gani a gefen bedside, ya miƙa mata, ya sassauta murya ya ce
"Mommie karɓi ki sha"
Ta karɓa ta sha, ya ce
"Mommie ban ce Jamila ta yi daidai ba, amma wannan karon ki amshi kaddara, ki yarda da ita, ki cinye wannan jarabawar, ki miƙa al'amuran ki wa ubangiji, zai kawo miki sauƙi cikin zuciyarki"
"To amma Yarona hoton Shalele fa ta goge"
"Ki kwantar da hankalin ki, ina dasu a laptop nawa zan tura miki, amma sai kina cin abinci"
"Yawwa Yarona ka tura min su"
Ya bata abinci ta ci, sannan ya bata magungunanta, ta sha nan da nan bacci ya ɗauke ta, ya sauke numfashi ya fito ya tadda Jamila zaune ta yi tagumi, ya iso ya zauna tare da cewa
"Jamila ya hanya?"
Ta ɗago ta share hawayenta ta ce
"Alhamdulillah Waahab, ya jikin Mommie?"
"Ta ci abinci ta sha magani, har ta yi bacci"
A hankali ta sauke numfashi ta ce
"Har yanzu jikin ne?"
"A'a ni ma abin da ta yi yanzu ya sa na faɗa cikin wani tunani, amma ba komai na gano bakin zaren"
Suhaima ta fito, ganin Dr Waahab da Aunty Jamila ya sa ta gaishe shi, ya yi musu sai da safe ya wuce side nasa, su ma suka shigo ciki...
****************************
Kasancewar night duty Dr Waahab yake da shi, yana gida don haka yana tashi daga kan dardumar sallah bayan ya yi lazumi ya fice wajen side, ya kira Sa'eed a waya, akan ya fito su motsa jiki. Sa'eed ya iso cikin kayan wasan motsa jiki, ya miƙa masa hannu su ka yi shaking hands ya ce
"Bro na fahimci ka fi ni missing wannan wasan"
Murmushi Dr Waahab ya yi ya mik'e, ya ajiye wayar ya iso ya ɗauki ƙwallon tare da cewa
"Sosai ma Sa'eed"
Suka ci gaba da buga wa, suna nishaɗi...
Ashfat da ke tsaye ta window take hango su daga nesa ta sauke numfashi ganin murmushi akan fuskar Ya Waahab, ta yi shirya za ta je aiki, ganin za ta makara ya sa ta sauke labulen ta fito ta yi wa Ammie sai ta dawo ta fice...
*********
Sun jima suna wasan ƙwallon hannu, har ƙannensu suka tashi a nasu wasan ƙwallon ƙafa, su ka yi musu sai anjima suka koma ciki, Dr Waahab kam bai daka ta ba sai da ya kada Sa'eed kusan sau uku sannan suka tashi a wasan, kowanne su ya wuce side nasa.
Dr Waahab ruwa ya watsa ko breakfast bai yi ba ya kwanta bacci ya ɗauke shi, ringing wayarsa ce ta tada shi, ya duba yaga kiran Alhaji Babba ne, ya ɗauka tare da yin sallama, ya amsa sannan ya ce
"Ka zo ka same mu a ɗakin tattaunawa"
Ƙirjinsa ya buga, a kasalance ya amsa da
"To"
Alhaji babba ya katse kiran, Dr Waahab sarkin tsafta sai da ya sake yin wanka ya shirya cikin riga da wando na shadda, ya yi kyau sai ƙamshi yake yi, ya fito zuwa ɗakin tattaunawa.
Da sallama ya shigo, ganin manyan su na family da iyayensu zaune akan kujeru, sai kuma ƙannensa da suke zaune kan carpet. A hankali ya zauna kan carpet ya sauke numfashi Allah ya sa lafiya...
"To ganin ba ka fito da wuri ba yasa mun kammala magana da ƴan'uwanka saura kai"
Cewar Alhaji babba, bai fahimci taron na menene ba, kuma bai fahimci in da maganganun Alhaji babba suka dosa ba, bai ce komai ba, don haka dokar familyn yake in ba zai yu su yi magana ba, sai manya sun gama, Alhaji babba ya ci gaba da cewa
"Wannan zaman mun yi ne akan kowanne ya fidda matar da zai aura in ya so sai a zauna a saka ranan biki"
Jikinsa ya yi sanyi, bai ce komai ba, Alhaji babba ya ci gaba da magana
"Ka gansu nan, ƙannenka su bakwai da abokinsa Sa'eed duk sun zaɓi wacce suke so a aura musu kuma abin farin ciki, anan cikin ƴan matan Ahali duk suka zaɓa, yanzu su takwas an gama maganar nasu saura kai"
Still kansa a ƙasa, ya ɗago a hankali ya kalli Sa'eed, jinjina masa kai Sa'eed ya yi alamun ya yi magana, su ka ji murya Daddy ya ce
"Kai ake sauraro, sai ka faɗi wacce ka zaɓe ta a matsayin matar da za ka aura"
A hankali ya ce
"Ba anan gidan ta ke ba"
Da mamaki suka tashi zaune, don duk sun kishingiɗe suna sauraron sa, Abbie ya ce
"Dr Waahab kana nufin wacce ka ke so ba a cikin wannan Ahalin ta ke ba?"
"Eh"
A hankali Daddyn Ashfat ya runtse idanunsa ya buɗe yana kallon Dr Waahab, Daddy ya ce
"A waje ka zaɓo matar da za ka aura?"
"Eh Daddy"
"Ta yaya ƴan'uwanka sun zaɓa daga cikin wannan Ahalin kai kuma ka ce daga waje za ka zaɓa?"
Abbie ya dakatar da Daddynsa ta hanyar ɗaga masa hannu alamun kada ka ɗau zafi, Alhaji babba ya ce
"Yaro ka shigo mana da bidi'a, amma a wacce unguwa ta ke?"
Kan Dr Waahab a ƙasa har wannan lokacin, yana ta addu'ar Allah yasa su amince, a hankali ya ce
"Ba anan garin ta ke ba, kuma ba ma a ƙasar ta ke ba"
Da mamaki suke dubansa, Alhaji babba ya ce
"Ba ƴar nan Ahalin ba, kuma ba ƴar nan garin Maiduguri ba, sannan ma ba ƴar Nigeria ba, to sai ka faɗa mana ƴar wacce ƙasa ce?"
"Ƴar ƙasar Ghana"
Ya faɗa a sanyaye, a take suka haɗa ba ki da ƙarfi cike da mamaki, suka furta
"GHANA!"
______________________
Sayyada na kwashe slippers nawa na sanya a hammta ƙafa me na ci ban baka, kada a haɗa da ni😃😃
Ayi hakuri da jinkirin da na ke yi wajen yin update abubuwa suna yi min yawa, amma in sha Allahu zan din ga yin long page.
Ayi hakuri da typing errors
Ina godiya fan's da addu'oin ku🥰
Comments and share fisabilillah