Free chapter · Read without an account
Chapter 34
WA ZAI FUSKANCE NI??
BOOK 1
Umma Mustapha
@umsar Arewapen
Wattpad: umma mustapha
PAGE 34
Bayan gama wayarsa da Nihla, wayar ya ajiye a gefensa. Bai daɗe ba sai ga Dr. Anwar ya shigo ɗakin tare da Jabir.
Ya zauna a gefen gadon da Irfan yake, ya fara shirya allurar da zai masa.
"Yaya kake jin jikinka yanzu?"
"Da sauƙi sosai."
"Masha Allah."
Ya ɗaure damtsen hannun Irfan, sannan ya fara ɗan bubbuga wurin a hankali har jijiya ta bayyana. Da ya tabbatar ta fito, ya ɗauki syringe ɗin ya tsira a kan jijiyar, a hankali ya fara zuba ruwan allurar.
Irfan ya yi shiru yana kallon yadda likitan yake aikin.
Da ya kammala, Dr. Anwar ya tattara kayansa yana mayar da su cikin jakar da ya zo da ita. Ya gyara zamansa, sannan ya kalli Jabir.
"Wai sai yaushe Irfan zai yi maganin matsalar da take damunsa? Akwai lokacin da allura da magani za su daina aiki a jikinsa kwata-kwata."
Jabir, wanda yake tsaye ya naɗe hannuwansa a kirjinsa, ya kalli Dr. Anwar.
"Dr., ka tambaye shi. Ga shi nan."
Irfan ya yi shiru, ya ƙi cewa komai.
Dr. Anwar ya juya ya kalleshi.
"Malami, ka ba shi amsa. Ka zauna kana yi wa mutane muzurai."
Irfan ya ɗan sosa gira, amma har yanzu bai ce komai ba.
Dr. Anwar ya sauke ajiyar zuciya.
"Ni dai a kullum ina ba ka shawara a matsayina na likitanka. Ya kamata ka nemawa kanka mafita."
Jabir ya kasa yin shiru.
"Ta ina zai samu lokacin neman mafita? Ya zauna yana kula ƙaramar yarinya. Har yanzu ana ƙoƙarin gina alaƙar, kuma ba mu da tabbacin za ta amince da shi ko ba za ta amince ba. Ka zauna kana fama da tarin sha'awa."
Jabir ya ƙarasa maganar cikin ɗan jin haushi.
Dr. Anwar ya kalli Irfan, sannan ya girgiza kai.
"IRFAN, ka daure ka yi aure. Ko a cikin matan da suke sonka, ka samu ka auri wata. Daga baya, idan abubuwa sun daidaita, sai ka auri wadda kake so. Tunda Jabir ya faɗa min cewa yanzu ta fara karatu ma."
Ya ɗan dakata, sannan ya ƙara da cewa:
"Ga Linda ma a gefe. Kullum cikin neman ka take."
Wani irin kallo Irfan ya watsawa Dr. Anwar, musamman da ya ji an ambaci sunan Linda.
Dr. Anwar kuwa ya kwashe da dariya, har ya buga ƙafa.
"Mai da wuƙar! Kada ka kawo min duka. Amma dai ka duba shawarata."
Jabir ya kalli Irfan, sai ya girgiza kai yana murmushi. Shi dai ya san abokinsa ba zai taɓa sauraron wata shawara da ta shafi barin Nihla ba.
Irfan kuwa ya yi shiru, amma kallon da yake yi ya isa ya nuna cewa maganar Linda ce kaɗai ta ɓata masa rai.
Miƙewa Dr. Anwar ya yi, ya ɗauki jakarsa yana kallon agogon da ke hannunsa.
"Ni zan wuce wajen aiki, kar na makara."
Ya miƙa wa Irfan da Jabir hannu. suka yi musabaha, ya juya ya fice daga ɗakin. Jabir kuma ya bi bayansa domin raka shi har zuwa harabar gidan.
Dr. Anwar ba sabon mutum ba ne a rayuwar Jabir da Irfan. Abokin karatunsu ne tun lokacin da suke karatu a ƙasar Amurka. Sun yi shekaru tare suna karatu, suna kuma taimakon juna a lokutan da suke buƙatar hakan. Bayan kammala karatunsa, Anwar ya dawo Najeriya, inda ya kafa nasa asibitin.
Tun daga lokacin ne ya zama likitan da ke kula da Irfan, musamman saboda matsalar da ta daɗe tana damunsa.
Irfan yana fama da wata irin matsananciyar sha'awa da ke yawan ɗaukar masa hankali, kuma a wasu lokuta hakan kan jawo masa rashin jin daɗi da ciwon ciki. Duk da haka, yana ƙoƙarin ya riƙa sarrafa kansa, domin bai son ya bari wannan matsalar ta kai shi ga yin abin da zai iya jefa rayuwarsa cikin nadama.
Sai dai a wannan karon, Dr. Anwar ya fara ganin kamar abin yana ƙara yin tsanani.
A zuciyarsa, ya san shawarar da yake ba Irfan ba wasa ba ce. Ya kamata ya fara fuskantar matsalar da ke damunsa tun kafin ta fi ƙarfin magani.
A can cikin ɗakin kuwa, Irfan ya jingina kansa da filo, idanunsa a lumshe.
Kalaman Nihla sun sake dawowa masa a rai.
"Me ya sa yanayinka ya sauya a lokacin?"
Ya sauke ajiyar zuciya a hankali.
Ba ciwon cikinsa ne kaɗai ke damunsa ba. A yanzu, akwai wata babbar tambaya da ta fi komai ɗaukar masa hankali:
Shin Nihla za ta amince da soyayyarsa?
Amsar wannan tambayar ce kaɗai zai iya sa zuciyarsa ta samu natsuwa... ko kuma ta ƙara dagule masa tunani.
Umsar ✍️