Free chapter · Read without an account

BABI NA TALATIN DA ƊAYA

by Zainab · Zaren Rayuwar Mu

Zaren Rayuwar Mu 

BAN GAJI da yiwa Zaid duk abubuwan da nake mishi ba duk da ɗakin shi a kodayaushe a gyare yake. Inaso na samu ranar da zan shiga na samu bedsheet ɗin a yamutse da duk ko ina na ɗakin amma har yanzu ban samu ba. Idan na shiga na kan gyara duk wani wuri da nake ga be yi ba. Ina son turaren wuta nayi wa Yaya Hauwa magana tace idan ina da lokaci ƙarfe biyar na yamma har dare tana gida nazo na amsa idan kuma na samu lokaci zata haɗa ni da me siyarwa. Nace yanzu zan zo na amsa a wurin ta kafin na samu lokaci mu tafi ta haɗa ni da me siyarwa. 

Na fito aiki na biya gidanta. A cikin compound naga motar Zaid ba wurin parking space ba. Ban yi wani mamakin ganin motar shi a gidan Yaya Hauwa ba na shiga ciki. Idan aka shiga gidan Yaya Hauwa da akwai corridor wanda an ɗaura madubi a bango me kyau kafin ka shiga ciki, so ina shiga corridor na fara jin sanyin AC da humming nashi se kuma hoarse tired voice na Zaid yana cewa “I don't know....I have no idea Yaya. I don't know what has been drawing me to her since time immemorial. I can't point to one thing that makes her so extraordinary , so different from other girls, I just know that I love her and I want to be with her for eternity” Gaba na ne ya fara duka gaba-ɗaya tunani na ko dai Zaid ya samu wata ce amma duka maganganun shi suna pointing to the love he has for me. Cigaba da magana yayi, Yaya Hauwa ba tace komai ba se sauraren shi da take “But I'm thinking of divorcing her, of letting her go forever without ever looking back”
  “Subhanallah Zaid! Me ya kawo tunanin maganar saki duk da ba tun yanzu nake so ka rabu da ita ba saboda matar nan taka na faɗa maka ban yarda da ita ba. Wallahi bana tunanin alkairanta sun fi sharrin ta, Zaid” itace maganar da naji Yaya Hauwa tayi. Tsayin da nake naji inayi kamar zan faɗi se na dafa bango na riƙe kaina da hannuna nayi steadying kaina da sauri na fito daga ciki saboda bana so naji inda maganar su zata ƙarisa. Bana so naji idan Zaid ze yi concluding saki na. A cikin mota na shiga na bar gidan da sauri ban tsaya a titi wani tunani ba na wuce gida. A chan ɗaki na na shiga na kwanta a gado ina kuka me haɗi da dana sani. 

A gefen su Zaid, Yaya Hauwa ya fara faɗawa dalilin da yasa yake so ya rabu da Hadiza. 
   “She married me because I was the only available option for her. She married me because she wanted to get married not because she loves me, Yaya. Gabaɗaya tunanina yanzu yana kan irin cutarwa da cin amana irin na Hadiza saboda har yanzu ban ga dalilin da ze sa ka auri mutumin da baka so ba. Ban fa mata dole ba. Nasan kawai ina ƙaunar ta ne kuma nasan zan iya auren ta duk yadda take ko ta zama saboda ina ƙaunar ta da gaskiya. Amma ki duba irin sakamakon da zata min saboda kawai ina ƙaunar ta. Idan ta faɗa min ba za ta taɓa aure na ba ko kuma bata yarda da auren ba bayan na mata magana zan sata dole ta aure ni ne? Itace ta kawo min kanta na amsa. Bana cutar da ita. Duk wani haƙƙi wanda yake kaina nata ina ƙoƙari na sauke babu inda na hana Hadiza. Babu takurawa a zamanmu nasan aiki take kuma nasan yadda aiki yake demanding I don't wait for her for anything. We lived as couple but we didn't looked as one. And I was patient all through. She aborted my babies. Shin Yaya wannan ce sakayyar ƙaunar da nake mata?”
Ajiyar zuciya Yaya Hauwa ta sauke tana kallon Zaid cike da tausayi “Wallahi a ranar da nazo gidanka mu kayi abinci da ita, a ranar na kula da akwai wani giɓi a auren ka Zaid. Nima na rasa dalilin da yasa se ita. There are thousands of women who are better than her at everything. And I love you here, we all love you, all of us your siblings. Don't go and make yourself miserable because of someone__someone like your wife. But you also know how the issue of divorce is for Dad. Idan da gaske zaka rabu da ita kaje ka faɗa mishi dalili kar yayi fushi idan yaji ka sake matar ka saboda kasan policyn shi gidannan idan yaran shi maza suka yi aure ba saki se idan babu yadda za'a yi. Kuma nima ban ce ka sake matar ka ba. Babu me ce maka ka sake matar ka anan amma idan kaga ba zaka iya ba, then you should let her go honorably. Idan kuma zaka iya zama da ita se kayi haƙuri ku zauna tare da juna most especially idan kaga ta chanja halayen ta”
Shiru Zaid yayi ya shiga tunani saboda tabbas yasan Abba be yarda da sakin nan ba. Idan zaka yi aure ze ce ka duba ka sake dubawa saboda shi yaran sa maza ba ze so suna aure suna sakin mata ba. Idan ka aure ta to da wuya kayi saki shiyasa yake basu dama su bincika su duba su ga.
   “Nasan kana son matar ka Zaid amma idan cutarwar ta a wurin ka yafi yawa kaga ba zaka iya ba, gida duk muna son ka, kayi haƙuri da zaman nan ka rabu da ita” 

Shiru Zaid yayi se kuma chan yace “Ta fara chanja halayen ta. Ta faɗa min abinda ke cikin ranta yanzu na irin ƙaunar da take min amma ban yarda da matar nan ba, Yaya. Ni fa na kasa zaman lafiya da zuciyata akan irin cutar da Hadiza ta min haɗi da irin wannan cin amana me zafi”
  “Oh Zaid! Ta fara chanjawa?”
  “Ta chanja sosai Yaya. She cooks and she clean my room and she deck up herself duk da ni ban damu da cleaning da take ba, i can clean my space”
   “Of course anyi haka saboda turare tace min tana so na gida”
Nodding Kai yayi. “Me ze hana kayi testing nata ka gani idan da gaske ta chanja?”
  “Yarda ce tsakanina da ita babu yanzu. She...she has the habits of a chameleon”
  “I'm sorry you're knowing this about a woman, Zaid. I don't want this for you but you decide what's best for you and I'll stand up with you for your choice because you're the one living that life”
  “I'm thinking of telling Abba about it”
   “You should if you can't stay with her, you should but I want you to giver her time and see where her devotion stands. Because I know you love her and you truly do, Zaid”
Kallon Yaya Hauwa Zaid ke yi ta gyaɗa kai tace “Ka jira kaga chanjawar nata”
Hannun ta ta kai a nashi a way of comforting. Hannun shi Hauwa ta ji yayi sanyi ta tashi domin kawo abinci ya ci kafin ya fita.
Tana dawowa da abinci yace ya koshi. Maidawa tayi ta dawo shi kuma ya tashi ze tafi. Har sun fara tafiya tare zata raka shi tace “Na baka turaren wuta ka kaiwa Hadizan?” girgiza kai yayi alamar a'a, Hauwa ita kuma bata matsa ba. 
Sun fito compound take ce mishi “Shine yasa duk ka damu? Kaga yadda ka zama? Your eyes looks tired ko de baka samun bacci?”
  “I'm okay, gajiyar aiki ne”
  “Aiki? Wane aiki tukun? Ba dai aiki kake dayawa ba kai da har yanzu kana recovery stage? Ban yarda da kai ba. Ka dai sa damuwa a ranka ko isasshen bacci baka samu idanun ka duk sun chanja”
   “How can i not be in this state? Duk yadda zan miki bayanin yadda Hadiza take ba zaki gane ba Yaya”
   “Nasan halin matar ka fa. Daga ganin ta nasan halin ta shiyasa ni bana ra'ayin ta. Matar da zata zubar da ciki har biyu ai kasan zuciyar ta bayi da kyau”
A jikin motar shi yasa jikin shi Yaya Hauwa tace “Nasan dole zaka damu. Abinda Hadiza tayi da akwai ciwo ko ni nan na ƙara jin haushin ta duk abinda zan mata saboda kai zanyi. Amma ka rage damuwa duk wani abu da yake saka farin ciki ka dinga yi bana so lafiyar ka ta samu matsala, ƙanin Hauwa. Idan baka son zama gidan, Please ka dinga fita daga ciki idan itace baka so gani you know what to do just don't let Hadiza be the reason you turn into a miserable man. There are thousands of good women you're just unfortunate to have ended with the likes of your wife. Da ina kan annual leave zamu je vacation ne a Berlin but.....just take care of yourself please Zaid. Ka rage damuwa i promise with time, everything will be fine. The world doesn't revolve around Hadiza”
Kallon Hauwa Zaid yake tana magana yasan duk abinda tace gaskiya ne yace “I have so much love for her. That's my only fault”
   “It'll be fine, don't worry about that” 

Hauwa da kanta ta buɗe mishi gaban mota ya shiga ta sake ce “Idan na ƙara jin wani abu against wannan Hadiza, wallahi Zaid idan rayuwar ka na hannun ta se ka rabu da ita. Yanzu de ba zan ce ka rabu da ita ba tunda har ta fara chanjawa bana so rabuwar da zaka yi da ita ya cuta maka but you heard what I said initially right? 
Murmushi Zaid yayi Hauwa tace “Take care of yourself. I'm available whenever you need me, just a call away or a visit. Take care of yourself I don't want your health to deteriorate”
Nodding Kai yayi tukunna ta rufa mishi murfin mota ya wuce. 

Bayan Zaid ya isa gida be ma tsaya duba ko Hadiza na ciki ko bata nan ba ya dai san yaga motar ta a parking space. Kwance yayi akan gado nan take yaji numfashin shi ba irin yadda yake ba. Ahankali ya tashi daga kwancen da yake yasan kwana biyu he's very negligent da yadda ze dinga numfashin da physiotherapist nashi ta nuna mishi. Fara numfashin yayi amma be ji da kyau ba ya tashi yaje wurin window ya riƙe numfashin shi sannan ya saki. 
   “Zaid” yaji muryar Hadiza, ba tare da sanin shigowar ta ba. 
Juyowa yayi ya kalle ta. Idanun ta sunyi jazir be ce komai ba. Da sauri ta dawo kusa dashi ganin he's not calm at all he even looks confused. 
  “Asibiti zamu tafi?” na tambaye shi tare da ɗaura hannuna wurin kafaɗar shi.
Shiru Zaid yayi yana kallo na kamar idanun shi zasu rufe. 
  “Zaid” na ƙara kiran sunan shi ahankali “You don't look ok. Let's go to the hospital” na faɗi tare da jan hannun shi
  “I'm okay” yace, muryar shi ma bata fitowa.
Girgiza kai nayi “You are not. Can you breath?”
Shiru yayi be ce komai ba na ja hannun shi da ƙarfi muka fito ɗakin. A compound na ja shi na sa shi a mota muka koma emergency a Cedacrest.

Amsar Zaid suka yi nayi tsaye nasa hannuna na rufe hancina da bakina se ga hawaye sun fara min zuba. Ban shigo da waya ta ba da na kira gidansu na faɗa musu ko yayar shi, Yaya Hauwa. 
Ina nan tsaye nasa jikina a bango na rufe idanuna ina tunanin fitowa doctor ze yi yace min Zaid has kicked the bucket abinda nake tsammani kenan bana tunanin ze fito da rai a cikin emergency. But I haven't have my last moment with Zaid. We should say goodbye to each other before he leaves. I'll tell him that I genuinely love him and I'll never stop loving him. Whether he's here or not, I'll love him as long as the world stands. 
Hawayen da suke zubo min suka yi yawa nasa ƙaramin gyalen dake kaina end nashi ina tarewa. Ban san da mutum a kusa dani ba naji muryar mutum ana cewa “Are you okay?”
Fashewa nayi da kukan da ban san ina riƙewa ba ya matso kusa dani. “Crying, they says, makes you feel better but I'd want to know what bothers you so much. A problem shared is a problem half solved”
Hannuna nasa a fuska ta ina son kukan da nake ya tsaya babu wanda nake faɗiwa matsala ta a duniyar nan. Komai yayi min tsaye a rayuwa. Babu wata ƙawa wacce nake iya cewa ina da. Idan nayi makaranta ɗaya da mutum da na bar makarantar kuma shikenan. Ina son zama cikin kaɗaici na nika ɗai amma yanzu ina buƙatar wanda zan faɗi wa matsalar da nake fuskanta a gidana da kuma rashin lafiyar mijina. 
   “Let's sit somewhere. What bothers you, my sister?” yace tare da leading na muka zauna nan kusa da emergency. 
  “Me yake faruwa?” yayi Hausa, ɗauka na baya jin Yaren Hausa. He might be in his late 30s. Yana sanye da suit amma banda rigar sama he looks like a doctor himself. 
“Mijina ne bayi da lafiya na kawo shi emergency and I just have this feeling that he won't come out alive zuciya ta bana jin daɗin ta tunani na duk ya hargitse bana so na rasa shi. Ina jin tsoron rasa shi. And I have this crisis at home, I heard him telling his sister that he's thinking of divorcing me I'm so tired of this life komai yayi min zafi a duniyar nan” ina yin shiru hawaye suka biyo baya. Shiru yayi be ce komai ba kamar yana tunani se kuma chan yace “Ki dena tunanin mijinki ba ze fito ba. Waya faɗa miki idan aka shiga emergency ba'a fitowa? Har ICU ana fitowa bale ma emergency. Ki kwantar da hankalin ki babu abinda ze faru dashi, zaki ji alkhairi kinji?”
Gyaɗa mishi kai nayi ya cigaba da magana “And of divorcing you, why? What brought up the divorce issue?”
   “Mun samu matsala dashi yana ganin kamar na cutar dashi kuma na ci amanar shi amma ina kan gyara duka halayena. Ban sani ba ko baya gani ko kuma yana tunanin duk ƙarya ne”
  “Yarda wani abu ne me yiwuwar samu for the second time, most especially idan anyi disappointing naka the first time”
 “But what happened to giving people second chance? Don't I deserve it?”
  “You betrayed him, didn't you?”
Shiru nayi saboda nasan nayi betraying Zaid. 
  “You did, stranger, and that's where everything get rough. If you could try harder and restore that trust, then you're good to go, you'll be living your best life with your husband”

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol