Free chapter · Read without an account

BABI NA TALATIN DA BIYU

by Zainab · Zaren Rayuwar Mu

Zaren Rayuwar Mu  

TSAYE NAYI na kasa zama ina kallon Zaid yana bacci cikin salama da natsuwa. Ban yi zaton za'a fito dashi ace min yana da rai ba amma gashi yana da rai kuma ina ganin yana sauke numfashi. Wannan phase yanzu da muke a rayuwar mu nake son mu fita. Ina son Zaid ya samu cikakkiyar lafiya kuma inaso nida shi mu shirya kamar wani abu be taɓa faruwa tsakanin mu ba. 

Idanun shi naga ya fara buɗewa ahankali se ya kalla surrounding ɗin shi two walls briefly. Cikin natsuwa na dawo kusa dashi na ɗaura hannuna a nashi. “Zaid” na kira sunan shi “I thought I'll lose you” na faɗa mishi softly ina kallon shi. Kallona yake be ce komai ba. “Babu inda yake maka ciwo?” na tambaye shi. “I'm okay” ya faɗa min muryar shi bata fitowa sosai.
  “Dama inaso naga ka tashi ne. Zan je gida yanzu na kawo maka abinci. Ban faɗawa su Abba ba saboda ba waya a hannuna amma idan na tafi gida zan sanar dasu. Doctor yace gobe da safe za'a mana sallama idan kayi faring sosai”
   “Kar ki faɗa musu” Zaid ya faɗa “You shouldn't, you don't have to”
   “Meyasa? Naga kamar suna da haƙƙi su sani”
  “I don't want them worried. Don't tell them” yace, tare da rufe idanun shi. Tsaye nayi ina kallon shi aƙalla ya kai minti biyu kafin na fito daga ɗakin na wuce gida. 

Ruwan tea na fara dafawa na haɗa basket na tea na ɗauko wayata da ATM card nawa na ɗauko wa Zaid wayar shi. Tsayawa nayi shago na siya sliced bread tukuna na wuce asibiti. Koda na tafi ɗakin da muke Zaid yana bacci. Inaso ya tashi ya sha tea amma kuma bana so na tada shi se kawai na zauna a kusa dashi a gadon asibitin. Idanuna har rufewa suke akan gajiya se na ɗan kwanta nayi stretching hannuna yana kaiwa kafaɗar Zaid ban san lokacin da na fara bacci ba. 

Ni na fara tashi daga baccin, ƙarfe tara na dare. Zaid kuma be tashi ba. Ƙarfe goma ma be tashi ba naga baccin yayi yawa be ci abinci ba yasa na tada shi. 
Rinsing bakin shi ya fara yi ya fito daga banɗaki na haɗa mishi tea na bashi. Sliced bread ɗin kuma yace baya ci. Tean ma be sha dayawa ba yace ya ishe shi. Bayan ya gama ya sake relaxing a gado ya rufe idanun shi. Tsaye nayi sosai a kusa dashi ina ji hawaye na cika min idanu nace “Dan Allah kar kayi bacci ya isa Zaid” 
Buɗe idanun shi yayi ya ɗaura akaina ina ganin yadda yake kallon cikin idanuna. 
  “I'm scared of losing you” na faɗa mishi tsorona tare da zama a kusa dashi nasa hannuna a nashi. Be cire hannun shi ba kuma be yi bacci ba. Yanzu ba ma magana nake so muyi dashi ba, mu de yi enjoying silence dake tsakaninmu i want his eyes open not closed sleeping. Ina tare da Zaid se ƙarfe goma sha biyu da rabi yayi bacci. 

Washegari bayan likita ya shigo yake faɗa min se an kula da Zaid kuma ya dinga yin breathing exercise nashi. Yace min mu bari har a jima kaɗan a mana sallama. Ba su suka sallame mu ba se huɗu na rana. 

Ɗakin shi muka wuce na shiga banɗaki na haɗa mishi ruwan wanka. Shiga yayi domin yayi wanka ni kuma na fitar mishi da kayan da ze sa. Ina nan a ɗakin nashi har ya gama abinda yake a banɗaki ya fito. Ina zaune a bedside ɗin shi ya shirya yasa kayan da na fitar mishi ya kwanta a gadon shi. 
   “Bacci zaka yi?”
Girgiza min kai yayi ya rufe idanun shi. 
  “Ba zaka fito a compound ba to? Zaman nan ba ze maka daɗi ba”
“I'm okay” ya faɗi ba tare da ya buɗe idanun shi ba. Nayi minti biyu ina kallon shi kafin na tashi na wuce ɗakina. Wanka nayi na shirya cikin doguwar riga na lace wanda yake daidai da jikina irin ɗinkin zamani. Ɗankwali na na ɗaura na fitar da sumar kaina ta baya. Ban shafa kwalli ba wannan karon, janbaki kawai na shafa ina ganin yadda baki na ke shining kamar nasa Vaseline. Har nasa takalmi na se kuma na cire na wuce ɗakin Zaid. 
“Are you sleeping?” nace cikin murya me sanyi ina kallon Zaid na zauna a gefen shi a gado.
Buɗe idanun shi yayi ya kalle ni ya girgiza min kai bana son wannan girgizar kai da yake min yayi magana tunda yana da baki. 
  “Baka so kayi magana ne, Zaid?”
   “I'm okay” ya faɗa min.
Tashi nayi daga gefen shi da na zauna na dawo gefen da mutum ke iya kwanciya and I lay down there kamar yadda yake kwance. Hannuna na kai a nashi, Zaid yayi saurin cire hannun shi. 
  “Didnt i look beautiful?” na tambaye shi ina kallon shi.
Kallona Zaid yake kamar be taɓa gani na ba kodai yana dubawa ne idan nayi kyau ko ban yi ba. 
Shiru yayi be bani amsa ba har yanzu akwai ciwo a idanun shi. 
  “Kayi haƙuri Zaid. Dan Allah kayi haƙuri ka yafe min”
Jin abubuwan da nake faɗa yasa Zaid tashi ya bar min ɗakin shi. Nima tashi nayi daga gadon na koma ɗakina. Koda na buɗe window na na hango shi da me gadin mu suna magana da juna. Ina so na tambaye shi shin saki na ze yi ko kuma yana tunanin lokacin da ya cancanta ya sake ni ne?
Na jima ina kallon shi yana magana da me gadi har dariyar shi ina gani ban san abinda suke tattaunawa ba. Ina ganin yadda yake magana cikin natsuwar shi da yake da ita tun ba yanzu ba. Idan yana magana jikin shi baya motsawa ahankali yake yi. Ya ɗan yi losing weight ƙasan idanun shi basu da hasken sauran jikin shi. 

Jin ƙarfe shida tayi yasa na wuce kitchen na dafa mana light food; pancake ne yayi kyau fluffy da omelette na kuma dafa kwai guda biyu. Na dafa mishi ruwan strawberry Lipton. 
Plate biyu nayi, fluffy pancakes nasa zuma akai, omelette each and one boiled egg each with a fork na kai a dinning table na dawo kitchen na ɗaukar mishi strawberry Lipton ɗin shi. Sallah Maghrib nayi na fito daga ɗaki nasan Zaid yanzu ze shigo tunda sun yi sallah. 
Kamar yadda nace se gashi ya shigo ciki. 
   “Zaid” na kira sunan shi tare da tashi tsaye inaso nazo wurin shi 
  “I cooked for us, Zaid” na faɗa mishi 
Kallona yayi yace “I'm okay, Hadiza”
  “Dan girman Allah ka duba ƙoƙarina akan girkin nan da na mana kazo mu ci abinci. Baka da lafiya fa”
Be ce a'a ba muka fara tafiya wurin dining table. Zama yayi a kujera na zauna kusa dashi. 
Kallon abinda na girka yayi tukuna ya kalle ni. 
  “Baka cin pancake?” nace “Ko zumar ne baka so na cire maka wanda keda shi?”
  “Just surprised you can make this kind of food” yace kamar in mockery.
Yana da gaskiya duk zaman mu dashi ko girkin bana yi bale nayi irin wannan. Shiru nayi ban ce komai saboda bani da abinda zan faɗa mishi. 
Abincin yaci amma ba dayawa ba ko dafaffen kwai be ci ba ya dai ci omelette kuma ya sha strawberry Lipton da na dafa mishi. 
Bayan ya gama ya tashi, kafin Zaid ya wuce yace min “Thank you.” Wani sanyi naji a cikin raina harda murmushi nayi irin na mutanen nan wanda suke cikin ƙaunar wani ɗan Adam.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol