Free chapter · Read without an account
Chapter 22
*_The Amazing Pen_ ✍️..........*
*Ba ni da Madogara*
(Sai Allah...)
022
Hajiyan sama kuwa ganin mutanan ɗakin sun kusa harbo jirginta sai kawai ta fashe da kuka tana cewa
"Shikenan don anga ban haihu ba shi ne a gaban kowa ɗiyar cikina take gasa min magana son ranta, babu wanda ya ce komai yeeee! Yeee!"
Babu wanda ya bi takan kukanta sai ma Alhaji da ya dubi Hujayrah cike da farin ciki ya ce
"To yanzu Hujayrah mene ne mafita"
Zuwa inda Hajiya momma take Hujayrah ta yi tana dubanta ta ce
"Ba yanzu zan faɗi abin da ya dace a yi ba saboda wani dalilina na daban" Tana maganar tana watsa wa su Hajiyan Sama da Hajiya Ramla mugun kallo. Fita daga ɗakin Hajiyan Sama ta yi tana shassheƙan kuka, ko mintuna biyar ba a yi ba aka kira wayan Hajiya Ramla wanda da sauri tabar ɗakin hankali tashe ba tare da ta yi sallama dasu ba. Hakan ba ƙaramin daɗi ya yi wa Hujayrah a rai ba don daman saboda su ne yasa ta ce ba yanzu ba. Matsowa ta yi daidai inda kan Hajiya momma take sai kuma da tsaya cak! Da sauri ta kalli gadon, lokaci guda da duƙa tana yaye janin gadon. Kowa dai a ɗakin ita yake kallo don yaga mai za ta yi. Abu kamar almara sai ga Hujayrah ta miƙe da wata laya a hannunta tana jujjuyawa. Mamaki na ya cika kowanne a cikin ɗakin musamman Alhaji, lokaci guda hankalinsu ya sake tashi jin wata razananniyar ƙara da Hajiya momma ta saki tana fizge-fizge gwanin ban tausayi, da sauri Hujayrah ta riƙeta tana mata tofi, sauran ƴan ɗakin matsowa suka yi kusa da ita , Nazima da Razina kuka suke sosai suna tausayi wa halin da Ammiensu da shiga ciki lokaci guda Allah ya sauya mata kamanni.
"Razina ɗauko min jakar nan tawa wacce take cikin drowar kusa da gado" Hujayrah ta ce tana saita bakinta daidai kunnan Hajiya momma tana mata addu'a. Da gudu Razina ta fita daga ɗakin kafin wani lokaci sai gata da jakar Hujayrah wacce ta zo da ita gidan. A kusa da ita ta ajiye tana matsar ƙwalla,sai da Hajiya momma ta lafa da fizge-fizgen da take yi sannan Hujayrah ta tsagaita da yi mata addu'a. Lokaci guda bacci ya yi awan gaba da ita,ɗaukar layar Hujayrah ta yi tare da miƙa wa Alhaji cike da girmamawa Sosai mamaki ya cika sa har ya rasa abin faɗa, juya layar yake yana mamaki. Arqam da Mas'ud kamar babu su a cikin ɗakin sun kasa cewa komai saboda ruɗanin daya shigesu lokaci guda. Gyara zama Hujayrah ta yi a bisa gadon sannan ta dubi Alhaji wanda ke juya laya ya kasa cewa komai ta fara magana da cewa
"Abbu kamar yadda na faɗa a baya, asiri biyu ne a jikin mammi sai dai Alhamdulillah tunda yanzu mun cire ɗaya saura ɗaya. Sannan fizge-fizgen da kaga tana yi yanzu ba wata matsala bace domin asirin ne ya karye shi ya haifar mata da fizge-fizge."
"Ikon Allah! Amma duk wanda ya yi wa Mubina wannan asirin mugu ne na ƙarshe kuma bai kyauta mata ba , Mubina da babu ruwanta da shiga harkar mutane , ni tsorana kar ciwonta ya tashi saboda damuwar da take ciki a yanzu " cewar Alhaji fuskarsa shimfiɗe da damuwa.
"In shaa Allah ba zai tashi ba, yanzu dai asiri ɗaya ya karye wanda nake tunanin ba wanda ya haifar mata da ƙurajan nan ba ne. Da alama aljanu aka turo mata sannan aka birne wani asirin daban duk don a wahalar da ita. Mafitarmu a nan ɗaya ce " cewar Hujayrah tana nazari.
"Mece ce mafitar Hujayrah?" cewar Alhaji wanda shi kaɗai yake iya magana don sauran ƴan ɗakin ido kawai suke bin su. Tun lokacin da Hujayrah ta ce akwai asiri a jikin Hajiya Nafisa ta ɗauke wuta, babu wanda take zargi sai kishiyarta Hajiya Zinatu domin alamu sun nuna bata yi farin ciki da juna biyun da take dashi ba.Wasu zafafan hawaye ne suka gangaro mata a bisa kuncinta, tabbas Hujayrah ba ƙarya ta yi ba domin daga jiya zuwa yau taga canji a jikinta, duk da tana lauyayi amma wannan ciwon da ya shigeta faradɗaya ya bambanta da lauyayi.
"Za a samo ruwan zam-zam na asali da Habbatul Saudah sannan idan da hali za a saka malamai su sauke mata Al Qur'ani mai girma ba sai sun zo nan ba.Bayan haka akwai wasu turaren Aljanu da ake siyar wa, mu a can Zaria Baba Musa yake zuwa ma Kakulleta dashi amma bansan a nan garin ba, sai a siyo mu gwada mu gani ko Allah zai sa a dace"
Nan take Alhaji ya kira waya ya sanar da abubuwan da Hujayrah ta sillafo wanda ake buƙata har da sauka karantun Al Qur'ani da ta ce a yi. Bayan ya kammala wayar dai ya dubi Hujayrah ya ce
"Bayan wannan shikenan ko akwai saura?"
Jinjina masa kai ta yi ta ce
"Akwai saura don na Mammi ne muka gama, abin da aka birne zan duba gidan nan baki ɗaya ƙila naga inda aka birne na cire,Bayan haka Hajiya Nafisa ma akwai asiri a jikinta wanda nake tunanin saboda cikin jikinta ne yasa aka yi asirin".
*Ƙarin bayani*
*Karku manta Hujayrah na da aljanu masu bada magani a kanta duk da kakarta na bada magani kuma ta bata laƙanin amma ba na abin da ya shafi sihiri ba ne, su suke hawa kanta a duk lokacin da hakan ta taso na bada maganin da ya shafi sihiri sai su bada ko kuma su kasa a yi kasancewarsu musulmai*
*Cikin labari*
Sunkuyar da kai Hajiya Nafisa ta yi saboda kunya, sosai hankalin Alhaji da sauran ƴan ɗakin ya sake tashi. Sai da Hujayrah ta ɗan nisa sannan ta ce
"Abbu amma nata bai kai na Mammi ƙarfi ba don da ruwan zam-zam ɗin da zan yi addu'a a ciki Allah zai sa asirin ya karye in shaa Allah"
"Allah ya yarda, yanzu sai mu koma falo mu barta da huta idan an kawo kayan sai Hujayrah ta fara, babu abin da zamu ce da ke Hujayrah sai Allah ya saka da..."
Da sauri Hujayrah ta ce
"Aa Abbu kai a matsayin uba kake a wurina, babu godiya a tsakaninmu, hakƙina ne na yi amfani da baiwar da Allah ya bani wurin taimaka muku, don bani da abin da zance sai Allah ya saka da alkhairi don kun ɗaukeni kamar ƴarku, kun nuna min soyayya a lokacin da mutane ke guduna, taya bazan taimaka muku ba, ai sai inda ƙarfina ya ƙare in shaa Allah "
Murmushi Alhaji ya yi daga bisani kowa ya dawo falo aka bar Hajiya momma a ɗaki bayan an kunna mata suratul Baqarah a cewar Hujayrah.
Kowa ya yi jugum-jugum a falo, baka jin motsin komai sai ƙarar A.C, kusan awa daya ta gota don har an fara kiran sallar Asr, Alhaji, Mas'ud da Arqam suka wuce masallaci, su kuma Halima, Nazima, Hujayrah da sauran matan suka yi shirin sallar Asr... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
A ɓangaren Hajiyan Sama a rikice ta koma ɗakinta, bata tsaya ko'ina ba sai a falonta na sama, abin duniya ya isheta, ɗan lissafinta da ya rage Hujayrah ta rushe. Wani irin zafi da raɗaɗi zuciyarta ke yi mata, sai faman kai kawo take yi a ɗakin tana furzar da iskan bakinta. Ta daɗe a haka daga bisani ta tsaya cak! Tana sauke ajiyar zuciya, wayarta ta ɗauka a saman centre table ta shiga received calls ta kira wayar Hajiya Zinatu. Ring biyu wayar ta yi Hajiya Zinatu ta ɗauki kiran lokacin tana asibiti inda Rayyan yake. Fuskarta ɗauke da fara'a ta kara wayar a kunnanta, kafin ta yi sallama Hajiya Sama ta yi saurin cewa
"Aminiya akwai matsala?"
Rasss! Ƙirjin Hajiya Zinatu ya bada duk da bata san wace matsala ce ba amma tabbas ya shafeta.
"Matsala kuma Aminiya, baki yi yadda boka mai zaki yace ba ne?" Hajiya Zinatu ta ce tana fita daga cikin asibitin zuwa wurin bishiyu don maganar tasu tana buƙatar sirri.
"Ko ɗaya Aminiya duk na yi abin da boka ya ce sai dai an samu wata tsinanniyar yarinyar da nake tunanin tana shirin lalata mana aiki ni da ke" Hajiyan Sama ta ce tana zama saman kujerarta mai cin mutum biyu tare da miƙar da ɗayan ƙafarta a saman kujerar.
Waro idanu Hajiya Zinatu ta yi waje kamar tana kallon Hajiyan Sama ta ce
"Kai! Wace ƴar kutumar uban yarinya ce haka take shirin jefa kanta cikin halaka, da alama bata san ko mu su waye ba ne ko?"
Murmushin takaici Hajiyan Sama ta saki tana tuno yadda Hujayrah ta gaggasa mata magana son ranta a gaban kowa amma babu wanda ya iya kwaɓa mata har Alhaji.
" Ina yarinyar da Razina ta taɓa shigowa da ita falona lokacin kin zo har ina cewa tsintattaciyar mage bata taɓa zamantowa mage. Hujayrah sunan yarinyar bata da kunya ko kaɗan, duk kwarjinina haka yarinyar take faɗa min magana son ranta ba tare da ta ji tsorona ba, anya ma yarinyar mutum ce kuwa, don kamar mai aljanu haka take"
"Amma kuwa ta ɗebo ruwan dafa kanta da kanta, yanzu dai mece ce mafita kar mu ɓata lokaci yarinyar ta yi nasarar warware mana aikinmu" cewar Hajiya Zinatu.
"Zuwa gobe ko jibi sai mu tafi Rigar Alhaji baushe, bana son a gane wani abu a tattare dani, Kema haka"
"Hakane yanzu haka ina asibiti dubo Rayyan, Kin san har yanzu Prof baisan da matsalar Rayyan ba?" cewar Hajiya Zinatu.
"To ya jikin nashi, fatan yana samun sauƙi ko?"
Taɓe baki Hajiya Zinatu ta yi sannan ta ce
"Aminiya ina wani samun sauƙi nan, kamar ƙara masa ciwon ake yi kullum ni abun ma tsoro yake bani wallahi, hauka fa ya koma yana yi tuburan"
"Zuwa goben idan mun je wurin boka mai Zaki, sai ki nemi taimako wurin shi ƙila a dace" cewar Hajiya Zinatu.
"Sai goben, bari na koma cikin asibitin na baro Nadiya ita kaɗai "
Daga haka suka yi sallama sai ta shiga cikin asibitin. Sauke wata nauyayyan ajiyar zuciya Hajiyan Sama ta sauke bayan ta yanke kiran.
"Za ki san kin taɓa tsuliyar dodo Hujayrah,taki ta kusa ƙarewa" cewar Hajiyan Sama tana sakar wa kanta wani munafikin murmushi sannan ta wuce bedroom ɗinta... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
Sosai hankalin Hajiya Ramla ya tashi jin Hajiya Mariya na ce mata Sabrin na nan tana fizge-fizge, kai tsaya driver ya kai ta asibitin. Da gudu-gudu da shiga ɗakin turuss! Ta tsaya gabanta na mugun bugawa ganin wani likita da lulluɓe fuskar Sabrin da farin mayafi, kowa a ɗakin kuka yake idan ka cire Alhaji Sambo Dala wanda idanunsa sun kaɗa sun yi ja kamar jan gauta. Fuskarsa ba a magana domin kamar an maresa haka ta yi ja kasancewarsa fari sosai sai Akmal shi ma idanunsa sun ƙadan sun yi ja ga hawaye na zubo masa ba tare da ya Share ba. Sakhiyya, Hajiya Mariya da Tahseen wacce ita ma shigowanta ke nan kuka suke sosai mai tsuma rai. Kamar wacce aka cire wa lakka a jiki haka Hajiya Ramla ta ƙaraso cikin ɗakin, wasu zafafan hawaye na zubowa daga kwarmin idanunta.
A Duk cikin yaran Yayanta Ayyub babu kamar Sabrin, akwai ta da haƙuri da wasa da dariya, ga hankali da natsuwa. Wani lokacin idan ta yi magana za ja yi tunanin faɗa mata aka yi saboda azancin da ke cikin maganar. Kuka ne ya suɓuce mata lokacin data yaye mayafin,sosai gabanta ya buga ganin kamar ba Sabrin ba, ta zama kamar ƙwarangwal, idanunta sun shige ciki, hancinta ya ƙara tsayi kumatunta sun shige ciki babu kyawun gani. Sun daɗe a haka daga bisani suka ɗauketa zuwa gida. Hajiya Ramla ta kira Yayanta Imran ta faɗa masa rasuyar Sabrin lokacin ya fito masallaci shi dasu Arqam, kai tsaye suka wuce mota saboda su isa da wuri a sallace gawar tare dasu. Duk da ba shiri yake da ƙanin nasa ba amma ya tausaya masa sosai, lokacin da suka isa gidan Limamin masallacin Juma'a na areas su ne ya gabatar da sallah, wata malamar islamiyya ce ta yi wa Sabrin wanka wanda daga bisani aka sallaceta. Kafin a wuce da ita maƙabarta Senata ya iso da wasu daga cikin abokansu, sai suka bi sahun masu tafiya maƙabarta.
Bayan sun dawo sai Alhaji Imran ya yi wa Alhaji Sambo Dala gaisuwa. Kasancewa ba a cikin natsuwarsa yake ba, sannan ba lokacin nuna kiyayya ba ne ko gaba, sosai ya amsa masa gaisuwar cike da kulawa. Haka Mas'ud da Arqam suka yi wa Akmal da Khalil gaisuwa kasancewar Khalil ya iso da wuri gidan tare dashi aka sallaci gawan. Mas'ud ya koma gida ya ɗauko Hajiya Nafisa dasu Nazima amma banda Hujayrah da Razina da yake har an kawo kayan da Hujayrah take buƙata, babu bata lokaci ta fara aikinta. (My Esteem fans kuna tunanin abin da nake tunani kuwa 🤭da a ce har da Hujayrah aka zo wurin ta'aziyya nan mai kuke tunanin zai faru,😂😂😂).
Sai bayan magrib Hajiya Nafisa da su Arqam suka koma gida. Hajiya Ramla da Tahseen a nan za su kwana, abu biyu ke cikin zuciyar Hajiya Ramla:mutuwar Sabrin wacce ta yi matuƙar girgizata sai tashin hankalin da ta baro a gidan Yayanta Imran wanda take tsoran kar wannan shaiɗaniyar yarinyar Hujayrah ta warware asirin. Idan kuwa hakan ta tabbata to babu makawa za a fasa auran tunda Hajiya momma ba son auran take ba tun fil-azal. Dole ta yi gaggawan ɗaukar mataki akan Hujayrah tun kafin ta ɓallo mata wani sabon aikin mai zaman kansa.
Babu wanda take zargi da yi wa Hajiya momma asirin ƙuraje sai kishiyarta Hajiyan Sama, tun ba yau ba tasan ba tsakani da Allah take zaune da Hajiya momma ba, Duk da bata san wace manufa take da shi akan Hajiya momma ba amma hakan da ta yi ya nuna akwai abin da take son cikawa akan Hajiya momma. Ta daɗe tana tunani-tunaninta a ɗakin da aka basu ita da Tahseen daga baya bacci ya ɗauketa ba tare da ta ankara ba... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*Legacy Housing Estate, Bulunkutu, Maiduguri, Borno State. Nijeriya*
A razane Sheikh Minnir ya miƙe daga zaunan da yake yana faɗin
"Ba a ganta ba?"
A can Ya kura take sanar masa har yanzu Halima bata dawo gidan ba, da yake lokacin da ta dawo daga gidan maƙotansu yarinyarta ta sanar mata Halima ta je amsar saƙo wurin mijin da za ta aura. Bata kawo komai a ranta ba, sai kawai ta shiga harkokinta na cikin gida, shiru-shiru babu Halima babu alamunta har kusan bayan Isha'i bata dawo ba, ita kuma bata da lambarta balle ta kira ta ji tana ina. Wata shawara ta zo mata akan ta kira mahaifinta Sheikh Munnir ta ji ko ta dawo gida ne. Sosai mamaki ya cikata jin bata dawo gida ba, shi ma hankalinsa ya tashi sosai, Mom ma dai ta nuna hankalinta a tashe yake a zahiri amma a baɗini ko a kwalar riganta duk da wani sashe na zuciyarta na jin tsoran kar dai guduwa ta yi wurin dangin mahaifiyarta, idan kuwa hakane shikenan ta rusa mata shirin da take yi akanta. Sheikh Munnir ya ce wa Ya kura ta bari shi zai bincika da kasan yanzu. Idan kuma da dawo gobe sai ta kira ta sanar masa. Washe gari ne Ya kura ta kira Sheikh Munnir ta sanar masa akan har yanzu Halima bata dawo ba. Katse kiran ya yi ya fara sintiri a falon hannunsa goye a bayansa yana cije lips ɗinsa, Mom da ke zaune ta dubesa cike da damuwa ta ce
"Kar dai Halima guduwa ta yi wurin dangin mahaifiyarta "
Cak! Ya tsaya daga kai kawon da yake a cikin falon, da sauri ya juyo ya kafeta da jajayan idanunsa wanda har sun sauya kala saboda ɓacin rai. Ciro wayarsa daga aljihu ya yi ya kira wata numba. Kamar jira ake Sheikh Munnir ya kira wayan bugu ɗaya aka ɗauki kiran. Bai jira mai za a ce ba ya fara magana cikin kakkausan muryarsa da cewa
"Ina so ku yi min kidnapping ɗin Abdul, zan tura muku hotonsa da address ɗinsa, idan Kuma ya yi muku jayayya ku bindige min kansa"
Ƙit! Ya katse kiran tare da sauke wata sassayyar ajiyar zuciya. Duban Mom ya yi da cewa
"Nasan ta gudu wurin dangin mahaifiyarta sannan ba kowa ya sakata gudu ba illa wannan shege yaro da yake tunanin wuyansa ya isa yanka, zan yi maganinsa da hannunsa sannan babu wanda ya isa ya hanani aura wa Halima mijin da na zaɓa mata,jin su kawai nake har ya yayyan mahaifiyarta ba ƙyalesu zan yi ba,Mts!"
Ba tare da ya saurari amsarta ba ya haye sama zuwa sashensa. Taɓe baki ta yi sannan ta ci gaba da latsa wayanta... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*Kwanar Faru ƙwai, Kaduna state. Nijeriya*
Bayan Kakulle ta riƙo little Zakari zuwa ɗakinta sai aka bar Alhaji Zakari daskare da mashin ɗinsa a tsakar gida, ya daɗe a tsaya daga bisani ya shige da mashin ɗinsa sashen Hannatu sannan ya nufo sashen Zaliha wanda yake kusa da sashen Hannatu . Sautin shassheƙan kuka ya ji yana tashi daga cikin ɗakin, da sauri ya ƙarasa ciki don ya ji ko lafiya. Turuss! Ya tsaya yana kallon Zaliha wacce take ta kuka kamar wata ƙaramar yarinyar, ciki ya ƙaraso hankalinsa tashe yana faɗin
"Zalihatuwata lafiya? Wa ya taɓaminke?"
Wani malolan baƙin ciki ne ya taso wa Zaliha tun daga ƙahon zuciyarta bai tsaya ko'ina ba sai a wuyanta, sosai ta ji ta tsani Alhaji Zakari, ko muryarsa bata son ji, madadin kalamansa su sakata farin ciki jin ya nuna damuwarsa a kanta sai ma ƙara mata wani ɓacin rai ya yi a bisa ɓacin ran da take ciki. Zai taɓata ta yi saurin matsawa gefe, a ɗan zafafe take cewa
"Ka sakeni Zakari! Wallahi na tsanake kamar yadda na tsani ranar mutuwata "
Sake matsowa kusa da ita ya yi kamar mara zuciya yana cewa
"Haba Zalihatuwata ni ne fa Masoyinki Zakari, wallahi bazan iya rabuwa da ke ba Zaliha, kece farin cikina, bar kukan kin ji"
"Wallahi bazan riƙe shege ba gwara ka dawo da matarka ta raineshi don ba zama zan yi gidan nan ba, idan kuma uwarka ce za ta riƙe shi shikenan, gwara ka sakeni don na fasa zaman auran da kai, a tunanina zan samu farin ciki ni da yarana a rayuwar aure da kai, sai kuma akasin haka, ko sati biyu ban yi a gidanka ba har na rasa babban ɗana Ɗahiru a dalilin auranka , wayyo ooo ni Zaliha Na shiga uku na lalace, Ɗahiruna ya tafi ya barni saboda son zuciya da ƙwaɗayina"
Alhaji Zakari ya rasa yadda zai ya lallashi Zaliha ta daina kukan, domin har cikin kwanyar kansa yake jin kukanta, ganin taƙi haƙura sai ya miƙe ya bar mata ɗakin. Bai zarce ko'ina ba sai ɗakin Kakulle. Sallama ya yi sai ta amsa masa ciki-ciki ba tare da ta ɗago ta dubesa ba. Kamar wanda yake tsoran ƙwai ya fashe masa ya cikin ciki, samun wuri ya yi ts rakuɓe. Little Zakari na kusa da ita yana saɓa loman tuwon kamar wanda ya shekera bai ci abinci ba. Ƙurawa yaron ido ya yi yana kallon yadda yake cikin abinci hankalinsa kwance. Sun daɗe a haka daga bisani Kakulle ta katse shirun da cewa
"Ɗan inna ka bani kunya! ban taɓa tunanin za ka iya aikata zina ba koda kuwa a mafarki ne! Yanzu da girmanka ka rasa abin da za ka aikata sai zina kamar baka da mata! Haba don Allah! Ko yaranka ka samu da aikata zina sai inda ƙarfinka ya ƙare wurin hukunta su amma kai ta karan kanka har da tsarabar shegen ɗa, Inna atuni minal zalimina ni Hindatu! "
Ko sau ɗaya Alhaji Zakari bai yi gigin ɗago kansa daga duƙyen da yake ba, sosai nadama da dana sani suka ɗarsu a zuciyarsa, tabbas ya yi laifi mai girma kuma mai munin gaske wanda mutane za su dinga jifansa da iyalansa dashi, yanzu wani daɗi ya ji a zinar da ya aikata illa dattin da ya kwaso wa kansa na haifan shege. Kakulle bata jira cewarsa ba ta ci gaba da maganarta da cewa
"Aikin gama ya gama, daman tun kan a iya ya dace a kiyaye. Gashi matarka ta ce baza ta riƙe shege ba, na rasa me ya shiga kanka ka saki Hannatu uwar yaranka Ɗan inna, wannan Zaliha da ka aura ba mutuniyar arziƙi bace, ko ni bata bari ba. Ni anya ba asiri ta yi maka ba kuwa Ɗan inna? "
Sai a sannan ya ɗago da rinannun idanunsa wanda suka sauya kala ya duban Kakulle ya ce
" Inna babu asirin data yi min Zaliha, kawai dai Allah ne ya jarabceni da so da ƙaunarta "
Taɓe baki ta yi san na ta ce
" To Allah shi kyauta, zai zauna dani a nan idan komai ya lafa sai an abin da ya dace a yi. Sannan maganar ta biyu ita ce ka shirya bayan kwana bakwan yaron matarka za mu je ka kaimu inda Hujayrah take aure muga gidanta , daman saboda rasuwar nan ne ya hana na tado da maganar"
Dummmmm! Da matuƙar ƙarfi zuciyarsa ta buga, babu shiri ya ɗago da jajayan idanunsa cikin tuɓutar baki ya furta
"Wacce yanzu haka ake nema"
"Ta ɓace ne Hujayrah? Na shiga uku na lalace ni Hindatu"
Sai a sannan ne tuna da katoɓarar da ya yi, da sauri ya gyara zancensa da cewa
"A'a Inna ba ita nake nufi ba, wata yarinya ce ta ɓace ɗazu, mai unguwa yake sanar min ko iyayenta sun ganta"
Tsura masa idanu kawai ta yi ba don ta yarda da abin da ya faɗa ba ne, koma mai yake ɓoyewa zai fito fili.
"Bayan an yi sadakar bakwai washe gari sai ka shirya ka kaimu garin da take"
"Allah ya kaimu"
Yana gama faɗin haka ya miƙe yabar ɗakin zuciyarsa a jagule.Bai tsaya ko'ina ba sai a gindin bishiyar da yake hutawa musamman idan duniyar ta yi masa zafi. Dole yasan abin yi tun kafin asirinsa ya tonu, gashi yanzu haka Alhaji Sambo Dala nemanta yake ruwa ijallo ya gaza samunta duk da yaran da suke mishi aiki ina gashi karan kaɗai miya. Samun mai unguwa zai yi ya nemi sharawararsa tun kafin wankin hula ya kai sa dare. Yana gama zance zucin ya miƙe tsaye yabar wurin zuwa fadar mai unguwa amininsa ... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
*Gida-dubu gubi Housing Estate, Bauchi state. Nijeriya*
A ɓangaren su Hujayrah bayan an kawo mata ruwan zam-zam da sauran kayan da take buƙata, sai Mas'ud ya zo ya ɗauki Hajiya Nafisa da su Nazima zuwa gidan Uncle Ayyub ta'aziyya. Razina ka ɗai ce ba a ta fi da ita ba saboda ta taya Hujayrah zama. Ruwan zam-zam ɗin ta zuba a tsaftatacciyar roba mai girma, sai data ɗauro alwala ta saka hijab sannan ta kalli gabas hannunta riƙe da carbi tana ja tana tofawa. Har su Alhaji da Hajiya Nafisa suka dawo gidan bata ƙarasa addu'o'in da take yi ba, ta yi kusan mintuna ashirin tana addu'ar daga bisani ta kammala. Kasancewar babbar jarkar ruwan zam-zam aka siyo a wani katafaren Islamin chemist, Sai kawai Hujayrah ta juye ruwan ta yi addu'a. Wata babbar gora ta zuba ruwan, ta kusan cikata sannan ta juye saurin cikin jarkar. Cike da girmamawa ta miƙa wa Hajiya Nafisa babbar gorar tare da cewa
"Mammi wannan ruwan goran nan ki maida shi ruwan shanki sannan ki dinga shafa sauran ruwan a saman cikinki tare da yin Bismillah, sannan idan ya ƙare sai a sake siyo wani ruwan zam-zam ɗin na yi addu'ar. Ina kyautata zaton in shaa Allah asirin zai warware, bayan haka ma ki yawaita sauraron suratul Baqarah koda kuwa bacci za ki yi, ki daina yarda da ƴan aikin ku saboda wani lokacin ta hanyarsu ake cutarku"
"In shaa Allah Hujayrah zan yi yadda kika ce, ban da abin ce miki sai Allah ya albarkaci rayuwarki, ya zaɓa miki gwarzo miji na gari"
"Ameen ya Rabb" cewar Arqam, sai da kowa ya juyo yana kallonsa, kauda kansa ya yi cike da basarwa. Ita kuwa Hujayrah wani miki ne Hajiya Nafisa ta fama mata, har mantawa take akwai aure a kanta. Sai wurin 8:10pm na dare su Hajiya Nafisa suka yi sallama da Alhaji suka koma gida. Bayan tafiyarsu Hujayrah da su Alhaji suka koma bedroom ɗin Hajiya momma, suna isa tana farkawa da wata razananniyar ƙara tare da banƙarewa tana fizge-fizge gwanin ban tausayi. Da sauri su Hujayrah suka isa bakin gadon. Kofi Hujayrah ta umurci Razina ta kawo, jiki na rawa ta ɗauko kofin ta kawo wa Hujayrah, buɗe jarkar ta yi ta tuttula ruwan a cikin kofin sannan da kafa a bakin Hajiya momma, rabin ruwan ya shiga sauran kuma suka zube. Ragowan daya rage Hujayrah ta fara shafa mata a duk ilahirin jikinta. Ihu kawai Hajiya momma take yi tana sumbatu, dole sai da Arqam da Alhaji suka riƙeta sannan Hujayrah ta samu damar kammala shafa ruwan addu'ar a jikinta. Wata azaba Hajiya momma take ji a jikinta a duk lokacin da Hujayrah ta shafa mata ruwan addu'ar. Sannan ruwan da tasha kamar ta zuba wa cikin ruwan dalma ne saboda wani irin tuƙuƙin azaba cikinta yake mata. Ihu da kururuwa take tana cewa
"Bana soo! Ki daina shafa min don Allah! Akwai azabaaaa, ki dai don Allah! Wayoooo! Allahnaaaaa!!"
Har Hujayrah ta kammala shafa mata bata bar ihun ba. Tana kammala shafa mata bacci ta ɗauketa sai sauke tagwayen ajiyar zuciya take akai-akai. Ɓoyayyan ajiyar zuciya kowanne a cikin ɗakin ya sauke.
" Abbu ni da Razina za mu kwana a falo saboda jikin Mammi, yanzu ta samu bacci nasan da matuƙar wuya ta farka cikin dare, zuwa gobe sai mu jira Ikon Ubangiji"
"Hakane Allah yasa a dace, Arqam kai sai ka koma part ɗinka, Ni yanzu zan wuce ɗakina, Allah ya tashemu lafiya"
"Ameen ya Rahman"
Daga haka Alhaji da Arqam suka bar part ɗin Hajiya momma kowa ya nufi nashi ɓangaren, su kuma Hujayrah suka kwanta a falo saman kujeru bayan an kunna wa Hajiya momma suratul Baqarah sai suka kulle kofar da addu'a... ✍️
🌎🌎🌎🌎🌎🌎
A ɓangaren Hajiyan Sama bayan sallar Asr Khalil ya kirata a waya ya sanar mata rasuwan Sabrin, da yake tana ɗan shiri sama-sama da Hajiya Mariya saboda abotar Khalil da Akmal. Ce masa ta yi sai sadakar uku za ta zo ta'aziyya saboda gobe za ta fita ita da aminiyarta zuwa jibi za ta je. Duk da ransa bai so ba haka ya haƙura, ya so a ce yau ɗin nan ta zo ko kuma shi ya zo ya ɗaukota amma tun da ta ce haka maybe she is not in good mood. Daren ranar Hajiyan Sama bata rintsa ba kamar yadda Hajiya Zinatu ta kasa bacci. Zance kusan haka yake gun Hajiya Ramla duk abu ɗaya suke wa tunani a kai wato *UWAR GAYYA HUJAYRAH* kowa yana da nasa mugun nufi a kanta. Baiwar Allah bata san suna yi ba don bacci mai daɗi ta yi har da mafarkai masu daɗi ta yi abinta. Kamar yadda su Hajiya Ramla suka kasa bacci haka Alhaji Sambo Dala ya kasa bacci shi ma tunaninsa akan abu ɗaya ne wato *Hujayrah* ina zai ganta hankalinsa ya kwanta, Ina zai samu koda kuwa labarinta ko ya samu natsuwar zuci yasan yana da hope ɗin samunta koda kuwa ba yanzu ba ne. Haƙiƙa idan bai yi wasa ba hukuncin ƙungiya yana gab da sauka a shi karan kansa. Dole ya zage damtse wurin nemota kar yaga fushin DODO ƘURNUSSA. domin fushinsa babbar matsala ce a wurinsu bama shi kaɗai ba.
*Washe Gari*
*Ƙarfe 9:15am na safe*
A daidai wannan lokacin motarsu Hajiya Sama ta iso Rigar Alhaji Baushe, bayan sun ɗan huta daga bisani amintaccen dribansu ya ci gaba da tafiya cikin ƙurmin dajin zuwa inda dribansu ya saba parking motar. Bayan ya yi parking Sai suka ƙarasa inda dutse da boka mai Zaki yake, kamar kodayaushe surkulle suka fara yi cikin ƙanƙanin lokaci dutsen ya tsage, tamfatsetsiyan ƙofa ta bayyana suka ci gaba ciki. Inda ake zama suka zauna a duk lokacin da suka zo. Lokacin guda wutar candles da ke kewaye a ɗakin ta ɗauke ɗufff! Wutar da ke ci a tsakiyar daƙin ta yawaita kamar tashin iska, girgiza ɗakin ya fara, wani irin sauti bara daɗin sauraro ke tashi. Lokaci guda candles ɗin ke kawo wuta suna ɗaukewa. Kamar walƙiya boka mai Zaki ya juyo yana daga musu wata uwar tsawa mai matuƙar firgitarwa wacce bai taɓa yi musu ba. Nan da nan hantar cikinsu ta kaɗa, tsoro da firgici ya ɗarsu a zukatansu lokaci guda. Babu za to babu tsammani suka ji amon muryarsa mai firgitarwa yana cewa... ✍️
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
***