Free chapter · Read without an account

MATAR GIDA PAGE 89

by Maimuna Bala · MATAR GIDA

*MATAR GIDA* BOOK 2


*SHUUKRAN*/022



P89



Washe gari misalin ƙarfe tara da wasu mintina na safe Amirah ta kai abin kare a hospital bayan ta kai yara makaranta ta biya ta asibiti,yau baza ta samu damar tafiya aiki ba,tun misalin karfe takwas ta kira oganta ta sanar masa Ɗalha na kwance asibiti babu lafiya wanna dalilin yasa ogan nata ya bata hutun kwanaki biyu yau da gobe,sosai Amirah ta masa godiya,sallama dauke a bakinta ta shiga emergency word inda aka shigar da Ɗalha daren jiya da suka kawo sa,ganin baya ɗakin yasa ta tambaye wata nurse dake duty, nan nurse ɗin ta faɗa mata an canzawa  Ɗalha ɗaki nan ta faɗa mata lamba ɗaki da Ɗalha yake,dai dai kofar ɗakin ta tadda Muhsin tsaye,kallo ɗaya ta masa ta ga tashin hankali da damuwa ƙarara kwance fuskarsa,nan take Amirah ta ji gabanta ya yanke ya faɗi amma sai ta daure ta ƙaraso inda Muhsin ke tsaye ta masa sallama fuska babu yabo babu fallasa ya amsa sallamar a hankali Amirah ta ajiye basket ɗin abinci da take riƙe da shi ta mayar da dubanta ga Muhsin daga haka ta ce ''lafiya na ganka tsaye waje?" Muhsin ya yi murmushi da iya karsa leɓe ya ce ''lafiya likita na ciki yana duba sa'' jinjina kai Amirah ta yi kafin ta ce ''likitan ya dade da shiga duba sa ne?" Muhsin ya ce ''eh za su iya kaiwa 20 minute a ciki'' a hankali Amirah ta ce ''ok,shi da wa suke ciki?" ba tare da kallon fuskar Amirah ba Muhsin ya ce ''tare yake da nurses biyu'' Amirah ta kafe Muhsin da ido ganin gaba ɗaya har sannan baya cikin nitsuwarsa sannan ya ƙi kallon fuskarta hakan yasa Amirah gyara tsayuwa ta ce ''akwai abinda ka ke ɓoye min ne?" da sauri Muhsin ya ce ''a'a babu me ki ka gani?" ɓoyayyar ajiyar zuciya Amirah ta sauke kafin daga bisani ta ce ''babu komai kawai gani na yi kamar baka cikin nitsuwarka da kamar akwai abinda ke faruwa da ka ke ɓoye min'' a hankali Muhsin ya kai hannu ya shafa fuskarsa, fuskarsa cike da damuwa daga haka ya juyu yana kallon Amirah da kyau ya ce ''ba haka bane bana son daga maki hankali ne,bayan sallar asuba ya ce na taimaka masa zai shiga bathroom,cikin ikon Allah da kafafunsa ya shiga bathroom amma ya ƙasa fita karshe ni na taimaka masa ya fita daga bathroom lafiya ƙalau ya yi sallar asuba bayan na taimaka masa ya kwanta sai yake faɗa min hannunsa na dama da kafarsa ta dama yana ji kamar ba a jikinsa suke ba kamar wasa na ce masa ya yi motsi da hannunsa na dama amma ya ƙasa haka ma kafar na ce ya yi motsi da shi nan mai bai iya ba,da na ga da gaske bai iya motsa ɓaren jikin sa ɗaya sai na kai masa duka a hannu amma bai ji komai ba haka ma kafar damar na yi ta buga kafar amma bai ji komai ba hakan yasa na fita kiran likita,tun misalin ƙarfe shidda na safe likita tare da nurses suke ta kaiwa da komowa a ɗakin na tambaye su halin da yake ciki amma ba su amsa ni ba'' cike da tashin hankali Amirah ke kallon Muhsin mai hakan ke nufi kenan Ɗalha ya samu shanyewar barin jiki ko mai yake nufi kenan Ɗalha ya samu nakasa ko mai hakan ke nufi?ta yiwa kanta tambaya cikin zuciyarta da babu wanda zai amsa mata, cikin ɗan kankanin lokaci idanun Amirah suka riƙida suka yi ja sosai hankalinta ya tashi,wani irin jiri ke dibanta a hankali ta samu waje ta zauna saman ɗaya daga cikin kujeru dake cooridor ɗin word da aka tanadar wa masu zuwa dubiya,Muhsin yana lura da yanayin da take ciki a hankali ya rintsa idanunsa cike da tausayin Amirah da Dalha cikin zuciyarsa yana addu'a Allah yasa Ɗalha bai samu shanyewar barin jiki ba,bayan wasu ƴan mintina Muhsin ya mayar da dubansa ga Amirah ya ce ''adda'u za ki masa Allah ya kubutar da shi daga abinda muke masa tsaro,bayan awa guda likita tare da nurses dake word ɗin da Ɗalha ke kwance suka fito da wani irin sauri Amirah tare da Muhsin suka nufi likitan sun tambayarsa jikin Ɗalha kallon su ya yi na wasu ƴan sakanni kafin daga bisani ya ce su biyo sa office dinsa,bayan shigowar su  office ɗin ne ya yi masu nuni da kujera ya ce su zauna duk zaune cike da zullume,bayan likitan ya zaune ne ya kalle Muhsin da Amirah ya ce ''kamar yadda na faɗa maku daren jiya mun yi bincike mun gano patient yana fama da hawan jini,to a yanzu dai jinin nasa ya haura sosai wanda hakan zai iya haifar masa da shanyewar ɓari guda a yanzu dai mun yi nasarar dakile matsalar amma zamu cigaba da sa masa ido da basa kulawa ta musamman dan  gujewa faruwar hakan'' cike da rashin gamsuwa da rashin fahimta Amirah ta kalle likitan ta ce ''kana nufin bai samu shanyewar barin jiki ba? ko me ban fahimta ba" ajiyar zuciya likita ya sauke kafin ya gyara zama daga haka ya ce ''akwai abinda ake kira da Paraparesis paralysis wato shanyewar jiki daga ƙasan sassan jikin dan adam kugu da kuma kafa,ƙafa ɗaya ko biyu,wanda ya samu wannan lalurar zai iya warkewa bi ma'ana ko a yanzu barin jikinsa ya shanye in aka yi masa amfani da magunguna da allurai in kuma ya bi dokokin magunguna  da zamu daura sa a kai zai iya warkewa'' fuskar Amirah dauke da damuwa ta ce ''kana nufin ya kamu da Paraparesis paralisis?" a hankali likita ya sunkuyar da kansa ƙasa kafin a hankali ya ce ''yes ma'am..amma ana warkewa,saboda haka ku kwantar da hankalin ku da yardar Allah zai samu lafiya''a hankali Amirah ta jingina bayanta da kujera da take zaune a kai sosai hankalinta ya tashi da kyar take iya sauke numfashi,lokaci guda hawaye ya shiga bin kuncinta ba tare da saninta ba kawai sai jin hawaye ta yi na bin fuskarta,zuciyarta cike da tambayoyi da babu mai amsa mata su me zai sameta ita da ƴaƴanta in Ɗalha bai samu lafiya ba?yaya rayuwarsu zata kasance shi kansa Ɗalha zai iya jure rayuwa a hakan?waɗan nan sune tambayoyi da suka cika mata zuciya jiki babu kwari Muhsin ya yunƙura tare da miƙewa tsaye fuskarsa cike da damuwa ya kalle Amirah cikin raunanniyar murya ya ce ''taso mu tafi'' Amirah da ta yi nisa cikin tunani ko kadan bata ji abinda Muhsin ya faɗa ba sai ya sake maimaita maganarsa a karo na biyu kafin Amirah ta kallesa idanunta sunyi ja sosai sun ciciko da hawaye tana son yin magana amma ta ƙasa hankali tashi ta bi bayan Muhsin







Misalin ƙarfe sha ɗaya na safiyar wannan rana Ammi ta diro garin Kaduna,ita ko Husnah tun misalin ƙarfe goma take asibiti kasancewar nan garin Kaduna take aure,bayan zuwan su Ammi ne Amirah ta sanar masu halin da Ɗalha yake ciki ba ƙaramin tashin hankali  Ammi ta shiga ba,duk yadda ta kai ga jureya sai da ta zubar da hawaye tana wa Ɗalha addu'a cikin zuciyarta,tunanuka iri iri cunkushe cikin zuciyarta, haka zalikah Husnah kuka ta rinƙa yi bil hakki da gaske tausayin Amirah da ƴaƴan Ɗalha ya cike mata zuciya,da ta kalle Ammi sai ta ji gaba ɗaya zuciyarta ta karaya,ganin su Ammi na tare da ita yasa Amirah cewa Muhsin ya je gida ya huta,amma Muhsin ya ce zai zauna har sai Ɗalha ya farfaɗo ganin da gaske yake yasa Amirah fadawa Ammi cewar tun daren Muhsin ke asibiti ya kamata ya je gida ya huta zuwa yamma sai ya dawo,bayan Amirah ta fadawa Ammi ne Ammi ta taso daga inda suke zaune ta nufi inda Muhsin ke zaune can nisa da su,wata kujera da babu kowa a kai Ammi ta zauna kafin ta fara yi magana cike da hikima,ba a son ran Muhsin ba ya tafi gida kamar yadda Ammi ta umurce sa,misalin karfe uku da wasu mintina na wannan rana Ɗalha ya farfaɗo,Amirah ce ta yi saurin zuwa kiran likita,a tare Amirah da likita suka jera har zuwa kofan word da Ɗalha yake,a kofar word Amirah ta tsaya yayin da likita ya shiga cikin ɗakin,bayan likita ya gama duba Ɗalha ne ya cewa Amirah da Ammi da kuma Husnah za su iya shiga wajen Ɗalha,bayan shigowarsu ɗakin bakunnansu dauke da sallam,Ɗalha na daga kwance bai iya amsa masu sallamar ba sai bin Amirah yake da ido, Ammi ta zauna saman kujera dake gefen gadon da Dalha ke kwance yayin da Amirah da Husnah na daga tsaye suna kallon Ɗalha kowacce fuskarta cike da tausayi,cikin muryarsa da bata fita sosai Ɗalha ya buɗe baki da naiyar gaida Ammi,a hankali Ammi ta kai hannunta saman nasa cikin kwantar da murya ta ce ''don't strees yourself is ok'' shiru Ammi ta yi tare da kai hannunta kan Ɗalha tana shafa sumar kansa,can ta bude baki a hankali ta ce ''duk muna lafiya ya jikin naka?" a hankali Ɗalha ya gyaɗa kansa alamar da sauki,daga haka Amirah da Husnah suka gaishi sa,shiru ya yi har sannan idonsa kan Amirah yana kare mata kallo ba tare da yace wani abu ba, bayan wasu ƴan sakanni ya buɗe baki a hankali tare da fadin ''ina son zan yi sallah'' ya faɗa tare da kallon drip dake hannunsa Amirah ce ta fita daga word ɗin zuwa office ɗin doctor ta faɗa masa Ɗalha na son zai yi sallah amma drip da aka sa masa bai ƙare ba,shiru likitan ya yi na wasu ƴan sakanni kafin ya fita daga office zuwa staff office Amirah na biye da shi,wasu nurses biyu maza ya umurce su da su bi Amirah su je su tsayar da drip ɗin Ɗalha,ya kuma umurce su da su daura Ɗalha a wheelchair in ba zai iya takawa ba,Amirah tare da nurses ɗin suka shiga word da Ɗalha yake,bayan shigowar su Ammi da Husnah suka fita word ɗin,ɗaya daga cikin nurses ɗin ne ya tsayar da drip da ke hannun Ɗalha tare da cire IV Turbing (wannan doguwar igiyar dake daukar ruwar drip daga drip bag zuwa hannun marar lafiya) cike da jure Ɗalha ya fara kokarin tashin zaune sai dai ko kaɗan  ƙafarsa ta dama taƙi motsawa kamar ba a jikinsa kafar take ba,ya yi iya yinsa amma ya ƙasa motsa kafar hakan yasa ya ɗago fuskarsa cike da tashin hankali yana kallon Amirah da nurses dake tsaye,a hankali Amirah ta sunkuyar da kanta ƙasa tana hana kanta kuka da ya taso mata,ɗaya daga cikin nurses ɗin ne ya yi karfen halin faɗin ''Sir, I think using a wheelchair will help relieve your physical stress'' ya kare magana cikin kwantar da murya fuskar Ɗalha dauke da wani irin expresion ya kalle nurse ɗin na wasu ƴan sakanni daga haka ya mayar da dubansa ga Amirah da taƙi kallonsa,jin ya yi shiru yasa nurses ɗin taimaka masa sun daura sa saman wheelchair,har cikin bathroom suka shigar da shi kafin daga bisani suka fita,bayan fitowarsu ne Amirah ta shiga bathroom ɗin har sannan taƙi kallon fuskarsa shima kuma bai ce mata komai ba,ita ta taimaka masa ya yi alwalah daga haka ta turasa zuwa ɗaki ta yi masa shimfida ya yi sallah, ya so yin Sallah a tsaye amma Sam ƙafarsa bata basa haɗin kai ba hakan yasa ya hukura ya yi sallar a zaune






*Ga masu bukatar karanta littafin matar gida yana arewapen daga farko,gaba ɗaya littafin kyauta ne*




*SHUUKRAN*

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol