Free chapter · Read without an account
ENGAGED
KADDARAR ZUCIYA
CHAPTER FORTY-THREE: 43
ENGAGED
JIDDAAH BARKUM
———-
Tun bayan da Inteesar ta ba Aliyu amincewar tura magabatansa gidan Daddy domin neman aurenta, wani irin natsuwa da farin ciki suka mamaye zuciyarsa, bai ƙara son ɓata lokaci ba, a gare shi, babu abin da ya fi so kamar ya mayar da Babygirl ɗinsa halal ɗinsa, a Katsina kuwa, Alhaji Kabeeru ya riga ya sanar da Yaya Abubakar da Adam cewa akwai baƙi da za su zo ranar Lahadi, tunda maganar Aliyu ce, babu wanda ya nuna mamaki, kowa ya san irin mutunci da tarbiyyar da Aliyu yake da su, da kuma yadda Daddy yake girmama shi, da misalin ƙarfe huɗu na yamma, wata baƙar mota da wata ash-coloured SUV suka tsaya a harabar gidan Alhaji Kabeeru, a cikin motocin akwai manyan ’yan uwan Aliyu, kawunsa Alhaji Sani, babban yayansa, da wasu dattawa da suka zo tare da su, Abubakar da Adam suka fito domin tarbarsu cikin girmamawa, “Barkan ku da zuwa,” “Barkanmu dai,” suka amsa cikin fara’a, bayan sun gaisa, Abubakar da Adam suka yi musu jagora zuwa falon baƙi, inda Alhaji Kabeeru yake zaune tare da wani tsohon abokinsa, Alhaji Musa, bayan an yi musabaha da gaisuwa, Daddy ya ɗaga kai yana kallon ɗaya daga cikin baƙin, nan take idanunsa suka faɗaɗa, “Laa ilaha illallah! Alhaji Sani?” Mutumin ya zaro ido cikin mamaki, “Alhaji Kabeeru?” A take suka fashe da dariya, “Subhanallah! Ashe kai ne?” Duk wanda yake falon ya yi murmushi, yana kallon yadda mutanen biyu suka nuna mamakin ganin juna, ashe Alhaji Sani da Daddy tsoffin abokai ne tun shekaru da dama da suka wuce, Alhaji Musa ma ya yi dariya, “Rayuwa kenan!” Bayan an gama dariya da tuna abubuwan baya, Alhaji Sani ya gyara zama, ya mayar da hankalinsa kan abin da ya kawo su, “Alhamdulillah, mun zo ne da alkhairi,” Daddy ya yi murmushi, “Madallah,” Alhaji Sani ya ɗan gyara zama, sannan ya yi magana cikin girmamawa, “Mun zo ne a madadin ɗanmu, Alhaji Aliyu Muhammad, ya ga ɗiyarku, Inteesar, kuma yana da niyyar aure, saboda haka, mun zo neman amanarta,” falon ya yi shiru na wasu daƙiƙu, Daddy ya ɗaga idanunsa ya kalli Abubakar, Abubakar ya amsa masa da murmushi, ya juya ya kalli Adam, shi ma ya yi murmushi, alamar sun gamsu da maganar da aka kawo, Daddy ya gyara zamansa, sannan ya dubi baƙin, “Alhamdulillah, Aliyu yaro ne mai tarbiyya da mutunci, mun san asalinsa, kuma mun san irin mutumin da yake, idan Allah ya kawo mutum na gari wajen ɗiyarka, bai kamata ka hana alkhairi ba,” ya yi murmushi mai cike da gamsuwa, “Mun ba ku amanar Inteesar, Allah Ya tabbatar mana da alkhairi,” nan take fuskokin baƙin suka haskaka da farin ciki, “Alhamdulillah!” “Allah Ya saka da alkhairi,” Alhaji Sani ya yi dariya, sannan ya girgiza kai cikin jin daɗi, “Alhaji Kabeeru kenan! Babu wahala a duk abin da aka saka da kai,” Daddy ya yi dariya tare da sauran mutanen, Abubakar ya yi murmushi, “Mu ma mun yi farin ciki da wannan haɗin,” Adam ya ƙara da cewa, “Allah Ya sanya alkhairi,” bayan an tattauna cikin girmamawa, aka cimma matsaya cewa za a ɗaura auren bayan wata takwas, domin Inteesar ta samu damar kammala final year ɗinta cikin kwanciyar hankali, kowa ya gamsu da wannan shawara, kowa ya yi farin ciki, bayan an gama komai, aka yi addu’o’i masu albarka, sannan baƙin suka yi sallama suka kama hanyarsu ta komawa, a wannan rana, an kammala wani muhimmin mataki na rayuwar Aliyu da Inteesar, amma Aliyu bai san yadda zai yi da farin cikin da yake jiransa ba.
Aliyu kuwa yana gida kamar wanda aka ɗora wa ƙaya, tun da safe ya kasa zama lafiya, ya yi ta zagayawa cikin gida, yana duban wayarsa lokaci-lokaci, har Safiyya ta fara lura da yadda hankalinsa yake wani wuri dabam, ta kalle shi, sannan ta tambaya, “Kamar dai akwai wani abu, ko?” Aliyu bai amsa ba, ya ɗan yi murmushi kawai, yana ƙoƙarin ɓoye yadda zuciyarsa take bugawa da sauri, a ransa, addu’a ɗaya yake ta yi, Ya Allah, Ka tabbatar min da alkhairi, yana zaune a parlour ɗin lokacin da wayarsa ta yi ringing, da ya ga sunan kawunsa, Alhaji Sani, sai ya miƙe tsaye nan take, ya fice zuwa harabar gidan kafin ya ɗaga wayar, kamar yana son ya samu wuri mai natsuwa domin jin abin da zai faɗa masa, “Assalamu alaikum, Uncle,” “Wa alaikumus salam,” Aliyu ya haɗiye yawu, “Uncle…” Dattijon ya yi murmushi a ɗayan ɓangaren wayar, yana jin yadda ɗan nasa ya kasa ɓoye fargabarsa, “Malam Aliyu,” “Na’am, Uncle?” “Ka shirya?” Gabansa ya faɗi, “Uncle?” Sai Alhaji Sani ya fashe da dariya, “An ba ka Inteesar Kabeeru, halal-malal!” Na ɗan lokaci, Aliyu ya kasa magana, wani irin shiru ya mamaye shi, idanunsa suka cika da hasken farin ciki, sannan ya lumshe su a hankali, “Alhamdulillah…” Muryarsa ta dashe, “Alhamdulillah…” Kafin kawunsa ya ƙara cewa komai, Aliyu ya durƙusa ƙasa, ya yi sujjadar godiya, hawayen farin ciki suka zubo daga idanunsa, tsawon watanni da dama… Bayan gwagwarmaya… Bayan addu’o’i marasa adadi… Allah Ya buɗe masa ƙofa, an ba shi Inteesar, Babygirl ɗinsa, matar da ta sa ya sake fahimtar ma’anar soyayya a wani sabon yanayi, matar da ya zaɓa duk da bambancin shekarunsu, duk da kasancewarsa mai mata biyu, da dukkan abubuwan da suka sa ta yi jinkirin amincewa da shi, yanzu iyayenta sun amince, sun ba shi amanarta, bayan ya gama sujjadar, ya zauna a hankali, yana murmushi shi kaɗai, ya share hawayensa, sannan ya ɗauki wayarsa, ba zai iya jira ya ji muryarta ba, amma kafin ya kira ta, sai ya fara rubuta mata saƙo, assalamu alaikum, Mrs. Future Aliyu ❤️, Alhamdulillah… You are officially mine, Babygirl, 💍❤️ Ya sake karanta saƙon, murmushi ya ƙara faɗaɗa a fuskarsa, sannan ya aika mata, a wannan lokacin, zuciyarsa ta samu wani irin natsuwa da ya daɗe bai ji ba, Inteesar tana zaune a gefen gadonta tana duba notes ɗinta lokacin da wayarta ta yi ƙarar shigowar saƙo, ta ɗauka cikin natsuwa, ba tare da ta san irin labarin da yake jiranta ba, da ta buɗe saƙon Aliyu ta karanta kalaman da ya rubuta, sai idanunta suka cika da hawaye, wani irin murmushi mai cike da kunya da farin ciki ya bayyana a fuskarta, ta matse wayar a ƙirjinta, zuciyarta na bugawa da sauri, “Alhamdulillah…” ta furta a hankali, “Thank you, Ya Allah…” Ta sake kallon saƙon, kamar tana son ta tabbatar da cewa ba mafarki take yi ba, you are officially mine, Babygirl, ta lumshe idanunta, tana jin wani irin farin ciki da ba ta iya bayyana wa kowa, daga wannan rana, ba Aliyu kaɗai ne yake kiranta Babygirl ba, a hukumance, iyayenta sun amince da aurenta da shi, ta riga ta zama matar da yake son ya aura, Mrs. Future Aliyu, ❤️
Yamma ta yi sosai a Abuja, bayan Inteesar ta idar da sallar Maghrib, ta fito zuwa falon sanye da wata doguwar riga mai launin lavender, fuskarta cike take da wani annuri da ba ta iya ɓoyewa, tun lokacin da Aliyu ya sanar da ita cewa an ba shi amanarta, murmushi ya ƙi barin fuskarta, ta zauna a kan kujera tana kallon wayarta lokaci-lokaci, tana sake karanta saƙonsa, you are officially mine, Babygirl, ❤️💍 Duk lokacin da ta karanta kalaman, sai ta ji zuciyarta na bugawa cikin wani irin farin ciki mai daɗi, Nana da ta fito daga kitchen tana riƙe da cup ɗin tea a hannunta, ta tsaya tana kallon ta, tun da safe ta lura da yadda Inteesar take murmushi ita kaɗai, kuma yanzu abin ya ƙara fitowa fili, ta ƙaraso ta zauna kusa da ita, tana murmushi, “Princess,” Inteesar ta ɗago cikin annuri, “Na’am, Yaya Nana?” Nana ta matsa kusa da ita, “Me ke faruwa ne? Tun ɗazu nake kallonki kina ta murmushi kamar wadda ta ci lottery,” Inteesar ta yi dariya, sannan ta sunkuyar da kai cikin kunya, “A’a fa,” Nana ta harare ta cikin wasa, “To, ki gaya min,” Inteesar ta lumshe idanunta tana murmushi, “Yaya Nana…” “Uhmm?” “Sun zo,” Nana ta ɗan yi mamaki, “Su wa?” Inteesar ta cusa fuskarta cikin pillow tana dariya, “Mutanen Mi Amor,” Nana ta zaro ido, “Da gaske?!” Inteesar ta gyada kai, “Sun je Katsina yau,” “Kuma?” Inteesar ta ɗago idanunta, cike da kunya da farin ciki, “Daddy ya ba su ni,” nan take fuskar Nana ta haskaka da murna, “La ilaha illallah! Alhamdulillah! Congratulations, Princess!” Hawaye suka taru a idanun Inteesar, “Yaya Nana…” “Na’am?” “An saka biki after eight months,” Nana ta rungume ta a jikinta, “Allah Ya sanya alkhairi,” “Ameen,” “Allah Ya ba ku zaman lafiya,” “Ameen,” “Allah Ya ba ku zuri’a ta gari,” “Ameen,” Inteesar ta yi murmushi, “Na gode, Yaya Nana,” Nana ta shafa kanta a hankali, “Ke ƙanwata ce, wallahi, farin cikinki farin cikina ne,” ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta ƙara da murmushi, “Kuma gaskiya, Alhaji Aliyu ya yi sa’a,” Inteesar ta yi dariya, “A’a, ni na yi sa’a,” dukansu suka fashe da dariya, rungumar Nana ta sa Inteesar ta ji wani irin natsuwa, a wannan lokacin, tana son ta yi imani cewa komai zai tafi daidai, cewa bayan duk abin da ta sha, Allah Ya buɗe mata wata sabuwar ƙofa ta farin ciki, amma ba kowa ne ke murna a wannan gidan ba, a can cikin study room, Umar yana zaune a kan kujerarsa, littafin da yake karantawa tun ɗazu ya riga ya zame daga hannunsa, tun lokacin da ya ji Nana ta ce, “Da gaske?!” Hankalinsa ya koma kansu, da farko, ya yi ƙoƙarin ya ci gaba da karatun da yake yi, yana mai cewa wataƙila wani abu ne na yau da kullum, amma da ya ji kalaman Inteesar… “Daddy ya ba su ni…” Sai ya ji kamar wani abu ya tsaya masa a ƙirji, ya daina motsi, ya kasa ko ɗaga kansa, a hankali, ya lumshe idanunsa, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…” Ya furta kalaman cikin raunin murya, amma duk da kalmar da bakinsa ya furta, zuciyarsa tana ci gaba da karyewa, ya jingina da bayan kujera, sannan ya dafe ƙirjinsa da hannu, wani irin zafi mai nauyi ya ratsa shi, zafin da bai san yadda zai bayyana ba, an ba Aliyu Inteesar, halal-malal, an saka ranar bikinsu, komai ya ƙare, a wannan karon, ba mafarki ba ne, ba fata ba ce, ba wani abu da zai iya jira ya gani ko ya yi ƙoƙarin canzawa ba, gaskiya ce, kuma a karon farko, Umar ya fara fahimtar cewa wataƙila ya rasa Inteesar har abada, kalaman Inteesar suka ci gaba da amsa kuwwa a cikin kunnensa, “Daddy ya ba su ni…” “An saka biki after eight months…” Ya matse idanunsa, yana ƙoƙarin hana hawayen da suka fara taruwa a idanunsa zubowa, “Alhamdulillah…” ya furta da ƙyar, yana son ya yi farin ciki dominta, yana son ya yarda cewa idan ita ta yi farin ciki, shi ma ya kamata ya yi farin ciki, amma ta yaya zai yi hakan alhali zuciyarsa tana jin kamar an cire mata wani ɓangare da ba zai taɓa dawowa ba? Ya sake dafe ƙirjinsa, a wannan lokacin, wani irin tari ya taso masa ba zato ba tsammani, “Cough! Cough!” Da sauri ya miƙe tsaye, ya nufi toilet ɗin da ke cikin study room ɗinsa, yana ƙoƙarin hana ƙarar tarin fitowa, ya tare bakinsa da tafin hannunsa, amma tarin ya ƙara ƙarfi, “Cough! Cough!” Ya sunkuya, yana ƙoƙarin samun damar numfashi daidai, bayan ɗan lokaci, tarin ya lafa, numfashinsa yana fita da sauri yayin da yake tsaye a gaban madubi, a hankali ya sauke hannunsa daga bakinsa, sai idanunsa suka zaro, jajayen tabon jini ne suka ɓata tafin hannunsa, ya tsaya cak, ya sake kallon hannunsa, kamar yana ƙoƙarin tabbatar wa kansa cewa abin da yake gani gaskiya ne, “Ya Allah…” ya furta a hankali, a karon farko, tsoro ya mamaye zuciyarsa, ba don kansa kaɗai ba, sai saboda Nana, saboda matarsa, matar da take ƙaunarsa, wadda ta sha wahala saboda rashin samun haihuwa, amma duk da haka take ƙoƙarin faranta masa rai, idan wani abu ya same shi… Me zai faru da Nana? Ta yaya za ta iya jurewa? A hankali ya buɗe famfo, ya wanke hannunsa, sannan ya jingina da bangon toilet ɗin, yana lumshe idanunsa, zuciyarsa cike take da tambayoyin da bai san amsarsu ba, a waje kuwa, dariyar Inteesar da Nana ce kawai ke tashi cikin farin ciki, alhali a can cikin study room, wani mutum ne yake ƙoƙarin koyon yadda zai rayu da ƙaddarar da bai taɓa tunanin za ta juya masa haka ba, a wannan rana, Inteesar ta samu tabbacin makomarta da Aliyu, amma Umar kuwa… ya fara fuskantar wata gaskiya da zuciyarsa ba ta shirya karɓa ba.