Free chapter · Read without an account
THE VISIT
KADDARAR ZUCIYA
CHAPTER FORTY-FOUR: 44
THE VISIT
JIDDAAH BARKUM
——-
Washegari da safe, Inteesar ta tashi da wani irin annuri da ya ƙi barin fuskarta, tun daga ranar da Aliyu ya sanar da ita cewa an ba shi amanarta halal-malal, har yanzu zuciyarta tana rayuwa ne cikin wani irin farin ciki mai daɗi, ko kallon kanta a madubi take yi, sai ta tsinci kanta da murmushi ita kaɗai, Nana ta lura da hakan, duk lokacin da ta kalli Inteesar, sai ta yi murmushi, domin ita ma farin cikin Inteesar farin cikinta ne, a makaranta ma haka abin yake, tun tana zaune a lecture hall, murmushi ya ƙi barin fuskarta, har lectures suka ƙare, Amira ta lura da yadda ƙawarta ke lumshe ido tana murmushi kamar wadda aka yi wa busharar aljanna, “Wallahi, Intee, idan ba ki gaya min abin da ke faruwa ba, zan fara zargin kina chatting da Mi Amor a ƙarƙashin desk,” Inteesar ta yi dariya, “Amira…” “A’a, gaskiya ne ai! Me ke faruwa? Tun safe kina ta murmushi kamar wadda ta ci lottery,” Inteesar ta cusa fuskarta cikin tafin hannunta tana dariya cikin kunya, “Ki bari mana,” Amira ta zaro ido, “Lallai akwai magana!” Inteesar ta ɗago idanunta tana murmushi, “Sun zo,” Amira ta dafe ƙirji, “Su wa?” “Iyayen mijina,” “What?! Wato mijinki, ko?!” Dukansu suka fashe da dariya kafin Amira ta sake tambaya, “Yaushe?” “Ranar Lahadi,” “Da gaske?” Inteesar ta gyada kai tana murmushi, “Daddy ya ba su ni,” “Oh, Allah!” Amira ta yi ihu har wasu students suka waigo, “Intee!” Ta rungume ta da ƙarfi, “Congratulations!” Hawaye suka taru a idanun Inteesar saboda farin ciki, “Thank you,” “Wait… kina nufin officially engaged kenan?” Inteesar ta yi murmushi, “Uhmm,” “Kuma an saka date?” “After eight months,” Amira ta sake rungume ta, “Mrs. Future Aliyu!” Inteesar ta ɓuya cikin kunya, “Amira!” “Wallahi, Alhaji ya dage da ƙarfinsa ya zo! Tun kina share shi ya jure, yau kuma ga shi kin zama fiancée ɗinsa,” dukansu suka yi dariya, Amira ta ɗan matsa baya tana kallonta daga sama har ƙasa, “Wallahi, har kin fara haske, soyayya ta yi aiki!” Ta faɗa cikin sigar tsokana, “Ki kyale ni mana,” “A’a, da gaske nake, ki duba fuskarki, wannan ba Inteesar ɗin da muka sani ba ce,” ta sake dariya, “Yanzu ma kina ta engagement glow!” Inteesar ta girgiza kai, “Kin cika surutu,” “Ni dai idan kin zama Hajiyar Aliyu, kar ki manta da ni,” “Allah ya shirye ki, Amira,” suna cikin dariya suka fito daga faculty, suna nufar cafeteria domin su ci wani abu kafin su koma class.
A can kuwa, Aliyu yana Abuja, tun da safe ya bar Katsina ba tare da ya sanar da Inteesar ba, a ransa, yana son ya ba ta surprise, tun daga lokacin da aka ba shi ita halal-malal, yana jin kamar ba zai iya jure rashin ganinta ba, ya yi missing ɗinta sosai, har ya yanke shawarar zuwa Abuja ba tare da ya gaya mata ba, da motarsa ta shiga harabar makarantar, sai ya kira ta, wayarta ta yi ringing, da ta ga sunansa, murmushi ya bayyana a fuskarta, “Mi Amor,” nan take Aliyu ma ya yi murmushi, “Babygirl,” “Uhmm,” “Yaya lectures?” “Alhamdulillah,” “Kina ina yanzu?” “Muna hanyar cafeteria ni da Amira,” ya yi murmushi, “Oh… okay,” “Me kake yi?” “Nothing,” ta yi dariya, “Mi Amor…” “Uhmm?” “I miss you,” ya lumshe idanunsa yana murmushi, “I miss you more, Babygirl,” a daidai lokacin ne wani ɗalibi daga department ɗinsu ya ƙaraso, “Excuse me, Inteesar,” ta juya, ta ɗan matsar da wayar daga kunnenta, “Oh, Ahmad,” “Ga handout ɗin da kika nema jiya,” “Thank you,” Amira kuma wayarta ta yi ringing, don haka ta ɗan matsa gefe domin ta amsa kiran, Ahmad ya fara yi wa Inteesar bayani game da wani assignment da lecturer ɗinsu ya bayar, yana miƙa mata papers ɗin, a cikin motarsa kuwa, Aliyu ya hango komai, murmushin da ke fuskarsa ya ɗan gushe, ya sake kallon wajen, yana tabbatar da abin da idanunsa suka gani, wani saurayi ne ke tsaye tare da Inteesar, kuma suna magana, ba tare da ya yi tunani sosai ba, ya kira sunanta a hankali, “Babygirl,” “Uhmm?” “Ki juya baya,” Inteesar ta waigo, da ganin motar Aliyu, idanunta suka zaro, “Mi Amor!” Ta buɗe baki cike da mamaki da farin ciki, “You came?!” Aliyu ya yi wani ɗan murmushi na gefen baki, “Ban sanar miki ba, ko?” “Oh my God!” Ta fara dariya cike da murna, “You came without notice?” “Eh,” sai dai nan take muryarsa ta ɗan sauya, “Kuma sai na same ki da saurayinki,” murmushin da ke fuskar Inteesar ya gushe, “What?” Aliyu ya yi wani ɗan murmushi mai ɗauke da ɓacin rai, “Sorry for disturbing,” “Mi Amor…” Bai jira ta ƙarasa ba, ya kashe wayar, ya ja motarsa da sauri ya bar harabar makarantar, Inteesar ta tsaya cak, wayar tana hannunta, idanunta cike da rashin yarda, “Mi Amor…” Ta sake kiransa, busy, ta sake kira, busy, ta sake kira, amma bai ɗaga ba, a daidai lokacin Amira ta dawo, “Intee?” Ta yi murmushi, “Waye ya kira?” Sai ta lura da yadda Inteesar ke tsaye kamar wadda aka daskarar, murmushin Amira ya gushe, “What happened?” Inteesar ta kalli hanyar da motar Aliyu ta bi, “Aliyu…” Amira ta yi saurin tambaya, “He came?” Inteesar ta gyada kai a hankali, Amira ta yi murmushi, “Really?” Sai dai da ta lura da damuwar da ke cikin idanun ƙawarta, murmushinta ya gushe, “Intee…” “Where is he?” Inteesar ta haɗiye miyau, muryarta na rawa, “…Ya tafi,” “What?!” “Ya gan ni ina magana da Ahmad… sai ya kira shi saurayina,” ta ƙarasa maganar cikin rashin yarda, yayin da zuciyarta ta fara bugawa da wani irin tashin hankali, a karo na farko tun bayan da ta san Aliyu, ya tafi ya bar ta cikin ruɗani, Amira ta zaro ido tana kallonta, “What?!” Inteesar ta gyada kai cikin ruɗani, “Wallahi, Amira, ban ma gane abin da ya faru ba,” “Wait… Aliyu yana nan Abuja?” Ta sake gyada kai, “Kuma bai gaya miki ba?” “Eh,” “Ya zo ya same ki kina magana da Ahmad…” Inteesar ta katse ta da sauri, “Ba wata magana ta musamman ba fa! Handout ya kawo min,” Amira ta dafe goshinta, “Ya Allah! Wannan Alhaji ya cika kishi,” sai ta lura da yadda idanun Inteesar suka fara cika da ƙwalla, “Intee…” “Uhmm?” “Ki kira shi,” nan take Inteesar ta danna lambarsa, ringing, babu amsa, ta sake kira, shiru, a karo na uku ma bai ɗaga ba, gabanta ya fara faɗuwa, “Amira…” “Ki sake kira,” har sau shida ta kira shi, amma shiru, ta buɗe WhatsApp ta ga last seen ɗinsa yanzu-yanzu, da sauri ta tura masa saƙonni, Mi Amor, please pick my call, wallahi, handout ne kawai ya kawo min, please don’t do this, har yanzu babu amsa, ta ɗago kai tana kallon Amira, “Ba ya amsawa,” Amira ta riƙe hannunta, “Intee, ki kwantar da hankalinki, zai huce,” “Amma wallahi, ba laifina ba ne,” “Na sani,” “Kinsan yadda ya zo ne da farin ciki? Ya ce min in juya baya…” Ta ƙarasa maganar idanunta cike da ƙwalla, “Kuma da ya gan ni, sai ya tafi,” Amira ta sauke numfashi, “Wannan soyayyar taku wallahi!” A hankali ta shafa hannunta, “Ki ba shi lokaci, zai dawo,” ko da suka ƙarasa wajen cin abinci, sam Inteesar ba ta iya cin komai ba, juice ɗin da ke gabanta ma ba ta taɓa ba, wayarta kawai take kallo lokaci-lokaci, tana fatan ko ta ga kiran Aliyu.
A can cikin mota kuwa, Aliyu yana tuƙi cikin nutsuwa, amma zuciyarsa cunkushe take da tunani, wayarsa ta cika da missed calls, sunanta ne kaɗai ke bayyana a kan screen ɗin, Babygirl ❤️ Ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci, wayar ta sake ringing, Babygirl ❤️ Ya kalli screen ɗin, sannan ya sauke numfashi, ya ƙi ɗagawa, mintuna kaɗan bayan haka, saƙo ya shigo, please don’t do this, Mi Amor, sai zuciyarsa ta yi wani irin laushi, ya jingina da kujerar motar, yana kallon saƙon, wani ɗan murmushi ya bayyana a fuskarsa, “Babygirl…” Ya furta a hankali, sai dai bai kira ta ba, ya san tana cikin tashin hankali a yanzu, kuma a wani ɓangaren zuciyarsa, duk da ɓacin ran da yake ji, akwai wani irin daɗi da yake samu saboda yadda take ta nemansa, amma bai san cewa shiru da yake yi yana ƙara mata ciwo ba.
A cafeteria kuwa, Inteesar ta kusa yin kuka, “Amira…” “Uhmm?” “Ban taɓa ganin shi haka ba,” ta sake haɗiye kukanta, “Kuma wallahi, ba laifina ba ne,” Amira ta riƙe hannunta, “Intee, ki kwantar da hankalinki, zai huce,” a daidai lokacin wayarta ta yi vibrating, da sauri ta ɗauka, idanunta suka haskaka, “Mi Amor…” Ta furta da fatan ko shi ne ya kira ta, amma murmushin da ke fuskarta ya gushe da ta ga ba Aliyu ba ne, Yaya Nana ce, “Assalamu alaikum, Princess,” “Wa alaikumus salam, Yaya Nana,” “Kin gama lectures?” “Eh,” “To, ki hanzarta dawowa gida,” “Me ya faru?” “Babu komai, kin manta ne? Yau za mu je gidan suna na Sameera,” nan take Inteesar ta tuna, “Allah na, na manta!” Nana ta yi dariya, “Kin san dai idan muka makara, Sameera ba za ta bar ni ba,” Inteesar ta yi murmushin dole, “In Sha Allah zan zo yanzu,” “Good girl, kar ki ɓata lokaci,” “To, Yaya Nana,” da ta kashe wayar, Amira ta lura da yadda idanunta suka sake cika da ƙwalla, “Intee…” Inteesar ta yi murmushi cikin ƙarfin hali, “Yaya Nana ce,” “Me ta ce?” “Ta ce na hanzarta dawowa gida saboda za mu je gidan suna,” “To, ai that’s good,” Inteesar ta gyada kai a hankali, sai dai a wannan karon, hawayen da take ta dannewa tun ɗazu suka zubo a hankali, domin duk abin da take so a wannan lokacin ba gidan suna ba ne, ba taro ba ne, ba komai ba ne, abin da take so kawai shi ne ta ji muryar Mi Amor ɗinta yana cewa… “Babygirl,” amma wayarta har yanzu shiru take.
Bayan sun yi sallama da Amira, Inteesar ta shiga mota ta nufi gida, duk hanyar dawowa, hankalinta yana kan wayarta, ko sau ɗaya Aliyu bai kira ta ba, da ta shiga WhatsApp, sai ta ga ya karanta duk saƙonninta, amma babu ko reply ɗaya, hakan ya sa wani irin sanyi da fargaba suka mamaye zuciyarta, ko da ta isa gida ma, ta kasa samun nutsuwa, sau da dama tana ɗaukar wayarta tana duba ko ya kira, ko akwai notification daga Mi Amor, amma shiru, da yamma, Nana ta turo ƙofar ɗakinta, “Princess,” Inteesar ta ɗago a hankali, “Ki shirya, kin ji? Za mu je gidan suna na Sameera, kin san na gaya miki, ko?” Ta yi murmushin dole, “To, Yaya Nana,” sai dai tun daga lokacin da ta fara shirya kanta, idanunta suka cika da ƙwalla, tana gyara mayafinta, zuciyarta na mata wani irin ciwo, ta kasa fahimtar dalilin da ya sa Aliyu ya yi mata haka, bayan sun shirya, Nana ce ta ja motar zuwa gidan suna na ƙawarta Sameera, tun daga bakin gida, hayaniya da annashuwa suka cika ko’ina, mata na ta kai da komowa, yara na gudu suna wasa, ana ta dariya da hirarraki, a gefe guda kuma, ana ta rabon abinci, Sameera da kanta ta zo ta rungume Nana, “Nana! Sannu da zuwa!” Sai ta juya ta rungume Inteesar, “Princess, kin yi kyau wallahi!” Inteesar ta yi murmushi kawai, amma Nana ta lura da yanayinta, tun da suka isa, Inteesar ba ta shiga hirar kowa ba, ba ta yi dariya sosai ba, ko lokacin da aka fara ɗaukar hotuna, murmushi kawai take yi saboda dole, a duk minti biyu, tana duba wayarta, har ta kai ga shiga WhatsApp ta sake dubawa, double blue tick, ya ga saƙonninta, amma har yanzu babu amsa, wani abu ya tsaya mata a maƙoshi, da ƙyar ta hana kanta yin kuka a gaban mutane, har aka gama komai, suka yi sallama da masu gidan.
A hanyar dawowa, Nana ce ke tuƙi, tun daga lokacin da suka fita daga gidan, ta lura Inteesar ta yi shiru, ba kamar yadda ta saba ba, ba ta hira, ba ta dariya, kai ko waƙar da ke kunne ma kamar ba ta ji ta, sai da suka kusa isa gida, Nana ta dubeta, “Intee…” Inteesar ta ɗago, “Hmm?” Nana ta rage gudun motar kaɗan, “Something is wrong with you, ba kya walwala,” ta sake kallonta, “Ko wani abu ya faru ne a school?” Inteesar ta girgiza kai da sauri, “A’a,” Nana ta yi murmushi, “Princess…” Inteesar ta yi shiru, “Intee, tun da muka taho daga gidan suna nan nake kallonki, kina da damuwa,” ta ɗan dafa hannunta, “Tell me,” nan take idanun Inteesar suka cika da ƙwalla, ta sunkuyar da kanta ƙasa, “Princess?” Sai hawayen suka fara zubo mata a hankali, Nana ta firgita, “Intee!” Ta yi saurin tsayar da motar a gefen titi, “Ya Salam! Me ya faru?” Inteesar ta kasa magana, sai kuka, kuka mai ciwo wanda ya fito daga can cikin zuciyarta, Nana ta kama hannunta, “Don Allah, ki gaya min,” da ƙyar Inteesar ta haɗiye kukanta, “Yaya Nana… muna cafeteria da Amira…” Ta fara ba ta labarin komai, yadda Aliyu ya zo Abuja ba tare da ya sanar da ita ba, yadda ya kira ta, yadda ta juya ta gan shi, yadda ta yi farin ciki, yadda kuma ya gan ta tare da wani ɗalibi da ya kawo mata handout, ta gaya mata yadda ya ce, “Sai na same ki da saurayinki,” sannan ya tafi cikin sauri ba tare da ya saurare ta ba, ta kuma gaya mata yadda tun daga lokacin bai sake kiranta ba, bai amsa saƙonninta ba, sai dai kawai ya karanta su ya yi shiru, a ƙarshe, ta fashe da kuka, “Wallahi, Yaya Nana, ban yi komai ba… Handout kawai ya kawo min, ban san me ya sa bai saurare ni ba, na yi ta tura masa saƙonni, ya gani, amma bai amsa ba, wallahi, Yaya Nana, zuciyata na min ciwo…” Nan take zuciyar Nana ta karye, ta janyo Inteesar jikinta, ta rungume ta sosai, “Ki yi shiru, Princess,” Inteesar ta ƙara fashewa da kuka, “…Kar ya daina sona,” nan take idanun Nana suka cika da ƙwalla, ta shafa kanta a hankali, tana jin tausayinta, “Wannan abin da ya faru ba yana nufin mutum zai daina son wanda yake so ba,” Inteesar ta girgiza kai, “Amma yana fushi da ni,” Nana ta yi murmushi mai cike da tausayi, “To, idan yana fushi, ai za ku shirya,” sai ta ɗaga fuskar Inteesar a hankali, “Kuma idan yana sonki kamar yadda nake gani, ba zai iya jurewa ya ci gaba da yin shiru ba,” Inteesar ta goge hawayenta, “Da gaske?” “Wallahi,” Nana ta shafa fuskarta, “Ki yi haƙuri, ki ba shi lokaci, wasu mazan idan suna kishi, sai su yi abubuwa cikin fushi, amma idan zuciyarsu ta huce, su ne za su dawo su fara lallashi,” Inteesar ta jingina kanta a kafaɗar Nana, tana ƙoƙarin kwantar da hankalinta, sai dai duk da kalaman rarrashin da Nana ke mata, zuciyarta har yanzu tana jiran abu guda, wayarta ta yi ringing, kuma sunan da take fatan gani a kan screen ɗin shi ne… Mi Amor