Free chapter · Read without an account
RECONCILIATION
KADDARAR ZUCIYA
CHAPTER FORTY-FIVE: 45
RECONCILIATION
JIDDAAH BARKUM
——-
Yammacin ranar a Abuja, Aliyu bai samu nutsuwa ba, yana zaune a cikin ɗakin otal ɗin da ya sauka, fitilar ɗakin tana haske kaɗan, wayarsa tana hannunsa, amma idanunsa suna kallon wuri guda kawai, kamar wanda zuciyarsa ta tsaya, sunanta yana nan a kan screen ɗin wayarsa, Babygirl ❤️ Ya lumshe idanunsa a hankali, “Handout…” Ya furta a ƙasan muryarsa, kamar kalmar tana masa nauyi, sai ya tuna yadda ya ga Inteesar tsaye tare da wani saurayi, suna magana, ko da yake bai ji abin da suke cewa ba, zuciyarsa ta riga ta fassara abin da idanunsa suka gani ta hanyar da ta fi masa zafi, ya miƙe ya fara takawa cikin ɗakin, “Why didn’t she tell me?” ya furta, sai wani ɓangare na zuciyarsa ya tambaye shi, did you even give her a chance to explain? Ya tsaya cak, shiru ya mamaye ɗakin, wayarsa ta yi vibration, da sauri ya kalli screen ɗin, Babygirl ❤️ calling… Ya kalli wayar na tsawon wasu seconds, zuciyarsa tana masa nauyi, ya so ya ɗaga, ya so ya ji muryarta, amma ɓacin ran da yake ji ya rinjaye shi, ya ƙi ɗagawa, kiran ya katse, sai wani saƙo ya shigo, Mi Amor, please talk to me, I swear it was just handout, ya rufe idanunsa da ƙarfi, “Stop it…” ya furta a hankali, kamar yana yi wa kansa magana, amma gaskiya ɗaya ce, yana jin kishi, yana jin zafi, kuma duk ƙoƙarin da yake yi na danne abin da yake ji bai hana zuciyarsa ci gaba da tunanin Inteesar ba.
A nata ɓangaren kuwa, Inteesar ba ta samu barci mai kyau ba tun bayan dawowarta gida, tana zaune a kan gado, mayafinta har yanzu a jikinta, idanunta sun kumbura saboda kuka, wayarta tana hannunta, amma babu kira, babu amsar saƙo, sai kawai seen, ta rufe wayar a hankali ta rungume pillow ɗinta, “Mi Amor…” ta furta cikin raɗaɗi, sai hawaye suka zubo mata ba tare da ta hana ba, ko me ta yi, zuciyarta tana maimaita tambaya guda, na rasa shi ne? Ƙofar ɗakin ta buɗe, Nana ta shigo a hankali, da ta ga Inteesar tana kuka, sai zuciyarta ta karye, “Intee…” ta kira a hankali, Inteesar ta ɗago da idanunta da suka yi jawur, “Yaya Nana…” Nana ta zauna kusa da ita, ta riƙe hannunta, “Ki daina wannan kukan haka, Princess,” “Ban san abin da na yi ba…” Inteesar ta faɗa cikin rawar murya, “Ya gan ni, ya tafi, ya ce ina da saurayi…” Nana ta sauke numfashi, “Sometimes love and jealousy make people blind,” Inteesar ta girgiza kai, “Amma ban yi laifi ba…” Nana ta gyada kai, “Na sani,” ta ɗan yi shiru kafin ta ci gaba, “Ki ba shi lokaci, amma kuma akwai abin da nake so ki yi,” “Me?” Nana ta kalle ta da gaske, “Ki rage yawan kiransa a yanzu, ki ba shi damar hucewa ya kuma yi tunani, kada ki ci gaba da cutar da kanki da yawan kiran da ba a amsawa,” Inteesar ta girgiza kai da sauri, “Amma idan ya daina sona fa?” Nana ta riƙe fuskarta a hankali, “Idan soyayyarku ta gaskiya ce, wannan rashin fahimtar ba zai zama ƙarshenta ba, amma ke ma ki tuna, ba dole sai kin ɗauki dukkan nauyin gyara komai ke kaɗai ba,” Inteesar ta sunkuyar da kanta, tana share hawayenta, bayan ɗan lokaci, ta shiga banɗaki ta yi wanka, sannan ta yi sallah, amma duk abin da take yi, zuciyarta tana wani wuri daban, a wurin Aliyu, sunansa kawai yake yawo a kanta, bayan sallar Maghrib, ta zauna a kan sallaya, hannayenta a kan cinyoyinta, idanunta a rufe, “Ya Allah… Ka sa ya fahimce ni, Ka kwantar masa da hankali, ka cire masa duk wani mummunan zato, Ka kuma taimake ni, Ya Allah…” Ta furta a hankali, hawayen da ta danne tun ɗazu suka sake taruwa a idanunta, a daidai lokacin ne wayarta ta yi ringing, sai ta ji zuciyarta ta tsinke, ta buɗe idanunta da sauri, Mi Amor ❤️ Hannunta ya fara rawa, “Ya Allah…” Ta ɗauka da sauri, muryarta ta fara dashewa tun kafin ta yi magana, “Mi Amor…” Sai hawayenta suka zubo, a ɗayan ɓangaren kuwa, Aliyu ya yi shiru na wasu seconds, ya ji yadda muryarta ta fito cikin rauni, kuma hakan ya taɓa wani wuri a zuciyarsa, ya sauke numfashi a hankali, “Babygirl…” Da jin muryarsa, Inteesar ta rufe idanunta, muryarsa kawai ta isa ta karya duk wani ƙarfin hali da ta yi ƙoƙarin tarawa tun bayan abin da ya faru, “I miss you,” ya ce a hankali, sai ya ɗan yi shiru, “I’m sorry…” Inteesar ta fashe da kuka sosai, “Wallahi, ba saurayina ba ne! Handout kawai ya kawo min…” Ta yi saurin magana, kamar tana tsoron kada ya kashe wayar kafin ta gama bayanin kanta, Aliyu ya katse ta a hankali, ba da tsawa ba, sai da natsuwa mai ɗauke da nauyin zuciya, “Wait,” sai shiru ya ɗan mamaye tsakaninsu, “Where are you now?” ya tambaya, Inteesar ta tsaya cak, “W-what?” “Ki fito waje,” idanunta suka zaro, “Waje? Ka zo?” “Eh,” muryarsa ta yi ƙasa sosai, amma tana ɗauke da wani irin tabbaci, “Come outside, Babygirl,” sai Inteesar ta miƙe da sauri, kamar wadda aka zungura, “Okay… okay…” Ta sauke wayar daga kunnenta, ta fara tafiya cikin sauri, ta fito daga ɗakin tana saukowa da sauri, zuciyarta na bugawa, Nana na zaune a falo tana kallon TV, amma ta ɗago kai da sauri da ta ga yanayin Inteesar, “Intee?” Inteesar ba ta tsaya ba, ta matsa wayar daga kunnenta da hannu mai rawa, “Yaya Nana… zan leka compound, ya zo,” Nana ta yi murmushi kaɗan, “Hmm,” ta kalle ta sosai, kamar wadda ta riga ta san abin da ke faruwa, “Ai na gaya miki zai huce,” Inteesar ta yi ƙoƙarin murmushi duk da hawayen da suka cika idanunta, “Zan je…” Nana ta gyada kai, “Maza, ki je, kar ya jira,” Inteesar ta juya da sauri ta nufi waje.
Iskar dare ta bugi fuskarta da ta fito waje, compound ɗin ya yi shiru, fitilun gidan suna haske kaɗan, ta tsaya tana zagaya idanuwanta ko’ina, zuciyarta na bugawa kamar za ta fito daga ƙirjinta, “Mi Amor…” ta furta a hankali, sai ta gan shi, yana tsaye kusa da motarsa, sanye da baƙar shirt da jeans, hannunsa a cikin aljihunsa, idanunsa a kanta, shiru, ba ya motsi, ba ya murmushi, kawai ya tsaya yana kallonta, kamar yana ƙoƙarin karanta duk abin da zuciyarta ta ɓoye, Inteesar ta yi ƙoƙarin yin gaba, amma ƙafafunta kamar sun yi nauyi, “Mi Amor…” ta kira a hankali, muryarta na rawa, sai ya motsa kaɗan ya fara tafiya zuwa gare ta, a hankali, mataki ɗaya… biyu… uku… Har ya tsaya a gabanta, suna tsaye kusa da juna, babu wanda ya yi magana, zuciyar Inteesar tana bugawa da sauri, idanunta cike da hawaye, “Mi Amor…” ta sake cewa a hankali, Aliyu ya kalleta sosai, a cikin idanunsa akwai abubuwa da dama, kishi, ɓacin rai, nadama da ya ga yadda idanunta suka kumbura, da kuma soyayyar da yake ƙoƙarin ɓoyewa, “Explain to me…” ya ce a hankali, sai ya ɗan yi shiru, “Or tell me I misunderstood everything,” hawayen Inteesar suka fara zuba, “Mi Amor… wallahi ba haka ba ne…” Ta kama hannunsa da sauri, kamar tana tsoron zai ja baya, “Wallahi handout ne kawai, Ahmad ya kawo min ne…” Sai muryarta ta karye, “Ban yi maka laifi ba…” Shiru ya sake ratsa tsakaninsu, Aliyu ya kalleta na tsawon wasu seconds kafin ya sauke numfashi a hankali, “Look at me,” Inteesar ta ɗago idanunta, idanunsu suka haɗu, muryarsa ta yi laushi sosai, kusan raɗa, “Do you know how it felt… seeing you with him?” Inteesar ta girgiza kai da sauri, “Ba saurayina ba ne, Mi Amor…” Aliyu ya ɗaga hannu ya shafi gefen fuskarsa, kamar yana ƙoƙarin kwantar da hankalinsa, “Na ji kishi,” ya faɗa a hankali, “Na ji kamar na rasa ki,” sai ya kalleta sosai, “Amma ban ba ki damar yin magana ba,” ya yi shiru na ɗan lokaci, kamar yana karɓar gaskiyar abin da ya aikata, Inteesar ta fashe da kuka sosai, “Ni ma na ji kamar na rasa ka…” Ta kama rigarsa da hannayenta biyu, “Ban san abin da na yi ba… Ka daina ɗaukar calls ɗina…” Muryarta ta karye gaba ɗaya, “Na ji zafi, Mi Amor, na kira ka sau da yawa, na tura maka saƙonni… amma ka karanta su ka yi shiru, na yi tunanin ko ka daina sona ne,” Aliyu ya kalleta, sai yanayin fuskarsa ya sauya, a hankali ya ɗaga hannu ya shafi kumatunta da ya jike da hawaye, “Babygirl…” Sai ya ja ta a hankali zuwa jikinsa, ya rungume ta sosai, cike da nadama, “I’m sorry…” ya ce a hankali a kunnenta, Inteesar ta fashe da kuka a kirjinsa, tana riƙe shi kamar ba ta son ya sake tafiya, “Kar ka sake yi min haka…” Aliyu ya ƙara matse ta a jikinsa, “Ba zan sake ba,” “Ya kamata na saurare ki kafin na yi hukunci, na yi kuskure,” Inteesar ta goge hawayenta da bayan hannunta, “Na yi tunanin ka daina sona…” Aliyu ya girgiza kai a hankali, “Ba zan daina sonki saboda na ga wani saurayi yana magana da ke ba, Babygirl, amma na yi fushi, kuma na bar kishina ya rinjaye ni,” ya ɗaga hannunsa ya share sauran hawayen da ke kan kumatunta, “I’m sorry for making you cry,” “Na yi missing ɗinka sosai…” Aliyu ya lumshe idanunsa, yana matse ta a jikinsa, “I missed you too,” iskar dare ta zagaye su yayin da suka tsaya a haka, suna ƙoƙarin dawo da nutsuwar da suka rasa tun lokacin da suka rabu, a wannan karon, shirun da ke tsakaninsu ba na zafi ba ne, na sulhu ne.
A daidai lokacin, Yaya Umar yana dawowa daga masallaci bayan sallar Maghrib, yana sanye da jallabiya mai launin ruwan kasa wadda ta yi wa fatarsa kyau, yana tafiya cikin nutsuwa, hankalinsa yana kan hanyar shiga gidan, amma kafin ya kai tsakiyar compound ɗin, idanunsa suka tsaya a kan wani abu, ya hango su, Inteesar, tana tsaye kusa da wani saurayi, rungume da shi, kanta a jikin mutumin, shi kuma ya rungume ta sosai, Umar ya tsaya cak, wani irin nauyi ya sauka a zuciyarsa, amma akwai abu guda da bai iya ganewa ba, fuskar saurayin, domin mutumin ya juya bayansa ne, ya rufe Inteesar da jikinsa, hannayensa a bayanta, yana riƙe da ita kamar yana kare ta daga duk wani abu da zai iya cutar da ita, Umar ya tsaya na wasu seconds, idanunsa a kansu, fuskarsa ba ta nuna komai ba, amma zuciyarsa tana bugawa da ƙarfi, kamar kowane numfashi yana ƙara masa wani sabon ciwo, ya ɗan sauke kansa, sannan ya ci gaba da tafiya, a hankali, ya ratsa gefensu ba tare da ya ce komai ba, Inteesar ta ji motsin wani a kusa da su, sai ta ɗago kai da sauri ta janye jikinta daga jikin Aliyu a hankali, tana kallon ƙasa.