Free chapter · Read without an account
PAGE 30
SAWU BIYU
Khadijah Sulaiman
Young Talented Writers Association (YOTA)
Book 1
Page 30
Da daddaren ranar da abin ya faru text message ya shigo wayarsa,ya ajiye towel ɗin hannun shi ya janyo wayar.
"This is just a little warning Captain Umar Sadauki,ka godewa Allah ka tsira a wannan karon,na biyun ba zai mana kyau ba,ka cire hannunka a abinda bai shafe ka ba."
Ya ajiye wayar ya tsaya jikin mirror ya ɗauki cream ya fara shafawa.
Lokaci ɗaya abinda ya faru a gidan Mami ya faɗo mishi a rai,take ya tuno yadda ta bi ta cukwuikuye mishi uniform,shaiɗan har da tuno mishi rabin cinyoyinta dake bayyane.
Take ya dafe kai ya ce"my bad".
Ya ajiye cream ɗin yayi guntun tsaki ya ce"wani irin soyayya take yiwa yaron da ba za ta iya rabuwa dashi ba,foolish girl".
Short kaɗai ne a jikin shi ya hau gado ya kwanta,duk yadda ya so bacci ya ɗauke shi kasawa yayi.
Suffar Zarah kawai ke mishi yawo a ido,ya sauka ya ƙure AC ko Allah zai sa bacci ya ɗauke shi.
Har ƙarfe biyu idon shi biyu,daga ƙarshe dai miƙewa yayi ya ɗauro alwala ya ta da sallah.
Bayan ya idar yayi addu'a ya koma bakin gado ya zauna ya janyo file ɗin Yaqub Tafida dake saman bed side drawer.
A hankali ya fara flipping file ɗin,idon shi ne kaɗai a wurin amma tunanin shi ya tafi wani wuri daban.
Ƙoƙarin haɗa puzzle ɗin kawai yake,tun daga kan cases daya gudanar, fara aikin shi har zuwa yau, abubuwan da suka biyo baya,abinda ya faru ranar da Ola da sauran officers suka rasa rayukansu,mutuwar matar Ola da yaranta.
Sace yaran makaranta da aka yi,kashe suspect dake ɗaure da har yau bai san kan zancen ba.
Dai dai nan ya dakata,da sauri ya buɗe file ɗin idon shi ya sauka inda Tafida yayi investigating similar case irin haka,kuma har yau a haka case ɗin yake babu ƙarshe.
Ya rufe file ɗin ya shiga shafa suman Yaqub Tafida kamar yana gaban shi ya ce"me ka sani Colonel,akwai abinda ya kamata na sani ne?"
Washegari haka ya shirya ya tafi office rai babu daɗi,ga rashin baccin da bai samu ba,shi yasa yana isa ya kulle ƙofar da key ya hau dogon kujera ya kwanta.
Tsaki ya dinga ja akai akai ganin har lokacin Zarah kawai yake gani a idon shi,ya sauke pillown da ya rufe fuskar shi da shi ya tashi ya zauna ya ce"wai yarinyar nan ko dai mayya ce bani da labari?"
Ya sauka ya shiga toilet,bai wani daɗe ba ya fito.
Knocking ƙofar da ake yasa ya ƙarasa ya buɗe,Bilal ya bishi da kallo ya ce"ban yarda da kai ba Dude,akwai abinda kake ɓoyewa".
Ya gyaɗa kai ya ce"yeah sure,tana ciki".
Da mamaki ya ce"tana ciki,ita wa?"
Ya ɗage kafada ya ce"ita wacce nake ɓoyewa mana,tana toilet,ni zan fita,idan ta fito ka ce mata ta kulle min ƙofa".
Bilal ya bishi da kallo har ya fita,har zai fita sai ya karasa jikin ƙofar yayi knocking,jin shiru babu amsa ya sa ya tura kawai.
Ganin wayam babu kowa sai ƙamshin da ke tashi ya gyaɗa kai ya ce"zan kama ka".
Office ɗin Brigadier ya nufa,bayan yayi knocking an bashi izinin shiga ya tura ƙofar a nutse.
Ya sara mishi ya ce"Captain Umar Sadauki Sir".
Ya ajiye pen ɗin hannun shi ya ce"Go ahead Captain".
Ya sauke kai ya ce"Sir,na gama nazarin files da aka turo min some day's back".
Ya gyaɗa kai ya ce"that's good,akwai wani matsala ne?"
Sadauki yayi shiru na ɗan lokaci, kafin a hankali ya ce"akwai abubuwan da nake son sake tabbatar da su Sir".
Brigadier yayi juyi da kujerar sa na ɗan lokaci sannan ya zauna da kyau yana kallon shi ya ce"Captain Sadauki,ban aika maka waɗannan files ɗin don ka ajiye saman table ka dinga kallonsu ba,na aika maka ne saboda na san za ka iya,akwai officers da yawa da zan iya basu wannan aikin amma sai na zaɓeka,ka fahimci abinda nake nufi?"
Ya ce"Yes,Sir".
Brigadier ya ce"good".
A hankali ya ce" Late Colonel Yaqub Tafida,akwai abinda ban gama fahimta akan nasa file ɗin ba Sir".
Brigadier yayi murmushi mai ƙayatarwa alamar an zo wurin sannan ya ce“Follow every lead. And don't be afraid to question what doesn't make sense.”
A hankali ya ce“Yes, sir.”
Bayan ya fita ya koma ya kwanta ya lumshe ido,a hankali ya ce"Captain Sadauki...."
**********
The Dark Network
Su goma ne wannan karon,Chief yayi gyaran murya ya ce"ya karɓi saƙo?"
"Ya karɓeta tun jiya Chief".
Ya juya ya kalli na kusa dashi ya ce"akwai wani motsi ne?"
Ya girgiza kai ya ce"babu for now,amma mun sami labarin ya shiga wurin Brigadier,akwai alamun report ya kai masa".
Chief ya jinjina kai ya ce"ashe akwai wanda zai iya fin Tafida taurin kai?"
Ya shafa gemu yana murmushi ya ce"yaro yaro ne,yaro man kaza".
Bracket ya ce"a kashe banza kawai Chief".
Wani kallo ya watsa mishi,na kusa da Bracket ya ce"shi ke da riba kenan,dole a masa tabon da zai mutu da baƙin ciki".
Chief ya ce"Scorpion".
"Yes, Chief".
"A shiga plan B,ku kira Zero".
Ya miƙe da sauri ya ɗauki wayarsa yana ƙoƙarin barin ɗakin ya ce"an gama Chief".
***********
Tun ranar da abin ya faru Sadauki bai sake komawa gidan ba,yana tashi daga aiki yayi sallama da Bilal ya wuce can.
A compound ya tarar da sabon drivern Zarah yana wanke mota,ya ɗan koma baya da sauri don sosai uniform ɗin Sadauki ke ɗaga masa hankali.
Da sauri ya ce"Ina wuni Sir".
Ya ɗan bishi da kallo ya ce"lafiya".
Har yayi gaba ya dawo ya ce"ya sunan ka?"
Da sauri ya ce"Sammani,sunana Sammani".
Kamar zai sake tambayarsa sai ya fasa ya shiga ciki, Mami na zaune tana kallo tare da Firdausi yayi sallama.
Ta amsa sallamar ta ce"shigo mana Faruq".
Ya shigo ya zauna ya ce"ina wuni Mami".
"Lafiya ƙalau Faruq,ya aiki?"
"Aiki Alhamdulilah".
"To masha Allah ,Allah ya cigaba da dafa mana".
Ta juya ta kalli Firdausi ta ce"zubo masa abinci Firdausi".
Dai dai nan Zarah ta fito,sanye da Navy green Abaya sai ƙaramin handbag da flat shoes sai baza ƙamshi take.
Ta tsaya kusa da Mami ta gaishe shi kanta a ƙasa,don tana ganin shi wani kunya ya dabaibayeta.
Ya juyo ya mata kallo ɗaya ya ɗauke kai.
Ta kalli Mami ta ce"na gama Mami".
Mami ta ce "sai kin dawo Allah ya ba da sa'a".
A waje ta tarar da driver ya gama wanke mota,ya buɗe mata ƙofa da sauri ta shiga ta rufe.
A gaban department ɗinsu ya ajiyeta,bayan ta fito ta juyo ta kalle shi ta ce"ƙarfe shida zan fito,ka jirani kawai ba sai ka koma gida ba".
"To Hajiya".
A nutse ta taka ta shiga ciki,bata wani jima ba lecturer ya shigo ya basu test,don dama dalilin fitowarta kenan,in ba haka ba babu abinda zai fito da ita da yamman nan.
Ƙarfe shida dai dai aka fara submitting,ta ƙarasa ta miƙa nata ta fito.
Yana hangota yayi saurin buɗe motar ta shiga ya maida ƙofar ya rufe.
Tunda ya shiga take danna wayarta,kallo ɗaya za ka mata ka hango ramar da tayi saboda damuwar da ta ɗorawa kanta.
Kaman ance ta ɗago ta ga kamar ba hanyar gida suka nufa ba,a tunaninta ko hanya zai canza shi yasa kawai tayi shiru.
Ganin abin yaƙi ci yaƙi cinyewa kuma kamar sun fara barin cikin gari ta ce"Mallam wani hanya ne nan?".
Tamkar da dutse take magana don ko gizau bai yi ba,ta ajiye wayar ta ce"Mallam tambayarka nake,hanyar ina ne nan?"
Still babu amsa,gashi sun bar cikin gari ga wuri ya fara duhu.
Ta sa hannu ta taɓa ƙofar ta ji a rufe,cike da matsanancin tashin hankali ta hau jijjiga ƙofar,amma ko juyowa bai yi ba balle ya san tana yi.
Ta fasa gigitaccen ihu ko Allah zai sa a jiyota at the same time tana jijjiga ƙofar.
Ganin duk a banza ya sa ta cakumo shi ta baya ta matse masa wuya,nan da nan yayi parking ya zuba mata mari.
Ta sake fasa wani ihun,tana ƙoƙarin miƙewa ya ciro handkerchief a aljihun shi ya manna mata a hanci.
Tun tana mutsu mutsun ƙwace kanta har jikinta ya saki gabaɗaya,ya kwantar da ita ya ta da motar suka bar wurin.
Sai da suka isa can bayan gari sannan ya tsaida motar gaban wata Black Rolls Royce,da sauri jibga jibgan maza guda biyar suka fito suka ɗaukota.
A nan suka bar motar da handbag ɗinta da takalmanta.
**********
Tun Mami na duba hanya har dai ta magantu,bayan ta idar da sallah ta sauko ƙasa ta shiga ɗakinsu Zarah, Firdausi na gyara kayan wardrobe ɗinta ta shigo.
"Har yanzu Zarah ba ta dawo ba?"
"Ba ta dawo ba Mami".
Da mamaki Mami ta ce"amma ƙarfe shida ta ce za su gama test,bari in kirata".
Tayi dailing numbern amma har ya gama ringing no answer,ta zauna bakin gado ta sake daliling shima shiru.
Ta koma contacts ta nemo numbern Sammani tayi dailing a kashe.
"Allah ya sa lafiya".
Firdausi ta ce "Amin".
Ta miƙe ta fita waje don hankalinta ya kasa kwanciya,har ƙarfe bakwai da rabi shiru kuma har lokacin wayarta babu amsa.
Ta ƙarasa wurin Iliya mai gadi ta ce"Mallam Iliya".
Ya taso da sauri ya ce"na'am Hajiya".
"Dan Allah ina Jamilu,ya zo ko akwai wani number da zan iya samun Sammani,har yanzu shiru Zarah ba ta dawo ba".
"Aiko yanzu Jamilu ya fita Hajiya,ya je siyo kati".
Dai dai nan aka yi horn,da sauri Iliya mai gadi ya koma jikin gate ya buɗe.
Daddy ya shigo ciki yana bin Mami da kallo,tun kafin ya ƙarasa parking ta nufi inda yake.
Ya fito yana kallonta ya ce"Lafiya kuwa?"
"Zarah ba ta dawo ba,kuma ƙarfe shida ta ce za su gama test gashi har ƙarfe takwas saura".
Ya ce"kin kirata a waya?"
"Na kira amma ko sau ɗaya bata ɗauka ba,hankalina bai kwanta ba wallahi".
Ya riƙo hannunta ganin yadda jikinta ke rawa ya ce"ki kwantar da hankalin ki,maybe suna hanya".
Ta ce"har shi Sammanin wayarsa a kashe".
Ya ciro wayarsa a aljihu ya ce"bani number".
Kasa karanto mishi number tayi,ya sa hannu ya ƙarba ya kwashe a wayarsa sannan yayi dailing.
Kamar dai yadda ta ce wayar a kashe take,ya sauke numfashi ya ce"mu je ciki".
Ta girgiza kai ta ce"bari in jira a nan,idan na shiga ciki hankalina ba zai kwanta ba".
Ya ce"menene haka Hafsah,ya kike abu kamar ba za ta dawo ba,maybe wani minor abu ne ya faru ko ba ta gama test ɗin da wuri ba kuma ga holdup,ki kwantar da hankalinki Please".
"Hayaniyar me na ke ji ne haka?"
Daddy ya juya ya kalli Hajja dake nufo inda suke.
"Hajiya babu komai,wai Zarah ce ba ta dawo daga School ba har yanzu, shine Hafsah ta bi ta ɗaga hankalinta".
Ta kalle shi da kyau ta ce"ƙarfe nawa ne yanzu?"
Ya duba wayar shi ya ce"ƙarfe takwas Hajja".
"To ai dole ta ɗaga hankalinta,yarinya budurwa kamar Zara'u ace ba ta shigo gida ba har yanzu kuma ba ta saba hakan ba dole hankalin uwarta ya tashi,yanzu dai an kira wayarta?"
"Na kira Hajja,har na drivernta na kira nashi a kashe".
Hajja ta ce"ina ɗan uwansa Jamilu ya ke ko Halilu,kira shi ya duba wayarsa ko yana da wata layin".
"Mai gadi ya ce ya fita siyo kati,gashi har yanzu shiru bai dawo ba Hajja".
Hajja ta ce"ikon Allah".
Wasa wasa har ƙarfe goma babu Sammani,babu Zarah babu Jamilu mai wanki.
Mami tayi kuka har idonta ya canza kala,cike da ƙarfin hali Daddy ke rarrashinta.
Wuraren goma da rabi ta tuna da Sadauki,yana zaune a parlour daga shi sai short da vest yana operating system kiranta ya shigo.
Da mamaki ya duba time,ya maida system ɗin gefe yayi picking.
"Mami lafi...?
Cikin Muryar kuka ta ce"Faruq".
Ya miƙe da sauri ya ce"Mami lafiya?"
Ta sake fashewa da wani kukan ta ce"Faruq ka zo dan Allah".
Da sauri ya kashe wayar ya nufi ƙofa,sai kuma ya dawo da sauri ya shiga ɗaki.
Jallabiyarsa dake kan gado ya dauka ya zura,Bilal ya fito daga ɗaki sanye da pyjamas ya ce"kai da wa cikin daren nan?"
Bai tsaya sauraron shi ba ya nufi waje, Bilal ya riƙe shi da sauri ya ce"lafiya Falcon?"
Ya dafe kai ya ce"ban sani ba Bilal,yanzu Mami ta kira ni".
Bilal ya ce"bari in ɗauko key ɗin machine mu tafi tare".
Dole ya tsaya har Bilal ya fito bayan ya canza kayan jikin shi riƙe da key.
Lokacin da suka isa gidan ƙarfe sha ɗaya na dare,har lokacin suna tsaye a waje,harda Hajiya Mama tayi tsuru tsuru jin abinda ya girmi tunaninta.
A taƙaice Daddy ya sanar dasu abinda ke faruwa don Mami bin kowa kawai take da ido.
Nan da nan idonsa ya kaɗa yayi jazur,cike da ƙarfin hali ya ƙarasa kusa da Mami ya karɓi wayarta.
Yayi dailing numbern kusan sau uku no answer,ya ciro wayar shi ya kira wata number,bayan an ɗauka ya ce
“Captain Sadauki speaking. I’m sending a number now. I need its current location immediately.”
END OF BOOK 1
Pay 1k into *** Khadijah Sulaiman Opay.
Evidence of Payment Via
***.
Oum Rijalain