Free chapter · Read without an account
BOOK ONE CHAPTER 24
*ZAINAB*
Ƙaddaran ko wani ɗan adam a rubuce take. Duk abinda Allah ya hukunta to duk yanda ɗan adam yaso ya guje mata ba zai yiwu ba.
Zaune take bayan sallahn magrib tana tinanin inda Khalid ya tafi tun la'asar har izuwa wannan lokacin bai dawo ba.
Wayanta dake gefe tai ringing. Kamar ba zata dubi wayarba sai kuma ta ɗago kanta ta kai dubanta ga kiran daya kusa tsinkewa da sabuwar number.
Kasancewar ta ƴar kasuwa ayanzu tana yawan amsan kira daga sabbin nombobi, sedai wannan numbern guda daya ta sanya zuciyarta dokawa aƙirjinta.
Seda kiran ya katse wani ya kuma shigowa shima ya kusan katsewa ta ɗauka tana sallama agaresa.
Muryan wani namiji ya amsa da tambayar ta"ina magana ne da maman Khalid Ahmed Maitama"
Da kai da bakinta dake rawa duka ta amsa masa "eh nice lafiya."
"Ah..lafiya ƙalau ki kwantarda hankalin ki, muna dai son ganin ki ne anan office ɗin mu na N.D.L.E.A dake tudun wada zaria."
"Anya kuwa yallaɓai ba kai kuskuren kiraba. Ni ɗana baya saida miyagun kwayoyi ko ta'ammali dasu."
Ɗan ƙaramin murmushi ya saki da sautinsa ya cika kunnuwanta tukuna yace "banyi kuskure ba amma bari kiji Khalid ɗin ko shine?"
Daga haka taji shiru, sai sautin maganganu ƙasa-ƙasa daganan muryan Khalid ya sanyata miƙewa daga zaunen datake tai tsayuwan sojoji ƙyam akan ƙafafuwanta.
"Ma..!mi.....!!..." Sunanta kawai ya kira, ya fashe da kuka mai sauti da tasan iyanzu jikinsa kyarma yakeyi yana kukan bilhaƙƙi sosai da sosai.
Batasan ƙwalla sun ciko kwarmin idanunta taba seda taji damshinsu akan fuskar ta. Bata damu da ta share hawayen taba ta sauke wayan.
Ko sauraron su Ramlat dake magana bata yiba ta shige ɗakinta. Hijjab ta ɗauka. Har ta kawo bakin ƙofa sai ta juya ta bude wadrope ta ɗauko ƴar jakan kudinta ta kuma fitowa.
"Mami lafiya."
"Ba komai ku jirani ina dawowa."
Shine kawai amsar da ta basu tai ficewarta daga ɗakin harma da gidan gabadaya.
Abakin titi ta sami adai-daita ta gaya mai inda ze kaita. suna isowa ta sauko tana kallon wurin da tsawon rayuwarta bata taɓa shiga cikin saba.
Tai ƙundun balan shiga wurin tana ƙoƙarin dai-daita natsuwarta. Abakin kanta taga wasu suna tsaye. Ta soma da gaidasu suka amsa sannan ta gabatarda kanta.
"Nice mahaifiyar Khalid Ahmed da kuka kira yanzu."
"Okay sannu da zuwa madam." Faɗin wani daga cikin su. Ya kalli na gefensa yace "case din na hannun Oga Yusuf ka kaita office ɗin shi."
Nan take kuwa yayi mata jagora zuwa office ɗin mutumin da aka kira da Yusuf. a zaune suka samesa yana cike wasu files. ya bata izinin zama akujeran dake gaban table dinsa bayan wanda ya kawota yayi mai bayani.
Da alama mutumin nada fara'a da sauƙin kai. Da fara'ansa ya soma mata magana"Barka da zuwa maman Khalid."
"Barka yallaɓai, mai Khalid din yayi?."
Ta fadi zuciyarta na tsinkewa don ita burinta kawai taji gamsashshiyar bayanin daya haɗa nagartaccen ɗanta da drugs.
"Maman Khalid kiya hakuri ba wani abu bane, mun dai kamashi ne ashagon pharmacy yaje siyan magungunan da aka haramta siyansu batareda izinin likita ba. So gaskiya mai shagon mu kaje kamawa sai mukai katari dashi wannan dalilin yasa muka ɗaukosa don ku iyayensa kusan halinda yake ciki."
"Shikenan yallaɓai mai zanyi?"
"Maman Khalid inason ki kira mana wani daga cikin dangin mahaifinsa yazo tunda yace mahaifinsa ya rasu, because inaso mui magana ta natsuwa dashi domin musan yanda abubuwa zasu kasance hardama batu akan lafiyar yaron."
Yayi magananne saboda yasan akwai iyaye mata da yawa da suke binne lalluran yaransu dama sirrinsu don kada mutane suji aimusu gori nan gaba, kuma dayawan lokaci hakan shike jawo bunƙasan masu shaye-shaye aduniya.
Zainab ta ɗanyi shiru idan ta fahimta kenan Khalid ne yace dasu mahaifinsa ya rasu! Ita bazata ƙaryata shi ba. Ta ɗauki waya ta kira Yaya Yusha'u ta gaya masa abinda ke faruwa, yace gayinan zuwa.
Bayan ta sauke wayan ta nimi izinin ganin Khalid. Yusuf ya sanya aje ataho dashi.
Tunda aka shigo dashi idanunta ke kansa. ya durƙusa agabanta yana sunkuyar da kansa. Taja iska mai kauri, bata kauda ganinta akansa ba tace
"Kayimin adalci kenan?!...."
Yayi shiru bai amsa ba. hawayen da take ta tattalawa suka zubo mata tacigaba"duk wahalar da na keyi arayuwa saboda kune... Don kawai rayuwar ku ta inganta!..shine zaka biyani da wannan!!!..innalillahi wa'inna ilaihirra jiun." Ta ƙarke tana rushewa da kuka mai sauti.
Khalid ya rarrafo da gudu shima yana gursheƙin kuka ya ƙanƙame ƙafafuwanta da duk hannuwansa biyu, ya ɗora kansa asaman ƙafarnata, ruwan hawayensa na jiƙe ƙafafunta da zafinsu ke sauka atsakiyar zuciyarta dake ciwon gaske. so yake yi yayi magana ya kasa sai kukan kawai.
Ana haka sai ga Yaya Yusha'u yazo. Zainab ta soma ƙoƙarin tsaida hawayenta ta kasa. Ya zauna akujeran dake fuskantar tata. Magana su keyi da Yusuf amma bata fahimtar komai har seda Yaya Yusha'u ya kira sunanta yana cewa
"Zainab tashi muje ki samu abin hawa."
"Amma ya...."karki damu idan an kammala komai zanzo dashi da kaina."
Tana matukar ganin girman mutumin nan, bazata iya musu dashi ba sai kawai ta miƙe tana shure hannun Khalid daga ƙafafunta suka fito yaya Yusha'u nata mata nasiha akan hakuri da rayuwa da kaddara.
Ita dai jinsa kawai ta keyi tana gyaɗa kai. Yasamamata abin hawa ta hau ya biya kudin suka bar wurin.
*
Mai napep na sauketa ta fito. lokacin gari yayi duhu sosai saboda dare yayi. Tun daga nesa take jin sautin kukan da amonsa yazo ɗaya dana Ramlat.
Seda ta ɗan ƙaro gaba kaɗan sannan hasken solar ya hasko mata Ahmed atsaye hannunsa ɗaukeda trolly ɗinta daye cilli dashi atsakar filin wurin.
Ramlat da Anis na durƙushe suna kuka haiƙan. Jikinta yayi sanyi na ban mamaki. Ta ƙarisa gabansa asanda yake jepha mata tambayar daya daskaradda ita atsaye.
*JAMILA*
Misalin ƙarfe goma na safe tana zaune tana wayada amarya taji muryan Baba yana kiranta.
Ta amsa tana miƙewa asanda zuciyarta ke raya mata ba alkhairi bane. baicin wani ɗan anace daya maƙale mata ajiya cikin abokan angon taƙi zuwa gidan amaryan ga yanzu Baba bai gantaba har yake mata kiran mafarauta da farar safiya.
Agabansa ta risina tana gaidasa"ina kwana Baba."
"Me kike yi har yanzu baki koma gidan mijinki ba?."
"Haba babansu wani irin abune kakema yarinyar nan? Sam baka ƙaunarta yanda ka..."
"Kinga Safiya ki kiyaye Ni. wallahi acike nake dake, ki guji ranar da zan fyace ki."
"Wani fyacewa zakai min bayan wannan? In banda tijara ba abinda kake min kullum ka..."
"Mommy don Allah ya isa haka."
Jamila ta katseta hawaye na sauko mata. Batareda ta kalli Baba ba tace"shikenan Baba zan tafi yau kaje abinka."
"Ai ba zaki tafi yau nakeson ji ba. Zuwa zakiyi ki fitar min daga gida."
Baki Mommy ta buɗe zatai magana Jamila ta girgiza mata kai, hakan yasanyata yin shiru ba don taso ba. sai jijjiga kai takeyi tana magana ƙasa-ƙasa yanda Baba bazai jitaba, sedai da alama rashin kunya take masa.
Sunanan atsaye Jamila ta fito. Baba yabi bayanta har ta shige mota, seda suka ƙulema ganinsa sannan ya juya gida ya ɗauko babur dinsa ya fita.
*
Tsanan Baba ba sabon abu bane agareta, tun batasan ciwon kanta ba yake nuna mata ƙiyayya, ƙiri-ƙiri yake nunama ƴan uwanta kauna banda ita.
Baicin Mommy iyanzu da dolenta ta rabu da gidan Baba. To ita fama duk ta ƙare baicin gidan ubanka ubankane ayau data barma Baba wannan gidannasa kamar zuciyar talaka ta huta.
Duk damuwar kaɗaici dake damunta agidanta aiyafi ta zauna acikinsa da rayuwa agidan Baba yana wulaƙanta ta.
Haka suka share tsawon awanni suna tafiya zuciyarta duk ajagule sai faman karanta wasiƙan jaki takeyi.
Yana packing ta fito. Duk ilahirin jikinta ciwo yake mata. Ta shiga ciki kai tsaye tasan driver zai biyota da kayanta.
Turuss! Ta tsaya afalon idanuwanta na buɗewa da mamakin ganin mutumin dake zaune afalo yana danna system da alama aiki ma yakeyi. Ga mug na koma menene yake sha agefensa kan hannun kujera. Hankalinsa akwance yake da alama don har wani fresh taga ye mata, zallan kyawunsa yaƙara fitowa ƙarara.
Ta rufe idanunta tana sauke numfashi da ƙasdin kuma buɗesu taga babu kuwwa amma ƙamshin tirarensa da yake sanyawa akodayaushe ya shiga cikin ƙofofin hancinta da wani yanayi mara daɗi da yasan yata jadabaya dasauri tana kallon Samir dake ƙoƙarin kamota.
Amai ne yataso mata, ta kwasa aguje tai hanyar bedroom din ta.
Amai sosai tayi kamar zata fitar da ƴan hanjinta ta bakinta.
Samir yazo daniyyan tai maka mata, wani sabon aman da babu komai yaƙara taso mata ta dingi yunƙuri babu abinda ke fitowa.
Hankali atashe ya ɗauraye mata bakinta da fuskanta. Ganin yanda ta ga labaita yasan yashi ɗaukanta suka nufi asibiti da ita kai tsaye.
Yana tsaye acikin ɗakin da aka shigar da ita, duk wani abu da likitan keyi da abokan aikinsa idanunsa na kansu.
Seda suka gama Doctor Emanuel ya miƙa mai hannu yana dariya da fadin"congratulations Sir."
#JAMA'A BOOK ONE PHA YAZO GANGARA DON HAKA KU SOMA KIMTSA KUDADEN KU DON SAMUN BOOK TWO#